Showing 21001 words to 24000 words out of 403653 words

Chapter 8 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

116

jikinta, hakan yasa ta ɗan yi tangal tangal kamar zata faɗi. Wannan tangal tangal da ta yi yasa hannunta ya ɗan motsa, hakan ya haifar da motsawar wannan wuƙa da a yanzu yake ƙarƙashin sarrafawar hasken hannunta.

Kara zaro idanu sosai ta yi tana kallon wanna abin al'ajabi. Da kyar da suɗin goshi ta iya kama kanta bata zube ƙasa ba. Har lokacin iska mai karfin nan dai yana cigaba da kaɗawa a cikin ɗakin, Black Tiger yana cikin wannan iskar, ya zuba mata idanu ne yana kallon gudun ruwanta, amma kuma ya yi matuƙar mamakin karfin irin na magic ɗinta da har ya iya tare wannan wuka da ya turo mata bai huda fatar wuyarta ba.

Idanunta a kan wukar, cikin karyewa da sanyin gaɓɓan jikinta ta yi iya ƙoƙarinta wajen motsa ɗan hannun.

Tana motsa shi ma wanna wuƙa ya motsa, dik in da hasken hannun nata ya bi wanna wuƙa ma yana bi, a hankali ta fara matsar da hannunta daga wuyarta, hakan yasa shi ma wukar ya matsa daga saitin wuyar tata da ya yi.

Abin al'ajabi ya bata matuƙa, sai kuma kamar wata zararriya ta saki murmushi wanda sai da yasa dimple ɗinta bayyana, ko me abin murmushi a wajen?.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin tana da hanyar cetan kanta, fara ƙoƙarin tabbatarwa da kanta hakan ta yi ta hanyar juya hannunta ta in da takeso.
Dik yadda ta juya wukarma sai ya juya ta nan, wani irin dariya ta fashe da shi kamar wata zararriya.

Yi take yi babu kakkautawa idanunta a kan wukar.

========================💔

Lokacin guda kuma ta tsayar da dariyar tata cak, kome ta tuna? Sai kuma idanunta suka ciko da kwallah, a hankali ta furta.

"Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, ya Allah.........."

Bata kai karshen maganar da take son amayarwa ba kenan taga wanna wuƙa ya faɗi a ƙasa, faɗuwarsa ke da wuya ya haifar da wani irin sauti mai ban tsoro, a take guguwar dake ɗakin ta kara karfafa kamar an watsawa aljanu ruwan addu'a yana konasu.

Ba ƙaramin kara razana ta yi ba, da karfi ta furta. "Wayyo Allahna ka kawo mun ɗauki......"

Ai bata gama rufe bakinta ba kofar ɗakin ya ɓalle ya buɗe kansa da kansa. A miliyan ɗari ta kwasa ta nufi waje, ta kasa gane cewa sunan Allah da ta ambata a wajen ya rikita dik wani tsafi dake waje, shiyasa take jin wanna guguwa ta kara karfafa wai dan su kare kansu daga kalamanta shi ne suka kara karfin iko.

Kai tsaye parlourn ƙasa ta nufo tana ihu, bata tsaya electric stair case ɗin ya yi kasa da ita ba ma, da kanta ta tattake shi ta yi ƙasa.

A wanna lokaci ta kasa iya sake ambatar sunan Allah, abin ku da shaiɗan da kuma shirka.

Bayanta Black Tiger ya biyo cikin wanna iska, dan ransa ta kara bakanta na sunan Allah da ta kira ta jijjiga mashi hankulan ruhohin tsafinsa. Ya sha alwashin yau zata gane kurenta.

Wanna iska ne yasa gabaɗaya kofofi da windows ɗin parlourn kasa suka rufe kansu, fara ƙoƙarin kamata Black Tiger ya yi, ihu take kurmawa tana neman hanyar tsira.

A wannan lokacin ne ya riƙiɗa ya zama mutum, da ainahin face ɗinsa ya bayyana, yana sanye da pj a jikinsa.

Like wow, kamar wani kafani, kaman ba mutum ba, ga shi ya juya idanunsa izuwa na magic, sai ya kara riƙiɗewa kamar ba mutum ba, zallar madarar kyau.

Cak ta dakata da neman hanya da take yi, bata yi zaton shi bane da ba zata gudu ba a cewarta, ita da take son ganin face ɗinsa daman! Ai da tsayawa zata yi kome zai faru ya faru.

