Showing 327001 words to 330000 words out of 403653 words

Chapter 110 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

95

sannan ya rage tsawonsa a in da ya ɗaura kansa a saman shoulder ɗinta, can ƙasa ƙasa a cikin kunnenta ya ce. "I think ba zan rasa baby a nan ba, because I play my game yadda yakamata, kuma irin wannan dogon jinya da kika sha nasan ma dole na ci kwallo". Yana magana yana shafa cikinta.... (Kam bala'i, wato ma kenan Ramish da gangan ya yi wannan aika aikan? Leesharh ta yi gaskiya kenan? Bala'in can, lallai ya kai ɗan duniya na karshe wlh, iye wai ya ci kwallo?.🤔 Yau ga ɗan iska da tsakiyar rana!🤔)

Ai bata san lokacin da a miliyan ta ce. "Wlh babu, kuma ba zai taɓa yiwuwa ba ko a mafarki, ba zan taɓa haifar ɗan shege ba, wlh babu, babu wani cikinka a jikina, ni babu komai". A tsananin rikice take maganar, tana yi tana zaro idanu, ya ɗaga mata hankali ainun, ina zata sanya ranta idan aka ce ciki ya shiga tsakaninsu? Ai kawai tana ga kashe kanta zata yi....... Ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin yadda ta rikice haka, koba komai ta sakar mashi jikinta a jikinsa yadda yakamata, da ta wani takure gabaɗaya baya jin daɗi yadda yakamata. "Kina ganin kamar wasa nike yi ko? To gara ma ki yarda mu yi aure sai mu haifi babynmu a gidanmu na aure na sunnah, idan ba haka ba zaki haifi babyn da zaki ƙasa bashi amsar wanene ubansa kuma ya aka yi kika same shi idan ya titsiyeki". Ya kai karshen maganar yana ɗage mata hijabinta cikin dabara.

"Na shiga uku na, Yah Ramish da gaske kake yi? Dan Allah ina da ciki? Shikenan na shiga uku na, na karya maganar da babana yake faɗa mun kullum, na karya alkawarin da na yi mashi cewa zan kare mutumcina, shikenan yanzu kowa zai san abin da ya faru? Shikenan kowa zai ganni da cikin da bani da amsar ina na same shi idan an tambayeni? Sharifat zata ganni da cikinka? Na shiga uku rayuwata ta kare a banza a wahale tare da rashin madogara!" Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa tab da kwallah, zuciyarta ya karaya matiƙa, ta shiga tashin hankali da fargaba.

Shi kuwa tura hannunsa ya yi cikin rigarta bayan ya ɗage mata hijabin, cigaba ya yi da shafa cikin nata, kamar mai raɗa ya ce. "Ina fatan babyna ya yi kama da ni, dan ma kowa ya san nine ubansa!!". Kam bala'i yau ga tabbatar rashin kunya da bushewar ido wajen Ramish........ Haba ai kara birkice mashi ta yi, jin hannunsa a saman fatar cikinta ya sa ta yi gagawar kwace kanta ta raba jikinta da nasa, tini hawaye sun gama wanke mata fuska, idanunta sun yi jajir, yanzu ta fara tinanin sauyawar da jikinta ya yi a ƴan kwanakin nan, gaskiya da alama gaskiya a zancensa, ciki ne da ita, tana da tabbacin cikin ne ma yasa take damuwa a kansa, shiyasa kenan take kasa iya barci in bata kallesa ba, babynsa kenan yake sanyata dik wannan abin?. Wani irin ihu mai sauti ta zunduma tare da zube gwiwowinta a ƙasa a wajen, sannan ta dafe kanta dake barazanar tarwatse mata, kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ta saki mai sautin gaske.

