Showing 12001 words to 15000 words out of 403653 words
are you panting like someone who is not honest? Then you sigh is like someone who has escaped from a group of enemies".
Fuskarta cike tab da mamaki ta yi maganar, dan ita mamaki ya bata!.
Janyota jikinsa ya yi kawai yana sauke ajiyar zuciya, har ga Allah a tsorace yake, baya burin ta sake haɗuwa da yayansa, dan shi yasan wanene Black Tiger, mutumin da bai taɓa yafiya ba a tsawon rayuwarsa, bai ma santa ba, baya ɗaga kafa koda kuwa ga tsinke ne, kana mashi ɗaya zai yi maka ɗari, dole ya ji tsoro!.
Jinta a jikinsa yasa ta farga babu riga a jikin nasa, cikin sauri ta ɗago ta kalli face ɗinsa, while shi ma ita yake kallo. Watsewar da gashin kanta ya yi har fuskarta yasa bata samu damar ganin face ɗinsa da kyau ba.
Hannu ya kai ya tattare mata gashin waje guda, dan su samu damar ganin juna da kyau. Dikkansu sun ji daɗin hakan, barema shi da har wani cool ajiyar zuciya ya sauke.
"Ronnie why are you looking at me like that?"
Ta yi maganar tana ƙoƙarin barin jikinsa, dan ta ɗan tsorata na ganin kirar halittarsa.
Girgiza mata kai ya yi ba tare da ya yi magana ba, a hankali hankali yake sauke numfashi, hannunsa dikka biyu ya ɗaura a saman bayanta ya hanata barin jikin nasa.
Da sauri ta ɗago kallonta a kansa. Kurawa juna idanu suka yi kamar waɗan da suka afka duniyar tunani.
An rasa mai kawar da kallonsa daga kan ɗan uwa, da alama sun mace a kallon junansu ne.
--------- KNOCKING DOOR-----------------
Knocking door da aka fara yi daga waje ne yasa suka farga tare da dawowa cikin hanyacinsu, a nutse ya sauke ajiyar zuciya tare da saketa, ya ɗan raba jikinsa da jikin door ɗin ya kuma saketa.
Idanunta na'a a kan kofar, ta wani zarosu irin like tana mamakin wanene?.
Fingerprint ɗinsa ya sanya a kofar ba password ba, sannan ya wuce ya nufi wajen bed ɗinsa. Kamar ba shi ya wani rungumi Sweetie a yanzu ba.
Shigowa ciki Floris ta yi tana ɗan tsuke fuska alamar shagwaɓa. Sanye take da irin wannan shiga tasu ta riga da kuma sket har ƙasa, kayan yana da bala'in kyau, ta ɗaure gashin kanta a tsakiya, hannunta riƙe da Bibel, da alama shirin zuwa church ta yi.
Kallo ɗaya Ronnie ya yi mata bai furta uppan ba ya nufi toilet dan ya yi wanka. Da ido ta bishi tana mamakin ganinsa babu riga, sai kuma ta kara yin wani mamakin ganin Sweetie a tsaye a bakin kofa.
Kasa haɗiye mamakin nata ta yi har sai da ta ce. "Sweetie me kike yi a nan?".
"Babu komai". Ta bata amsa kai tsaye tare da wucewa ta nufi wajen bed ɗinsa.
Bayanta Floris ta bi tana faɗin. "Ya ke baki yi shirin zuwa church ba?".
Tana ƙoƙarin zama a bakin bed ɗinsa ta answer da. "Na faɗa maki mu bama zuwa church, masallaci muke zuwa, idan kuna da musque zan je can on Friday".
Tin da ta fara magana idanun Floris yake a kan ɗan bakinta har ta dire aya.
"Sweetie kin mun kama da wata mata da na taɓa gani cikin birnin nan! Sai dai ba sosai kuke kama ba, idan an ganki a fisge ne dai sai a ga kamar ita ce". Cewar Floris.
