Showing 72001 words to 75000 words out of 403653 words
na tashi alkiyama!".
Ɗan jinjina kai ya yi tare da maimaita kalmar tashin alkiyama, kara rikiɗa face ɗinsa ta yi izuwa na mamaki sosai, shi dai bai san wani tashin alkiyama ba.
"Menene kuma tashin alkiyama?". Ya yi tambayar kamar ba shi ya yi ta ba, irin mutum ya yi magana unexpext haka.
"Ranar girban abin da ka shuka, ranar da kowa zai karɓi sakamakonsa..........".
"Dama akwai ranar da kowa zai karɓi sakamakonsa ne?"................... Kai ta jinjina mashi alamar tabbatarwa, tabbas akwai ranar da kowa zai karɓi sakamakon aikinsa da ya aikata a duniya.
Girgiza kai ya yi............... "Impossible, gaskiya ban yarda ba, ta ya za'ayi ki ce mun dikka mutanen dake duniyar nan kowa zai karɓi sakamakonsa? Waye zai basu sakamakon kuma a ina zai gansu har ya basu? Ke kin san adadin mutanen dake duniya kuwa?!".................. Da ɗan kaifi a voice ɗinsa yayin da ya kai karshen maganar.
Dama tasan da wuya ya yarda da hakan, amma da yake tana da kaifin ƙwaƙwalwa sosai, ta iya bin mutun dik ta yadda ya zo mata, tasan irin kalamai da hujojin da zata yi amfani da su wajen sanya mutum ya yarda da ita ko yaki ko ya so, sai bata ji komai da jin kalamansa ba, bata wani damu ba, cikin sanyin murya ta ce.
"Ronnie ku nawa ne a school ɗinku?".
Kai tsaye ya amsa mata da. "Muna da yawa ba zan iya kirgawa ba!".
"Good......... Amma kuma dik yawankun nan ya aka yi mai school ɗin naku yasan adadinku da har yake iya shirya maku jarabawa, idan kunci ya bawa kowa marking na adadin amsar da ya bada, sannan waɗan da suka faɗi a sanya masu sun faɗi, har ya rubutawa kowa result ɗinsa ya bashi da sakamakon abin da ya ci dai'dai wa dai'dai babu zalunci?".
Shiru Ronnie ya yi dan ta buga mashi misali da hujja mai karfi, shi kansa ya fahimci maganganunta abin dubawa ne, amma da yake shaiɗan la'anannen Allah ne sai ya zuga shi a in da ya ce mata.
"To ai mai makarantar makarantarsa ne, dik wanda zai shiga school ɗin dole yasan shi, kuma dole sai ya bada sunansa an rubuta, wannan dalilin yasa ya san sunan kowa".
Wani irin daɗi ta ji ya ratsa zuciyarta, haƙiƙa ta ji daɗin wannan amsa nasa, Ronnie ya ɗaure kansa da kansa, ai ko ta ina aka bi da mumini bayyana Allah a wajensa ba abu bane mai wahala, har ta ji ta samu confidence a tattare da ita, dik wani ciwo da take ji gaɓoɓɓinta suna yi mata sai ta ji dik sun ware, cike da murna ta ce.
"Mai makaranta sai ya san sunan kowa idan za'a shigar da shi makaranta ko?".
Kai ya gyaɗa mata alamar e haka ya ce, yana nan with his full confidence, shi yana jin ya kureta ai.
"And dik wanda zai shiga makaranta dole mai makaranta yasan da zamansa ko?".
Nan ma jinjina mata kai ya yi idanunsa a kan face ɗinta.
"Good.......... Na ji daɗin wannan bayanai ɗin naka, a nan duniya ma mutun ɗan adam ma dan ya gina makaranta sai ya san da zaman kowa wanda yake cikin makarantar, sannan sai ya san sunan kowa kafin ya shiga makarantar bare kuma Allah da ya halicci dikkan duniya da abin da yake cikinta?".
Da ɗan mamaki ya ce. "Me kike nufi kenan, ban gane ba".
"Girma na Ubangiji ya wuci tinaninka Ronnie, ina san ka sani cewa dai'dai da kwayar zarra a duniyar nan Allah ya san da zamansa, malaman makaranta sai an kawo masu yara ake faɗa masu sunansu har su rike sunan su san da yaran ko?".