His first time kasakcewarsa a cikin wanna parlon, bayan ɗakin Ronnie da yake kai ziyara ta hanyar magic bai taɓa fita ko ina ba, yau karo na farko Sweetie ta sanya shi fitowa.

Ita ce mutun ta farko da ta fara ganin face ɗinsa bayan babansa, and ita ce mutun ta farko da ta fara sanya shi fitowa har parlon ƙasa, lallai ya tabbata idan bai tsaya ya bada himma ba zata iya cin nasara fa a kansada gaske.

Zuba mashi idanu ta yi tana kallonsa, face ɗinsa babu alamar mutumci ko kaɗan, zallar mugunta ce a samanta, in ka gansa sai ka razana, amma yarinyar nan Sweetie ko a jikinta, bata ji tsoron ganin cikin idonsa ba.

Wani irin ihu mai sauti na ruhohin tsafinsa ne ya fara karaɗe ko'ina a cikin parlon, hakan ya ja dikkansu biyu suka ɗan yi shock, abin ya bashi mamaki jin wanna ihu.

Cigaba da kura mashi kallo Sweetie ta yi tana mamakin hali irin nasa, ga shi kyakkyawa amma kyan ɗan maciji ne, ɗan kunama!. Shi kuma gabaɗaya hankalinsa ya koma a kan sautikan da yake ji wanda ita Sweetie bata iya jiyo hakan, da yake ta ɓangaren tsafinsa ne, shi kaɗai yake ji.

Can kamar saukar aradu haka ya tsinkayo wata iriyar murya mai tashin kai, mai kuma karfin gaske cikin guguwa da kuwa, tamkar muryan kartin maza ya ce.

"Autan duniyoyi ya bayyana, Autan ruhohi ya bayyana".
Shi ne abin da yake fita daga wanna sauti.

Jin haka yasa ya tuna wasiyar babansa na karshe a idan yake ce mashi.

"Wasiyata a gareka shi ne, kada ka yarda ya fita waje dik rintsi dik kuma wuya, kai ba kamar kowani mutum kake ba, kai ruhin ruhohine, autan duniyoyi ne, jagoran rundunoni ne, gatan manya manya ruhohi ne, nemanka suke yi kamar hauka, kai ɗan baiwa ne, da baiwa aka haifa mun kai, wanna dalilin yasa suka mayar da kai autansu, ni kuma ban yarda da hakan ba, saboda nasan me hakan yake nufi, wanna dalilin yasa na baro duniyar shaiɗanu da kai tin kana karami baka wuci 5 years ba, wannan dalilin yasa ban taɓa barinka kaje wani waje ba, saboda fitarka zai sa DUNIYAR SHAIƊANU su shaida in da kake, bana son su rabani da kai! Kada ka fita daga Black world har sai ka tara karfi sosai wanda zaka iya sanya barazana da tsoro a cikin zuƙatan DUNIYAR SHAIƊANU, wanda karfin ikonka zai iya sanyawa ka kwaci kanka daga ɗaukarka da zasu zo yi...............".

"Ka tara karfin iko mai karfin gaske ɗana, na jima ina karɓar yaya maza daga hannun matan garin nan ina sanyawa ana basu horo dik dan na yi maka tanadi ɗana, ka cigaba da horar da su dan su zame maka bayi masu bada rayukansu a kanka!!".

A lokacin da babansa yake yi mashi wanna bayanai hankalinsa baya'a jikinsa, a lokacin yana tunanin rashin lafiyar baban ne kawai, bai ɗauki zancen da wani muhimmanci ba, and bayar ɓacewar baban daga fuskar duniya bai sake tunawa da zancen ba sai yanzu.

============💘🔥===========


FOREST NE. Wajen yana cikin tsakiyar dokar daji mai cike da bishiyoyi masu girma, wadanda ganyensu suna rufe hasken rana. Akwai hayaniya mai ban tsoro kamar kuka na tsuntsaye da dabbar da ba a iya ganinta.

Duwatsu da Tsaunika. Duwatsu sun kewaye wajen, suna ɗauke da layuka masu kama da alamomin tsafi, suna haskawa da ɗan wuta mai launin kore. Tsaunukan suna da tsayi, kuma akwai tsallake-tsallake na ruwa mai fitowa daga saman tsauni yana ƙara tsoratarwa.

