Showing 126001 words to 129000 words out of 403653 words

Chapter 43 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

59

yi tare da ƙara mata kwarin gwiwa a kan ta koyi jajircewa.

Aunty MieMie ma data ga hakan sai ta tsoma baki suka fara rarrashinta a tare. Uncle Jahiz ne ya fayyace masu cewa Zee fa ba ita ce uwar yaron ba, sisterta ce uwar yaron. Dik da suka ji hakan sun tausayawa Zee sosai, dan daga yadda ta nuna reaction ɗinta a kan yaron nan alamu sun nuna akwai damuwa.......... Wai dan ma basu san tarihinsu ba kenan, da sun sani sai yaya kenan?. Ai su Zee su suga rayuwa, sun sha gwagwarmaya kam ba kaɗan ba.

Shiru parlourn ya ɗauka na ɗan lokaci, sai shessheƙar kukan Zee ne yake tashi a hankali hankali gwanin ban tausayi.

Aunty MieMie da ta lura kamar akwai yunwa sosai a tattare da Zee sai ta ce yakamata a kawo mata abinci ta ci. Momma ma ta lura da hakan, sai ta amsa da yakamata kam.

Aunty MieMie ce ta mika hannu ta karɓi babyn daga hannunta, sannan ta ce uncle Jahiz ya sanya a kawo mata abinci ta ci. Sam bata tambayi wacece Zee ba, dan su suna da ɗabi'ar dik wanda suka gani a tare da ɗan uwansu to fa zasu bashi mahimmanci. Tun da suka ganta tare da uncle Jahiz sun san ba banza take ba, saboda su basa kula abu idan ba ya kasance ya shafesu ba.

Miƙewa uncle Jahiz ya yi ya nufi waje. Jim kaɗan ya dawo tare da wasu kuyangu guda biyu da suke ɗauke da tampatsetsan tray mai girma, shake take tap da abinci launika daban daban da a kallah zasu kai kala goma. Kun san larabawa da yawan girke girke kala kala.

Kai tsaye saman dining table na momma suka nufa suka shirge abincin, ga kayan drinks kala kala, ferfesu kaji dana ɗawisu, kun san gidan sarauta suna da ɗawisu sosai, ga dahuwar Chinese rice kala daban daban, kai waɗan nan tray sun haɗe komai, har da kayan marmari.

Umartar Zee ya yi da ta tashi ta je ta ci abinci, da yake parlourn yana da girma, daga wajen da table ɗin yake zuwa in da suke akwai tazara mai tsayi.

Da yake yunwa baiwar Allah take ji sai bata musa ba ta tashi, jikinta har ɓari yake yi ta nufi wajen table ɗin. Da kallo suka bita har ta kai wajen, sannan suka dawo da kallonsu a kan uncle Jahiz dan jin wacece ita daga ina kuma ya samosu.

Yasan abin da suke wa binsa da kallo, karin bayani suke jira ya kora masu. Dan haka cikin nitsuwa ya yi gyara murya kafin ya fara kora masu dik abin da suke tsumayan jira daga garesa. Ya yi masu bayanin ne kuma ba tare da ya bawa kowa damar jin abin da ya faɗa ba, zance ake ta sirri!!.

Ko ita Zee dake zaune saman table bata ji abin da suke tattaunawa ba, ita dai ta zauna shiru tana bin kayan abincin da kallo, Allah sarki taga duniya, ta rasa da wanne zata fara, yunwa take ji over, dan ma Allah yasa ita ba wawiya bace, da ɗan wayewarta, amma dik da haka sai da ta yi kauyanci a ɓoye, dan kuma kun san zaren ba kalar yadin bane.

Dikkansu babu wanda fuskarsa bai nuna alamar mamaki ba a lokacin da uncle Jahiz ya gama basu wannan labari da ya ɗauko ɗan sanar da su su wacece Zee, a fili momma ta furta.
"Dikka wannan zalincin su kaɗai?".

Jinjina masu kai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Aunty MieMie da ranta ya gama ɓaci har idanunta sun kaɗa sun yi jajir ne ta ce. "Gaskiya ba zata saƙu ba, dole mu kwatar masu ƴancinsu".

