Showing 246001 words to 249000 words out of 403653 words

Chapter 83 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

31

wuni guda yana kallan guy ɗin nan bai gaji ba!

Dark black curly hair nan nasa ya yi mata wani irin gyara na musamman da ya sha bambam da gyaran da yake yi kullun, kai daga ganinsa kasan yau rana ne na musamman a garesa.

Tana shigowa ƙamshin perfume ɗinta ya haɗe da nasa sai ya bada wani sihirtatcen kamshi na musamman. Tin da ta shigo idanunta suke a kansa, baki ta saki tana kallah halittar Allah, lallai ba shakka Allah ya yi halitta a wannan waje, Black Tiger ya haɗu.

Like wow abin yaƙayatar over, ita da shi sai suka fito tamkar amarya da ango, saboda yanayin shigarsu. Sarai ya ji shigowarta, amma yaki ɗagowa ya kallesa, dan kada ku manta kashin wuyarsa ta zame mashi. Tin daga kan haɗadɗun cover da suke kafafunsa har zuwa dark black curly hairnsa ta bi da kallo a cikin zuciyarta tana furta wow. Kuma abin da zai baku mamaki da ita dik wannan yabon kyansa da take yi tana mutuwa da san kallansa fa bata taɓa jin sansa a ranta ba, ita dai Kamran take so, shi kuma yanayi mata kyau tana jin daɗin kallonsa, hasali ma ta fi jin Ronnie a ranta sosai fiye da shi, ko kila saboda krista ne yasa hakan?.

Misali yanzu da ace babu Kamran to tabbas zata iya yin soyayya da Ronnie, amma ban da Black Tiger, amma fa Kamran na raye, dan haka babu kowa a ranta sai shi.

Cike da yanka irin ita mai class ɗin nan ta tako izuwa gabansa, zuciyarta na harbawa da karfi tasa hannu ta riko necktie ɗin nasa da yake ƙoƙarin ɗaurewa tana faɗin. "Big bro bari in hutar da kai".

Sam baya san ɗaga ido ya kalleta, dan haka sai ya yi ƙasa da idanunsa wai dan ma kada su haɗa ido. Sai da unexpect ya sauke kallan nasa a kan yatsun kafafunta. Waro idanu ya yi da kyau a kansu, da yake ta cire takalman nata a kasan carpet dake gaban bed ɗin kafin ta ƙariso in da yake, hakan ya bashi damar ganin yatsunta, sosai ya zaro idanunsa waje a kansu. Kafarta na dana yatsunta guda shidda ne ba biyar kamar na sauran mutane ba. Ganin hakan ya yi mugun ɗaga mashi hankali, lokaci guda ya ji jiri ya ɗebesa, kafin ya ankara ya tafi zai kifa, gabaɗaya ya rinjayeta suka faɗa saman mattress ɗin, tsikar jikinsa ne ya fara tashi sosai na ganin yatsun nata da ya yi.

To me dalili kenan?.

Jikinsa har kerma yake yi, lokaci guda ya ɗago da kansa da kallonsa a saman face ɗinta, ya danneta ta yadda ko numfashi bata iya yi da kyau. A take idanunsa suka rikiɗe suka yi jajir kamar wuta, kwayar idanunsa suka tura olive sosai, harta kumatunsa sai da ya fara kerma kamar mai rawan sanyi, wani irin yanayi da ya shiga ya in ka gansa sai ka razana.

Lokacin guda ya fara yin wani irin jijjiga mai karfi gaske a kanta. Wani irin mahaukacin razana ta yi, bata san lokacin da ta fara ambatar sunansa da kyar da kyar tana ƙoƙarin yadda zata yi ta turesa daga kanta, da yake yana kanta sai tana iya jiyo yadda zuciyarsa take harbawa da karfi karfi gudu gudu sosai na wuce misali.

