Showing 30001 words to 33000 words out of 403653 words

Chapter 11 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

20

akwai tsorata mutum.

Sun ɗauki lokaci a wannan ɗaki, daga karshe uncle Abbas ya buƙaci da ya tsaya ayi ɗaurin aure da shi kafin ya tafi. Da farko yaki yarda, ya ce.

"Daddy zuciyata ba zata iya ɗaukar ganin auren Jannat da ɗan uwana ba, Please ka barni in tafi kawai ko zan samu sauki cikin rai'na, burina kawai in bar kasar nan".

"A'a Rizwan, babu wani abin da zai sami zuciyarka, Allah yana tare da kai, please ka tsaya ayi wannan ɗaurin aure da kai".

Baya iya yi wa daddyn nasa musu, dan haka ya hakura ya tsaya ɗaurin auren, shiyasa a wajen ɗaurin auren kowa ya gansa a wani sake sukuku haka kamar dai wanda baya cikin hayyacinsa, dayawan mutane suna tunanin saboda rashin lafiyan ɗan uwansa ne.

A lokacin da uncle Abbas ya kammala gaya masu yadda aka yi suka mallaki juna, gabaɗayansu hawaye ya gama wanke fuskokinsu, jikinsu ya yi matuƙar sanyi, sun ji sun karaya sosai, tsananin tausayin Rizwan ya mamaye duƙatansu!.

Da kyar Jawad ya iya cewa. "Daddy ina Yah Rizwan ɗin yake yanzu?".

Miƙewa tsaye uncle Abbas ya yi yana faɗin. "Rizwan ya wuce Dubai tun bayan barinsa wajen ɗaurin aure, ina zargin da zazzaɓi a jikinsa ma ya tafi".

A ɗan razane Chuchu ta ce. "Zazzaɓi kuma daddy?".

Kai ya gyaɗa masu tare da nufar hanyar fita dan ya basu waje su ga juna a matsayin ma'aurata yanzu.

Da ido suka bishi har ya fice, kamar abin haɗin baki suka dawo da kallonsu a kan juna a tare, dikkansu fuska jaga jaga da hawaye.

Hawayen farinciki, na tausayin Rizwan da kuma na ƙoƙarin rabasu da akayi.

"Jannat kin ji sadaukarwar da Yah Rizwan ya yi mana ko? Kin ji ƙoƙarin da Auta ta yi a kanmu dan kada a rabamu ko? Ashe ita ta je ta gayawa Yah Rizwan muna san juma?"?

Jinjina mashi kai ta yi tana cigaba da hawaye.

"Miƙo mun wayata bari in kira Yah Rizwan ɗin, in mun gama waya sai ki kira mun Autaa cikin gida".

Allah sarki anata shagalin biki babu wanda ya lura da auta bata a gidan, baki sun yi yawa kowa zai zaci tana ɓangaren ɗan uwansa ne, sai dai kuma, kowa yasan bata rabuwa da Chuchu, so idan aka yi wa Chuchu kallon farko basa tare, aka sake ganinta na biyu basa a tare, a karo na uku dole a tambaya ina take?.

Miƙewa ta yi a hanzarce ta zagaya ta ɗayan gefen bed ɗin ta ɗauko mashi wayar tasa.

Zuwa ta yi gabansa ta miƙa mashi tana faɗin. "Ga shi nan".

A maimakon ya karɓi wayar sai ya janyo hannunta ta faɗa jikinsa. A tare suka sauke sanyayyar ajiyar zuciya. Hannunta dake rike da wayar ya riko, kamar mai raɗa ya ce.

"Wannan flowers ɗin sun yi kyau sosai, wadda ta zana maki ta iya sosai".

A ɗan shagwaɓe ta amsa da. "Ai saboda kai aka yi".

Ɗan karkata kansa kaɗan ya yi tare da ɗan leƙo face ɗinta. "Anya kuwa? Dan Yah Rizwan dai aka yi, kuma nasan sai da aka kai ruwa rana dake kafin ki aminta ayi shi ko?".

Kai ta gyaɗa mashi alamar e.

