Showing 54001 words to 57000 words out of 403653 words

Chapter 19 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

49

baya wajen, kamar zai je ya tambayi momma, sai kuma ya tuna kila shi ma ya tafi wajen dinner ɗin ne. Hakan yasa ya ɗan ji sanyi a ransa. Bedroom ɗinsa ya koma.

Wayarsa ya ɗauko, number Abdussalam ya kira domin ya tabbatar, ana tsaka da taro kira ya shigo.

Cikin girmamawa Abdussalam ya ɗauka.

"Omar yana wajen taron ne?".

Shi ne abin da King ya tambaya. A lokacin guyson yana tsaye a kusa da shi yana san tamnayarsa ina Auta. Dan haka da e ya amsawa King.

Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya King ya sauke wanda har sai da Abdussalam ya ji hakan a kunnuwansa.

Katse kiran ya yi tare da ɗaura wayar a saman drawer, ya kwanta ya janyo bargo, hankali ya kwanta tun da Guyson yana wajen taron.

=========================🔥

Guyson kuwa, yana sako ƙafafunsa cikin hall ɗin dai'dai lokacin MC ya ce da Jawad ya riƙe waist ɗin Chuchu ya sumbaceta.

Shiru guyson ya yi yana mamakin abin, shi ba saba zuwa wajen biki ya yi ba, kunsan brothers ɗinsa dik gwabraye ne babu wanda ya yi aure bare ya san yadda ake yi, so bai taɓa sanin yadda ake wasu abubuwa ba, hakan yasa ya haɗe dik waɗan da suke cikin hall ɗin har da su Jawad ɗin da mc ya yi masu sunan ƴan iska..............😂

Bai kare tsinkewa da mamaki bama sai da yaga da gaske Yah Jawad ɗinsa ya mannawa Chuchu sumbata a baki, hakan yasa ya kara zaro idanu waje yana mamaki bawan Allah ustadz.

Tabbas yasan hakan ba laifi bane tun da Jannat matar Jawad ɗin ne, shi abin da ya bashi mamaki shi ne ko kunyar mutane basu ji suke wannan iskanci, abin da ya kasance sirrinsu suke bayyanata ga duniya, ina laifin iya ƴan uwansu ne kawai, shi ne har da baki...........?

Ni kuwa nace guyson kenan, dan dai bai faɗa soyayya bane, yana faɗawa zumuɗi zai sa ya mance da cewa kiss sirri ne, kila ma abin da zai yi sai ya fi nasu......😂

Ciki ya ƙarisa yana ta aikin rarraba idanu a kan ta ina zai ga Auta?. Har ya ƙariso kusa da su Jawad bai hango Auta ba.

Kusa da Abdussalam ya tsaya, yana ƙoƙarin tambayarsa ina Auta sai ga kiran King a lokacin ta shigo.

Shiru ya tsaya har sai da Abdussalam ya karisa call ɗin, nan ne ya ce. "Yah Abdussalam ina Auta?".

"Kana nufin my wife?". Cewar Abdussalam.

Jinjina kai Omar ya yi kafin ya amsa da. "E ita nike nema".

"Ai tin da nazo ban haɗu da ita ba, kila tana cikin gida, bata zo nan ba, muma nemanta muke yi".

Guyson bai kawo komai a ransa ba, ya juna ya nufi hanyar fita, dan a tunaninsa ko tana ɓangaren Akka, dan haka zai je can ya duba ta.

Ƴan dinner sai cin uwar sabada ake yi ana sharholiya, Jawad ansami abin da ake so, wato yiwa Jannat sumbata, ko kunyar mutane baya ji, shi ba goshinta ya sumbata bama, bakinta ya sumbata mai gabaɗaya, buri ta cika yau. Kada ku manta wannan ƙaramin dinner da iya ƴaƴan sarakuna da masu mulki ne kawai a ciki, akwai babbar dinner da za'a gabatar gobe da misalin karfe 12 na dare.

===========================🔥

••••••••••• BLACK WORLD•••••••••••••🔥

A hankali idanunta suka fara buɗewa, kunnuwanta suka fara jiyo mata sautika na kukan abubuwan da bata taɓa jin irinsu ba.

