Showing 87001 words to 90000 words out of 403653 words

Chapter 30 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

43

sai ya yi ta kewaye a cikin dajin yana neman Sweetie, kun san na gaya maku kungurmin daji ne mai girman gaske, yana da ɓangarori da dama, idan kana wannan ɓangere ba zaka taɓa zatan akwai mutane a wani ɓangare ba saboda nisan dake tsakani.

So kullum a cikin daji yake yawon neman Sweetie, bai taɓa kawowa ransa bata a wannan dajin ba.

Har ciki ya rakasu, ya kuma gargaɗi Pretty a kan kada su yarda su fito waje, dan yasan halinta sarai da shegen san zama wajen ruwa, kullum sai ya gargaɗeta a kan fitowa waje, amma kuma kullun idan ya kawo masu ziyara a waje yake samunta, shegen san zama wajen koramu dake aman ruwa ne da ita. Kamar wata ƴar ruwa!.

Da kansa ya rufe masu kofar ramin nasu dan ma kada su fito, sai dai kash yana tafiya Pretty ta ce da Auta ta zo su je wajen korama su zauna hai, ita bata san zaman cikin nan, ta fi san waje. Auta kuwa ta bita suka fita, wajen wata korama mai aman ruwa suka je suka zauna suna kallan ruwa......... Pretty sai shirin Allah.

•••••••••••••••••••DUBAI••••••••••••••••••🔥

Kwance Sharifat take a saman bed ɗinta, ta ci kuka har ta godewa Allah, yau tsawon kwanaki tara kenan ba tare da Leesharh ba, tana cikin damuwa da alhinin hakan sosai sun rigada sun saba.

Gobe zata koma school, dama rashin Leesharh ya ja mata zazzaɓi har na tsawon kwanakin nan bata je school ba, idan kuka ganta sai kun tausaya mata, da alama ba'a taɓa breaking heart ɗinta ba sai a wannan karon baiwar Allah.

Miƙewa ta yi zaune, tinanin guyson ne ya faɗo mata a ranta, ta tina kullum sai ya tambayeta ina Leesharh, Allah sarki yakamata ta sanar da shi kalar cin amanar da Leesharh ta yi masu. Can tinanin maganganun su Omaid a kan Leesharh ya faɗo mata ranta, kenan ya tabbata su Omaid suna da gaskiya, dama tin da suka ɗaura idanunsu a kanta suka ce she looks like a criminal, Guyson ya yi ta yi masu faɗa, ashe kuwa zancensu haka ne.

Tun da aka kama Leesharh bata yi waya da kowa ba, wayarta ma a cikin jakarta da suka je taron nan da shi ta barshi, dan haka sai ta sauko kasa daga saman gadon. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi bags rack ɗinsu. Tana sanye da Pakistan a jikinta, ta ɗaura gyalen kayan a matsayin ɗan'kwali.

Wani irin jiri ne taji yana ƙoƙarin kayar da ita, da kyar ta iya kame kanta ta tsaya da kafafunta. A hankali ta zuge zip ɗin jakar ta buɗe.

A miliyan ɗari ta kai hannunta ta murza idanunta tana kara zarosu waje, sam bata san lokacin da bakinta ta furta what!! Ba, da karfi ta yi maganar. Nan take jikinta ya fara kerma, a hanzarce ta zira hannunta a cikin jakar ta fito da wayoyinsu. Wayarta ce da na Leesharh. Da karfi ta furta. "Kenan da gaske kamar yadda Yah Bilal ya ce mun Leesharh ta ce wancan wayar ba nata bane kenan hakan ce? Kenan tana da gaskiya ba wayarta bace wancan?".

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, Allah sarki su Yah Ramish sun azabtar da baiwar Allah a banza!".

Cikin ɗaga murya ta yi maganar. Jikinta har tsuma ya fara yi, burinta ta ganta a gaban Ramish ta sanar da shi wancan waya da gaske ba na Leesharh bane, tabbas Leesharh ba muguwa bace, dama ta kafe a kan wayar ba tata bace, ashe tana da gaskiya.

