Showing 177001 words to 180000 words out of 403653 words

Chapter 60 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

137

girma, dik wasu manya masu ji da kansu a faɗin Dubai sun hallara a cikin wannan taron. Abbie yana zaune tare da Ummie a saman wani haɗaɗɗun kujeru da aka tanadawa familyn King Badeen, su Dr Raj dik suna gefensu except Ramish da yake saman stage yana speech cikin harshen larabci.

Sharifat tana zaune a tare da Leesharh waje guda, sun yi shiga iri ɗaya, bakin Leesharh ya ɗan kumbura haka zalika goshinta ma ya ɗan kumbura, tana sanye da face mask a face ɗinta, sannan yi rolling veil ɗinga har ya rufe mata ciwon nata da aka sanya mata white bandeji a wajen.

Waye ya yi wa Leesharh dressing na ciwukanta? Ya aka yi hakan ta faru? Me Abbie da Yah Ramish suke shiryawa? Dik kada ku damu zan warware maku komai, ku dai mu je zuwa.

Miƙewa Leesharh ta yi, cikin sanyin murya ta ce da Sharifat zata je toilet tana zuwa. Da okey Sharifat ta amsa mata, sannan ta ɗaura mata da cewa ta kula. Jinjina kai kawai ta yi.

Hall ɗin cike yake da manya manyan jami'an tsaron, securitys ta ko'ina, tsaro ya yawaita sosai a wajen ne saboda Abbie da yake matsayin ministan tsaron sannan ga manyan jami'ai irinsu Ramish a wajen.

Wani keɓaɓɓen waje Leesharh ta je ta samu domin amsa call ɗin masu nikaf da suke ta kiranta tun ɗazun, dama ba wani toilet da zata je, call take san ɗagawa. Filin da ta je a cikin wajen taron ne, amma ta baya wajen wasu ɗakuna da babu kafar mutane a wajen.

Ciro wayarta ta yi daga cikin hand back dake hannunta kalar abayar jikinta wato maroon color, ta yi kyau sosai. Tana ƙoƙarin yin picking na call ɗin ta tsinkayo muryar mutane daga ɗaya daga cikin ɗakin dake bayanta suna magana kasa kasa. Fasa ɗaukar kiran ta yi a in da ta ƙasa kunne take sauraransu.

Zaro idanu sosai ta yi a lokacin da ta ji suna shirya shirin yadda zasu harbi Ramish, dik yadda aka yi sun riga masu taron shiga wannan hall ɗin, sosai Leesharh ta yi mamakin jin maganganunsu, tasan dai a yadda wannan hall ɗin yake wlh idan ba da wani na jikin family ba babu wanda ya isa ya shigo nan wajen, saboda tsaron da aka zuba ko tsuntsuwa bata isa ta gifta a wajen ba ba tare da an harbeta ba, to ta ina waɗan nan mutane suka shigo wajen?.

Yanzu ta kara tabbatarwa tabbas da sa hannun na gida a shirin kashe Ramish, tabbas dole da sa hannun na gida, to waye? Ta jefawa kanta wannan tambayar.

Taba tsaka da tinani ta ji ana ƙoƙarin buɗe kofar a fito. A a miliyan ta watsa ta bar wajen ta yi baya, a bayan wasu curtains dake wajen wasu windows kusa da wajen ta ɓuya, a hankali ta ɗan buɗe curtains ɗin tana leƙo kanta dan taga su wanene zasu fito daga cikin ɗakin, daga in da take tana iya gano kofar ɗakin.

Wasu maza ne su biyu suka fito cikin shigar three-piece suit launin ash mai haske, fuskokinsu dik sanye da face mask sannan hannayensu rike da sillent pistol gun, kafafunsu na cikin cover shoes na maza, sun yi shiga irin dai shigar dik wasu manyan baki da suka halacci wannan yaran, sun saje da mutane kenan.

Mamaki ne ya kamata ganin zanen dake wuyarsu na scorpio, shiru ta ɗan yi taba tinanin a in da ta taɓa ganin irin wannan zane a gidan Abbie, tabbas akwai mai irin wannan zane a gidan Abbie, to waye?.

Tana tsaka da tinani sai ta ga sun sa kai sun nufi wajen taron. A hankali ta lallaɓa ta fito ta rufa masu baya, tana tafiya kirjinta na dukan uku uku, a dai'dai wannan lokacin ƙwaƙwalwarta ya tunano mata tabbas wanda ya kawo mata hari daren jiya ma yana da wannan zane a wuya! And bayan shi akwai wani mai irin wannan zanen a gidan.