Jiri jiri ta fara gani kamar zata faɗi ƙasa. Lokaci guda ta ji wani irin sanyi ya ratsa mata jikinta har izuwa cikin ƙashi da ɓargo, ga kafafunta babu takalma.

Dishi dishi ta fara gani haɗe da wani irin yana kamar ɗakin da ya ɗebi shekaru aru aru babu mutane a ciki, a hankali idanun nata suka fara washewa.

Sai kuma menene? Wani irin tabkeken tekun kankara ta gani a gabanta mai shake da ruwa mai bala'in sanyi har da ice a ciki, wannan dalilin ya haifar da uban sanyi da ta ji ya ratsata.

A tsorace ta zaro idanunta waje sosai, ta yi iya kallonta bata iya gano karshen wannan kogi ba, tsoron juyawa bayanta ta yi dan kada ta sake cin karon da abin da ta gani ya makantar mata da idanu ɗazun.

Tamkar wadda aka ture haka ta tafi luuuu sai cikin wannan tapkeken teku ba zato ba tsammani.

Wani irin ihun azaba ta saki sakamakon wani irin sanyi da ya ratsa kashin jikinta, a tsananin razane ta fara ƙoƙarin cetan kanta, Pretty ta fita iya ruwa, dan in baku manta ba Pretty mayyar san ruwa ce, kada ku manta kullum a wajen korama Kamran yake iskota, ita kuma Sweetie kullum tana ɗakinsu.

So bata wani iya ruwa ba, hakan yasa ta fara shan ruwan, ita dik ba wannan bane ma damuwarta, bala'in sanyin dake cikin ruwan ne matsalarta, sanyin ya yi mata over.

Sai fafutuka take yi tana san cetar kanta, abin mamaki kuma bata nitse kasa ba, ruwan kuma yana da bala'in zurfi. Kamar daga sama taga bayyanarsa a bakin tekun.

Kamar wani aljani haka ya bayyana, sleeping dress launin white color ce a jikinsa, ya yi bala'in kyau matuƙa, gashin kansa a sake, hakan yasa ya kara wani irin bala'in kyau, da alama ya kwanta zai yi barci ne ma ta shiga cikin gonarsa ta sanya shi tashi, dan dik wasu alamu na wanda ya kwanta zai yi barci ta bayyana a tattare da shi.

Idanunsa suna ɗan lumshe alamar yana jin barci, kwayar idanunsa sun kara tsananta olive green sosai, sai shining suke yi, haka zalika ita ma olive green eyes ɗinta sun kara tsananta kala saboda ɗan duhun dake wajen.

Farincikin idanunsa dama idan baku manta ba milk color ne ba fari tas ba, so yanzu ya yi jajir sosai. My people's Black Tiger karshe ne a kyau wlh, dik wasu cikar kyau na ɗan adam ya haɗesu sai rashin mutunci cike a kai.

Kafafunsa na sanye da sps, hakan yasa baka iya ganinsu.

Ganin shi ne ya bayyana yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, wato ita fa Sweetie wlh ko kaɗan bata jin tsoronsa, in short soma take ta ga bayyanarsa a waje,..........😂


Yanzu da ta ga shi ne har ta ji sanyin ruwan da take ciki ya ragu. Idanunsa a kanta babu ko kyaftawa, ita ma kura mashi kallo ta yi, suka ga juna ido cikin ido like wow, ga idanun nasu kalar iri ɗaya sak, sai abin ya bada wani citta.

In a low cool voice sosai ya furta.

"Where is Spender? Live or die!". Lion voice ɗinsa ya daki dodan kunnenta ba tare da ya buɗi baki ya yi magana ba, abin yana bata mamaki yadda baya buɗe baki kuma muryarsa take fita har ta furta words.

Wani irin kallo ta yi mashi mai kama da harara kafin ta ce. "What's Spender?".................... Ko shakka babu ta yi maganar!.

Tashin hankali. Gaskiya Sweetie ƴar yi ce ita ma!.

Jiji da kansa ne ta motsa, dan shi baya bada gurbin wasa a lamuransa, wato Sweetie bata ji tsoron in da take bama tukun nan ko?.

Da hannunsa ya nunata nan take ta fara nutsuwa kasan wannan tekun. Zaro idanu ta yi haɗe da fara ƙoƙarin yadda zata kwaci kanta.

