Showing 75001 words to 78000 words out of 403653 words

Chapter 26 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

74

ce. "Meyasa kike murmushi? Sumbatar ta yi maki daɗi ne?".

Bata san time ɗin da ta gyaɗa mashi kai alamar e ba. Sai ji ta yi ya ce. "In kara ɗaya?".

Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a. Yadda ta yi saurin dojewa yasa shi kara faɗaɗa murmushinsa.

"Gaskiya kyakkyawa ce ke Sweetie". A kunne ya yi mata wannan raɗan.

"Kafini kyau ai........." Bata ƙarisa maganar ba ya yi sauri ɗaura babban yatsarsa a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru.

"Your lips is so very very soft and sweet like your name Sweetie". Da muryarsa kaman na ƴan maye ya yi maganar.

Master Devil ne ya sake yi masu knocking a karo na uku. Ƙoƙarin zullewa ta yi daga kusa da shi dan tana tsoron master ya shigo ya gansu a haka. Ina cikin sauri ya capko waist ɗinta tare da kara matso da ita kusa da shi.

"Meyasa kika ce kada na kara sumbatarki?".

Ƙasa sosai ta yi da murya wai dan kada master Devil ya jiyota......... "Saboda a addinina hakan bai dace ba, sai idan matarka ce zaka yi mata hakan".

"To meyasa?". Ya jefa mata tambaya yana ɗan shafa lips ɗinta da yatsarsa, hannunsa ɗaya yana saman waist ɗinta.

"Addinina yana da tsabta sosai, kai kanka ba zaka so ace kowani namiji zai iya taɓa kowace macen da kuke tare wadda ba mallakinsa ba, misali yanzu kaddara ni matarka ce, kenan kowani namiji zai yi mun kiss kamar yadda zaka yi mun, zaka yarda da hakan?".

Ai a miliyan ya girgiza kai haɗe da cewa. "A'a ba zan yarda ba, sai dai ni kaɗai zan taɓa matata".

"Good...... To kaga addinina akwai hikima da tsabta a cikinsa, shiyasa ya saka dokar matan mutun shi kaɗai zai iya amfani da ita, addinina bai yarda kowa ya taɓa matar wani ba".

Sosai ya kara samun kwanciyar hankali da addinin nan nata, saboda kyawawan ayyuka, ga tsabta da cikar dik wani abin da ake so.

Master da gajen hakuri sake yi masu knocking ya yi. Ronnie tamkar bai ji shi ba, ya bawa banza ajiyarsa.

A hankali yasa hannu ya janye mata dogon gashinta da ya zubo wajen wuyarta, slowly ya kai ɗan bakinsa saman wuyarta, sumbata ya manna mata kafin ya saketa yana lumshe idanu kamar wanda yake duniyar sama jannati, ita kuma murmushi ta ɗan saki kafin ta juya da sauri ta nufi toilet.

Shi kuma ya bita da kallo yana ganin yadda round butt ɗinta suke motsawa cikin kayan barcin Floris, gabaɗaya sai ya ji kasalarsa ta kara karuwa mashi, ya ji kamar ya sake janyota jikinsa.

Har ta kai bakin toilet zata shiga sai ta juyo, a take idanunsu suka sarkafe cikin na juna. Wani irin abu ya ji yana taso mashi a cikin zuciyarsa, ga wani abu dake tsikararsa a tsakiyar kansa kamar wanda ake tsirawa allura.

"Ronnie bari in yi wanka, kuma ina jin yunwa sosai, ko sallan ban yi ba". A ɗan shagwaɓe ta yi maganar.

Banda kallo babu abin da yake binta da shi, tamkar wanda ya ga bakon halitta daga wata duniyar.

"Ronnie lafiya?". Cike da mamaki ta yi tambayar, tana magana tana ɗan tsuke fuska tana ɗan ɗaure fuska.

In a low voice sosai, a kasale kamar wanda yake cikin maye ya ce. "Zallar madarar kyau ne ya hanani yin magana"........... Har cikin ranta ta ji wannan magana, tana matuƙar jin daɗi idan ya yabeta.

Ɗan juya idanunta sama kaɗan ta yi, kafin ta ce. "To ni dai kam yunwa nike ji".