"Da baki bari anyi maki ba da kin yi mun asarar kyau kenan, kin ga yadda kika yi kyau kuwa?".

Ɗaga kai ta yi suna kallon juna, hawayen fuskarta har ya fara bushewa, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Da gaske na yi kyau?".

Kai ya gyaɗa mata alamar e, yana yi mata wani irin mayen kallo mai wuyar fassaruwa.

"To shikenan yanzu kam tin da kai ne mijina bari in je mama Haulat ta kara gyara mun jikina".

Bai san sadda ya ɗan saki murmushi ba a lokacin da ta yi wannan magana. Ya ji sanyi a ransa har da ajiyar zuciya.

Kamar mai raɗa ya ce. "Da gaske nine mijinki yanzu? Ke mallakina ce kenan?".

Kai ta gyaɗa idanunta sarƙafe cikin nasa babu ko kyaftawa, ko kunyarsa bata ji ba.

Shi ma babu ko kunya ya matso dab da ita kamar zai sumbaci lips ɗinta, har ta zaro mashi idanu tana kallonsa, sai kuma ya karɓi wayarsa dake hannunta ya ɗan ja baya yana kallonta.

Number Rizwan ya shigar dan ya kira, ta kafe da kallonsa kamar nace zan kwace mata shi.

Na'urar ce ta sanar masu da cewa number wayar Rizwan a kashe, sosai ya ji babu daɗi, sai ya ji ya kara karaya, nan take ya kara jin ya shiga damuwa matuƙa.

Ganin ya shiga damuwa yasa ta kai hannu ta ɗan shafa kumatunsa. "Yah Jawad ka yi hakuri nasan yana hanya ne, idan ya sauka zai kunna wayarsa".

Dawo da kallonsa sosai a kanta ya yi, tin da ta fara magana yake kallon lips ɗinta har ta kai aya.

Ɗan rankwafo kanta kaɗan ya yi. "Jannat ina kaunar Yah Rizwan, ba zan iya jure ganinsa a cikin damuwa ba, ban san ya zan yi da rai'na ba".
Cikin tsananin damuwa ya yi maganar.

Hannunsa ta ɗan riko a cikin nata, can kasa cikin kasalalliyar murya ya ce...........

Idan kunga tsayin page ɗinku yana raguwa to rashin comment ɗinku ne sila.🥱




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





Hannunsa ya ɗan riko a cikin nasa, can kasa cikin kasalalliyar murya ya ce. "A'a Jannat, na tabbata damuwa ba zata bari ya kunna wayarsa ba, lallai ina san tafiya Dubai a yau".

Zaro idanunta waje sosai ta yi, kamar zata yi kuka ta ce.
"Dan Allah Yah Jawad ka yi hakuri, babu abin da zai same shi, kuma In Sha Allah anjima yana sauka daga jirgi zamu samu wayarsa a buɗe".

Tana magana tana share mashi hawayen dake bin ƙuncinsa, ya shiga damuwa sosai na jin halin da ɗan uwansa yake a ciki.

Shiru bai sake yin magana ba, dan shi kaɗai yasan kalar raɗaɗin dake a cikin ransa.

==========================💘

Sosai King ya yi mamakin jin busoshin yaki da ake ta famar busawa a cikin kingdom ɗin, sai dai bai tashi hankalinsa ba, saboda shi ɗin dakakken namiji ne wanda babu tsoro ko miskala zarratin a cikin jininsa.

Kai tsaye fada ya nufa domin yasan me yake gudana ake ta buga mashi bososhin yaki har haka.

A nan ya isko commander Zafar da sauran wakilan fada gabaɗaya, cikin takun jarumta ya ƙarisa saman kujerar mulkinsa, tin da ya shigo kuma warriors guda biyu suka take mashi baya har izuwa wajen kujerar tasa.

Miƙewa tsaye daga saman kujerunsu su commander Zafar suka yi domin bashi girma, har sai da ya zauna saman tasa kujerar sannan suma suka zauna.

Dik sun kasa kunne suna jiran umarninsa da abin da zai faɗa. Shi ma idanu ya bisu da shi har na tsawon good 5 mins, kun san halinsa akwai jin kai da izzar sarauta, su kuma suna tsoron fara yin magana hukunci ya hau kansu a kan bai basu iznin ba.