Amma ina ta kasa, tana ji tana gani ta nitse can ƙasa. Wasu irin macizan ruwa ta fara gani a kasan masu kai irin siffar na mutane, abin tsoro, ba halin yin ihu, sai ma ɗirkar ruwa da take yi.

Wintsila kafafunta ta fara yi gwanin ban tausayi, ga ruwa tana ɗirka, shi kuwa yana ganinta a kasar ruwan with his magic eyes.

Tana ji tana gani kamar zata mutu haka waɗan nan macizan suka zo suka mannewa jikinta, sai dai basu cijeta ba, babu yadda zata yi, sai wiwwintsila kafafu da hannaye take yi, ji take yi kamar ma an shaketa a cikin ruwan ne, yadda take shan ruwan sai ta baka tausayi.

Yana ganinta har sai da ya ga ta sha ruwa sosai, kamar zata mutu, idanunta sun yi jajir kamar wuta, ta wahala iya wahala, ta ji kamshin mutuwa, sannan ne ya ɗago da ita saman ruwan.

Haba tana yin sama ta fara tari kamar zata mutu, ga macizan dake manne da jikinta tsoronsu take ji kamar ta mutu, amma ba halin ta gudu ko ta rabasu da jikinta, yanzu ta numfashinta ma take yi, tana ƙoƙarin dai'dai ta shi!.

A karo na biyu ta sake jin Lion voice ɗinsa unexpext a kunnenta yana sake jefa mata tambayar ina Spender?.

Cak ta dakata da kakarin da take yi kamar zata yi amai. A hankali ta ɗago da rinannun jajayen idanunta a kansa. Kamar zata yi kuka ta ɗan tsuke fuska, yana kallonta sosai a cikin ido.

Ɗaure fuska sosai ta yi kamar bata san menene dariya ba, sak irin yadda ya wani uban ɗaure fuska, wani irin harara ta dalla mashi ko tsoro babu, a karo na biyu ta sake cewa.

"What's Spender?" Babbar magana!.

Ta yi maganar ne a kule, wato idan zai kasheta ma gara ya kasheta ba faɗa mashi in da Spender yake zata yi ba.

Hannunsa ya sake saitata da shi da nufin ya sake mayar da ita kasar ruwan dan mugunta, ko tausayi bata bashi ba, ko da yake shi wannan mai bakar zuciyar ina ya san wani abu wai shi tausayi? Ai bai santa ba.

A hanzarce ta sanya hannunta irin mutum ya tare fuskarsa ɗin nan, haka ta yi saboda tana tsoron komawa cikin ruwan, kuma bata jin komai azabar da zai gana mata zata iya bashi Spender, sai dai ya kasheta amma wlh ba zata bayar ba!.

Tana sanya hannunta unexpect magic ɗinta ya fita, ga shi suna saiti da juna, kai tsaye sai kan saitin zuciyarsa magic ɗin nata ya dakesa.

Da yake unexpect ne abin hakan ya haifar mashi da jijjiga mai karfin gaske, wani irin jiri ne ya kwashesa ba zato ya afaka da karfi cikin ruwan tekun shi ma, dab kusa da ita ya faɗa.

Ba ƙaramin razana ta yi ba na ganin irin jijjigar da ya yi kafin ya faɗo cikin ruwan, ga shi kuma ya faɗo kusa da ita.

Wani irin tsoro ne ya lulluɓeta, sai ta kasa juyowa ta kalli in da yake. Shi kuma miƙewa tsaye a kan kafafunsa ya yi a cikin ruwan bayan faɗawarsa kenan.

Sai da ya ji a jikinsa lokacin da ruwan sanyin nan ta ratsa jikinsa, ashe babu daɗi ya jefata cikin ruwan sanyin, dik jikinsa sai da ta amsa har ƙashi da ɓargo.

Idan ransa ya kai miliyan to ya ɓaci, nan take Black heart ɗinsa ta matso kusa, a fusace ya juyo gareta.

Wannan juyowa da ya yi sai da gashin kansa ya pyaɗe mata rugun wuyarta, sannan ya watsa mata ruwan da ya tattaro daga gashin nata a saman face ɗinta.

