Showing 168001 words to 171000 words out of 403653 words

Chapter 57 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

127

fahimtar kika sansa sosai. So yana da kyau dikkan mata su yi koyi da halin momma, ita ake cewa uwa ta gari wlh. Daga karshe Allah ka haɗamu da iyayen miji na gari irin momma.

(Amma fa momma ta gama kwancewa Jaish namu na amana zani a kasuwa😅 zata sa Mahnoor ta raina shi😅🥱)

Daga haka Momma ta sanar da Mahnoor abin sa yasa Jaish ya ce bai sansu ba a yanzu, dan haka kada su ji haushinsa ko su ga laifinsa, ya so ta ne a lokacin da baya cikin hayyacinsa, daga karshe ta ɗaura da cewa. "A yanzu ma In Sha Allah zai so ki, zan tayaki yakin neman shawo kansa, kada ki sare ko ki cire rai, mu nan gidan jajirtattune, kema jajircewa zaki yi ki jure har mu yi nasara, sai abu nagaba da zan faɗa maki, in dai ba kin lura ransa a ɓace ba to in ya ce ki bar gabansa ko ki tashi a kusa da shi kada ki tafi, amma idan ransa a ɓace wannan kam ki tafi in ba haka ba ayi ɓatacciya, ki yawaita kasancewa a tare da shi, a kullum karfe 9 na dare yana shan cappuccinon, ni kuma nike haɗa mashi da kai'na, ki zo ki rinƙa ɗauka mashi kina kai mashi, kada ki yarda yana zaune a waje shi kaɗai, kada ki ji tsoronsa dan a labarinku na baya na ji kina tsoronsa, to a yanzu ki ajiye tsoron nan ki rinƙa kusantarsa sosai".

"Muhimmin abu nagaba shi ne, yanzu ki sani dik wata ɗawainiya nasa zai dawo kanki, kama daga kai mashi abinci, sanya shi ya ci, shinfiɗa gadonsa, mace mai dabara bata bari kowa ya ga makwancin mijinta, dan haka kada ki bada kofar da zai ce a dawo mashi da kuyangu masu yi mashi hidima a zuwan ke baki iya gyara mashi shinfiɗa ba, ki koyi yi mashi shinfiɗa da kyau, ki ɗara dik kuyangun da suke yi mashi hidima a baya yin komai yadda yakamata kuma yadda zai ƙayatar da shi, dik Haulat zata koyar dake kin ji ko?".

Kai ta gyaɗa tana amsawa da e ta ji.

Sosai ta fayyace mata dik wasu abubuwan da Jaish yake so da wanda baya so. Dik abin da take faɗe yana shiga kunnuwan Mahnoor yadda yakamata. Suna tsaka da hiran ne Omaid and Obaid suka shigo cikin ɗakin baki ɗauke da sallama.

Momma ce ta amsa masu sallamar tana jinsu da kallo.

Saman gadon Omaid ya haye yana turɓe fuska ya kwanta a can gefe. Shi kuwa Obaid sarki a rashin hakuri, wani kallo mai kama da harara ya wurgawa Mahnoor. "Momma who is she? She looks like Aunty Chuchu". Ya yi maganar yana kare mata kallo.

Baki ɗauke da sallama guyson ya shigo, dikkansu suna cikin white arabs jallabiyas masu bala'in kyau, yau sun fito a larabawansu sak.
Saman gado kusa da Omaid guyson ya haye yana turo baki, cikinsa ce take ɗan yi mashi ciwo kaɗan kaɗan, da alama ciwonsa ce take san tashi. Yana kwanciya kallonsa ya sauka a kan Mahnoor da ta yi ƙasa da kanta tana ta satar kallansu Omaid, a ganinta sak suke kama da Jaish, kun san jini ba wasa ba, sun yi mata bala'in kyau, sai dai ta shiga ruɗani wajen ƙasa tantance Omaid and Obaid mutun ɗaya ne ko biyu saboda kamanninsu.

Zaro idanu guyson ya yi, da ɗan karfi ya furta. "Momma wannan ba matar Yah Jaish ɗin nan ba ce?". Ya yi maganar yana miƙewa zaune an fasa kwanciya, yaga ta goge ta yi kyau kamar ba ita ba........ Lallai guyson yana da basira sosai, bai fa wani jima da sanin Mahnoor ba, amma dik wannan gyara da ta sha ya iya ganeta.