Har cikin ransa ya ji kukan nata ya ratsa shi, sai ya ji wani irin tausayinta ya ninku a ransa, tamkar zai faɗa mata gaskiyar cewa zolayarta yake yi, amma kuma ya ji dole ya barta a kan hakan dan ta aminta da shi su yi aure su rufawa juna asiri. Tsugunnawa ya yi a kusa da ita, ajiye cup ɗin hannunsa a gefensu ya yi sannan ya janyota jikinsa, ya rungumeta sosai tare da fara rarrashinta. Ai ina, taki sauraronsa, sai ma kara tsananta kukan nata da take yi tana faɗin ta shiga ukunta. Shiru ya ɗan yi yana tinanin me ya dace ya yi mata wanda zai iya shawo kanta cikin gaggawa ta yi shiru su samu su yi magana.
Ya yi iya tinanin da zai yi amma dik ya kasa iya tinano hanyar da zai shawo kanta, saboda shi soyayya ba layinsa bane, bai kware a kanta ba. Zuba mata idanu kawai ya yi yana kallan yadda take kukan, har cikin ransa hakan yake sosa zuciyarsa, ganin fa ba zai iya jurar kukan bane yasa ya yanke shawarar yin abin da yake ganin ita ce mafita a garesa. Wato ya matsa dab da ita, cikin zafa ya haɗe bakinsu waje guda domin ya bata hot kiss da zai sanyata haɗiye kukan dan dolenta.

Aikuwa ya yi nasara, dan kuwa suman zaune ta yi mashi, ta yi tsit tamkar ruwa ya cinyeta, yau ne ranarta na farko da wani ya fara kissing ɗinta, shi kuwa daga neman hanyar da zai samu ta yi shiru, sai ya zarce da bata zazzafa mai kwance notikan ƙwaƙwalwa. Bai ma san time ɗin da ya miƙe da ita a jikinsa ba, gabaɗaya ya wuce balconynsa da ita bakinsu manne cikin na juna, ita dai ta ƙasa koda motsawa, saman rest chiar ya zauna da ita tare da kara manneta da jikinsa. Sai da ya bata masu zafi san ransa, sannan ya saketa tare da rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.

Almost 10 mins suna a haka kafin ya ɗan saussauta rikon da ya yi mata, word in out of control ya shiga yi. "Please Aesh believe that zan dawo maki da dikkan farincikinki da ya gushe, ki yarda mu yi aure, i promised you that ba zan taɓa bari ki yi kunci ba, you will never regret kasancewarmu a ma'aurata, please Aesh trust me"...... Cikin wata iriyar murya tamkar wadda take a buge, kamar bata cikin hayyacinta ta ce. "Yah Ramish zaka aureni ne kawai ba dan kana sona ba, sai dai kana tausayina kuma kana san rufe ɓarnar da ka aikata a gareni, baka san familynka su san cewa ga abin da ya faru, na san halin larabawa sosai, na zauna da su tin ina karama, wlh dan ka rufe ɓarnarka yasa ka aminta zaka aureni, na tabbata baka sona, saboda ko a ƴar aikin gidanku ban kai na zo ba, tsautsayi da rufe maku gaskiya yasa na shigo cikin familynku, masu aikin gidanku dik mutane ne da suka kammala diploma, baku ɗaukar jahilai a masu aiki, amma ni jahila ce da ko secondary ban kammala ba, babu wani ilimi a kai na, amma an rufe maku hakan ta hanyar kirkirar mun takardu na karya wanda ke nuna na yi karatu, bayan ko kusa ko alama ban yi ba, kaga kai ba saa'ata bane, ba zaka taɓa san jahila wadda bata da gata ba, wacce kuma aka ɗauki hayarta domin ta kasheka, ko ka manta ni ɗin na shigo gidanku dan in kasheka ne? Ka mance da cewa na taɓa poisoning ɗinka? Ka manta da cewa na taɓa zama silar da aka harbeka da gun? Ka manta da cewa na yi maka abubuwa dayawa dan ganin ka mutu?". Ta kai karshen maganar tana ruwan hawaye.