Cigaba da bin bayansu ta yi ƙwaƙwalwarta yana tinano mata abubuwa kala kala da ya danganci abin zargi a gidan Abbie. Tabbas Hajiya two seater ma tana da wannan zanen, hakan na nuni da zanen na kungiyarsu ce kenan? Ko dai yaya?. Sake tunawa ta yi Ummie ta taɓa yin wani bakon matashi mai irin wannan zanen a wuya, babbar magana.

Binsu ta yi har zuwa cikin hall ɗin, tana ganinsu suka koma can baya wajen da ba mutane sosai, a nan suka zauna. Jikinta na rawa ta haura saman stage da Ramish yake, dik da tana shakkarsa tana tsoronsa amma ba zata iya bari a kasheshi ba, dole ta je ta sanar da shi, da sauri ta nufi in da yake.

Sai dai bata kai ga isa wajen ba wasu jiga jigan jami'ai guda biyu suka tareta, dama suna saman stage ɗin suna tsaron Ramish ɗin ta both sides ɗinsa dikka, so ganinta yasa suka bar wajen suka je suka tareta.

Sai maganarsa yake yi cikin kwanciyar hankali ba tare da ya kalli in da take ba, yana ji dai jami'ansa suka ce ta koma ƙasa ba zata samu damar yin magana da shi ba, ita kuwa saboda karfin hali sai ta ce masu ita dole tana san yin magana da shi yanzu, tana yi masu magana tana kallan waɗan can mutane su biyun.

Hankalin jama'a ne gabaɗaya ya koma kanta, ta jajirce wai ba zata bar wajen ba, kuma tsoronsu kamar ya kasheta, amma ta ce ba zata bar nan ba har sai sun barta ta isa garesa. Zaro idanu Sharifat ta yi tana kallanta, shi ma Abbie kallanta kawai yake yi.

Ganin hankalin jama'a dik ya koma kanta yasa waɗan can mutane suka ga sun samu damar harbin Ramish a yanzu, dan haka sai suka ciro bindigarsu cikin dabara, ga face mask a face ɗinsu saboda sun san akwai cameras a wajen.

Saita saitin zuciyar Ramish suka yi, Leesharh tana ganin sun saita zasu yi harbi ta yi kukan kura da gudu ta keta tsakiyar jami'an, cikin zafa suka rufa mata baya dan su kamata, ita kuwa tana zuwa ta daddage da ita karfinta ta ture Ramish daga wajen da yake tsaye bullet ɗin da wadan can suka harbo ya sameta a kirjinta pass. Shi kuwa Ramish gefe ya yi ya faɗi kasa saboda bai wani kame jikinsa ba a lokacin da yake tsaye a wajen.

A take Leesharh ta zube ƙasa jini na malala a kamar hanyar ruwa. A zabure Abbie ya miƙe tsaye, jama'ar dake wajen ne suka kiɗime. Cikin abin da bai gaza second talatin ba jami'ai suka kewaye saman stage ɗin, su kuwa waɗan can mutane biyun jami'ai suka nufesu da nufin su kamasu, sai dai me, basu kai ga isa wajen ba mutanen suka miƙe tsaye tare da ɓalle botirin suit ɗin jikinsu, nan take rigar bomb ya bayyana a jikinsu.

Cike da barazana suka ce dik wanda ya motsa to zasu tashi wannan waje, so basu damu da rayuwarsu ba, a shirye suke da su mutu, dan haka kowa ya nitsu a sauraresu a kuma basu abin da suke so ko kuma kowa ya mutu.

To ni dai ba za'ayi wannan mace macen da ni ba, bari na haɗa kayana na je zuwa gidan baby da Ammo in sha maltina mai sanyi a can ko na huce takaicin mutuwar Leesharh.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





🔥🔥🔥BABYN BABY🔥🔥🔥

Safiyar yau dik jikinta a mace ta farka daga barci, kamar wadda aka jibga gaɓɓanta gabaɗaya ciwo suke yi mata. Da kyar ma ta iya tashi daga barci, sai da Ammo ta matsa mata, kuma tana da Exams in baku manta ba.

Saukowa kasan bed ɗin ta yi ta nufi toilet tana hararar Ammo da ta tasheta, ita a dole ranta ya ɓaci.
Wanka ta shiga ta yi, sannan ta fito a gurguje ta hau shiryawa, a lokacin har 7:30 ya yi. Sai da ta kammala shiryawa tsab, sannan ta dawo bakin bed ɗinta ta zauna. Sai tashin kamshi take yi.

Wayarta ta ɗauko tare da kunna wutar screen ɗin, a gaggauce ta cire password ɗin da nufin ta yi kira, sai kuma ta ga massage da aka turo mata tin karfe 5 na asuba. Baby shi ne sunan da aka yi saving number wanda ya turo wannan sakon. Lokacin guda wani ƙayataccen murmushi ya kubce mata, a hankali ta danna kan massage ɗin ta buɗe cike da matsuwar san ganin me aka rubuta.