Wani irin ɗan iskan dariyar ƙeta Obaid ya yi kafin ya ce. "Yah Jaish ɗin ne da mata? Tab hau kenan". Ya kai karshen maganar yana sake watsewa da dariya.

Shi kansa Omaid jin zancen sai da yasa ya miƙe zaune. "Da gaske Yah Jaish ya yi aure?". Ya yi tambayar yana zare idanu.

Guyson ne ya wurgawa Obaid harara kafin ya ce. "To dariyar me kake yi sarki?". Zama Obaid ya yi a saman sofa, cike da iyashege ya fara faɗin. "Yah Omar ba dole in yi dariya ba, wai Yah Jaish da mata? Amma wannan ta shiryawa azabansa ko? Dan dik gidan nan bayan Yah Ramish babu bakin mugu biyunsa, wlh i pity for his wife".

Omaid ne ya capki zance da cewa. "Waye ya ce maka ma akwai wadda zata iya zaman aure da shi? Mutumin da bayan bada umarnin babu wani abin da ya iya, su kuma mata suna san soyayya da kulawa haɗe da lallaɓawa kamar jarurai, shi kuma yana abu kamar bosawa bashi da wani shaukin love".

Tab wato Omaid ɗan duniya ne, ko daga ina ya san shaukin love kuma? Kana ganinsa kaman shiru shiru ashe A ne shi ma, dama fa masu shiru shirun nan hmmm idan suka yi wata tsiyar sai ƙwaƙwalwa ta kasa ɗauka.

Momma dai binsu da kallo kawai take yi abinta.

Harara Guyson ya wurgawa Omaid kafin ya ce. "Kai daga ina ka san shaukin love ɗin?".

Obaid ne ya amshi zancen da cewa. "Tab ai Omaid ƴan'matansa sun kai uku a school, har faɗa ake yi a kansa sosai, love yake bugawa over"........... Momma ce ta katsesu da cewa. "Kai kuma ƴan'matanka nawa?"....... Ɗan ɗaure fuska kaɗan ya yi. "Momma ni ai bana soyayya, me zan yi da mata? Bani da lokacinsu gaskiya".

Girgiza kai kawai guyson ya yi, cikin sanyin murya ya ce da Mahnoor. "Kada ki biyewa waɗan nan, kin yi kyau sosai, ina sisterki da ta yi mun kallan matsayin Yah Jaish ɗin nan take?".

Kanta a ƙasa ta amsa mashi da Mahreen tana ɗakin da aka yi masu gyaran jiki....... "Kada ki takura kanki wajen sunkuyar da kanki da sunan kina jin kunyarnmu, mu kannen Yah Jaish ne, kinga mu kannenki ne, ki ɗaukemu a haka kin ji?". Cewar guyson again, yaro mai sanyin hali.

"Waye kaninta?". Cewar Obaid, a kule ya yi maganar. Hararar wasa guyson ya wurga mashi kafin ya ce. "Mu mana, mune kannenta". Kallon uku saura kwata ya bita da shi kafin ya amsa da. "A'a sai dai ku, amma ni wannan ƴar karamar yarinyar ba zan ce mata aunty ba, na fita shekaru fa". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa fuuuu ya nufi waje.

Da kallo dikkansu suka bisa har Mahnoor ɗin ma, shi a dole ransa ya ɓaci ance shi kanin Mahnoor ba zai ɗauki hakan ba.

Dab zai fita Jaish yana sako kai zai shigo. Karo suka ɗan yi, da sauri ya ja baya a ransa yana cewa shikenan yau ranata ba zata yi kyau ba tun da na haɗu da Yah Jaish. A fili kuma sai cewa ya yi. "Good afternoon Yah Jaish".

Kallon tsab Jaish ya yi mashi kafin ya amsa da. "Afternoon, from where to where?". Fuska a ɗaure tamau ya yi maganar. Guyson ne ya fara yi mashi dariya, suna bashi dariya yadda suke nitsuwa a gaban Jaish, zaka rantse da Allah malaman da'awa ne idan ka gansu a gaban Jaish ko Ramish, a bayansu kuwa ko shaiɗan sai ya sara masu a rashin mutunci.