Hannu tasa dan ta sharce ruwan da ya watsa mata ɗin. Kamar daga sama ta ji saukar hannunsa a bayan wuyarta. Da karfi ya damketa.

Babu tausayi babu imani ya danna kanta a cikin ruwan nan, da alama kasheta yake da niya.

Buga buga ta fara yi tana shan ruwa.

Azaba da ya ratsata bata san lokacin da ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ba, ƙoƙarin juyowa garesa ta fara yi, ko kaɗan ta kasa iya motsa shi, fafutuka ta fara yi da hannunta tana neman abin da zata kama dan ta cece ranta, ta ji azaba ƴar kaniya, har ta ji a ranta Spender banza zata iya bashi a yanzu kam, saboda taga alamar mutuwa.

Unexpect hannunta ya kai kan heronsa (bananarsa) saboda tana neman abin kamawa sai kawai ta capkoshi da karfi.

Ai bai san lokacin da a miliyan ya saketa ba, har baya kaɗan ya yi, ya ji abin da bai taɓa tsammanin zai ji ba a rayuwarsa, dan ma Allah yasa a cikin ruwa suke.

Sweetie akwai zuciya, ko da yake haka twins or triplets or quadruple suke, abin a jininsu yake.

Yana saketa ta ɗago kanta da karfi, wani irin numfashi da ta ja da karfi sai ta baka tausayi, da karfi ta fara layi a cikin ruwar kamar wadda ta sha wine ta bugu, neman in da zata tsaya domin ta samu numfashinta ya dawo daidai take yi.

Tana tsaka da juyi a cikin ruwan ta matso kusa da shi, dama in baku manta ba ai ya ɗan ja baya kaɗan.

Tana matsowa kusa da shi, idanunta a datse kam, jin alamar abu yasa ta sanya hannun bibbiyu ta riko shi tana wani irin numfashi mai ban tausayi, da alama ta fita hayyacinta sosai, shiyasa ma bata ji abin da ta kama da farko ba!.

Kirjinsa ta kama a yanzu kuma, hakan yasa ta ji kamar dutse ta kama, saboda a dake yake sosai. Da hannunta dikka biyu ta dafa kirjin nasa tana ƙoƙarin fara kwararo amai na uban ruwan da ta sha.

Shi kuwa tun da ya koma baya ya datse idanunsa gam, ko me yake tunawa? Kamar dai abin ya yi mugun baƙanta mashi rai ne!.

After some minutes.......... Suna tsaye haka. A hankali ta fara dawowa cikin hayyacinta.

Idanunta ta fara kokarin warowa waje dan ta ga ina yake? Yanzu kam ta iya tuna in sa take.

Tana buɗe ido sai a kansa, yana tsaye idanunsa a datse kam kamar wanda ruwa ya cisa.

Wani irin karfinta dikka ta tattaro, da karfi ta danna hannunta dake dafe da kirjinsa, dagewa ta yi harda ciza laɓɓanta da karfi, wureshi ta yi a cewarta ta samu hanya ta fita.

Sai dai kash, ko motsawa bai yi ba, kamar dutse mai girman gaske ta yi yunkurin turewa, ko gezau bai yi ba.

Ransa ne ya kara ɓaci, da karfi ya waro idanunsa waje, idanunsa sun juya izuwa magic eyes.

A maimakon ya bawa Sweetie tsoro sai ma kafe shi da kallo ta yi, dan ita magic eyes ɗin nasa ma kyau suke yi mata........... Trust me Sweetie ƴar duniya ce, ƴar ikka ce, wai magic eyes ɗinsa suna yi mata kyau, kai wannan yarinya tana goge mun hadda.

Kamar walkiya haka ya yi amfani da magic ɗinsa ya janyeta baya nesa daga kusa da shi. Ganin ya buɗe hannunsa ya janyeta baya yasa ita ma ta tuna a ranta cewa bari ta gwada buɗe hannunta taga me zai faru tun da ranar taga ta buɗe hannu ta iya sarrafa chandelier.

Tana buɗewa magic ɗinta ya fita, da karfi magic ɗinta ya janyo shi kusa da ita, suka sake haɗewa kamar chewing gum, har sai da kanta ya bugi kirjinsa. Yau Black Tiger ya haɗu da ƴar bala'i dai'dai da shi!.