Jinjina mata kai ya yi alamar e.
"To shi Ubangiji shi ne da kansa yake sanyawa bawa suna! Kowani yaro da kake gani da sunansa yake zuwa duniya, iyaye kawai suna isar da sakon sunan ne ga al'umma cewa ga sunan ɗansu".
"Ban gane ba, ki mun bayani yadda zan gane"......... Yadda ya yi maganar da alama ransa ya ɗan sosu kaɗan.
Tuni ta ji karfi ya zo mata, an taɓo addininta ana bukatar hujoji, ita ai dama abin da take so kenan, su taɓota su ce ta kawo hujoji, dan dole kuma su gamsu, dan kafa hujoji take yi da malamullah wato Alqur'ani mai girma, maganar Allah wasa ce? Idan ka samu mutum mai daɗin baki ya yi maka magana ma ji zaka yi tamkar baka duniya bare kuma ace maganar Allah? Ai ta wuci tinanin mutum.
Jingina bayanta da jikin headboard na gadon ta yi, cike da kwarin gwiwa ta fara magana kamar haka.
"A cikin Alƙur'ani da hadisi. Allah ya bayyana cewa yana sane da dukkan halittunsa tun kafin su zo duniya. Wannan ya fito fili a cikin Suratul Maryam, Sura ta 19 a cikin Alqur'ani, Aya ta 7, lokacin da Allah ya yi magana game da annabcin da haihuwar Annabi Yahaya A.S".
"Yaa Zakariyyaa innaa nubashshiruka bighulaaminismuhuu Yahyaa lam naj'al lahoo min qablu samiyyaa."................
"Ya Zakariyya! Lalle ne, ina yi maka bushara da wani yaro, sunansa Yahaya, ban taɓa sanya wa wani suna kamar shi ba a gabani wato kafin zuwan Annabi yahaya kenan, ba'a taɓa samun mai suna irin nasa ba, shi ne farkon sunan yaya a duniya, zaka iya duba wannan sura da wannan aya dan ka gani"
"A wannan aya, Allah ya bayyana cewa ya ba wa Annabi Yahaya suna tun kafin a haife shi. Wannan yana nuna cewa Allah yana sane da mutum, ya kuma ƙaddara duk abin da zai faru da shi, har da sunansa".
"Haka kuma, a cikin Suratul A’araf Sura ta 7 a cikin Alqur'ani mai girma, Aya ta 172 da 173, Allah ya ambaci cewa ya ɗauki alkawari da ƴaƴan Adam tun lokacin da suke cikin tsatson iyayensu, yana tabbatar da cewa ya san dukkan halittunsa tun farkon wanzuwarsu. Duk wannan na nuni cewa sunan mutum, tare da ƙaddararsa, yana cikin ilimin Allah tun kafin haihuwarsa".
Tsit Ronnie ya nitsu yana sauraronta, shi ma fa yanzu yana san ya ji tana gaya mashi girma da niimomi haɗe da isar Ubangiji, hakan na sanyaya mashi rai.
Cigaba ta yi da bashi hujoji, dan tana ganin kamar iya haka basu wadace shi ba, bari ta kara mashi ko kaɗan ne dan narkar mashi da zuciya sosai!.
"Cikin hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama wanda Abdullah ibn Mas'ud R.A ya ruwaito shi, Manzon Allah (SAW) ya ce. Lallai hakika kowane ɗayanku ana haɗa halittarsa cikin mahaifar mahaifiyarsa tsawon kwanaki arba'in (a matsayin maniyyi kenan) sannan ya zama ɗigon jini har tsawon kwanaki arba'in, sannan ya zama tsoka tsawon kwanaki arba'in, sai mala'ika ya zo ya hura masa rai, to a wannan gaɓar ne ake rubuta masa abubuwa guda huɗu. Na farko arzikinsa, ajalinsa, aikinsa, da kuma ko zai kasance mai farinciki ko mai baƙinciki, dan haka kada wani bawa ya takura kansa a kan abin duniya, already Ubangiji ya rubuta arzikinsa tin kafin zuwansa duniya"
"Ingantaccen hadisi ne cikin Sahihul al-Bukhari, Hadisi mai lamba 3208. Sai Sahihul Muslim, Hadisi mai lamba 2643 dik zaka iya nemo littafan ka duba lambobin dan ka tabbatar!!".