"Good morning, my love. Waking up every day with the thought of you in my heart is a blessing beyond words. You are the light that brightens my world, the melody that soothes my soul, and the dream I never want to wake up from. This morning, I just want to remind you how deeply I adore you. Your smile is my sunshine, your voice is my favorite song, and your love is the air I breathe. May your day be as beautiful as your heart, as radiant as your smile, and as peaceful as your embrace. I love you more than words can say. Have a wonderful morning, my queen!". A karshen sakon sai ya sanya mata emojin heart da na kiss guda bibbiyu. Shi ne abin da saƙon ya ƙunsa.

Tin da ta fara karanta saƙon nan take sakin cool murmushi, wani irin sanyi ta ji yana ratsa zuciyarta, kaunarsa yasa har ta mance da abin da ya faru daren jiya, nan take kewarsa ya kamata. Danna kan reply ta yi domin ta mayar mashi da martani. Rubuta sako kamar haka ta farayi tana yi tana murmushi mai ƙayatar da mai kallanta.

"Good morning, my baby. Waking up to your sweet words fills my heart with warmth and joy. You are my sunshine, my peace, and the love that completes me. Every moment with you feels like a beautiful dream I never want to end. Knowing that I have your love makes my world brighter and my heart lighter. I cherish you more than words can express, and I can't wait for the day when I can wake up beside you every morning. I love you endlessly. Have a wonderful day, my baby!" A karshen rubutun ita ma sai ta sanya emojin heart dana kiss guda bibbiyu kamar nasa.

Kewarsa da zumuɗin daɗaɗan kalamansa ya ja ta rubuta mashi wannan reply ɗin ba tare da ya mayar da hankalinta a kan kalaman da ta zuba, sai ya yi mata kamar sarauyinta zata rubutawa, bata ma sake bin sakon ta karanta ba kawai ta tura mashi.

Tana turawa ko minti ɗaya ba'ayi ba sai ga call ɗinsa ya biyo baya, ta yunkura zata tashi kenan sai ga kiran nasa ya shigo. Cike da zumuɗi ta koma ta zauna tare da yin picking na call ɗin.

Kara wayar a kunnenta ta yi, cikin sanyin murya ta ce Hello baby. Daga cikin wayar ta ji saukar ajiyar zuciyarsa, sai da ya ɗan yi gyaran murya saboda ɗan saisaita voice ɗinsa da ya sarkafe saboda daɗin kalamanta kafin ya ce.

"Sai yanzu kika tash daga barci ko?". Kai ta gyaɗa kamar tana a gabansa, sannan ta bisa da e.
"Menene ya dawo mun dake haka ne baki tashi da wuri?".

Shiru ta ɗan yi ta rasa abin faɗe. "Kin shirya tafiya school ne?". Ya katse mata shirun. Kai ta gyaɗa tana haɗawa da e ta shirya.

"Ina zuwa yanzu in kai ki, wait for me"....... Mamaki ne ya kamata, bai taɓa kaita school da kansa ba, to why yau ya zaɓi kaita da kansa? Ta jefawa kanta tambayar, tana can tana tunani bata san time da ya katse kiran bama, sai kawai ta ji shiru.

Miƙewa ta yi ta fito parlon ɗauke da school back ɗinta a hannunta. Already an shirya mata breakfast ɗinta da komai da komai, so tana fitowa ta haye saman table ta fara cin abincinta cikin nitsuwa. Bayan ta kammala ta goge bakinta da tissue, sannan ta nufi bedroom ɗin Ammo dan su ɗan yi hira kafin ya zo.

Bata kai ga shiga ba ta tsinkayo kamshin perfume ɗinsa alamar ya nufo parlourn kenan. Da ƴar gudunta ta juyo ta isa bakin kofa ta laɓe tana ƙunshe dariya. Yana sako kai unexpext ta saka ƙara wai dan ta bashi tsoro.

Ko kaɗan bai tsorata ba, sai ma binta da kallan mamaki ya yi. Turɓune fuska ta yi shagwaɓar ta motsa, kamar zata yi kuka ta ce.

"Baby, why didn’t you get scared? Do I look like someone who wouldn’t scare you? Is that why you refused to be scared? Well, you’ve disappointed me".
She finished her words and turned to head toward Ammo’s room.

Quickly, he grabbed her hand and said, "You’re just too dramatic. Alright, I’m sorry. Next time you scare me, I’ll act scared. But for now, time is up, and you’ll be late for school. There’s no time for games. Just go and inform Ammo that we’re leaving".
He finished his statement as he released her hand.

"Do you promise that next time if I scare you, you’ll act scared?". She asked, pouting.