Matsawa kusa da Mahnoor guyson ya yi, yana dariya ƙasa ƙasa ya ce. "Kinga dik iskancin nan nasu mijinki maganinsu yake yi, tsoronsa suke ji kamar su mutu, baki ga sun nitsu ba?".

Ita kanta sai da abin ya so sakata dariya, yadda Obaid ya rinƙa tada jijiyoyin wuya yanzu a nan, amma daga ganin Jaish kamar wani kurman da ya wuni bai ci abinci ba ya zama, ya nitsu tsit.

Cikin in ina Obaid ya amsa da. Daga wajen momma ɗaki kuma zai tafi ya kwanta. "Ka aikata wani abin ko?". Jaish ya faɗa yana wurgawa momma dake kallonsa ido. Wato Jaish yasan halinsu sarai, basa zama basu yi wani laifin ba, shiyasa dik in ya haɗu da su sai ya ce sun aikata wani abin.

Wani irin faɗuwar gaba Mahnoor ta ji na jin sanyayyar muryar mijin nata, wani irin azabbabben sonsa ne yake kara taso mata, ji ta yi tana san ɗago kai ta kallesa amma tana tsoron su haɗa ido, kuma tana kunyar momma ta kamata tana kallansa, sai kawai ta danne ta ƙara yin ƙasa da kai, amma tabbas tana kewansa, yanzu an kusa sati biyar rabonta da su kasance a hare kenan.

Sarai momma ta fahimci har yanzu Mahnoor tana tsoron Jaish sosai, kamar ma yanzu tsoron nasa karuwa ya yi a ranta, lallai sai ta tsaya tsayin daka ta cire mata wannan tsoro idan suna san yin nasara.

Wani irin kallo Jaish ya wurgawa Obaid har sai da ya haɗiyi wani yawu mai wuyar wucewa, sannan tin kafin Jaish ɗin ya sake yin magana ya yi saurin faɗa mashi dik abin da ya aikata, wato guyson ya ce Mahnoor Auntynsu ce shi kuma ya ce ba Auntynsu bace dan ya fita shekaru, dan haka ba zai ce mata Aunty ba, tsab ya faɗi abin da ya yi.

Momma da guyson sai murmushi suke binsu da shi. Jin abinda Obaid ya faɗa yasa ya ja siririn tsaki tare da karisowa ciki, dan a cewarsa shi ma ai bashi da haɗi da Mahnoor ɗin bare ya ji babu daɗi dan sun ki accepting ɗinta sun yi mata rashin kunya.

Saman sofa Jaish ya zauna, shi kuma Obaid ya yi saurin ficewa waje. Cikin girmamawa Omaid ya ɗagawa Jaish gaisuwa, amsa ɗaya ya yi hankalinsa gabaɗaya a kan momma.

Ƙasa Omaid ya yi, da sauri ya bi bayan Obaid, dan basa zama inuwa guda da Jaish. Guyson kuma cigaba da hira da Mahnoor ya yi ba tare da damuwa ba, dama abin da yasa a kauye ya ji kyamarsu ma, saboda datti ne, yanzu kuma sun yi tsab dan haka bashi da wata matsala da su.

Tin Mahnoor tana noƙewa bata yi mashi magana har ta fara sakin jiki suna hira ƙasa ƙasa, har murmushi ya sakata yi, ko ɗaya kuma bai ambaci sunanta ba, Aunty yake ce mata cikin girmamawa, ita ma ta tambayesa sunansa, ya ce mata Omar amma ana kiransa da Guyson, dan haka sai ta fara ce mashi Yah Omar saboda ya fita shekaru, yanzu kusan 19 years yake da shi.

Kallan tsab Momma ta yi wa Jaish kafin ta ce. "Lafiya kake kuwa? Ya ka dawo office da wuri?".
Ɗago kansa ya yi da nufin ya yi magana, sai a lokacin ya lura da Mahnoor dake saman bed ɗin ita ma, kallo ɗaya ya yi mata ya dawo da kallonsa a kan momma, irin kallan da ya wurga mata mai kama da yana san tambayar wacece wannan kuma? Sai dai bai tambaya ɗin ba ya ce da momma..