Nan take ta ji karfi ya zo mata, dik wani kasala ya gudu. Da gudu ta juya ta nufi hanyar fita daga ɗakin. A dab kofar fita suka yi karo da Ummie zata shigo ta dubata. Ai tsabar farincikin da zumuɗin ta isa ga Ramish bata tsaya bin ta kan Ummie ba ta yi waje a miliyan.

Bata zame ko'ina ba sai part ɗinsu Bilal, Ummie na kiranta amma ina bata saurara ba, wasu irin zafafan hawayen farinciki ne ya rinƙa tsere a saman face ɗinta, ji take kamar ta ɗaura hannu bisa kai ta yi ta zunduma ihu mai sautin gaske ko zata ɗan samu sassauci.

Dr Raj kawai ta iso a cikin parlournsu, yana zaune ya tasa laptop a gaba yana bincike a kan wata cuta da ake yawan korafi a kanta a hospital ɗinsu, kamar sabuwar cuta ce da ta keta tsaron likitoci, so a matsayinsa na babban likita ya dukufu a kan neman maganinta babu dare babu rana.

Ko sallama babu ta afko masu cikin parlon, a yadda ta shigo da wani ne zai razana sosai, amma da yake jinin Modarawa ne shi ɗin ko kaɗan bai razana ba, sai da ma ya ɗauki 1 min kafin ya ɗago da kallonsa a kanta, izzar sarauta ta motsa.

Kallo mai wuyar fassaruwa ya wurga mata, ta wani shigo kamar wadda aka koro, ko sallama babu. Nan take ta sha jinin jikinta, dama idan ba Yah Rizwan ba babu mai sakar mata fuska a cikinsu, shiyasa sam bata wani yinsu sosai.

Bai ce mata ko uppan ba ta fara ƴan kame kame tana ɗan juye juye, still dai bai ce ko sannu ba, ya mayar da kansa a kan laptop ɗinsa ya cigaba da aikin dake gabansa.

Tsabar tsarguwa da tsorata bai tambayeta ba ta fara magana a rikice tana haɗe word....... "Yah Raj dama Yah Ramish nike nema, dama zan bashi wayar Leesharh ce wlh ba ita ta..............".

A miliyan ta haɗiye sauran maganganun a cikinta bata kai karshe ba saboda sauka da idanunta ya yi a kan Ramish dake tsaye bakin kofar shigowa cikin parlourn daga bedroom side ɗinsu.
Ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, Bluetooth mai kyau da tsada ce manne a kunnensa, da alama waya yake yi, amma saboda tsabar nitsuwa irin nasa daga sharifat har Dr Raj babu wanda ya iya jin abin da yake faɗe, ƙasa ƙasa cike da class da nitsuwa yake wayar.

Yana sanye da sexy sleeping dress a jikinsa, tamkar wani mai aure, ga idonsa kamar dai, to na dai yi shiru, amma da alamar tambaya fa a tattare da shi, sai tashin kamshi yake yi, da alama bai jima da farkawa daga barci ba, yanayin kayan barcin nasa idan ka gansa sai gabanka ya faɗi, shiyasa nace kamar wani mai aure, da alama wlh Yah Ramish ɗan duniya ne sosai, gabaɗaya gaban rigar a buɗe take, faffaɗar kirjinsa a waje, dik macen da ta gansa haka sai kirjinta ya buga, kai ko namiji ya gansa a haka sai kirjinsa ya buga bare mace, ka gansa cikin full kaya ya rufe ko'ina nasa ma sai ka ji ka faɗa da shi bare kuma ya buɗewa mutane gaban kirjinsa dan iya hege.

Sharifat da ta zama kamar wadda aka sassaƙa a waje ya wurgawa hegun sexy eyes ɗin nan nasa yana cigaba da magana da wanda suke waya. Yadda kuka san idanunsa allura suka yi mata, wani irin zabura ta yi da ya kalleta, da karfi ta furta. "WAYYO ALLAH". Ta yi maganar tare da juya mashi baya.

Allah sarki a take ta birkice kamar wadda aka zarewa kaso hamsin cikin ɗari na hankalinta.