He nodded in agreement. Aminta da hakan ta yi, sannan ta nufi room ɗin Ammo. Da kallo ya bita yana jin wani irin kifiya na santa yana kara cakar kahon zuciyarsa.

Yana tsaye a wajen har suka fito a tare da Ammo. Cikin mutunta juna suka gaisa shi da Ammo, sannan ya riko hannunta yana yi wa Ammo sallama suka fice daga gidan.

Su kansu drivers da suke kaita school sun yi mamakin ganin ogan nasu zai kaita school da kansa yau, sai dai basu ce komai ba suka bisu da fatan alkhairi. Gidan gaba na motarsa ta shiga, ya shiga mazaunin driver, idanunsa a kanta ya tada motar, da alama fa da gaske ta manta abin da ya faru daren jiya.

Da ɗan madaidaicin gudu ya ja motar suka nufi waje. Shiru ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar tana tinanin Exams da take da shi, bata ankara ba sai ji ta yi ya kashe motar.

Da sauri ta ɗago kanta ta kalli hanya, tabbas basu iso school ba, bakin wani katafaren super market suka tsaya. Dawo da kallanta a kansa ta yi. Ita yake kallan shi ma, ta buɗi baki zata yi magana ya rigata da cewa. "Wait for me am coming". Ya kai karshen maganar tare da buɗe kofar motar zai fita.

Da sauri ta riko hannunsa, hakan yasa ya juyo gareta. "Baby ka saya mun chocolate ga ji? Kullum idan na ce ka saya mun baya saya mun sai ka ce cikina zai yi ciwo, ba zan sha dayawa bafa".

Lips ɗinta kawai ya zubawa idanu yana kallan yadda take magana, bai san ko da ya furta. "Ni da kayana amma am mun shamaki da shi". Bai san ya faɗi hakan ba sai da ya ga ta zaro mashi idanu, nan ne ya fara tinanin wai shin me ma ya faɗa ne?. Gudun kada ta jefa mashi wata tambayar yasa ya yi saurin janye hannunsa daga riƙon da ta yi mashi ya fice waje.
Yana ji tana ambatar sunansa yaki dakatawa, dan ya yi suɓul da baka. Turo baki ta yi a fili ta ce na yi fushi da kai, ba zan sake yi maka magana ba.

Mai da kanta jikin kujerar ta yi ya kwanta tana turɓune fuska. Good 20 mins ya ɗauka a cikin wajen kafin ya fito, tana ganin ya doso motar ta kara turɓune fuska tana harararsa.

Bayan mota ya zo ya buɗewa yaran super market ɗin suka jibge mashi niki nikin kayan da ya saya, sannan ya dawo ya shiga gidan gaba. Kunna motar ya yi da gudun gaske suka nufi school, dan ta yi latti. Dik bayan minti sai ya juyo ya kalleta, tabbas ya fahimci fushi take yi da shi, amma bai kulata ba saboda saurin da suke yi.

Bai dakata a ko'ina ba sai a cikin katafaren parking space na school ɗinsu, yana yin parking ya sanya hannu a gidan baya ya ɗauki ƙaramin lada daga cikin shopping da ya yi ya miƙa mata. Kin karɓa ta yi a in da ta sanya hannu zata buɗe kofar motar ta fita, ita dai ta yi fushi da shi.

Zuba mata ido ya yi yana kallanta har ta buɗe kofar ta fita, bai hanata ba kuma bai yi magana ba, cikin nitsuwa ta fara takawa ta nufi barin parking space ɗin, ko kyafta idanu daga kanta ta gagara yi, kallanta kawai yake yi.

Sai da ta ɗan yi nisa, sai kuma ta dakata cak da tafiyar tata, da sauri ta juyo garesa, ganin ita yake kallo yasa ta yi saurin dawowa garesa. Yana dai kallanta bai motsa ba, ta side ɗin da yake ta zo ta buɗe kofar motar tana huci irin na shagwaɓa.

A saman laps ɗinsa ta zauna, hannu tasa ta ja dogon hancinsa da karfi har sai da ya furta wash, ƙara ja ta yi tana faɗin. "Shi ne ba zaka rarrasheni ba, kuma kasan na yi fushi, amma shi ne kake kallona zan tafi baka rarrasheni ba ko? To ba kai ka ɓata mun rai bane?".

Daga ganin idanunsa zaka fahimci yana cikin yanayi, dik jikinsa a mace, idanunsa sun sauya sun yi ja, sai faman lumshe su yake yi, da kyar ya iya riko hannunta da take ta faman jan dogon hancinsa da shi, can ƙasan maƙoshinsa ya furta.

"Ba zaki iya yin fushi da babynki ba ai, shiyasa na zuba maki idanu ina

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login