Jinjina kai momma ta yi alamar tabbas kuwa. Shi ma jinjina kai ya yi alamar haka ne. Da alama labarin tarihin su Zee ɗin ya basu, dan tabbas ya lallaɓa Zee a asibiti, ya gwada mata fifikon shekaru a in da ya yi mata dabara har ta yarda ta bashi tarihin rayuwarsu.

Amm kuma sai dai akwai wani abin da ya sanar da su momma bayan tarihin su Khadija ɗin, dan yanayin mamakin da ya bayyana a kan fuskokinsu abu ne mai girma da ya fi tarihin su Zee suka ji, dole akwai wani sirri da ya sanar da su wanda baya buƙatar a ji........... Ni kam nace koma dai me ka sanar da su idan lokaci ya yi ruwan ta yi tsami ni da my people's ai zamu ji ko? Sai kwan ta fashe In Sha Allah mun ji komai ato, mu je dai zuwa.

"Gaskiya akwai azzalumai a duniya, yanzu ko ta ina zalinci kawai ake yi, ya ilahi ya lillahi, wannan musifa dame ta yi kama". Cewar Momma da alamar jikinta a sanyayye.

Ita ma Aunty MieMie ta yi laushi, kamar wanda ya sheka masu ruwan sanyi, dik da alamar karyewar zuciya da tausayi a tattare da su.

"Uncle Jahiz taki cin abincin fa, ko zaka je ka yi mata dabara ta ci tun da kun saba da ita". Cewar Aunty MieMie da ta farga da Zee bata cin abinci.

Miƙewa tsaye ya yi, ya nufi table ɗin yana faɗin. "Dama kullum sai mun kai ruwa rana da ita take yarda ta ɗan tsakuri abincin ai, bari na gwada yanzu ma".

Momma ce ta karɓi zance da cewa. "Ai dole ne ta shiga damuwa Jahiz, amma In Sha Allah damuwarta ya zo karshe, bari daddunsu ya sarara da musifar da muke ciki na ɓatar Zunaira, tabbas za'a biwa yaran nan hakkinsu, sai mun tsaya masu In Sha Allah".

Jinjina kai Aunty MieMie ta yi, kun san tana san jinin ƴan Nigeria ita, saboda jinin mummynsu ne, dan haka ta kudurta a ranta wlh ba zata sarara ba a kan wannan case na su Zee, sai ta ɗaukar masu fansa, kai jama'a jinin modarawa ake magana, su da basa yafe ko harararsu ka yi........😅

Saman table chair dake kusa da ita ya zauna, su momma kuma suka miƙe izuwa cikin bedroom ɗin momma dan su tattauna wani sirri nasu, momma tana mugun shiri da Aunty MieMie sosai, ta su ta zo ɗaya, kun san sai hali ya zo ɗaya ake abota, batu na Allah aunty MieMie mutuniyar kirkice number ɗaya.

Chinese fried rice ya zubawa Zee, sai kallan face ɗinta yake yi, ta yi ƙasa da kai tana ɗan murza ƴan ƴatsun hannunta. Cikin harshen turanci ya ce da ita. "Bari in baki abincin a baki to tin da ba zaki iya ci ba".

Da sauri ta girgiza mashi kai alamar bata buƙata.

"Baki san zuwa ki kalli Khadija ne?". Da sauri ta buɗi baki ta amsa da tana so. "To in dai kina san zuwa wajen Khadija lallai ki ci abincin nan, idan kika ƙoshi sai in kira Fanan ta kaiki ɗaki ki yi wanka sai in kai ki wajen Khadija".

Kamar zata yi kuka ta ce. "Zan ci ko dan in ga ƴar uwata, amma dan Allah ka faɗa mun kasan Khadija ne? Ya kai sati kenan ina yi maka wannan tambayar sai ka ce mun ni kaɗai ka sani baka san ta ba, nace maka a ina kasanni ni ɗin ka ce mun a Nigeria, ka fayyace mun komai yadda zan fahimta kuma kaki". Da kyar ta iya karisa maganar, saboda wani irin kwarjini da yake yi mata, kuma ita gaskiya abin yana cinta a rai tana san samun amsa, tabbas ita hotonsa ta gani a hannun Khadija, wlh ko ratsuwa ta yi ba zaga yi kaffara ba shi ne, sannan shi ma da ya ganta ya ce ta yi mashi kama da wata da ya taɓa gani sai dai ya manta a ina, to da waye zata yi kama idan ba Khadija ba?.