Dr Raj da ya ji ta furta wayyo Allah ta, sai ya ɗago da kallonsa a kanta, dai'dai lokacin ta juyawa Ramish baya hannayenta sai kerma suke yi. Ganin yadda ta juya baya da sauri yasa ya juya ya kai kallansa a kan kofar da zata sadaka da bedrooms side ɗinsu, dama tin da yaga ta yi irin wannan juyi ya yi tinanin Ramish ta gani, dan shi kaɗai take yi wa irin wannan abin.

Ganinsa a tsaye yasa ya mayar da kallonsa a kan laptop ɗinsa, dan a cewarsa sun fi kusa, baya shiga shirginsu. Tana san gudu ta bar part ɗin, tana kuma san yi mashi magana dan ta ceto ƴar uwarta Leesharh, sai dai ba zata iya juyowa ta sake kallansa a irin wannan shiga ba, yana ɗaga mata hankali kuma yana rikitata, ga shi wandon sleeping dress ɗin ma sai wanda ya gani, ku baku ji sunan kayan bane ma, sexy sleeping dress, ai daga nan zaku gane ba kayan arziki bane, na masu aure ne, shi kuma shirgegen gwauro da shi ya zo ya wani saka su.

(Sai su Yah Rizwan sun yi mashi fyaɗe da tsakar dare kila zai dai'na saka kayan ma'aurata 😅😅😅😅😅 na faɗa a saka mun gas🥱😅 ni bana tsoron Ramish da💪🌝)

Dr Raj ya cigaba da aikin gabansa, shi ma Ramish juyawa ya yi ya koma cikin room ɗinsa, saboda dama ya leƙo parlourn ne dan ya duba Bilal yana nan ko baya nan.

Jin alamar ya bar wajen yasa ta wani sauke nannauyar ajiyar zuciya wanda har sai da Dr Raj ya jiyota, amma ko a gefen takalmarsa ya cigaba da abin da yake yi.

A hanzarce ta juyo, kirjinta na dukan uku uku ta bi bayan Ramish da kallo, har ya kurewa ganinta, komai nasa abin burgewa ne. Wani irin ta ji a ranta, wani ɓangare na zuciyarta yana ce mata ta bi bayansa, wani kuma yana ce mata ta koma cikin ɗakinta.

Juyawa ta yi da nufin ta koma ɗakinta, sai kuma ta tuna Leesharh tana cikin azaba, nan take ta ji zuciyarta ya karfafa, tausayin ƴar uwarta ya ratsata, da sauri ta bi bayansa tana karanta dik addu'ar da ya zo bakinta.

Tana sako kafarta cikin room ɗin nasa shi kuma yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa zai shiga wanka, ya bawa kofar shigowa baya.

Sai da ta ji gabanta ya faɗi time da taga faffaɗar bayansa kamar madara. A bakin kofa ta tsaya kamar wadda take jira ace pet ta yanka a guje ta fita, like tana tsoron cikin ɗakin dai.

Sarai ya ji motsinta, sai dai bai juyo ba, ya cigaba da abin da yake yi, tsabar tabbatar bashi da kunya wandon jikinsa yake ƙoƙari zamewa, dan shi babu ruwansa da tana tsaye, meyaka kawota ɗakinsa? Ko ɗakinta ne?.

Kamar ta dalla ihu take ji, shi ko kamar wanda bai san da halittarta a wajen ba.

Ai bata san time da ta juya a miliyan zata fita ba ganin ya zame wandan jikinsa, tana juyowa kuma suka ci karo da Bilal da yake ƙoƙarin shigowa yanzu. Da karfi sosai ta juya, hakan yasa ta bugesa da karfi, wani irin baya baya ta yi zata faɗi. Cikin sauri ya damko wuyar rigarta dan taimaka mata kada ta faɗi.

Ai bata san time ɗin da ta kurma ihu ba, wayoyin dake hannunta dikka biyu suka faɗi ƙasa, ba komai ya saka ta ihu ba face yadda Bilal ya riko wuyar rigarta kusan hannunsa dikka a saman tudun tula tulanta, shiyasata ihu ba shiri.

Janyota Bilal ya yi ta tsaya da kafafunta, sannan ya saketa tare da ɗaure fuska sosai, a takaice ya ce. "Meyakawoki nan?".