"Wannan hadisi ya nuna cewa Allah yana sane da mutum da duk abin da zai kasance tun kafin a haife shi, ciki har da ƙaddararsa da sunansa. Wannan shi ne alamar cewa Allah mai ilimi ne da kuma iko akan dukkan halitta, dan haka Allah yasan komai dake duniya, in takaice maka ma babu wani abin da ya isa ya motsa ba tare da izinin Allah ba, dan haka dik abin da kake yi a duniya Mala'iku suna nan suna rubuta maka, so akwai ranar da zaka girbi sakamako kamar yadda ka aikata ko in ce ka shuka"..
(Kai my people's ku tafawa Sweetie!! wani irin fata zaku yi wa Sweetie tamu ta amana? Kun ji wata iriyar basira na misali da ta yi wa Ronnie da makarantarsu kuwa?. To dik wanda ya karanta littafina ya samu karin ilimi da darusa ina rokon da ya ɗaga hannu ya mun addu'a ni da iyayena da ƴan uwana, addu'a kowacce iriyace in dai ta alkhairi ce a gareni wlh ina so, ba abin da zaku biyani da shi face wannan addu'ar, ku mun ita ni da iyayena da ƴan uwana, Allah ya bar kauna 💘)
Dik jikin Ronnie ta yi la'asar kai har ma da mangariba, kamar ba shi ba, tabbas ya yarda da maganganunta, musamman ma yadda ta kafa mashi hujoji da malaman makaranta ma, tabbas su da suke mutane kamar kowa ma har suna iya sanin wanda ya shiga makarantarsu da sunansa, su rubuta mashi jarabawa su kuma bashi sakamako bare wanda ya halicci dikkan duniya?! Tabbas babban kuskure ne ma bawa ya yi tinanin Ubangiji baya ganinsa a kan dik abin da yake yi, kuskure ne bawa ya yi tinanin ba za'a je lahira ayi hisabi ba!!.
Sau uku Sweetie tana ambatar sunan Ronnie, amma ina bai jita ba, ya afka duniyar tinanin maganganunta. Har sai da ta kai hannu ta ɗan taɓa shi, a ɗan zabure ya sauke ajiyar zuciya.
Lafiya Ronnie?"........... Ta faɗa kamar bata san tinanin me yake yi ba.
"Sweetie gaskiya na ji kamar na yarda da addininki........." ......... To fah, babbar magana.
Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Na tabbata da zaka ji ko ka daure ka koya daga addinina, to da hakika zaka gasgata cewa babu wani addini da ya kaishi, ka daure ka ji kuma ka koya ka ji?".
Yau Black Tiger ya shiga fada, ana can anata hidimar shigarsa fada su kuma suna nan, mutane sai shiɗewa suke yi na ganin bayyanarsa, shi kam Ronnie bashi da labari.
Kuma hakan ba karamar nasara bace a garesu, dan kuwa wlh da Black Tiger yana nan yana jinsu ba zai taɓa bari Sweetie ta yi waɗan nan jawabin dangane da Addinin Musulunci har ta kawowa Ronnie hujoji cikin hikima wanda zasu ratsa shi har ya ce ya fara yarda da addininta ba, da tuni zai katse masu hiran koma ya rabasu na har abada, kunga kuwa shigarsa fada mu gaba ta kaimu, ko ba komai al'umma dayawa sun samu karin ilimi a kan addininmu.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
"Sweetie na ji kuma na yarda da tashin alkiyama, amma ki faɗa mun menene alamominta?".................. Cewar Ronnie.
Haba wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, hamdala ta yi wa Allah da Ronnie ya fara yi mata irin waɗan nan tambayoyi, Allah abin godiya, da ta samu nasara Ronnie ya musulunta tana da tabbacin dayawa zasu musulunta ta dalilinsa, sai dai suna da babban kalubale da barazana a gabansu wanda sai ta tsaya da addu'a matuƙa.
"Ronnie alamomin tashin alkiyama suna da yawa, akwai ƙananan alamomi akwai kuma manya manya wanne kake san in fara faɗa maka?".
Kai tsaye ya amsa da. "Dikka nike so"........... Ya yi maganar cike da matsuwar san jin wannan bayani, yana san bayananta, saboda komai dallah dallah take yi kuma a nitse yadda komai jahilci da toshewar ƙwaƙwalwar mutun zai fahimceta.