Bugu da kari shi da bakinsa ya ce babyn Khadija yana kama da shi, ga shi likitoci sun hanasu ganin Khadija saboda condition da take ciki, an yi mata aiki a ciki baiwar Allah, ashe matar nan da ta basu wajen zama a gidata a Abuja ita ta cucesu lokacin haihuwar Khadija bai yi ba ta bata maganin tasar da naƙuda, dalilin haka mahaifar Khadija ya tsage, sai da aka yi mata aiki yanzu, Allah ma yasa tana da rabon shan ruwa a gaba, ai da ta jima da mutuwa saboda irin jinin da ta rasa, amma Allah ya ƙaddara zata rayu.

"Zee ni har yau ban ga face ɗin Khadija ba bare in san nasanta ko ban santa ba, sannan kuma na faɗa maki ke na sani kawai, ki ci abinci, likitoci sun ce mun zuwa yamma zan samu damar ganin Khadija, idan muka je sai in ga ko na santa".

Shiru Zee ta ɗan yi, ita dai wlh tasan shi ne na jikin hoton nan, sai ma da ta gansa a zahiri yanzu ta kara yarda, amma bari Khadija ta farfaɗo komai zai bayyana ai.

Tana can tana duniyar tinani sai gani ta yi ya kawo mata abinci saitin ɗan bakinta. Kai ta girgiza mashi alamar bata so, ta kai hannu ta karɓi spoon ɗin tana sunkuyar da kai. Ta ƙasan ido take satar kallansa, Arabs jallabiya tana yi mashi mugun kyau.

A hankali ta fara cin abincin kamar tana tsoron taunawa kada hakwaranta su karye, shi kuma ya zuba mata idanu yana kallanta, ji yake yi tamkar ya santa.

My people's me kuke tinani a wannan al'amari, wacece mai kama da Zee da ya sani? Meyasa ya yi kama da babyn Khadija? Kada ku manta babyn Khadija korean ne, ko da yake fa idan akwai jini wlh ba ta yadda ba zaka ga mutum ba, fata na dai Allah ya tashi kafaɗun Akka, dan idan zarginmu ya tabbata babu wadda ta dace da yi mashi hukunci sai Akka. (Ni ina da tantanama, anya uncle Jahiz ko ya gane Khadija zai yarda ya nuna ya ganeta kuwa?🤔 Ya kuke tinanin wannan al'amari?)

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Luv Bird 🕊️🔥

Shi da ya sami abin da yake so, ai bai saki Chuchu ba sai da ita da kanta ta kwace bakinta, a lokacin kuma ta gama kai shi ƙololuwa, dik ya rasa nitsuwarsa, idanunsa a lumshe, jinsa a sama kawai yake yi, yana ƙoƙarin dakewa ya capki tula tulanta ta yi saurin kwatar bakinta ta yunkura zata bar jikinsa.

Cikin magaggin soyayya da sha'awarta ya riƙota, kamar wani ɗan shaye shaye da kyar ya furta. "My Jannawad ina zaki je?".

"Knocking na door fa na ji ana yi". Ta faɗa tana kallan zakarar wuyarsa, wato wannan kashi nasu na maza, kashin ta miƙe sosai tana ɗan harbawa.

Sai da ta yi magana kunnuwansa suka tsinkayo mashi knocking da ake yi. Sake ta ya yi ba dan ya so ba, da alama da mai buga wannan kofar ya ɗan kara masu ƴan mintuna da Jawad ya yi disvirjin ɗinta, saboda ya luluƙa duniyar chaskale dayawa.

Da kyar ya iya miƙewa. Ƙasan bed ɗin ya sauko, jikinsa dik wani iri. Door ya nufa yana ɗan layi. Ya ƙasa iya tambayar wanene saboda nauyi da tongue ɗinsa ya yi mashi.