Kasa tsayuwa a kan kafafunta ta yi, cikin sauri ta durkushe kasa tare da fara ruwan zafafan hawaye, hannu tasa ta fara laluɓar wayoyin da suka faɗi ƙasa, tsikar jikinta dik sai wani mimmikewa tsaye yake yi.

A karo na biyu Bilal ya sake tambayart me ya kawota nan.............. Sai a lokacin ta ɗago da kanta a kansa, cikin sarkewar murya haɗe da tashin hankali a tattare da ita ta ce.

"Yah Bilal dama nazo ne in faɗa maku wancan waya wlh bana Leesharh bace, ashe irin namu ne da kasaya mana, wlh tana da gaskiya ba nata bane, kaga namu wayoyin". Ta yi maganar tana ɗagowa, tana kai karshen maganar kuma ta miƙa mashi wayoyinsu dake hannun, sai kerma hannun nata yake yi yaki tsayawa waje guda.

Sai a wannan lokaci Ramish ya juyo, ya ɗaura towel a waist ɗinsa, kallo ɗaya ya yi masu ya wuce ya nufi toilet............ Karɓar wayoyin Bilal ya yi haɗe da furta alhamdulillah da ɗan sauti, da alama shi ma ya ji matuƙar daɗi, bai yi magana ba sai ya nuna mata hanyar fita kawai, a kan ta je.

Cike da tsoro ta ce. "Yah Bilal to Leesharh ɗin fa? Zaku dawo mun da ita?".

Kai kawai ya jinjina mata tare da kara nuna mata hanya. Da gudu ta raɓa gefensa ta fice tana toshe bakinta saboda wani iri kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro da ya kubce mata.

Ajiyar zuciya Bilal ya sauke tare da ɗaura kallonsa a kan wayoyi, tabbas wannan ne wayoyin da ya saya masu, wancan kenan irin nasu ne kawai? To waye mamallakin wancan wayar? Ya jefa kansa tambayar.

My people's da ni da ku idan baku manta ba mun san ya aka yi wayoyin nan suka fita iri ɗaya, in baku manta ba a baya na gaya maku masu nikaf sun canza mata ainahin wayar da suka bata da farko, har na ce maku sun bata wani irin wanda Bilal ya saya mata ita da Sharifat sak ko? To wannan shi ya kawo ruɗani a cikin al'amurran, wayoyin iri ɗaya ne, Sharifat guda ɗaya tasan Leesharh da shi shi ne wanda Bilal ya basu, bata san da na masu nikaf ba! Wannan shi ne, kunga Sharifat zata wanke Leesharh ba tare da tasan da gaske wancan wayar ma na Leesharh ɗin bace. Wai akwai case a gaba gaskiya!!.

Dama kuma tun farko Leesharh ta ce da su Bilal ba wayarta bane, kunga kuwa yanzu da Sharifat ta kawo wannan tsab zasu iya yarda ba nata ɗin bane, akwai cakwakiya fa sosai, shin masu nikaf zasu ɗauki mataki ko dai shirun banza suka yi? Muje zuwa!.

Karisawa cikin ɗakin Bilal ya yi, saman bed ya haye tare da jawo laptop na Ramish ya fara latse latsensa.

•••••••••••••••••FOREST•••••••••••••••🔥

Tsaye take gaban wannan korama dake aman ruwan, yanayin yadda ruwan yake zuba abin gwanin ban sha'awa, ka korayen ganyayyaki kewaye da wajen, sannan ga ruwa gudu a kasan koramar yana ta gudu mai haske tar, tsabar haskensa har ya ɗauki kalar sararin samaniya wato sky blue.

Ta ko'ina kamshin furanni ne yake tashi saboda yawaitansu a wajen, daga gefe can tsuntsaye nau'ika daban daban ne suke dira a kasa bakin ruwan dake gudun suna shan ruwa sai su sake tashi, yanayi mai daɗi ga iska na ɗan kaɗawa a hankali hankali yana kaɗa furannin dake wajen kamshinsu yana kara tashi.