Gyaran murya ta yi haɗe da kara gyara zamanta kafin ta fara bayanai kamar haka.
"Alamomin tashin alkiyama sun kasu kashi biyu. Alamomin kanana wato al-alamat al-sughra kenan, sai kuma alamomin manya wato al-alamat al-kubra, gasu kamar haka".
"Alamomin Kanana sun haɗa da. Mutane za su ga lokaci yana tafiya da sauri, da rana ya yi dare zata yi, kamar kyaftawa da Bismillah, alama ta farko kenan. Ta biyu. Rashin sanin addini. Mutane za su bar koyon addini, ilimin shari’a zai ragu, zasu koma san jin gulmace gulmace da karairayi haɗe da abin da bai shafi addini ba. Na uku. Yawaitar zunubi. Zina, shaye-shaye, da rashin kunya, rashin kamun kai, rashin darana iyaye da magabata, a ci mutuncin malamai da masu faɗar Allah, dik wannan za su yawaita a doron ƙasa. Na huɗu Yawaitar yaƙe-yaƙe, jama'a zasu yi ta yakar junansu, su yi ta kashe kawunansu ba tare da wata dalili ba, su kansu idan ka tambayi meyasa suke kashe juna ba zasu faɗe shi ba!. Na biyan. Matsalolin shugabanci. Shugabannin azzalumai zasu yawaita, zai zamana shuwagabannin basa tsoron Allah, basu da tausayi, suna aikata ɓarna, suna zaluntar waɗan da suke mulka, suna take hakkokin bayin Allah da shi kansa Allahn ba tare da suna nadama ko kwayar zarra ba. Na shida. Kuma na karshe a ƙananan alamumi shi ne. Zama ababen al’ajabi. Mutane za su gina manyan gine-gine suna takama da shi, su rinƙa gasa a gine gine masu girma da tsawo".
My people's a nan zan ɗan yi tsokaci, a cikin waɗan nan alamomi na tashin alkiyama ku faɗa mun wanenen bai bayyana ba?!! Dik wanda ya yi imani da Allah da Manzonsa yakamata yasan da cewa duniya ta zo karshe, jama'a har yanzu muna da sauran dama ta tuba, mu tuba mu koma ga Allah dan mu rabauta, wlh babu in da duniya zata kai mutum face halaka, mu yawaita sadaka da istigifari, mu yawaita jin kan na kasa da mu, kada mu rinƙa duba na sama da mu, mu rinƙa duba na ƙasa ne hakan zai sa mu kyautata lahiranmu, mu guji cin amana juna da zalintar mutane!.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
A dai'dai wannan gaɓa Ronnie jikinsa ta sanyaya, saboda yadda Sweetie ta ce jama'a zasu rinƙa kashe junansu babu gaira babu dalili sai ya ji tamkar da mulkinsu take yi, tabbas Black Tiger yana kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba, kuma yasan da hakan yake kara goyawa yayan nasa baya, gaskiya wannan abin ya yi matuƙar taɓa mashi zuciya, yasan dai ita Sweetie bata san ya suke gudanar da mulkinsu ba, dan haka ba dan zalincinsu ta yi maganar shuwagabannin marasa adalci ba, gaskiya ne kawai zallarta.
Ganin alamar nadama da tashin hankali a saman face ɗinsa ne yasa Sweetie ta kara samun kwarin gwiwa, ta cigaba da cewa.
"Alamomin Manya na tashin alkiyama sun haɗa da Bayyanar Imam Mahdi. Bayyanar Dajjal. Saukar Annabi Isa (A.S). Bayyanar dabba mai magana da mutane wato Dabbat al-Ardh. Fitowar Yajuj wa Majuj. Fitowar rana daga yamma. Babban girgizar ƙasa. A cikin Al-Qur'ani mai girma Allah ya yi Magana Kan tashin Alkyiyama da alamominta a wurare daban-daban, amma ga wasu daga ciki.
"A cikin Suratul Zalzalah surata 99 a cikin Alqur'ani kenan, aya ta 1 zuwa ta 8. Allah ya bayyana girgizar ƙasa ta tashin alkiyama. Iza zulzulatil ardu zilzalaha, wato Idan ƙasa ta yi girgiza girgizawarta mai tsanani".