A hankali ya motsa lips ɗinsa, voice ɗinsa bai fita ba irin magana mai alama da bakin nan ya yi mata wajen furta. "Jeki kiyi wanka ina kawo maki abinci".

Jinjina mashi kai ta yi, har zata juya sai ta tuna wani love story da ta fara karantawa a cikin littafinsa da ta gani a ɗakin nasa, dan haka sai ta tsaya ta mannawa tafin hannunta sumbata, sannan ta huro mashi.

Wani irin lumshe idanu ya yi dai'dai lokacin master ya sake yi mashi knocking. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya motsa lips ɗinsa ya yi mata raɗa da. "Shige ciki".

Juyawa ta yi da sauri ta shige, shi kuma ya nufi kofar. Yana buɗewa master ya tsaresa da kallo yana mamakin meyasa idanunsa ta rikiɗe haka? Anya yana da gaskiya kuwa?. Ya jefawa kansa tambaya.

Shi kuwa ɗaure fuska ya yi tamkar bai taɓa yin dariya ba, a ɗan takaice ya tambayi master da lafiya kuwa?.

"Babban yaya yana fada yana jiranka". Cewar master.

Sosai Ronnie ya yi mamakin jin furucin master, amma sai ya danne mamakin nasa ya nuna kamar yasan da yayan nasa ya shiga fada. Rufu kofar ɗakin nasa ya yi sannan ya wuce ya nufi escalator ba tare da ya sake bi ta kan master ba. A hanzarce master ya rufa mashi baya, yana tafiya yana waiwayi ɗakin Ronnien, hankalinsa bai kwanta da ɗakin ba, bai yarda da shi ba, yana ganin kamar akwai abin da Ronnie ya ɓoye a ciki, kunsan master da shegen gulma.

=============================🔥

••••••••••••••••••JIMETA•••••••••••••••••🔥

Dirama iya dirama ake bugawa a wannan gida, Nenne dai tin da ta gudu gidan Arɗo a ranar bata dawo ba, dan haka amarya Mairo dai ƴan uwanta suka sake hakura suka rakota gidan bappa.

Da daddare bappa ya kwana da amaryarsa ita kuma Nenne tana gidan Arɗo ta yi kwanan bakinciki, tana tsoron dawowa kuma saboda tasan aika aikan da ta yi, tana san dawowa kuma saboda ta hana su bappa kwanan farinciki shi da Mairo.

Haka dai ta daure ta kwana a gidan Arɗo, da asuban fari sai da ta daidai ci lokacin da maza gabaɗaya suka tafi masallaci, sai ta sato hanya ta dawo gida.

Nan ta isko Mairo saman dadduma tana addu'a, bata ce mata ko uppan ba ta wuce izuwa ɗakinsu Mahnoor.

Tabbas Mahnoor ta ji shigowarta, amma da yake barci ya ci karfinta sai ta kasa motsawa, daren jiya bata yi barci ba, ta kwana kukan rashin mijinta, barci ya kauracewa idanunta, sai yanzu gabanin asuba ɗin nan ne barci ya ɗauketa, da kyar ta iya gabatar da sallah.

Ganin Mahnoor tana barci Mahreen kuma tana cikin ɗakinta ne yasa Nenne ta fito ta shiga kitchen, a dai'dai lokacin ita ma Mairo ta fito domin ta hura wuta, karo suka yi a cikin kitchen Mairo ta ɗaga mata gaisuwa.

Ai yadda kuka san bango Mairo ta yi wa magana ba ita ba, ta yi banza da ita. Ita ma Mairo sai ta wuce ta ɗauki bokiti zata ɗebo ruwa. Kwace bokitin Nenne ta yi ta ɗebi ruwa a ciki ta wuce fuuuu sai ɗakin Mahnoor.

Ita kuwa Mairo baiwar Allah sai ta koma cikin ɗakinta ta ɗauko wani bokitin mai ragowar ruwan da ta shiga da shi daren jiya dan kada ya yi sanyi sosai idan zasu yi alwala, dama suna shiga da ruwa a bikiti su ajiye a cikin ɗakinsu, da asuba da shi suke yin alwala, ruwan cikin kitchen iska na bugasa ya yi sanyin da in suka zo yin alwala zasu wahala, so yanzu da asuba ita da bappa sun yi alwala sun bar ragowar, sai ya ɗaukosa ta nufo waje.