Sai da ya cika ya hantse sannan ya ɗan yi gyaran murya cikin nutsuwa, cike da izza ya fara ƙoƙarin buɗe bakinsa domin ya yi magana.

Wani bujumin warriors ne ya shigo cikin fadan bisa umarnin salama, sanye yake cikin kayansa na mayaka, dik da cikin hular kayan yaki yake zaka iya fahimtar face ɗinsa babu alama sassauci ko annuri.

Shigowarsa ya dakatar da King daga maganar da yake da niyar yi, suka zubawa wanna warriors ɗin idanu.

Takowa ya yi cike da jarumta har izuwa tsakiyar fada, sannan ya ɗan risinar da kai wanda kun san wanna dole ce a gidan sarauta, girmamawa ce ga sarki wanda ya rataya a wuyoyinsu dole!.

Cike da girmamawa ya ce. "Ranka ya daɗe ina neman izinin yin magana".
Muryarsa akwai kaifi a cikinta, maganarsa akwai zarra a cikinta, yanayinsa akwai tsantsar jarumtaka matuƙa, tsayayyen namiji sosai, ga tsawo da cikar halitta matuƙa. Cikin kwararriyar larabcinsa ya yi maganar.

King ya ɗauki almost 3 mins kafin ya ɗan motsa lips ɗinsa, cike da izza ya bashi izinin yin magana.

Ba tare da ɓata lokaci ba wannan warriors ɗin ya kyankyasa mashi cewa akwai baki a wajen babban gate na Kingdom ɗin wanda suke da buƙatar a basu izinin shigowa dan su yi magana da shi.

Nan ma sai da King ya ɗauki ƴan mintoci kafin ya buƙaci sanin wasu irin baki ne?.

Kamar ba mutun ne yane magana ba wanna warriors ɗin ya amsa da. "Ga dikkan alamu wani sarki ne da tawagarsa, bamu da masaniyar daga ina suke, amma ga dikkan alamu a kan hanya suke".

"Sune silar buga waɗan nan busoshin yakin?". King ya jefa mashi tambaya cikin nutsuwarsa.

Cikin dakiya ya amsa da. "Sune ranka ya daɗe".

Kallan commander Zafar King ya yi kafin ya dawo da kallonsa a kan sarkin fada da kuma sarkin gida da suke binsa da kallo.

"Commander ina san sanin su wanene waɗan nan cikin ƙankanin lokaci". Ya kai karshen maganar tare da ɗagawa wanna warriors ɗin hannu alamar shi kuma zai iya tafiya ba tare da King ɗin ya sake waiwayarsa ba.

Cikin zafa ya juya yana taku manyan maza ya nufi waje.
Miƙewa tsaye commander Zafar ya yi tare da ɗan risinar da kai alamar ya karɓi umarni, sannan ya nufi waje, sarkin gida ne ya take mashi baya da kara karfafa ida nufin King.

=========HOORAIN=========💘

Zaune suke cikin wannan small garden in da Auta ta kamasu suna hiranta ranar da daddare, shi da Ansar da Anwar, hannunsa na riƙe da wayar Auta while tasa wayar tana a cikin aljihunsa, ya kurawa wayar kallo babu ko kyaftawa, Ansar da Anwar suna ta hira a kan bikin da ake gudanarwa, ba'a taɓa biki a cikin gidan ba bayan na uncle Abbas da ya zamana shi ne na karshe tsawon shekaru, daga King har uncle Abbas babu wanda ya taɓa aurar da ɗa or ƴa sai yau, shiyasa murnar ta zarce tinanin mai tinani.

Hotonta ya zubawa idanu yana ta kallo, tana tsaye kusa da wasu flowers dake cikin lambun daddynsu, hannunta ɗauke da Felix ɗinta tana shafe lallausan gashin jikinsa, murmushin dake kan fuskarta ya yi matuƙar kara tsatso tsantsar kyan da Allah ya zuba mata, dimples ɗinta dikka sun lotsa, yarinya mai kyau da haiba game da kamala, ga farinjini da sace zuƙatan mutane da murmushi ɗaya kawai!. Tana sanye da alkyabbarta har kasa launin golden and white.