Da kallo Jannawad ta bisa tana jin wani irin kaunarsa a ranta yana kara ratsata.

Yana zuwa ya buɗe kofar babu tambaya. Duka Jaish ya kai mashi a kirji daga buɗewarsa. Har sai da ya yi layi kamar zai faɗi, da kyar ya kama kansa tare da waro idanunsa da kyau.

"Wani irin iskanci ne wannan? Na kai 5 mins tsaye ina dukan kofar nan, mema na rufe kofar..........?". Bai kai karshen faɗar tasa ba idanunsa suka hango mashi cikin ɗakin, Chuchu dake zaune a saman bed tana binsu da kallo.

Idan baku manta ba shi Jaish bai san Jawad ya yi aure ba, ya ɗebo zafin kansa kawai zai zo ya sauke a kansu, ransa ne a matuƙar ɓace saboda momma ta same shi da safen nan a kan batun Mahnoor matarsa ce, shi ne fa ransa yake ɓace, ya zo wajen Jawad dan su tattauna wannan bala'in in jisa, shiyasa ya rinƙa dukar kofar da karfi.

Cike da mamaki ya dawo da kallonsa a kan Jawad ɗin, zaro idanu ya yi, shi da farko ma bai lura da yanayin da ɗan uwan nasa yake a ciki ba, sai da yaga Chuchu zaune a tsakiyar bed ne ya fahimci Jawad fa a cikin mayen sha'awa yake.

Wani irin bugawa ya ji kirjinsa ta yi, da karfi ya bugi kirjin Jawad har sai da Jawad ya ji ya wastsake, cikin zafa ya danko wuyar rigarsa haɗe da daka mashi tsawa.

"Me Jannat take yi a cikin ɗakinka har saman bed ɗinka da sanyin safiyar nan? And wani irin shiga ce a jikinku?". Cikin lokaci ƙanƙani Jaish ya rikiɗe tamkar ba shi ba, har wani huci yake yi, a tinaninsa sheke aya Jawad yake yi da kanwarsa, ga shi ya gansu a wani irin yanayi.

Gyaran murya da uncle Abbas ya yi ta bayansu ne yasa suka yi saurin kai kallansu a wajen. Da sauri Jaish ya ɗauke kansa daga kan kallan uncle ɗin nasa, domin kuwa in dai abin da yake zargi Jawad yake aikatawa babu abin da zai ana shi yi mashi hukunci mai tsanani yau, dama su a dokarsu dik wanda ya yi zina dandaƙa ake yi mashi.

Chuchu da dama bala'in tsoron Jaish take yi tuni ya sha jinin jikinta, ta takure waje guda jiki na kerma.

"My son sake shi, ba abin da kake zargi bane, Jannat matarsa ce, kai ne baka sani ba". Cewar uncle Abbas da ya ji komai da Jaish ya faɗa, dan tun time da Jawad ya buɗe kofar ya shigo cikin parlourn shi ma.

A miliyan Jaish ya juyo da kallansa a kan uncle Abbas. Jinjina kai uncle Abbas ya yi alamar tabbatar da abin da ya faɗa. Kara zaro idanu Jaish ya yi. Da sauri ya juyo ga Jawad.

Shi ma kai ya jinjina mashi alamar e haka. A wani irin slow Jaish ya zame hannunsa daga wuyar rigar Jawad, like wow he was so surprised.

Uncle Abbas ne ya ce. "Jawad P.a ɗinka ne ya kirani wai yana ta kiranka baka picking time na tashin jirginku ya kusa".

Da sauri Jawad ya juyar da kallansa izuwa cikin ɗakin, kan wayarsa ya sauke kallansa, lallai kuwa soyayya ta yi daɗi, har ma anyi sallar asuba shi yana nan ya afka wata duniyar.

Ɗan dafe kansa ya yi, babu ko kunyan daddyn nasa ya ce. "Sorry daddy, Jannat tasa ban ji kiran ba, amma yanzu zamu shirya mu fito".