Hankalinta ne ya ƙara tsananta tashi sosai, cikin ruɗani ta rinƙa ƙoƙarin turesa daga kanta, amma ta ƙasa koda motsa shi. Shi kuwa ya ɗauki a kallah minti biyu yana wannan jijjiga kafin gabaɗaya ilahirin jikinsa ya sake alamar ya mutu ko ya suma a kanta. Tashin hankali, to ita yanzu tayaya zata iya cetan ranta? Kun dai san ba iya ɗaukar nauyinsa zata yi ba ko? Ga shi ko numfashi bata iya yi, wai menene ma ya rikiɗashi lokaci guda haka? Meyasa ya shiga wannan hali daga ganin yatsunta shidda ne ba biyar ba?. Uhm akwai matsala fa.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️







Azabar da ta ji tamkar zata mutu ne yasa ta ware tafukan hannunta tana san yin amfani da magic ɗinta ta ɗaga shi daga kanta. Ta kuwa yi sa'a ta samu damar yin hakan. A gefenta ta kwantar da shi, sannan ta shiga mayar da numfashi da karfi karfi, kun san idan mutum ya rike numfashinsa na ƴan sakannin yana saki da karfi karfi zai fita. To haka ita ma ta yi, ta kwanta shiru tana mamaki wani irin masifa ce yau take shirin faruwa da su kuma? Black Tiger da suma? Kai abin babba ne dik da a wajen Allah wannan ba komai ba ne, amma da mamaki daga kallan yatsun kafafunta sai ya suma, dik taurin zuciyar da balai'nsa, ga magic, amma farar ɗaya ya sume haka? Kai akwai matsala gaskiya.

Ta ɗauki a kallah 3 mins kwance shiru haka kafin ta samu numfashinta ya daidaita, miƙewa tsaye ta yi da kyar, har lokacin tana yin ɗan nishi kaɗan kaɗan alamar da gaske ya yi mata nauyi over. Juyo da kallonta a kansa ta yi, yana kwance flat tamkar babu rai a jikinsa. Shiru ta ɗan yi tana tinanin abin da ya faru da ita daren jiya ga mafarke mafarken da ta rinƙa yi.
Me ya faru daren jiya kenan?.

Saman bed ɗin ta haye, a daidai wajen kansa ta zauna tare da haɗe hannayenta dikka biyu ta tallabo kumatunta idanunta a kan face ɗinsa. Cikin natsuwa ta fara ambatan sunansa da big bro. Sai dai ina ko motsawa bai yi ba, cire hannunta ɗaya ta yi daga kumatunta ta mayar saman nasa kumatun.

A zabure ta zare hannunta daga jikinsa saboda wani irin azabbabben zafi da jikinsa ya yi kamar wuta, lokaci guda jikinsa ya yi wani irin zafin zaw. Miƙewa daga zaune ta yi ta durkusa a kan gwiwowinta, sannan ta kai hannunta saman necktie da yake ƙoƙarin ɗaurawa kafin ya sume. Kwance tie ɗin ta yi ta ajiye a gefe, sannan ta hau ɓalle botiran rigar jikinsa, ta buɗe rigar sama ya rage saura na biyun da na ciki. Addu'oi ta fara tofa mashi tana fatan Allah ya tashi kafaɗunsa, tana san zuwa ta kira Ronnie amma bata san tafiya ta barshi dan bata san me zai iya faru a bayanta ba, baya bata kaɗan.

Ta jima sosai tana yi mashi tofin addu'oi ba tare da wata barazana ba, sannan ta sauko ƙasa ta nufi toilet, bowl ta ɗauko mai ɗauke da ruwa mai sanyi a ciki, sai towel fari tas ɗan madaidaici da ta ɗauko. Har zata nufosa sai ta ce bari ta ɗauko almakashi dan ta tsaga singlet ɗin jikinsa tun da shi bashi da botir bare ta buɗesa kamar yadda zata buɗe sauran kayan jikinsa, ba iya ɗagasa zata yi ta cire shi ba kuma, so dole ta tsaga shi da almakashi kawai.