Nisawa ya yi kafin ya ce. "Dik nasan da hakan, amma ina san ki san cewa in har zan ki ki saboda wannan dalilin, to tabbas zan ki Bilal, saboda dik abin da yake faruwa da sa hannunsa a ciki dik da bani da cikakkiyar hujja mai karfi sosai a kan hakan, dik hujjojin da nike da su a kansa basu da karfi sosai, amma suna tabbatar mun da yana da sa hannu a ciki, ki sani ni ba dan na rufe abin da na aikata a gareki yasa zan aureki ba, sonki nike yi Aesh". Babbar magana, kenan Ramish yasan da sa hannun Bilal a yunƙurin kashe shi da ake yi? Shiyasa ya juya masu baya kenan? To mu je zuwa. Wlh Ramish karya yake yi mata, bawani yana sonta ne, batu na gaskiya yana tinanin tana da ciki shiyasa yake san ta yarda su yi aure dan kada su haifi cikin a waje, ta yadda Allah ya tashi kama shi kuma sai ya sanya mashi kaunar yara ta yadda baya jin zai iya zubar da ciki, yana san ta haifa mashi, kamar yadda Leesharh ta yi hasashe hakan ce, ba wai dan hana sonta zai aureta ba ɗan rainin wayo. Amma kuma dani da ku dik mun san akwai son nata a zuciyarsa, sai dai shi ɗin ne bai yarda da hakan ba, baku jin baya wani magana sai su yi sauri su yi aure ne? Idan da ya yardanwa kansa sonta yake yi, to da tabbas zai rinƙa yi mata abubuwa na masoya, amma a'a, shi damuwarsa kawai su yi aure.

"No Yah Ramish, na tabbata baka sona, nafa san halin larabawa, tin ina karama na tashi a cikinku, nasan dik wani hali naku, kuna da kishin zubewar mutumcinku, bare ma kai da ka fito daga cikin babban family masu karfin faɗa aji a kasar, dole ka yi komai dan mutumcin gidanku". Ta kai karshen maganar tana tari mara sauti sosai. "Aesh yanzu baki yarda da maganata ba kenan?". Shiru bata iya amsa mashi ba. Kara matsawa jikinta sosai ya yi, cikin sigar rarrashi ya fara yi mata dabara dan ta yarda. Ko da sunan wasa ba ya san abin da ya aikata ta fita, ko dan kakansu King Badeen, and ace ɗa ga King Zuhair yana da ɗan shege? Kai ai abin babba ne.

Uhm aka ce maka namiji a fagen kalaman yaudara to fa an rufe kofa, dan kuwa Ramish sai da yasa ta yarda da cewa da gaske yake sonta, amma taki yarda ta amsa zata auresa, sai ta ce ta yarda da yana sonta, amma dan Allah ya kyaleta haka nan, idan ma saboda ciki ne ya mayar da ita Nigeria in da babu wanda ya sansa bare har mutumcinsa ya zube, zata reni cikinta a can ta haifesa ta kuma rike kayanta, ba zata taɓa kama sunansa a bakinta ba.
Kai kawai ya girgiza, lallai yau ya yarda Leesharh yarinya ce sosai mai ƙaramin tinani, wai ba zata taɓa ambatar sunansa ba, tab bata san me haihuwar bane, ai wlh time da yaron zai titsiyeta a kan ina ubanta san da zata ji takura ta faɗa mashi ma babu wanda ya sani, kuma dik bama wannan ba, a Nigeria tasan ƴan uwanta ne? Sannan shi dik bama wannan ba, yana bala'in san yara, bare kuma ace jininsa, a gaskiya yana son kayansa, dole idan akwai cikin nan ta haifa mashi kayansa ta bashi ko me zai faru sai dai ya faru, babu wani Nigeria da zai maida ta da ɗansa!!. Babbar magana, ya kuke ganin wanna cakwakiya zata kaya?. Bala'in can, ya mama uwar jiji da kai zata ji a lokacin da Ramish zai kawo mata bastard matsayin jika? Tab ya King zai yi?.