Jaish dai kamar ruwa ya cinyesa a wajen, faɗi yake yi a cikin ransa shikenan Jawad ya gama yi mashi fata fata da mutumci a idanun kannensu, Jawad ya gama da shi ya ja mashi kima a kan titi, yanzu shikenan Jannat tasan komai, gaskiya idan ya kyale Jawad bai yi mashi hukunci ba ya cuce shi dayawa.

Uncle Abbas kuwa cewa ya yi. "Ina zaku je ne dama?".

Ɗan sunkuyar da kai na munafinci Jawad ya yi, sannan ya ce. "Daddy wai dama Jannat ce ta ƙasa samun nitsuwa a nan, sai kuka take yi mun ta ƙasa barci, shi ne fa dama zan ɗauketa mu je honeymoon a Dubai".

Da yake uncle Abbas ma ɗan zamani ne sai ya ce. "Yanzu kai Jawad ba zaka iya kwantar mata da hankali a nan ba sai kun je Dubai?".

Shiru ya ɗan yi yana ƴan kame kame.

"Anya kai namiji ne kuwa?". Uncle Abbas ya sake jefa mashi tambaya. Nan ma dai shiru ya yi.
"To ni ban yarda ku je ko'ina ba, ku na nan, idan baka iya kwantar mata da hankali a nan na ga ɗan uwanka ya koya maka". Yana kai karshen maganar ya juya ya fice abinsa.

Jaish ya gama zuwa har wuya, ɓacin rai kan ɓacin rai, sarai Jawad ya lura da shi, shiyasa ya yi readyn guduwa, dan yasa saboda uncle Abbas yana wajen ne yasa Jaish ɗin ya daure bai aiwatar da abin da ya yi niyya ba.

Tsabar tsakiyanci irin na Jawad, uncle Abbas na tafi ya dawo da kallansa a kan Jaish, cike da neman tsokana ya ce. "Babban abokin ango kuma yaya babba zo mu je ka gaisa da amarya, dama tana kewarka ai.........." Bai kai karshen maganar ba ya yanka a miliyan ya fito waje saboda wani irin capka da Jaish ya kai masa a wuya, Allah ya taimakesa ya zulle ya yo waje.

Da gudun gaske Jaish ya biyo bayansa, dan yau wlh ba zai kyalesa ba, ya zubar mashi da mutunci, wannan ai iskanci ne, dama ga zafin ɓacin ran anki ƴar kauye Mahnoor matsayin matarsa, sai ya haɗa dikka zai sauke a kan Jawad.................

Wayyo abubuwa sun haɗewa Jaish fa😅

Bari mu leƙa wani part mu dawo.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥 DUBAI🔥🔥🔥🔥

AFTER SOME WEEKS.

Zaune Sharifat take a saman bed, Leesharh na tsaye a wajen dressing mirror tana ɗan gyara face ɗinta, har ta mayar da jikinta ta yi ɓulɓul abinta saboda kulawa na musamman da ta samu daga Abbie, Yah Bilal, and Sharifat, sai ta yi saurin recovery.

Sanye take da riga da wando Pakistan mai bala'in kyau launin purple color. Ta gyara gashin kanta, sai dai hannunta har yanzu bai gama warkewa sosai ba, sun koma kamar yadda suke a da ita da Sharifat, suna kula da juna haɗe da nunawa juna soyayya.

Irin kayan jikin Leesharh shi ne a jikin Sharifat, sai dai ita nata maroon color ne. Hira da guyson Sharifat take yi a Whatsapp a in da take faɗa mashi Obaid and Omaid sun samu hutun karshen shekara suna gidan King Badeen, sun ki zuwa gidansu sun ce Tunisia kawai zasu wuce.

Shi ma guyson kwance yake a saman bed ɗin momma daga shi sai Short, ya rungumo pillow a kirjinsa yana aikin wannan sakalancin nasa da ya saba, shi kaɗai sai turo baki yake yi.

Sun nitsa cikin hiran da suke yi wayar Leesharh dake kusa da Sharifat ya hau ƙara.

A razane Leesharh ta ɗago da kallanta a kan Sharifat ta cikin mirror, ita ma Sharifat kai kallanta a kan wayar ta yi.

Private number ne yake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login