Dan haka sai ta duba a cikin drawers ɗinsa, a wajen mirror ta samu almakashi. Har zata juya ta bar gaban mirror idanunta suka sauka a kan wajen partyn Ronnie da abin da yake faruwa a wajen. Shiru ta ɗan tsaya tana kallan gabaɗaya al'ummar dake wajen, lokaci guda ta ji wani irin mummunar faɗuwar gaba a lokacin da taga fuskar Ronnie, shi kuwa sai murna yake yi yana farinciki.

A cikin zuciyarta ta ce. "Dik in da faɗuwar gaba yake ba alkhairi bane yake biyowa baya, ya Allah ka dubemu da idanun rahma, ina jin kamar wani abin ne zai faru, ga big bro ya suma, idan na tina Ronnie ko in na gansa sai gabana ya faɗi, ya Allah ka juya mummunar kaddararmu izuwa kyakkyawa ko kuma ka sassauta mana ita daga cikin niimominka ya rahmanin rahim". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta nufi Black Tiger, tana tafiya tana waigo mirror nasa.

Har ta haye saman bed ɗin hankalinta na a kan mirrorn. A gefenta ta ajiye bowl and towel ɗin, sannan ta hau cire botiran sauran kayan ciki, tas ta cire kafin ta sa almakashin zata tsaga farar singlet ɗin ciki. Tana kan yankawa sai ta ji mirror ta yi wani irin kara. A tsorace ta kai kallanta kansa jikinta na kermar kirjinta ya bada bugun dum dum lokaci guda.

Sai dai ko da ta kai kallanta a kai bata iya gane komai ba, domin wannan kara da ya yi alama ce da akwai matsala a birnin, so ba aikinta bane ba zata gane ba, dawo da kallonta a kan abin da take yi ta yi. Wani irin zabura ta yi a lokacin da ta kalli ta yanke jikin Black Tiger da almakashin da ta kai kallanta a kan mirrorsa, karar mirrorn ne ya razata har ta yankesa bata sani ba.

Sosai ta tsorata tsikar jikinta na tashi ganin jininsa jajir kamar wuta. Sai dai kuma jininsa na fita gabaɗaya ɗakin sai da ya amsa, a take wani irin haske mai karfin gaske ya gauraye ɗakin, zuciyar Duniyar shaiɗanu ta buga alamar autansu ya samu wani ɗan matsala kenan, take suka hau kururuwa mai karfin gaske, sai dai ita bata ji saboda ɗakinsa babansa ya tsareta, idan baku manta ba sai da ya fita main parlour ne ma Duniyar shaiɗanu ta iya gane cewa yana raye ko? To basa iya gane komai idan yana ɗakinsa, yanzu ma saboda jininsa da ya zuba ne yasa suka ji zuciyarsu ta girgiza. Da alama Sweetie zata shiga komarsu, dan kuwa wanda ya fitarwa da Black Tiger jini wlh ba zasu taɓa kyalesa ya rayu ba, sai sun ga bayansa! Wannan alkawari ne, a kan autansu babu abin da ba zasu yi ba!!.

Hmmm akwai matsala fa, Sweetie ita ta fara ganin Black Tiger ido da ido, ita ta fara sa ya fita fada har duniya tasan face ɗinsa, yanzu kuma ita ta fara fitar mashi da jini a jiki!!.

A gaggauce tasa wannan towel ɗin ta hau goge mashi jinin jikinta na kerma. Ko kaɗan jinin yaki tsayawa, hakan ba karamin ɗaga mata hankali ya yi ba, da gudu ta diro kasan bed ɗin ta nufi waje dan ta je ta kira Ronnie ya zo ya kawo mata agaji, dan abubuwan is getting out of hand a gareta. Sun fi karfinta!.

A tsakiyar main parlour suka ci karo da Ronnie, karo suka yi ta yi baya zata faɗi tana jan numfashi da sauri sauri. Rikota da hannu ɗaya ya yi yana faɗin lafiya kuwa take irin wannan gudun?. Ƙasa yin magana ta yi tana sauke numfashi da ɗan sauri sauri.