Izazullilatil ardu zilzalaha, wato Idan ƙasa ta yi girgiza girgizawarta mai tsanani.
Sai kuma cikin Suratul Qiyamah, surata 75, aya ta 1 zuwa 40. Wannan sura tana magana game da tsanani da al’amuran tashin alkiyama. Sai Suratul Takwir sura ta 81 aya ta 1 zuwa ta 14, An bayyana canje-canjen duniya yayin tashin alkiyama, Idan rana ta birkice, kuma taurari suka fadi"................ WAYYO ALLAH KA HANAMU GANIN WANNAN TASHIN HANKALI, MY PEOPLE'S KU CE AMIN, KU KANKU BAKU JI FAƊUWAR GABA DA AKA CE IDAN RANA TA BIRKICE TAURARI SUKA FAƊI BA?..😥💔
"Sai cikin Suratul Inshiqaq surata 84 aya ta 1 zuwa ta 6. Allah ya bayyana yadda duniya za ta karye"........... Ya Allah kasa mu cika da imani.
Ronnie sai da ya ji gabansa ta yi wani irin faɗuwa, kirjinsa ne ta bada dukan uku uku, ya ji maganganu masu girman gaske daga bakin yarinya ƙanƙanuwa mai ƙananun shekaru.
Shiru ya yi ya kasa magana tamkar wanda ruwa ya cinye shi, har sai da Sweetie ta kai hannunta ta taɓa shi.
Firgita ya yi tare da miƙewa tsaye. "Ronnie lafiya kuwa?".
Girgiza mata kai ya yi ba tare da iya furta word ba, Allah sarki nan take zuciyarsa ta karaya, ta yi matukar laushi, ya ji girman Allah bawan Allah, a take ya ji ya aminta da ita ɗari bisa ɗari, ya kuma yarda da addininta, tabbas adininta shi ne gaskiya, tabbas Ubangijin da take ambata shi ne na gaskiya.
A cikin wannan hali da suke master Devil ya yi knocking na kofar. Kallonta a kan kofa Sweetie ta kai shi kuma Ronnie ya kai kallonsa saman tv dake kunne.
Ganin master ne a bakin kofar yasa ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya matso dab da Sweetie, jikinsa dik ya mutu, kamar zai rungumeta, ya fita tsawo nesa ba kusa ba.
Dan haka sai ya rankwafo kanta, kamar zai sumbaci kumatunta, sai kuma ya mayar da bakinsa saitin kunnenta. Har ta zaro idanu tana jiran jin saukar kyawawan lips ɗinsa a saman bakinta, sai kuma ta ji yana yi mata raɗa a kunne.
Wani irin ƙayatatcen murmushi ta saki, da alama ta ji daɗin abin da yake faɗa mata, cikin sanyin murya ta ce.
"Amma dai sai............"
Katseta ya yi ta hanyar zuro hannunsa ta saman shoulder ɗinta ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru. Ba musu ta haɗiye maganar ta cigaba da sauraron abin da yake faɗa mata.
Ya ɗauki a kallah 2 mins yana yi mata raɗa kafin daga bisa ya furta. "Anjuma da daddare zaki kara mun bayani a kan Annbi Isa da kuma Imam Madih? Ina san jin tarihinsu sosai, ina tsananin san Annabi Isa sosai".
Jinjina mashi kai ta yi alamar to ba tare da ta yi magana ba.
Shiru ya yi yana kallan gurun wuyarta, ya dakata da yin dik wata magana ya mace da kallanta. Jin ya yi shiru baya magana, kuma bai ɗago kansa daga gareta ba, sai ta ɗan juyo domin ta kalli me yake yi.
Tana juyowa fuskokinsu ya haɗe waje guda, bai ɓata lokaci wajen manna mata sumbata a ɗan bakinta yana sakar mata cool murmushi ba.
Gabanta ne ya faɗi sosai lokacin da ta ji saukar lips ɗinsa a saman tata, lokaci guda ta ji wani abu ya tsoki zuciyarta, bata san time da ta sakar mashi murmushi ba, kun san fa murmushin Ronnie idan ya yi wa mutun ko baka so sai ka mayar mashi da martani, sai ka murmusa kai ma.
Ƙasa ƙasa cikin salo mai jan hankali kamar mai raɗa ya