Ya luluƙa duniyar tinanin da shi kaɗai ya barwa kansa sanin me yake tinawa, dik da ba'a iya ganin face ɗinsa alamu sun nuna yana cikin kunci da bakinciki game da damuwa, kwata kwata baya tare da su Anwar.

Nisawa ya yi a lokacin da ya ji saukar hannun Ansar a saman shoulder ɗinsa.

"Mekake tunani ne angon gimbiya?". Cewar Ansar.

Ɗan girgiza kansa kawai ya yi alamar babu komai ba tare da ya yi yunƙurin yin magana ba.

Anwar ne ya ce. "Our Hero ka kwantar da hankalinka, In Sha Allah ba za'a hanaka gimbiya ba, da izinin Allah ita ɗin rabonka ce".

Ansar ne ya amsa da. "Gaskiya ya cika sanyawa kansa pressure dayawa, gimbiya fa ita ta nuna tana sanka, kaga kuwa ina da tabbacin In Sha Allah babu wanda zai yi maka shamaki a tsakaninku, ko King sai ya sarara a wannan al'amari".

Shi dai ko uppan bai da niyar cewa, hasali ma kansa a ƙasa bai da niyar ɗagowa bare asa ran zai yi magana.

"Kai ma dai Ansar ka faɗa, dik ya bi ya takura kansa kamar...........".
Ɗaga mashi hannu Ansar ya yi alamar ya yi shiru, dan ya lura da gaske Hoorain yake a cikin damuwa ba kamar yadda suka saba ganinsa a ɗan siririn damuwa a kan Zunaira ba, yau abin na daban ne, gabaɗaya yanayinsa ya canza, sam baya cikin sukuninsa, yana nan a wani birkice haka.

Ni kuwa nace rai wasa ne? Ka ɗauki ran makiyinka ma ya ka kare da faɗuwar gaba da fargaba bare kuma ka ɗauki ran wadda ta fi kaunarka sama da kowa a duniya?! Ai dole nema ka birkice, bama kaga komai ba tukun nan, sai gaba idan abin ya yi tsamari, soyayya ai ba karya bace, aya sukutum Allah ya saukar saboda soyayya,

A cikin Al-Qur’ani mai girma, Allah ya yi magana a kan soyayya a wurare da dama. Daya daga cikin shahararrun wurare da Allah ya yi magana a kan soyayya shi ne a cikin Suratul Rum, aya ta 21

Wannan aya tana nuna cewa soyayya da tausayi suna daga cikin ni’imomin Allah, kuma an sanya su domin mutane su more zaman lafiya da juna a rayuwar aure, so kunga kuwa soyayya ba karya bace ba kuma abin wasa bace, mukaddari ne daga Allah.

"Hoorain lafiya kake kuwa? Meyake damunka?". Ansar ne ya jefa mashi wanna tambaya.

Sun shiga damuwa matuƙa cikin kankanin lokaci na ganinsa a cikin mawuyacin hali.

Bai amsasu ba, sai ma kara risinar da kansa kasa da ya yi haɗe da kashe hasken screen ɗin wayar tata yana jan dogon numfashi.

Anwar ne da ƙaguwa da san jin me yake damun abokin nasu ya cika mashi ciki ya sake jefa mashi tambayar menene yake damunsa a karo na biyu.

Ɗan siririn tsaki ya ja tare da miƙewa cikin zafa ya nufi barin wajen, dan kwata kwata baya san jin magana a kusa da shi, dik wanda zai yi mashi magana muryar Zunaira yake ji a tattare da shi, koma wannene, hakan ba karamun ɗaga mashi hankali yake kara yi ba.

Da ido suka bishi har ya kurewa ganinsu, a tare suka dawo da kallonsu a kan juna suna mamakin birkicewar da ya yi har haka, basu taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayi ba!.