Babban kogon dutse shi ne cibiyar wajen matsafan. An yi ƙofofinsa da baƙin duwatsu mai siffar fuskokin aljannu. Jikin kogon yana ɗauke da rubutun tsafi a harshe da ba a fahimta. A ƙofar akwai fitila masu kunne da harshen wuta mai ruwan zuma da jajaye.


======CIKIN KOGON DUTSE=======

Ɗakuna Tsafi. Babban ɗaki ne da ke tsakiyar kogon, yana da stage mai ɗauke da kayan tsafi, kayan al'ajabi, kwalabe masu kunshe da ruwa mai launi, ƙananan gumaka, da wukake masu ban tsoro.

Ɗakin Hada Magani. A cikin babban ɗakin yake shi ma ta gefe guda. Cike yake da tukwane masu hayaƙi, ganye iri-iri, da fararen ƙasusuwa. Akwai ƙanshi mai kaɗaici da hayaki mai ɗan duhu yana tashi daga cikin tukwanen.

Ɗakin Ajiya. Wannan ɗaki yana da duwatsu masu haske kamar gold, manyan littattafai na tsafi da aka ɗaure da sarƙoƙi, da wasu abubuwan al'ajabi kamar ƙwayoyin ido da ƙananan gumaka.

Ɗakin Ƙulle-ƙulle. Wannan ɗakin yana da tagwayen layukan duhu a kasa, fitilu masu koren wuta, da gumaka masu kama da halittun ban tsoro suna kewaye.

Tsarin Haske. Hasken daga fitila ko wutar tsafi shi kadai yake cike kogon, kuma wutar tana ja da baya idan mutum ya matso kusa.

Sautuka. Akwai sautin iska mai ban tsoro, kuka na dabba mara ganuwa, da muryoyin mata suna magana a hankali kamar suna yin tsafi.

Halittun Ban Tsoro. Akwai dodanni da halittun matsafa masu kama da inuwa suna yawo a wajen.

Daga cikin wani keɓaɓɓen ɗaki dake gefe wanna murya take fitowa, sai faɗi ake yi autan ruhohi ya bayyana, lokacin girgiza duniya ta yi.

Ɗaki ne mai cike da ababen al'ajabi da ban tsoro, sai dai akwai tarin takardun tsafi cike a cikin ɗakin, wasu irin dogayen mutane ne su goma tsaye a cikin ɗakin saman stage, dikkansu suna cikin shigar wani irin dogayen kaya har yana jan kasa launin ruwan zuma, sai suka ɗaura fara kal a sama, gashin kansu ya kasance white hair ne, ga shi sun saki gashi dogo har bayansu, dikkansu riƙe suke da litattafan tsafinsu, ga dikkan alamu su ne manya manyan malaman duniyar shaiɗanu.

Wani irin mutun mutumi na wata mata dake a cikin ɗakin sai ya tashi hankalin dik wanda ya ɗaura idanunsa a kanta, macece tsirara aka ginata, ga wani sanda wanda daga gani zaka san na tsafi ne wanda aka zira mata shi daga gabanta har ya fito ta bakinta, dik yadda aka yi ta haka suke aiwatar da tsafe tsafensu, shiyasa suka bar alama a wannan waje.

Burin waɗan nan azzaluman su cure duniya ta zama abu guda, ya zamana babu wata ƙasa ko gari, dik a zama abu guda ne, su ruguje ɗakin kaba dake kasar Makka su gina fadarsu a wajen, ya zamana gabaɗaya duniya shugaban kasa kuda ɗaya ne wato su kenan, sun shafe tsawon lokaci suna yin wanna shirye shiryen ta hanyar tsaface tsaface dan samun karfin iko.. KOWA DAI BURINSA MULKI, WAI SHIN BASU SAN AKWAI MUTUWA BANE? BURINSU SU MULKI DUNIYA KAMAR SU SUKA HALICCI DUNIYAR?.

Bacewar Black Tiger daga cikinsu ya dakatar da su da yin dik wani shirye shiryen da su ke yi domin nufar ɗakin kaba. My people's kun gane cewa ikirarin Black Tiger na mallake duniya a jikinsa abin yake ko?.

Mahaifin Black Tiger shi ne shugaban malamai ko in ce bokayen DUNIYAR SHAIƊANU, yanzu da kuka gansu su goma a wanna ɗaki to mahaifinsa shi ne sarkinsu, shi ne shugabansu, shi ne kuma cikon na sha ɗayansu, shi ne mai faɗa aji, rana ɗaya ya ɗauki Black Tiger suka bar DUNIYAR SHAIƊANU, ya je ya sari daji ya kafa birnin BLACK WORLD, ko me dalilinsa na yin hakan?. Kada ku manta fa shi ne sarki a wanna daula, amma ya gudu ya bar wajen, to me dalili?.