Ba tare da kawo wani dogon tunani ko wani nazari ba ta amsa da. "Kinsan halittun Allah dayawa, dama dai yarinya kika ce ina kama da ita to da sai in ce Pretty ce kila, amma ba yadda Ubangijinmu baya halitta".
Karisowa wajenta Floris ta yi, tana mamakin hali irin nata, yarinya sam bata taɓa ɗaukar abubuwa da mahimmanci, akwaita da careless, bata sanya damuwa a ranta, hasalima ba zaka taɓa gane ina alkiblarta a zamantakewa ya dosa ba, ji yadda ta bada amsar cewa da aka yi anga mai kama da ita, tamkar bata da uwa ko wasu ƴan uwan, a yanayin yadda suka taso su biyu cikin maraici ai zasu so ace ga mai kama da su ko dan su ji sanyi a ransu, ko da ba ɗan uwansu bane zasu ji matuƙar daɗin hakan suma yau sun ga mai kama da su, amma ta nuna halin ko in kula, dik yadda aka yi ba iya baiwa kawai gareta ba, ta san tarihin iyayenta, tasan in da za'a iya samunsu, dole akwai abin da take ɓoyewa, yarinya ƴar karama da ko 13 years bata cika ba sai shegen wayo........
Wannan cikin nata ba shakka ya fi tara sirri a cikinsa fiye da yadda yake ɗaukar abinci, dole a jinjinawa Sweetie yarinya mai wayo kuma ƴar baiwa.
"Sweetie wai ke baki mamakin abubuwa ne?".
Floris da abin yake damunta a rai ta gaza haɗiyewa ce ta jefa mata wanna tambayar, dan ita dai gaskiya tana mamakin rashin bayyana farinciki ko bakincinkin da Sweetie bata yi, baka taɓa gane a wani irin yanayi take!.
Ɗan motsa gefen bakinta sweetie ta yi kamar zata ɗan yi tsaki haka, alama ce ta amsa magana ba tare da ta buɗi baki ba, alama ta yi mata da ita bata wani jin mamakin komai a rayuwarta, dan ta ga abubuwa daban daban da suka girmi shekarunta kuma kwakwalwarta ya ɗauka, taga kaddarori da jarabawa daban daban, so yanzu ta daina nuna damuwa.
"Kina burgeni sosai Sweetie, and kyanki yana tafiya da ni, Please can we be a friends?". Cewar Floris.
Ta yi maganar tana miƙa mata hannu kamar mai shirin yin musabaha.
Babu wani ɗaukin hakan a tattare da Sweetie, babu wani shauki, ta jinjina mata kai tare da miƙo mata nata hannun tana faɗin. "Yeah we can".
Sam Floris bata ji daɗin ganin yadda Sweetie bata nuna shaukin hakan ba, amma bata nuna rashin jin daɗin nata a fili ba, ta danne ta kama hannunta suka gaisa, daga yau sun zama abokai kuma ƴan uwa.
"Amatsayina na abokiyarki kuma ƴar uwarki na ɗauki alawarin koya maki dik abubuwan da na sani a duniyar nan". Cewar Floris.
Kanta a kasa tana kallon ƴan yatsun kafafunta da suke ɗan yi mata zafi saboda karon da suka yi da Ronnie a lokacin da take ƙoƙarin shiga room na Black Tiger, so a lokacin ya taka mata ƴan yatsun kafafunta, ƴar ƙaniya tun ɗazun da take tare da shi bata ji zafin ƴatsun nata ba sai yanzu da ya shiga toilet ne ta gane ashe suna yi mata zogi, ɗazun ganinsa ya kwashe zogin.
So kanta a ƙasa ta amsawa Floris da. "For sure nima zan koya maki dik abin da na sani a rayuwata, ciki kuma harda addinina".
A hanzarce Floris ta amsa da. "Nima zan koya maki nawa addinin".
Jinjina kai Sweetie ta yi. "Na yarda ki koya mun dik abin da kika sani dangane da addininki, na kuma yi maki alkawari a dik lokacin da muka yi zurfi cikin koyan addinan guda biyu, idan har baki ji addinina ya burgeki ko kuma ya kwanta maki a rai ba, ko kin gane addinin gaskiya daga ciki ba to ni zan koma naki addinin!". Babbar magana!!