Tana sako kai zata fito waje ta ji ihun Mahnoor.

Da gudu ta karisa fitowa, ita ma Mahnoor da gudu ta fito daga cikin ɗakin nata jikinta sharkaf da ruwa. Bayanta Nenne ta biyo da sauri, sai huci take yi

Kamar aljanna haka Mahreen ta fito da gudu daga ɗakinta ita ma. Tana ɗaura idanunta da suke gani dishi dishi a kan Nemne ta san cewa ita ce nan ta jiƙa mata ƴar uwa.

Nenne zata fara surfa bala'i kenan bappa ya yi sallama, hakan yasa ta haɗiye maganar da take san yi.

Da mamaki bappa ya fara binsu da kallo. Tin bai yi magana ba Nenne ta yi saurin cewa. "Wlh Mairo kin ji kunya, yanzu fisabilillah me Mahnoor ta yi maki a cikin sanyin nan zaki jikata da ruwa fisabilillahi?".

A hanzarce bappa ya dawo da kallonsa a kan Mairo wadda ta zaro idanu tana al'ajabin maganar Nenne.

"Nenne ki ji tsoron Allah, ni yaushe na jiƙa Mahnoor?". Baiwar Allah maganata sanyi sanyi kamar na Mahnoor ɗin.

"Oh karya kenan zan yi maki? Wlh idan kika sake ina magana kina magana sai na dirje maki baki".

Shiru babba ya yi yana binsu da kallo. Mairo ta buɗe baki zata yi magana kenan Nenne ta sake cewa.

"Idan har mace ta kai mace to wlh ta furta uppan taga idan ban dirje bakin hegiya ba! Ni saarki ce?". Tana magana tana girgiza sak dai yadda Mahreen take yi idan tana masifa, ashe gado ta yi.

Ita dai Mahnoor baiwar Allah da sai rawan sanyi take yi ta takure waje guda ko ɗaga idanu ta kasa yi bare ma har ta kallesu, sai kerma jikinta yake yi saboda iskar dake kaɗata, ga jikinta sai ɗigar ruwa yake yi.

Bappa dai ya rasa wanene mai gaskiya a cikinsu, domin kuwa dikkansu ga bokiti a hannunsu, kuma dik bokitin da ragowar ruwa a ciki, to wacece ta watsa Mahnoor ruwa kenan? Ya kasa gane gaskiya, ga shi Nenne ta fi uban kowa baki a wajen, dole ka yarda da ita ce mai gaskiya.
Mahreen da idanunta ke ganin mata dishi dishi saboda barci ne ta fara magana kamar wata ƴar maye.
"Bappa wlh dik in da za'a je a dawo ni nasan Nenne ce ta daki Adda Mahnoor kuma ta zuba mata ruwa, dan ita ce bata sonta, Diddi Mairo kam nasan tana sonmu wlh".

Mairo da tin da Nenne ta buga mata warning bakinta ya mutu ne ta sauke nannauyar ajiyar zuciya jin cewa Mahreen ƴar cikin Nenne ta yarda da ita, sai dai ita yanzu ta zama ƴar kallo, saboda wlh munafurcin Nenne da iya lauye zancenta ya sha tunanin Mairo. Balai'n Nenne ya wuci yadda ake tunani, zata aikata abu amma cikin second zata mayar da laifin kan Mairo tare da hujojin da dole ka yarda Mairo ta aikata, baiwar Allah Mairo bata da hanyar wanke kanta sai dai Mahreeh ta shigar mata ta faɗi gaskiya, ita yanzu Nenne ta dai'na bata mamaki.

Kuma a al'adarsu idan babba yana magana yaro baya saka baki kome zai faru, shiyasa kuma ji Nenne ta dakawa Mairo warning a kan kada ta sake saka mata baki a magana.

"Kai makahone baka ganin bokiti da ruwa a hannunta? Ai ruwan dake ciki ne ta jiƙa Mahnoor da ita, tsawon shekara nawa muke tare da kai? Tin Mahnoor tana jaririya na riketa, ban taɓa zuba mata ruwa na sai yau? Meyasa zan yi mata hakan? Meyasa ban yi mata a baya ba sai yanzu?". Cewar Nenne kenan.