Wajen zai yi matukar dacewa da masoyan dake bala'in kaunar junansu. Ta yi shiru kamar mai kallan ruwan dake kwaranya daga koramar, amma kuma ba shi take kallah ba, hakika hankalinta ya luluƙa duniyar tinanin kingdom of power da kuma Hoorain, wannan abin da ya yi mata ya zame mata babban tabo a rayuwarta da ba zai taɓa gogewa ba.

Pretty bata a tare da ita, ta tafi ɗauko masu fruits, so ita kaɗai take tsaye a wajen.

Ta yi nisa cikin tinaninsa da take yi ba zato ba tsammani ta ji an rufe mata idanu daga ta bayanta. Hakika ta tsorata matuƙa, dan yanzu abu kaɗan yake razanata yake kuma ɗaga mata hankali.

Ihu ta zunduma tare da fara ƙoƙarin kwatar kanta zata zulle. Saura kaɗan ta afaka cikin wannan ruwan gudu a ƙoƙarinta na zullewa. Da sauri ya riketa da kyau, kamar mai raɗa ya ce mata shi ne fa ta nitsuwa kada ta jewa kanta ciwo.

Dik da ta ji muryarsa bata yarda ba, dan yanzu bata jin zata yarda da wani a rayuwarta, babu wani sauran yarda a zuciyarta, ƙoƙari ta cigaba da yi dan kwatar kanta.

Da yaga haka sai ya zame hannunsa daga idanun nata, dan taga zahiri, sai dai bai saki hannunta da rike dan kada ta faɗi ba, sai ya sanya ɗayan hannunsa a saman Waist ɗinta.

Cak ta tsaya da ƙoƙarin zillewa da take yi, nan take ta ji mummunar faɗuwar gaba, da sauri ta yi ƙoƙarin jiyowa dan ta tabbatarwa da kanta shi ne ko ba shi bane.

Ganin yadda ta juyo da sauri yasa ya yi saurin saketa tare da ce mata. "Kiyi hakuri"........... Jinjina mashi kai kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba, sai ta buƙaci matsawa daga kusa da shi.

Bai bari ta yi hakan na shi sai ya ɗan matsa baya yana kara ce mata ta yi hakuri. Da okey ta amsa mashi tana mayar da kallonta a wajen koramar.

Wai shin me ya dawo da shi bayan ya ce ya tafi?. E to tinanin Zunaira ya hana shi tafiya, dan haka sai ya samu waje kasan wani bishiya ya zauna yana ƙoƙarin yankewa kanshi shawarar ya dawo ya sake ganinta ne ko kuma ya hakura ya tafi sai gobe?.

Yana tsaka da wannan tinani ya hango gungun mayaka sun dinfarko cikin dajin wanda ko ba'a faɗa mashi ba yasan su Pretty suke nema, tun da ya sha artabo da su a kan hakan. Wannan dalilin yasa ya hau saman bishiyar da yake karkashin ya ɓuya, sai da suka wuce sannan ya sauko ya bi bayansu dan yaga ina suka nufa.

Ganin sun bi wani hanya ba ta in da su Pretty suke bane yasa ya ce to bari ya leƙo su Pretty su ɗan sake ɓata lokaci a tare kafin nan ya wuce, kun ji dalilin dawowarsa. Har zai wuce wajen nasu sai ya hango Zunaira tsaye a bakin koramar nan shi ne ya ƙariso gareta, dama tinaninta ne a ransa.

"Ina Omnish?". Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.

Kamar ba zata amsa mashi ba, amma ita ɗin ƴar halak ce, akwai tina alkhari, dan haka sai ta daure ta ce. "Ta je kawo fruits".

"Amma ba nace kada ku fita waje ba?".

Kasa ta yi da kanta tana tinanin amsar da ya kamata ta bashi, a dai'dai lokacin Pretty ta dawo hannunta ɗauke da fruits a kwando.

Shiru suka yi daga shi har Auta, cike da mamaki Pretty ta ce. "Kai ne ka dawo?". Yadda ta yi maganar sai ku zaci bata yi wani laifi ba.

Binta da kallo ya yi yana mamakin halin Omnish ɗin nan nasa, yarinya ce sai ka rasa a wani mataki zaka ajiyeta.

"Omnish wai ba nace kada ku fito waje ba? Ke kika ja Zunaira kuka fito ko?"............ Baki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login