A ɗan ruɗe Floris ta zaro idanu waje, mamaki fal a ranta ta ce. "Zaki dawo addinina? Da gaske kike yi please?".
Girgiza kai Sweetie ta yi tare da dawo da kallonta a kan Floris, ya tabbata Floris yarinya ce, ai shi addinin gaskiya baya ɓuya yarinya, wuyarta ki fara koyan ilimi daga cikinta, kina farawa ko ance ki bari ba bari zaki yi ba, yo Allah wasa ne?!.
"Tabbas in dai kika nutsu kika sami ishasshen ilimi a kan addinina, kika zurfafa tunani, kika yi dik abin da na gaya maki to ba shakka in baki gamsu da addinina ita ce ta gaskiya ba zan bi taki". Cewar Sweetie.
Sosai Floris ta ji daɗin wannan furuci na Sweetie, kuruci dangin hauka, ita yanzu a ganinta zata yi wa Sweetie wayo ne ta shigo addininsu, bata san Sweetie kam da wayonta aka haifo ta ba, ko mai shekara 20 ba ya gwada mata dabara ba, yarinya kamar renon tsafaffi, Floris sai dai mu ce welcome to Islam, dan na tabbata dabarar Sweetie ba zai barki ki iya tsallake wanna challenge ɗin ba, bari ma mu zo mu fara shirin tarbar sabuwar baƙuwa a cikin addininmu..............🤸🕊️
Fitowa Ronnie ya yi ɗaure da bathrobe a jikinsa, launin milk color, white hairnsa yana ɗigar da ruwa.
Kallonsu dikkansu suka kai a kansa, yana da sexy gorgeous body shi ma, kamar yayansa, ga yanayin koreans skin ɗinsa sai dai muce masha Allah.
"Beb kai fa nike jira tun ɗazun, ka zo mu tafi". Cewar Floris.
Idanunsa a kan Sweetie ya amsa da. "Ten minutes".
Daga haka ya wuce dressing room ɗinsa.
A gaggauce ya shirya cikin ƙananan kaya crazy, ya fito fes abinsa, ya tsaya gaban mirror ya canza ɗankunnen dake kunnensa, dama suna dayawa har da wani ta saman kunne, dik ya canzasu, ya ɗauki wani haɗaɗen gold pil ya sanya a kusa da lips ɗinsa ta ƙasa, sai ya so ya yi kama da mace, sai ma da ya busar da gashin kansa ya tara ya ɗaure, idan baka ga kirar sexy badynsa ba kaga iya face ɗinsa zaka yi zaton mace ce ba namiji ba, kyau iya kyau.
Time da ya fito kasa hakuri Sweetie ta yi har sai da ta ce. "Ni Ronnie na rasa gane da kai da yayanka waye ya fi wani kyau? Kuma sam baku kama da shi fa, shi kamanninsa ma daban yake".
Tabbas basa kama, dan Black Tiger dai ba koreans bane, Black Tiger ya fi kama da turawa gaskiya.
Ɗan lumshe idanu ya yi yana sakar mata murmushi.
"Na fi yaya kyau mana". Cikin zolaya ya yi maganar.
A hanzarce ta ce. "Tun da ka amsa ka fi shi to tabbas baka fishi ba, shi ya fika, dan dik wanda yake da abu baya fitowa ya ce yana da shi, sai dai a gaya mashi yana da shi, dan haka baka da kyau".
Floris da mamaki ya gama kasheta ne ta tsoma baki kamar wata mara lafiya a in da ta ce.
"A ina kika taɓa ganin yayansa har kika san yana da kyau haka?".
Ta ji abin da bata taɓa ji bane, dan tasan ko Ronnie bai san kamaninsa ba, mamaki kamar ta sume a zaune.