Kunsan dik abin da take yi wa Mahnoor bappa bai sani ba, bai taɓa sanin tana azabtar mashi da ƴar marainiyarsa ba, so ya ɗauka tsakani da Allah take rike da ita, wannan dalilin yasa ya fara zargin da gaske Mairo ce ta zuba mata ruwa, saboda tsawon shekaru bai taɓa ganin Nenne ta musguna mata ba!.

E kam akwai cakwakiya Mairo ta faɗa kaidin Nemne, to ni dai ina bayan fage.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





12


"Allah bappa ba Daddi Mairo bace, ni nasan Nenne ce". Cewar Mahreen.

Bappa da ya gama sanin Mahreen bata karya ne ya jinjina kai, ya ji kuma zuciyarsa ta yarda da Mahreen ɗin, dan balai'n Nenne sai ita, Allah mai sakayya a lokacin da bawa bai zata ba, shi ya kasance masifaffe kuma bala'i ga mahaifiyar Mahnoor, shi kuma Nenne ta kasance kwatankwacin hakan a garesa, shiyasa dayawan lokuta baya kula Nenne idan tana yin wannan abin nata, yana kallan hakan a matsayin shi da maman Mahnoor.

A kan Mairo ya tsayar da kallonsa, cikin nitsuwa ya ce. "Taimaka mata ta canza kaya".

Yana gama faɗar hakan ya wuce ɗaki ba tare da ya sake bi ta kan Nenne ba, ba komai ya sa bai kulata a yanzu fa face dan su Mahreen suna wajen, baya san su rinƙa samun saɓani har suna sa in sa a idanun su Mahreen, hakan zai gurɓata tarbiyar da suke da shi sosai, kuma hakan yanasakawa yara su rage ganin girman iyayen nasu, idan baku dai'na ba a hankali hankali dik wani mutunci da girma ƴaƴan zasu dai'na ganinku da shi.

Daga nan sai raini ya shigo tsakani, kana yi wa yaro magana yana kallanka yana cigaba da abin da yake yi, kunga ai hakan ba daɗi, to sai ku kiyaye, faɗar iyaye a gaban yara bama iya rai'nin kawai yake haifarwa ba, zaku saka mashi sha'awar faɗar, idan macece ba zata rinƙa jin shakkar ta gaggayawa mijinta maganganun ba idan ta yi aure, in namiji ne ba zai rinƙa shakkar zagin mata kai har da duka ba idan ya yi aure, akwai abubuwa da dama wanda faɗar iyaye a gaban ƴaƴansu yake haifarwa, kome za'ayi maki ki danne a gaban yara sai kun keɓe nan kam in kin ga dama ɗaga shi ki maka da kasa..........................😒🙄😅

Ajiye bokitin hannunta Mairo ta yi, ta karisa in da Mahnoor take sanyi ya gama lallasata, hannunta ta riko suka koma cikin ɗakin nata, Nenne muguwa ta jiƙa mata mattress ɗinta sosai.

Bayansu Mahreen ta bi, Nenne na kiranta ta bawa banza ajiyarta ta shige ɗakin Mahnoor.

Bokitin ta ajiye kamar zata bi bayansu, sai kuma ta fasa ta wuce cikin ɗakinta rai a matuƙar ɓace, da ta so ne bappa ya ci mutuncin Mairo, ya yi mata tas, amma bata samu hakan ba.

After some minutes.

Mairo ta fito daga ɗakin Mahnoor ta wuce cikin kitchen dan yin abin da ya fito da ita dama, ƙoƙarin fara hura wuta ta yi, sannan ta ɗauko bokitin ta cika shi da ruwa ta kawo kusa da murhu, tana ƙoƙarin ɗaura sabon tukunyarta a wuta sai ga Mahnoor ta shigo cikin kitchen ɗin.

Ta canza kaya izuwa dogon rigar da bappa ya saya mata a lokacin bikinta. Tana sanye da hujabinta kamar kullum.

Cikin girmamawa ta ce. "Daddi ina kwana".