"Kai'na ne yake ciwo shiyasa na tashi office, and am felling hungry". A ɗan takaice momma ta ce. "Baka yi breakfast ba ka fita ko?". Kai ya gyaɗa mata alamar e.
"Meyasa baka san cin abinci a kan lokaci ne? Yanzu karfe 12 ta kusa fa amma baka yi breakfast ba? Dole ma kanka zai yi ciwo ai". Shiru ya yi yana ɗan satar kallan lallen dake kyawawan fararen hannun Mahnoor, ga zanen lallen sun fita sosai, sun yi kyau, mayen san lalle ne shi kuma, sai yana magana yana satar kallonsu, da a hannun Mommarsa ce ko hannun Zunaira yake da sai ya ɗauki hannun hoto, amma ita wannan bai santa ba, amma dik da haka ya ji yana kaunar lallenta.

Sarai momma tana kallansa dik abin da yake yi, ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin yadda yake satar kallan lallen, lallai ne kowani mutum yana da rauninsa, kuma abin da yake so shi ne rauninsa, tabbas zasu yi nasara In Sha Allah, haka momma take faɗe a ranta.

"Ayya sorry, jeka huta yanzu za'a kawo maka abincinka, idan ka ci sai ka sha magani". Cewar momma, ta yi maganar tana kallansa.

Sarai ya ji abin da ta faɗa, amma hankalinsa yana a kan lallen Mahnoor, dan haka sai ya jinjina kai kawai ba tare da ya yi magana ba, sannan ya miƙe da nufin ya tafi. Har zai juya sai kuma ya tuna bari ya kalli face ɗin mai wannan lalle. Ya ilahi ya lilliahi, sai da ya ji gabansa ya faɗi time da ya ɗaura idanunsa a kanta. Da sauri kamar wani maras gaskiya ya kawar da kansa tare da wucewa waje da sauri.

Murmushi a cikin zuciyarta momma ta saki, har ta harbo jirgi ɗan nata, dan har cikin ransa ya ji kyan Mahnoor ya taɓa shi.

Yana fita momma ta dawo da kallonta a kan Mahnoor da Guyson da suke ta hira ƙasa ƙasa ba zaka jiyosu sosai ba, cikin nitsuwa da giramma juna.

"Mahnoor tashi Omar ya rakaki wajen Haulat, ku je Omar ka ce da Haulat ta shirya mun ita sosai ta bata kayan da suka dace zata je kaiwa mijinta abinci, bari in je in duba kitchen me suka shirya mashi". Ta kai karshen maganar tana miƙewa tsaye.

Miƙewa guyson ma ya yi ya sauko kasa yana faɗin Mahnoor ta tashi su tafi, har lokacin yana jin cikinsa tana ciwo kaɗan kaɗan, amma ya daure suka nufi waje.

After some minutes, momma ta dauke cikin parlonnta wasu kuyangu guda biyu suna biye da ita a baya ɗauke da manya manyan trays masu shake da kayan cima wanda ta sa suka shiryawa Jaish. A saman dining table ɗinta suka ɗaura mata, sannan suka zube gwiwowinsu a ƙasa suna jiran jin ko akwai wani umarni da zata basu.

Da hannu ta yi masu nuni da su tafi, sannan ta samu waje saman sofa ta zauna tana tunanin irin nasihar da yakamata ta yi wa Jaish a kan Mahnoor. Tana tsaka da wannan tinani mama Haulat ta yi sallama rike da hannun Mahreen.

Like wow my people's, wai kunga Mahreen kuwa? Tamkar ba ita ba, har ɗan kumatu ta yi, fatarta ya yi jajir kamar ka taɓa jini ya fita, ta sha gyara da ingantattun kayan gyara daga Dubai, kayan gyara na musamman, tana sanye da abaya mai bala'in kyau wanda momma tasa aka sayo masu.

Ita kanta momma tasan yarinyar nan ta yi kyau, sai da ta yi fatan dama ace ita ma Mahreen ta zama sirikarta mana.