Shiru ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi a hankali hankali. Tamkar a mafarki suka ga wutar gidan ta ɗauke gabaɗaya, a ɗan razane ta yunkura zata bar jikinsa, ta ɗago kai tana kallan saman ɗakin. Tin da ya ga hakan yasan akwai matsala, dan wuta bata taɓa ɗaukewa haka nan. Tana ƙoƙarin barin jikinsa ya yi saurin rikota, kamar mai raɗa ya ce mata. "Yi shiru kada ki motsa". Muryarta a dashe ta ce. "Yah Ramish meyasa wutar ta ɗauke? Ni dai nasan tsawon shekaru ba'a ɗauke wuta a kasar nan! Ko dai kai ka kashe ne?............"

Yatsa ya ɗaura mata a saman lips ɗinta. "Kada ki sake yin magana, yi shiru, and ki zauna a nan ina zuwa, kome zai faru kada ki motsa daga nan". Ya kai karshen maganar tare da saketa. Tana san tambayarsa ina zai je, tana tsoron ya ce ta yi shiru kada ta yi magana, wayarsa na aljihinsa, amma bai kunna ligh ɗinta ba, cikin sanɗa ya nufi waje. Yana fitowa ya ji takun tafiyar kartin mutane suna haurowa saman stair case ɗin, shiru ya ɗan yi yana mamakin yadda suke da karfin hali da dabarar iya kashe wutar gidan dan kada camera ta ɗaukesu, dama shi yasan zasu biyosu, saboda dama bai yarda mota ɗaya ce ta bi bayan Leesharh ba, dole sun saka masu ido, sai dai bai sa a ransa zasu yi saurin biyosu ba, ya yi zatan zasu ɗan kwana biyu su yi shiri, fatansa a nan yanzu shi ne Allah ya bashi sa'ar kama ko mutum ɗaya ne da ransa, dan samu amsoshin wasu tambayoyi nasa.

Yana tsaye yana tinani sai ji ya yi an bangajesa za'a wuce, har sun iso in da yake ba tare da ya farga ba. Wanda ya bangajesa ɗin ya yi gaggawar fitar da light mai bala'in haske ya dalle mashi fuska da shi, hakan yasa ya kashe mashi kwayar idanunsa baya iya ganin su waye ne. Ya yi ƙoƙarin kwace hasken, amma ina ba zai yiwu ba, dan baya iya ganinsu ma bare har yasan waye ya rike hasken ya kwace.

Tamkar saukar aradu haka ya ji saukar wani irin karfe a kansa, sun kashe mashi ido da haske baya ganinsu sun dakesa da wani katan karfe a kai, take wani irin jiri mai karfin gaske ta ɗebesa, dik hasken dake haska shi duhu yake gani a wannan lokaci, kan ka ce me ya zube ƙasa baya numfashi. Kawar da light ɗin daga kansa suka yi zuwa kan wasu dake bayan mai rike da light ɗin, wasu irin shirga shirgan mutane ne masu sanye da bakaken kaya haɗi da manya manyan boots a kafafunsu, ga hands gloves, mask, baka iya ganin komai a jikinsu sai jajayen idanun da suka yi ja saboda kayan maye!!.

"Ku shiga ku ɗauko mun ita, shi wanna angama da shi!". Wanda ya rike light. Wucewa karti uku suka yi izuwa cikin ɗakin, saura suka tsaya a tare da ogan nasu mai rike da light ɗin.

My people's me kuke tinanin zai faru ne? Ni kaina page ɗin yau sai dai in kora Maltina and exotic kawai in yi shiru, mu leƙa Paris mu dawo!!.


🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥


Smart ya ɗauki a kallah 10 mins suna tattaunawa da King, da alamar rashin jituwa kuma a maganganun nasu, dan yadda Smart yake maganar zaka fahimci dikkansu ransu a ɓace yake. Daga karshe cikin fushi ya katse kiran, sannan ya yi off na wayar gabaɗaya tare da miƙewa ya nufi cikin ɗakin, haka ya rinƙa rarrashin Auta har tsawon kwanaki.