=========================💘

Cikin ƙanƙanin lokaci commander Zafar ya dawowa King da labarin sarkin Daular Qahtan wato Qahtaniyawa ne ya zo, kunsan manya manyan labarawa sun kasu kabila kashi uku ne, nasan dayawa baku taɓa sanin larabawa mabanbanta bane ko? To gaskiya mabanbanta ne, amma manyan kabilunsu sun kasu kashi uku ne, babbar kabila mafi ɗaukaka a duniya cikin larabawa sune ƙuraishawan Modarawa, kabilun modarawa daga cikin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) ya fito, shiyasa ta kasance ma ɗaukakiyar kabila, daga ƙuraishawan Modarawa sai kuma Qahtan wato Qahtaniyawa, su ne na biyu, sai kuma larabawan kangi, su ne kabilun da suka fi kowanne shahara da ɗaukaka a cikin larabawa.

Sosai King Zuhair ya fusata jin cewa sarkin Daular Qahtaniyawa ne ya ziyarcesu, cikin ɓacin rai haɗe da kakkausan murya ya umarci commander Zafar da a je ya yakesu yanzun nan ba tare da ɗaga kafa ba!.

To me dalili?.

Wanna furuci tasa ta yi dai'dai da shigowar aunty miemie cikin fada, ta dan tsorata jin mahaifin nata yana magana da kakkausar murya haka, dan haka sai ta zama mai risinar da kai game da sanyaya kalamanta da kuma tausasasu a wajen yi mashi magana.

Cikin girmamawa ta tambayesa me yake faruwa a dai'dai lokacin da take zaka saman kujerar kusa da shi!.

Bai so sanar da ita abin da yake faruwa ba saboda sanin halinta da ya yi, amma bashi da biyunta a kaf kingdom of power, da ita suke yin shawara, yana kaunarta ya kuma san ba ta kawo shawarar banza, dan haka sai ya sanar da ita ga abin da yake faruwa.

Shiru ta ɗan yi na ƴan mintuna tana nazari, akwaita da hangen nesa, shiyasa irin su King Zuhair masu saurin fusata suna buƙatar irinta a gefensu dan in sun fusata ta dakatar da su daga ɗaukar hukunci cikin fushi, babu wanda ya fi karfin kuskure da kuma ayi mashi gyara!!.

"Daddyna Allah ya kara maka tsawon rai da tsawon kwana, nasan yardar da ka bani yasa ka sanyani a sahun gaba wajen yin shawara domin mu tantance abin da yake dai'dai da kuma ba dai'dai ba, yardar da ka mun yasa nake jin kaina a matsayin mace zaƙwaƙura mai yin abin da ya dace, dan yardarka ga mutum ba ƙaramin abu bane, sai mutun ya cika mai sifofin kamala zai samu wannan matsayi, ina alfahari da kai kuma ina farincikin kasancewa yar cikinka, bana fatan rana ɗaya da zata zo na saɓa maganarka komai kankantarta, hakika da dikkanin ƴaƴan duniya zasu samu uba irinka to tabbas da kowa ba zai so matsawa kusa da mahaifinsa ko nan da can ba, kai ne bangona kuma farincikina, abin alfaharina sanyin idaniyata ni da ƴan uwana, duniyarmu gabaɗaya, ɓacin ranka dai'dai yake da rugujewar Daular Qahtaniyawa daddyna, meyasa zaka ɓata ranka a kan waɗan da kasan already bayinmu ne?"................. Ta kare maganar haɗe da jefa mashi tambayar tana kallonsa.

Tun da ta fara magana ransa ya fara sanyaya, yana shiga tsananin farinciki a dik lokacin da ƴaƴansa suka furta suna alfahari da shi, farincikinsa ba mai misiltuwa bane, hakan yasa ransa ta wani irin sanyaya sosai.

Fahimtar ya yi farinciki da jin kalamanta yasa ta ɗaura da cewa. "Daddyn yin yaki a halin yanzu da muke cikin nan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, saboda kaga muna da baki daga ƙasashe daban daban, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya rasa rayukansu, ina neman alfarmar da a janye batun yakin nan ayi masu lamauni, nasan kai mai afuwa ne mai kuma tausayin jama'arsa ne".

Sosai su commander Zafar suka ji daɗin furucinta, sun kara ganin girmanta, dama can

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login