Mahreen yanzu ta ɗan nitsu fa, kun san da san kwalliya, dik abin da mama Haulat take son ta yi mata sai ta ce ta yi zata yi mata kwalliya, idan ta ce haka sai kuga Mahreen ta nitsu ta bi umarni, a haka aka samu aka yi mata wannan gyara.

Tin da ta kalli kanta a cikin mirror taga ta yi kyau shikenan ta kara nitsuwa, yanzu dik bayan awa sai ta ce zata yi wanka a sake yi mata wani make up ɗin mai kyau, dan shegen bala'in san kwalliya.

Da hannu momma ta nuna mata kusa da ita a kan ta zo ta zauna, sannan ta dubi Mama Haulat kafin ta ce. "Haulat kawo mun ɗiyata ya zo ta kaiwa mijinta abinci, daga nan ki shirya ki je part ɗinsa ki shirya ɗaki ɗaya wanda zaki koma can da zama".

Shiru mama Haulat ta ɗan yi, mace mai amana, ta kasa tafiya kuma.

"Lafiya Haulat?". Momma ta tambaya ganin bata tafi ba. Kasa ta yi da kai, cikin girmamawa ta ce. "Ranki ya daɗe wlh bana san matsawa daga kusa da ke ne". Allah sarki, sun saba sosai.

Momma tana ƙoƙarin janyo Mahreen jikinta ta rungume ta ce. "Ai baki bar kusa da ni ba, jahadi zaki je ki yi wajen ganin kin saita aure, daga nan ai zaki dawo, yanzu dai ki kuka da yaran naki da kyau".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa da to, sannan ta juya ta nufi waje. Dawo da kallonta a kan Mahreen momma ta yi, yarinya ta yi kyau kamar ba gajin bappa ba. Janta da hira momma ta fara yi tana kara wayar mata da kai.

Suka tsaka da hira mama Haulat ta dawo rike da hannun Mahnoor, ya subhanallah, mama Haulat ta iya shirya amarya fa, ta tsara mata kwalliya mai bala'in kyau da dik wanda ya kalla sai ya sake kallah, sannan ya bata wani haɗaɗɗen malesian gown mai bala'in kyau da tsada kaunin brown color, ga Mahnoor da hasken fata sai kalar ta yi mata kyau.

Rigar ta bi coca colar shape ɗinta ta zauna ɗas, sannan rigar ta fito da komai yadda yakamata, sai dai sun ɗaura mata kyakkyawan alkyabba a saman kayan, kanta babu ɗan'kwali sai hular alkyabbar, gashin kanta ya sha gyara sai tashin kamshi yake yi yana wani sheki, kai my people's wlh Mahnoor ta haɗu matuƙa.

Mahreen tana ganinta ta miƙe da nufin ta je ta rungumota, rikota momma ta yi tana faɗin. "Zauna kada ki ɓatawa amarya kyalliyarta". Jin haka yasa ta koma ta zauna tana faɗin. "Ni momma ba zan yarda ba kwalliyar Adda Mahnoor ya fi nawa kyau".

Murmushi kaɗan momma ta yi kafin ta sake cewa. "Anjuma da yamma idan zaku je gaishe da daddy za'ayi maki kwalliya irin nata kema"

Cike da yarinta ta ce da momma. "Ki ce Allah za'ayi mun?". Ɗan zaro idanu Mahnoor da mama Haulat suka yi. Har mama Haulat zata yi mata faɗa ta gaya mata ba fa wajen wasa take bai sai momma ta rigata da cewa.

"Ba sai na ce Allah ba, za'ayi maki ke dai". Make kafaɗa ta yi tana faɗin. "Idan baki ce Allah ba ni na zan yarda ba........".

Bata kai karshen maganar ba mama Haulat ta ɗan daka mata tsawa. "Ke baki da hankali ne? Sa'arki ce ita? Wai bana ce maki ki rinƙa girmama manya ba?.........".

Ɗaga mata hannu momma ta yi tare da cewa. "A'a Haulat rabu mun da ƴa, dauki kayan abincin nan ki raka Mahnoor izuwa wajen Jaish saboda yana jin yunwa, ba ruwanku da ƴa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login