Ɗago kai Sweetie ta yi da nufin ta bata amsa unexpect idanunta suka sauka cikin nashi. Girgiza mata kai ya yi a kan kada ta faɗawa Floris yadda aka yi da kuma yadda yayansa yake, ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru, hakan yasa ta mayar da kanta ƙasa ta rasa abin cewa, ita ga shi ba karya ta iya yi ba.
"Sweetie ki amsa mun mana". Cike da ƙaguwar son jin amsa Floris ta sake tamnayarta.
Hakan yasa Ronnie ya katsesu da cewa. "Let's go beb".
Ya yi maganar tare da miƙawa Floris hannu a kan ta tashi su tafi.
Miƙa mashi hannu ta yi ya kamata ta miƙe tsaye, tana matuƙar son ta ji amsa amma ya hanata ta hanyar janta suka nufi waje yana yi wa Sweetie bye bye haɗe da ce mata kada ta kuskura ta fita waje, ta zauna a ɗaki by 7 zasu dawo.
Da okey kawai ta bisu har suka fice, gyarawa ta yi ta kwanta tana tunanin rayuwa haɗe da masoyinta Kamran, true love never end, har yau har gobe soyayyar Kamran yana ranta, soyayyar gaskiya take yi mashi, ga shi bata san kamanninsa ba, a haka dai take balai'n kaunarsa, shi kuma kada ku manta soyayyar a mutu yake yi wa Pretty, dan tun faɗowarta duniya sonta ya dasu a ransa, ko yaya wannan abin zai kasance? Mu je dai zuwa.
===========🔥💘============
IDAN MUKA WAIWAIYA FRANCE KUWA.
SMART🔥🕊️
Tsulundun yake tsundume a cikin jacuzzi cikin toilet ɗinsa, har saman lion chest ɗinsa ruwan take, haɗaɗɗen kunfa fari tas ne cike a cikin jacuzzin, hakan ya hana damar ganin tsiraicinsa, ya jiƙa haɗaɗɗen dark black hairnsa da ruwa, hakan yasa gashin ya kwanto mashi rabi a gefe gefen face ɗinsa, rabi kuma a bayan wuyarsa, face ɗinsa gabaɗaya a jike yake da ruwa, zara zara eyelashes ɗinsa suna jike, hakan ya bada damar kyansa ya kara bayyana sosai.
Tinanika kala kala ne cike a cikin ransa, wani irin binciken kwakkwafi a kan wani technology da zata ciyar da duniya gaba yake yi, a part from duniyar wata da yake shirin zuwa yana nan yana wata aiki ma dan kara bunƙasa kimiya.
So yake ya leƙa duniyar karkashin ruwa bayan idan ya dawo daga duniyar wata, ya sa ana shirya kashi nautilus, wato wani katafaren jirgin ruwa ne wanda zai kai ka karkashin teku cikin kwanciyar hankali, yana dawowa daga duniyar wata yake son afkawa can, burinsa a kullum ya kawo wata kimiya da zata tashi kan duniya, ga shi da bala'in iya zurfafa tunaninsa a kan dik wata aiki da yasa a gaba, ga dogaro ga Allah hakan yasa yake yin nasara a dikkan lamuransa, dayawan masu fikira daga wajensa suke samun fasaha, nutsuwarsa da bin komai daki daki shi ke kara bawa mutane mamaki, jan ajinsa da halin ko in kulansa, bai ɗauki komai matsayin wani abin a zo a gani ba, wasa da makaman kare dangi kamar mai wasa da dunkulen wasa yakan ɗaga hankulan jama'a matuƙa, musamman wasa da rocket da yake yi, yana ɗaga hankulan makusantansa, saboda suna tsoron rasashi, shi kuwa lafiya lou yake komai ɗinsa.
Ya ɗaga kai sama idanunsa a lumshe, da alama ba ƙaramin daɗin ruwan yake ji ba, kuma ga dikkan alamu tunaninsa da yake faɗaɗawa tana tafiya mashi yadda ya dace duba da yadda ta nutsu ya nutsa cikin tunanin nasa.