Allah sarki Ronnie, haka kawai ya ji jikinsa ta bashi ba lafiya ba, saboda har cikin ransa ya ji wannan fitar jini na Black Tiger, shiyasa ya ce bari ya zo ya duba. Da hannu ta nuna mashi sama ta ƙasa yin magana. Hannunta ya ja da gudu suka haura sama ɗin yana jin gabansa na faɗuwa.

A yadda ta bar Black Tiger haka suka shigo suka same shi. Da gudu Ronnie ya haye bed ɗin yana tambayarta me yake faruwa?. Bata ɓoye mashi ba ta faɗa mashi dik abin da yake faruwa. Zaro idanu sosai ya yi kafin ya ce mata.
"In kalli kafan naki da ya gani ya suma" a hanzarce ta fito da kafar tata ta nuna mashi. Yana ganin yatsunta shidda ne wani irin zabura ya yi zai miƙe tsaye, sai kuma ya daure ya koma ya zauna.

"Bro lafiya?". Ta jefa mashi tambaya. Kai ya girgiza mata alamar babu komai. Shiru ta yi tana tinanin lallai akwai matsala wanda Ronnie ya sani kawai faɗa mata ne ba zai yi ba, amma tana fatan Allah yasa alkari ce a garesu bakiɗaya. Ronnie a matsayinsa na likita A-box ya ɗauko domin taimakawa yayan nasa, ga shi a kusa da kirji ta yankesa.

Tsab ya gyare komai, sannan ya ce ta ɗebo wani ruwa su sanyayawa Black Tiger jiki saboda zafin da jikin ta yi. Tana ƙoƙarin sauka daga bed ɗin mirror ta kara yin kara a karo na biyu. A miliyan Ronnie ya kai kallansa a wajen. Ai bai san lokacin da ya diro kasa daga saman bed ɗin ba, kamar walkiya ya isa gaban mirror ya tsaya.

"Sis zo ki ga wani abin". Ya faɗa yana zaro idanu waje sosai. Da sauri ta kariso wajen tana faɗin. "Meyake faruwa ne? Ɗazun ma mirror ya yi kara lafiya kuwa?". Tamkar idanunsa zasu faɗi ƙasa saboda zarosu da ya yi ya ce. "Ina fa lafiya, muna cikin tashin hankali, birnin nan babu lafiya ga yaya ya suma yanzu ya zamu yi?".

A kusa da shi ta tsaya kafin ta ce. "Meyake faruwa da birnin?". .......... Yatsansa yasa ya yi mata pointing na wani ɓangare daga jikin mirror kafin ya ce. "Kinga nan wajen birnin nan ne, kinga mutanen da suke wajen nan to yaki suka kawo mana, dama jiya yaya ya faɗa mun akwai waɗan da suke haransa dan su kwace birnin nan daga hannunsa bayan kowa yasan birnin nan nasa ne, to ga shi yanzu sun dinfaro cikin birnin nan da shirinsu yaya kuma babu shi yanzu ya zamu yi". Cike da tashin hankali da fargaba ya yi maganar!!.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Ka taɓa ganin wanda ya rike Allah ya rasa mafita?"........................ Kai ya girgiza mata alamar a'a...... "To ka yarda dani zamu yi nasara ko da big bro ko babu shi, trust me ba zamu taɓa faɗuwa ba dan mun rike Allah, Allah ina mai rantsuwa ina kuma mai imani da Allah Allah ba zai taɓa kunyata mu ba, ka yarda dani". Ta kai karshen maganar tare da ware mashi tafin hannunta. Ba tare da shayin komai ba ya ɗaura nasa tafin hannun a kan hannunta alamar ya yarda da ita. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Mu je wajen mayakan da suke birnin nan ka ji?".