Yau takama weekend, Saturday, Smart yana tare da su a gida, bai je ko'ina ba, a ƴan kwanakin nan ya yi matuƙar sabo da su Pretty, tin tana bakanta mashi rai har ta dawo tana burgesa a dik abin da take yi, ba abin da ya fi ɗaukar hankalinsa a tattare da ita sai olive eyes ɗinta da kuma shegen shariyarta na jinin sarauta, tana bala'in burgesa yadda bata daga idanu ta kalli mutum, sannan tana matuƙar burgesa yadda take da tsoro, idan ta tsorata ba ƙaramin kyau take mashi tana tafiya da imaninsa ba, wani lokaci da gangan yake tafiya waje filin dolphins na Auta ya barsu a ciki, idan ta farga da baya kusa da su ta tsorata ta fara kuka kyau matuƙa take yi mashi.

Sanye yake da pj a jikinsa, suna sama gabaɗayansu, Auta tana gyarawa Pretty gashin kanta suna ta hira, shi kuma ya tasa laptop a gabansa yana ta aiki dangane da bincikensa. Auta da Pretty suna sanye da hoodies na mata a jikunansu, Auta ta sanya hular kayan a kanta, ita kuwa Pretty daman kun san ba sanya ɗankwaki take ba koda ba gyaran gashi ake yi mata ba!.

"Yah Omerish me kake yi ne haka? Naga kamar zanen kunnan mutum da ido?". Cewar Auta, ta yi maganar idanunta a kan laptop dake gabansa, da yake suna kusa da shi sosai, a saman duguwar sofa set guda suke.

Hankalinsa a kan aikinsa ya amsa mata da. "Ina san kirkirar karfin ji ne fiye da komai, abin da zai iya dauko sauti tin daga nisan kilomita 10 a tafiya da ƙafa". Cike da mamaki ta sake cewa. "Yah Omerish to naga hoton kunne, me kake yi da shi?"........ "Kwaikwayon halittar Allah zan yi! Kamar yadda muka kwaikwayi halittar idanun mutum muka fidda camera haka nike san kwaikwayar halittar kunne dan in samu majiya mai karfi".

Ai Auta bata san time ɗin da ta saki Pretty ta miƙe ta dawo kusa da shi sosai ba, cike da mamaki ta ce. "Yah Omerish dama Camera idanun mutum aka kwaikwaya ne?".... Kai ya jinjina mata kafin ya amsa da. "Komai da kimiya take kirkira ai kwaikwayo muke daga halittar Allah, babu wanda ya isa ya kirkiro wani sabon abu a duniya, sai dai ya kwaikwayi wanda Allah ya yi, Ubangiji ya rigada ya halicci komai, kawai dai mu muna zamanantar da shi ne"..... Kara shiga mamaki sosai Auta ta yi, ita kuwa Pretty bama su isheta kallo ba, mashirmaciya, kwanciya ta yi tana kallan sama kamar wata dake da motsi a kai, babu ruwanta da tattaunawarsu.

"Yah Omerish to tayaya kuka kwaikwayi ido? Tayaya Camera yake kama da shi?". Cike da zaƙuwa da san jin amsa ta tambayesa. Dakatawa da aikin da yake yi ya yi, sannan ya juyo da kallonsa game da hankalinsa a kanta, cikin sanyin murya ya fara bata ilimi kamar haka!.

"Abubuwa da dama muka kwaikwaya daga idon mutum muka kirkiro Camera, cikin abubuwan da muka kwaikwaya sun haɗa da. Lens da Focusing wato mayar da hankali. Kamar yadda ruwan ido wato lens yake daidaita haske domin samar da kallo mai kyau, ya iya fahimtar menene a gabansa, haka ma camera ke amfani da lens dan mayar da hankali wato focus ga abubuwan da take ɗauka, kin ga a nan mun kwaikwayi ido".

"Abu na gaba shi ne. Aperture wato kofar shigar hasken shiga. Ido yana da wani ɓangare da ake kira da pupil, wanda ke buɗewa ko rufewa don daidaita adadin hasken da ke shiga. To haka camera ma, tana amfani da aperture wanda ke sarrafa yawan hasken da ke shiga camerar, nan ma kinga idanu muka kwaikwaya".

"Na uku shi ne. Retina da image sensor, wato fuskar karɓar hoto. A cikin idon mutum, retina ce

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login