Fuska ɗauke da fara'a Mairo ta amsa mata da lafiya ta tashi lafiya. Ita ma da lafiya ta amsa kafin ta ɗaura da cewa.
"Bari in tayaki Daddi".

"A'a Mahnoor, jeki ki kwanta kawai, ba sai kin tayani ba, ai ba wani aiki mai wahala bane, tuwo zan yi sai sanya maku ruwan wanka".

"Ayya Daddi ki bari in tayaki kin ji?". Yadda ta yi magana murya a marairace, Allah sarki barci fa take ji, amma kuma ba zata iya kwanciya ta yi ɗin ba, dan yanzu tana jin tsoron Nennen ta sake zuwa ta jiƙata da ruwa.

Da kyar Mairo ta yarda ta tayata ɗin, dan haka sai ta ce to ta yi shara ita kuma bari ta ɗaura ruwa sai ta haɗa kayan wanke wanke kafin nan Mahnoor ta gama shara sai su yi wanke wanke a tare.

A bisa ka'ida yau Nenne ce zata yi abinci ba amarya ba, amma da yake bappa yasan bata kwana a gidan ba sai ya ce da Mairo ta ɗaura mashi girkin kawai, kunji dalilin fitowarta da sassafe kenan.

Tsintsiya Mahnoor ta je ta ɗauko, cikin nitsuwa ta fara shara hankalinta gabaɗaya yana a kan tinanin mijinta, Allah sarki yau ta kai kololuwa a kewarsa, ji take kamar ta yi ta kuka babu dakatawa, yau da yana nan yanzu warhaka tana kwnace a jikinsa bata fito ba, a gaskiya ta yarda ta yi babban rashi a rayuwarta wanda ba zata taɓa manta shi ba har abada.

Dai'dai wannan lokacin da take shara tana tinaninsa.......... Shi kuma yana tsaye a jikin window ɗin ɗakinsa, ya yaye labulen tamkar mai kallan wani abin a harabar kingdom ɗin, a zahiri babu abin da yake kallo, tinani kawai yake yi, tinanin ma wanda bai san namenene ba, kawai a ransa ne yana jin tamkar akwai wani gurbi a ransa da yakamata ya cike wannan gurbin, ya rasa ganewa zuciyarsa, tana yi mashi babu daɗi, kamar akwai abin da ya rasa haka.

Hannunsa rike da cup mai ɗauke da cappuccino, yana sha a hankali hankali yana tunane tunane, yanzu ba jimawa suka dawo saga masallaci sallar asuba, sanye yake da kayan barci masu bala'in kyau a jikinsa, sun haɗu da Jawad, amma a hospital ya je ya ga Jawad ɗin.

Allah sarki tamkar su cinye junansu saboda so, sai dai Jawad bai faɗa mashi cewa ya yi aure ba, ya dai ce mashi Jannat ce bata da lafiya yake jinyarta.

And bai san guyson yana hospital ɗin ba, Jawad kawai ya je dubawa, yana duba shi kuma ya dawo, dan dik baya jin daɗin jikinsa, baya san fita daga cikin ɗakinsa, dama shi ba mai san fita bane sai idan ya zame mashi dole.

Yana cikin kuncin da ya rasa me dalili, while ita kuma tana cikin kuncin da ta san dalili. A haka ta gama sharan nan tas, suka yi wanke wanke a tare da Mairo, Mairo na wankewa ita kuma tana ɗaurayewa ta sanya cikin baf, tas suka gama gwanin birgewa sannan Mairo ta kwashe tuwo a kwanikan.

Mahreen kuwa tuni ta kwnata a mattress na Mahnoor ta mayar da barci abinta.

Bayan Mairo ta sauke ruwan wanka, ta sirkawa bappa ta kai mashi banɗaki, sai ta fito ta shiga ɗaki domin ta faɗa mashi, ita kuma Mahnoor ta fara kwasan kayan abincin ta fara kaiwa kowa ɗakinsa.

Tamkar wadda aka koro haka Nenne ta fito daga cikin ɗakinta, tamkar wata ɓarauniya haka ta fara sanɗo, a haka ta nufi cikin toilet ɗin.

Jim kaɗan ta fito sai muzurai take yi tamkar an kama ɓera a tarko, dik alamar rashin gaskiya ne a tattare da ita,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login