Hannunta ya damke sosai yana faɗin. "That's why I love u my sis, kina da basirar saurin warware mana matsala, lets go to". Ya kai karshen maganar yana sakin hannunta. Haɗa hannun suka sake yi alamar zasu yi aiki a tare kuma zasu yi nasara In Sha Allah. A tare suka nufi wajen Black Tiger, sannan a tare suka ja bargo suka rufesa tare da yi mashi fatan farkawa cikin gaggawa kafin abubuwa su fi karfinsu su caɓe masu.

Da gudu Ronnie ya ja hannnunta suka nufi waje Sweetie tana ta ƙoƙarin sanya ƙwaƙwalwarta a chaji wajen san gano menene ya janyowa Black Tiger wannan matsalar?. A gurguje suka fito kofar empeir ɗin, akwai wani stairs case mai bala'in tsawo a bakin empeir ɗin wanda ya kai step 30 haka, a gurguje suka tattakasa suka sauko ƙasa.

Master Devil suka fara nema, dan shi ne master ɗin warriors ɗinsu, dan haka sai suka nufi ɓangaren mayakan Daular, hannunsu rike cikin na juna, Allah sarki abin da basu sani ba shi ne master Devil ya haɗa hannu da mutanen can, ya ci amanarsu dik saboda dukan da Ronnie ya yi mashi ranar. Amma fa shi Black Tiger yasan da cewa master ya haɗa hannu da mutanen, kuma master ɗin ne ma ya nuna masu hanyar da zasu bi su shigo Daular a saukake su ci su da yaki. Dik Black Tiger yasan komai, sai dai a yanzu babu amfanin sanin da ya yi, bai tina hakan zata faru da shi ba shiyasa ya yi shirin yakarsu shi kaɗai, sai dai kana naka Allah yana nasa, ga shi dai yanzu ya shiga wani hali.

A can part na warriors suka isko master Devil yana zaune saman chairs kamar bai san komai ba. Suna shiga wajen tin kafin su ƙarisa in da yake suka fara faɗin. "Master ka haɗa kan warriors ɗin nan yaki ya tinkaromu a kurarren lokaci"......... Master dake zaune ko a jikinsa ya ce. "Babu wani mayaki da zai shirya yaki har sai King Lucian (Black Tiger) ya bada umarnin hakan".
Cak Ronnie ya tsaya jin amsar master, ransa a ɗan ɓace ya ce. "Ni na bada wannan umarni dan haka ka haɗa kansu".

Miƙewa tsaye daga saman kujarar da yake zaune ya yi, cikin kakkausar murya ya ce. "To ba zan yi ba! Ba zan bi umarnin naka ba!!". A fusace Ronnien ya nufesa da nufin sake dakasa kamar a baya. Yana tsaye bai yi wani motsi ba irin alamar akwai abin da ya taka haka. Da sauri Sweetie ta rike hannun Ronnien tana faɗin. "Bro don't mind him, ka manta muna da abubuwa a gabanmu ne?".

Ciza laɓɓansa master ya yi, ya so ne dama Ronnie ya zo da nufin su kaure da faɗa ya janye masu hankali har gungun matanen can su yi wa Daular zobe su rufesu da yaki ba tare da sun farga sun shirya ba, amma sai Sweetie ta hana shi, ya ji zafin hakan kuma ya kara tsanar Sweetie sosai.

"Bro kai da kanka ka bawa warriors ɗin umarnin da su shiryawa yaki kada ka daka ta wannan kazamin mutumin". Cewar Sweetie, tana bala'in tsoron master Devil idan baku manta ba tun farkon zuwanta birnin, sai dai kuma yanzu wutar tsanansa ne yake ruruwa a cikin zuciyarta saboda lalatar da yake yi, and tana tare da Ronnie, dan haka tana jin kwarin gwiwar zaginsa dan Ronnie ya fisa karfi kuma zai tsaya mata.

"Babu wanda ya isa ya bawa warriors ɗin nan umarni a nan sai ni". Cewar master, dik abin da yake yi fa yana so ne ya ɗauke masu hankali har a cin masu. Ronnie zai yi mashi martani Sweetie ta hana shi, daga karshe ta ja hannunsa suka haye saman dogon stage dake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login