Magana ta gaskiya ya fi Sweetie karfin magic, yana dannewa baya san kashetan ne kawai, yasan idan zai kara karfin magic ɗinsa ya fi yadda yake a yanzu yana yin amfani da shi sau ɗaya a kanta zata rasa ranta, baya san ta mutu, saboda yana da buƙatar Spender a hannunta ta kowace hali ne, ita kaɗai ce kuma yanzu a duniya tasan in da yake, kunga dole ya danne.

Ita kuma Sweetie dama bata tsoronsa sosai, sai kuma Ronnie ya ce mata yayansa ba zai taɓa kasheta ba har sai ta bashi Spender, sai dai ta sha wahala a hannunsa, dik ranar da ta bashi Spender to ta sani tana yi mashi abu kaɗan zata mutu. Jin ba zai kasheta bane yasa ta kara samun kwarin gwiwa haɗe da kara rage tsoronsa da take ji, shiyasa zaku ga tana yi mashi wasu abubuwa bata nuna tsoronsa.

Wannan shi ne dalilan da yasa kuke ganin in sun haɗu kamar magic nata ya fi nasa, kuga kuma kamar bata jin tsoronsa, to ba haka bane, kun ji dalilan.

Ƙoƙarin danne Black heart ɗinsa ya fara yi dan kada ya kasheta, ita kuma ture shi daga kusa da ita ta fara ƙoƙarin yi.

Hakan ya kona ransa matuƙa, har da sanya hannunta bibbiyu zata ture shi. Cikin fusata ya capko wuyarta ta gaba da hannunsa ɗaya. Da karfi ya shaketa har sai da ba shiri tongue ɗinta ya yo waje.

Zaro mata dara daran idanunsa ya yi ba shiri ta lumshe nata idanun, saboda kaifin idanunsa ya ratsata har sai da ta ji kamar an tsira mata allura a jikinta.

Hannunta ta ɗaura a saman nasa tana son ya sake mata wuya. Tin da Allah ya haliccita a duniya bata taɓa jin hannu mai laushin nasa ba, she has a very very smooth and soft skin, ko da yake baya fita rana ai dole dama skin ɗinsa ta yi haka.

Sai dai akwai yawan jijiyoyi a hannun nasa sosai, gasu ɓaro ɓaro. Bubbuga hannunsa da karfi ta fara yi tana neman agaji.

Kada ku manta basu nitse kasan ruwan bane saboda magic ɗinsa, shiyasa suke a sama.

Azaba ne ya yi azaba kuma taga bashi da miyar sake mata wuya. A hankali ta sauke hannayenta kasa daga saman nasa, jikinta ne ya fara sakewa alamar rai ya yi halinsa.

Sake hannunta da ta yi ya ja magic nata ya fara nitsar da su kasar ruwan.

Yana rike da wuyarta unexpect ya ga sun fara nitsewa kasan ruwa, ko kaɗan bai damu ba, da alama ɓacin rai yasa ya fita a hayyacinsa, ya manta ita kaɗai tasan in da Spender yake ga shi ya kasheta bai ankara ba. Zuciya ta ja mashi.

Har sai da suka ka kai kasan wannan tekun ne ya farga da in da suke da kuma ta mutu.

A hankali ya zame hannunsa daga wuyar tata.

Sulalewa ta yi ta kwanta a kasan wannan ruwa ta zama gawa.

Ransa a tsananin ɓace, yana ta huci mai zafi ya yi amfani da magic ya dawo da su saman ruwan. Da hannu ɗaya yasa ya saɓi gawarta a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya fito daga cikin ruwan. Idanunsa a datse ya tsaya a bakin ruwan, ko kaɗan bai yi nadamar abin da ya aikata ba. Cikin kungurmin dajin ya kutsa da ita, yana taku cikin zafa, daga shi har ita jikinsu na ɗigar da ruwa!.

To ina kuma zai kai gawarta? Me kuke tunanin zai faru?.

=========================🔥

•••••••••••••••FOREST••••••••••••••🔥

Zaune take saman wani dutse wanda ruwa yake ɓulɓula daga kasansa, daga gaba kaɗan tabkeken kogi ne a wajen, ita kaɗai take zaune kamar marainiya, tana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login