While ita kuma mom suna can gym ita da dad suna motsa jiki, mom tana bawa furenta ruwa, kun san ta kware a wannan harkar, wajen gym ɗin gabaɗaya kewaye yake da tsaro na ban mamaki, amma hakan bai hana mom soyewanta da ɗan dattijon mijinta ba. Su fa sam basa tsufanwa soyayya.
A hankali ya waro idanunsa jin alamar shigowar mutum cikin room ɗinsa. Kamar wanda baya son motsawa ya juya idanunsa izuwa saman katafaren Tv dake manne da jikin bango a cikin toilet ɗin.
Heleena ce tsaye a tsakiyar room ɗin nasa tana bin ko'ina da kallo, ta kwana biyu rabonta da ta shigo cikin ɗakin, yanzu ma sai da ta je ta taso dad a gaba tasa ya yi amfani da laptop ɗinsa ya cire mata door securityn sannan ta shigo.
Tana nan dai cikin wannan ɗan iskan shigar tata, sai dai yau abin ta taazzara, dan fa cibiya a waje ne yau, ga wasu ƴan iskan breast ɗinta kamar............ Bari na raga mata kada nan gaba kaɗan ta zama matar Smart in shiga uku.
Yau wandon ma tsabar iskanci bai kai kaurin kafafunta kamar na Nennen Mahreen ɗin nan ba, hannunta na ɗauke da tray mai shake da small chop, ita dai ta dage sai ta kawowa Smart small chop ɗin nan, anya ma ba wani abin ta banka a ciki ba kuwa?
Baiwar Allah bata san ma kyamarta yake ji kamar ya yi amai idan ya ganta ba, ta bi ta matsawa kanta a kan son shi da son kyatata mashi, ina ga sai mun taimaka mata da tsayuwar dare kila ta dace, matsalar dai taki musulunta ne ita da mom.
Ji ya yi tamkar zai yi amai na ganinta da ya yi, ko bai tambaya ba yasan dad ne ya buɗe mata door ɗin nan, to ya zai yi da dattijon nasa? Ai sai hakuri kawai.
A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta tare da mayar da idanunsa ya lumshe su, cikin ransa ya fara tunani wanda shi kaɗai ya barwa kansa damar sanin me yake tunawa.
Kamar wanda yake mafarki ya furta. "Am coming for it soon". Ya yi maganar tare da sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya miƙe tsaye tare da zuro kyawawan kafafunsa kasa, ya fito daga cikin ruwa ya nufi ɓangaren towels dake shirye cikin show glass tamkar shop na sayar da su ne.
Wata fara kal ya ɗauko mai ɗan girma wadda ta tsaya mashi dai'dai kaurinsa, sannan ya ɗauki wata mai ɗan girma ya nannaɗo hair ɗinsa a ciki domin tsane ruwan. Gaban wash hand base ya nufa. Tsayuwa ya yi a wajen tare da kurawa kansa kallo a jikin mirror dake wajen.
Kamar wanda bai san ya face ɗinsa take ba haka ya kafe kansa da waɗan nan idanun nasa.
Ya ɗan ɗauki lokaci a wajen kafin ya nufi fita waje, shi da kansa yasan shi ɗin smart ne na gasken gaske, gifted ba.
Jin motsin fitowarsa daga cikin toilet ɗin yasa Heleena yin saurin ajiye mashi tray dake hannunta ta juya da sauri, har da haɗawa da ɗan gudu ko ɗar bata ji ba na wannan uban high heel dake kafanta, tana son sanya shi a idanunta amma tafi jin tsoron haɗuwa da shi sama son kallonsa da take, dan a kullum hata kyau, ita ake bari da dakon danasani in suka haɗu.
Sarai ya ga fitarta, amma ko a karkashin sillpers ɗinsa ya wuce izuwa dressing room. Jim kaɗan ya fito shirye cikin tsadaddiyar jogger a jikinsa ta kasa, ta sama kuma round neck polo shirt ce, dikka white colors ne.
Hanunsa