Burin DUNIYAR SHAIƊANU shi ne su fara ruguje musulunci a idon duniya, burinsu su shafe babin addinin musulunci, su ruguje ɗakin kaba, su gina fadar mulkinsu a filin na ɗakin kaba, su cure duniya waje guda domin su cigaba da juyata ta yadda zasu samu dama su shafe addinin musulunci da gasken gaske, a yanzu haka sai yaki suke yi da musulunci amma ta karkashin ƙasa, ba zaka gane suna yin hakan ba in ba'a faɗa maka ba, kwantan ɓauna suke yi a yanzu, ta ƙarƙashin ƙasa suke aiwatar da komai.

Suna ta ƙoƙarin kawo rarrabuwar kai a cikin musulmi, suna ta sanyawa musulmi suna kashe kawunansu, suna ta hasasa gaba a tsakanin musulmi ba tare da musulmai sun gane ba!.

(LABARIN EVIL WORLD WATO DUNIYAR SHAIƊANU FA KU KALLE SHI A MATSAYIN LABARIN GASKIYAR ABIN DA YAKE FARUWA A DUNIYA NE, DA KARFI DA YAJI SO AKE YI A YAKI ADDININ MUSULUNCI TA KOWACCE HANYA, DAN HAKA KU TSAYA DA ADDU'A SOSAI, NASAN WASU ZASU GA ABIN KAMAR TATSUNIYA, TO WLH YA WUCI HAKA, YA ZARCE TUNANINKU, KU TSAYA DA ADDU'A KAWAI.)

Su waye ne a DAULAR DUNIYAR SHAIƊANU?. Wasu gungun kafurai da yahudawa ne da suka haɗa kawunansu, suka cure a wanna waje domin ganin sun cinwa burinsu a kan musulmai da Musulunci, suna da yawa a wajen, shararrun gima giman matsafansu ko in ce bokayensu su ne waɗan nan mutum 11 ɗin, sannan suna da Jiga jigan TITANS waɗan da suka zarce tunaninku a horarwa.

Kusan da tsafi suka yi amfani wajen haɓaka waɗan nan TITANS ɗin, burinsu a nan shi ne idan suka ci addinin musulunci da yaki ta karkashin kasa sosai, idan ya rage masu saura kaɗan, sai waɗan nan TITANS ɗin su karisa yakin su je su ruguje masu ɗakin gaba, tsawon lokaci suka ɗauka suna bawa waɗan nan TITANS ɗin horo na ban mamaki, burinsu shi ne bayyanar TITANS a duniya ya girgiza kowa, ya zamana babu wani makami da zai iya yaƙarsu, sannan babu wani ɗan adam da zai iya tinkararsu, ganinsu kawai yasa hantar duniya ta kaɗa...... Tashin hankali.

Ƴaƴan mutane suke satowa su mayar da su TITANS dan gudanar da wannan aiki, a kallah yanzu suna da TITANS mugaye masu zuƙatan shaiɗanu sun kai TITANS 10000, kuma har yanzu ba su daina sato wasu yaran ba.

Su waye TITANS? Wasu irin karfafa jaruman da suka jiku da horo ne, wuƙa ko bullet baya iya huda fatar jikinsu, tamkar ba mutane ba haka suke, suna da tsawo da faɗi sosai, sun zarce tunanin dik yadda kuke tunani!!. Da su za'ayi amfani wajen ruguje ɗakin kaba ɗakin Allah.

Ya Ubangiji ka kare musulmi da musulunci a dik in da suke, kada ku kalli wanna a iya labari kawai, ku dai ku yi addu'a kawai, Allah ya cigaba da ɗaukaka musulunci!!.

======================🕊️

Ganin ya yi shiru kaman mai sauraran wani abin ne yasa Sweetie ta lallaɓa a sace ta bar parlon, bai ankara da ita ba, ta gudu izuwa sama.

Shi kuwa ya tsunduma a kogin tunanin waɗan nan zantuka da ya jiyo ne, yana kuma tariyo zantukan babansa.

Amma ku me kuke tunanin yasa mahaifin Black Tiger ya bar DUNIYAR SHAIƊANU? bayan kuma shi ne shugabansu a wajen?.

Ya ɗan jima a haka kafin ya juyo da magic eyes ɗinsa, sannan Black heart ɗinsa ta matso kusa. Kudurtawa ya yi a ransa in dai haka ne to tabbas sai ya riga Duniyar shaiɗanu mallakar kambun mulkar duniya, dole ya tashi tsaye, dan ba zai taɓa yarda su rigasa ba, bai san cewa shi ne makullin mulkar duniyar da suke shirin yi ɗin ba, dan kuwa in dai baya Duniyar shaiɗanu to tabbas da wuya su iya isar da wanna aiki da suka ɗauko.... Hmmm akwai tashin hankali fa matuƙa.

A cikin zuciyarsa ya furta cewa. Lokacin bayyanarsa ga duniya ya yi, lokacin kara tsananta horar da warriors ɗinsa ya yi, lokacin farautar Spender ta kowacce hali ya yi, dole ya mulki duniya cikin kankanin lokaci, dan haka dole ya shiga fadar birnin Black world dan fara gudanar da mulkinsa........... Sweetie ta zame mashi silar abubuwa da dama a ɗan zuwanta birnin, dalilinta yanzu zai bayyana kansa wa birnin Black world.

To wai ina Spender ɗin yake? Tayaya zai samo shi? Dan dai kunga dik wahalar da ya bawa Sweetie ta ki gaya mashi in da Spender yake, ya zai yi kenan?.

Ɓacewa ya yi daga in da yake tsaye, bai bayyana a ko'ina ba sai a katafaren fadar birnin Black world.

Fadar sarki tana da kyan gani mai matukar birgewa. Daga waje, an gina ta da duwatsu masu daraja da aka kawata da zinari da lu'ulu'u. Babban kofar shiga tana da girma fiye da yadda mutum zai iya hangowa, kuma an kawata ta da hotunan zaki da bakar damisa, wanda ke nuna ƙarfin iko da jarumta.

A cikin fadar, daki-daki za ku ga hasken fitilu masu daraja da aka yi da lu’ulu’u na musamman suna haskaka ko'ina. Rufi kuwa an kawata shi da zane mai launuka masu kama da taurarin dare, wanda ke nuna darajar sarauta.

Kujerar Sarauta
A tsakiyar fadar, kujerar sarautar mai martaba take tsaye tamkar zuciyar duniya. An yi ta da zinari mai tsabta, tare da kawata ta da dutse mai daraja na lu'ulu'u da furannin jade. Kafafun kujerar sun kasance kamar zaki da suka yi alamar girmamawa ga sarki, kuma kujerar tana haskawa tamkar rana saboda yawan kayan ado na zinariya da azurfa da aka yi mata, sai dai ta saman kayin kujerar kan bakar damusa ce, sannan ta bayan kujerar gabaɗaya kaifafan kifiyoyi ne da aka yi su da zallar gold, darajar wanna kujera ta wuci tunaninku, a kaf tarihi ba'a taɓa yin kujera mai tsada da kyanta ba.

Zauren Masarauta
Fadarsa tana da manyan ginshiƙai da aka kawata da rubuce-rubucen hikima cikin harsuna daban-daban. Kowane bangare na fadar yana cike da hotuna masu ban sha'awa na yaƙe-yaƙe da nasarorin da suka bayyana tarihin sarautar. Idan baku manta ba na gaya maku sun sha gwabza yaki wajen durkusar da dik wasu masarautu da suka fisu karfin iko sabdoa zalunci, to hotunan yakin ne na nasarorinsu a manne a bangon!.

Tsarin Sarauta

An ware wani sashe na musamman ga makullai na zinariya, inda ake adana takardun mulki, kayan alatu, da RAWANIN ZALINCI da sarki ke amfani da su. Kamar yadda aka saba, masu gadi sanye da kayan mayaƙa suna tsaye kowane lokaci suna tabbatar da tsaron fadar.

Sam warrios dake gadin fada basu ga giftawar kowa ba a wajen, da magic ya yi amfani wajen shigewa ciki ta babbar kofar shiga.

A tsakiyar fadar ya tsaya, babu kowa a cikinta, ko'ina a share fes yana kyalli, ɗan jujjuya idanunsa ya fara yi yana bin dik wata kusurwa lunguna da saƙuna da kallo.

A kan dangerous kujerar mulkin ya tsayar da kallonsa. Gizo idanunsa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login