Showing 120001 words to 123000 words out of 403653 words

Chapter 41 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

36

hular a kansa ta yi saurin sanya hannunta a kumatunsa. Hakan yasa ya tsaya yana kallanta. Girgiza mashi kai ta yi alamar bata san ya saka.

"Meyafaru?. Baki san in saka ne?". Murya can ƙasa ƙasa ya yi maganar.......... Kai ta gyaɗa mashi alamar e bata, ta yi hakan tare da karɓe hular ta wuce gaba. Shiru ya ɗan tsaya kamar wani mai tinani. Da yaga ta ɗan yi nisa a tafiya sai ya yi saurin bin bayanta suka nufi wajen Pretty.

Tun daga nesa Auta ta hango babu Pretty a wajen, hakan yasa ta ƙara ɗaga kafa dan ta isa wajen da sauri, shima cikin zafa ya kara sauri dan isa wajen, saboda a ɗan zamansa da Pretty kafin Auta ta farfaɗo sun saba, kunsan halin Pretty da san jiki da shagwaɓa, hakan yasa suka yi sabo, har fargabar isa wajen yake yi, dan ba zai juri rashin samunta a wajen ba.

To nima dai bari na leƙa Black world wata kila kafin na dawo sun samu matsa, amma ina kuke tinanin Pretty ta tafi? Ko waye ya ɗauketa?.

••••••••••••••BLACK WORLD••••••••••••🔥

Wani irin haɗaɗɗen ɗaki ne wanda yake tamkar hospital, komai da kuka sani wanda ya danganci kula da lafiya cikin gaggawa akwaisa a cikin wannan ɗaki, ga bed na majinyata guda uku a ciki manya manyan suna shinfiɗe da kyakkyawar bedsheet na alfarma.

Na'urorin gwaje gwaje da na bincikar cuta dik akwai su. Komai na cikin ɗakin nan white color ne, ɗakin ya haɗu matuƙa, ga shi ko'ina tsab tsab sai tashin daddaɗar kamshi yake yi tamkar ba ɗakin jinya ba.

Tsaye yake a gaban bed ɗin da take kwance, yana sanye da long coat fari tas har zuwa gwiwarsa, daga ƙasa wandon jeans ne mai bala'in tsada a jikinsa, idanuwansa na sanye da wata iriyar na'ura mai kama da glass, idan ka ganta zaka yi zatan glass ya sanyawa dan fashion ne, amma ba haka bane, na'ura ce da ake iya ganin cikin jikin mutum dan bincike.

Duniya ta cigaba sosai, dik in da ya tsayar da idanunsa a nan na'urar zata ɗauko mashi dik abin dake waje a cikin fata da tsoka. Ya zubawa wuyarta idanu yana kallon yadda wani irin kululun jini bakin kirin ya taru a wajen, ba komai ya haifar da shi a wajen ba face take mata wuya da ya yi a daren jiya.

Ba ƙaramin kyau Black Tiger ya yi a cikin wannan shiga ba, wlh kamar ka zauna ka tasa shi gaba ba ci ba sha ka yi ta kallansa babu kawar da ido.

Ita kuwa tana sanye da kayanta na jiya ɗin, ba'a canza mata ba, Sweetie ta ji wuya maras kunya, da ta ce bata ji ai.

Hannunsa dake cikin white hands gloves ya kai saman wani kyakkyawan table dake kusa da bed ɗin wanda yake shake da kayan aiki da dik wani abin da zai buƙata.

Cotton and zolpidem ya ɗauko, fasa zolpidem ya yi, cikin kwarewa ya kai hannunsa saman ɗan bakinta, da ɗan karfi ya buɗe bakin nata ya ɗaura mata kwayar zolpidem ɗaya a saman tongue ɗinta, sannan ya sanya cotton dake hannunsa a saman bed saitin wuyar tata ta yadda jini ba zai taɓa bedsheet ba idan ya fasa wuyar tata.

Scalpel ya ɗauko don yin yankan, ko ɗigon tausayi babu a ransa yasa wannan Scalpel ɗin a saman fatar wuyarta, ɗago idanunsa ya yi ya kalli face ɗinta na ƴan sakanni kafin ya mayar da kallansa a saman wuyar tata.

Cikin nitsuwa ya yanka fatar wuyar yanka mai ɗan girma. Nan take wani irin jini jajir ya faso hanya, wai a haka ma fa ta gefen wuya ne jinin ya taru ba ta gaba ba.

Wani cutton ya ɗauko mai ɗan girma ya fara goge jinin dake bulbula kamar famfo. Tiyata fa likita guda ɗaya baya yinsa, saboda babban aiki ne, dole sai da taimakawan wasu a kusa suna miƙo maka wasu abubuwan, amma shi saboda kwarewa shi kaɗai yake yinta.

Ganin jinin yaki raguwa ya samu ya yi aikinsa yadda yakamata ne yasa ya ɗauko suction device dan tsotse jinin dake waje a hankali. Nan take kuwa jinin ta tsotse.

Sake ɗauko ecy da hemostat ya yi dan ya tsaida jinin da zasu iya yi wa aikinsa barazana daga ƙananan jijiyoyi.

Cikin nitsuwa ya sake sanya Scalpel ya yanka namar ciki in da jinin ya taru. Nan take jini bakin kirin ya fara zuba, kurawa namar wajen ido ya yi, sai yaga wajen ya yi wani irin dark brown haka alamar kamar ya samu matsala, ya taketa sosai ne wlh.

Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, dan ya gano dole ya yanke namar dake wannan wajen, dan haka sai ya ɗauko electrocautery bayan da wannan bakin jinin ya gama zuba. Amfani da shi ya yi ya yanke namar dake wajen haɗe da tsotse jinin tas.

Dik da tana sume sai da ta tsuke fuska alamar azaba. Tsab ya fitar da jinin kafin ya kara sa cotton fari tas mai tsabta ya kara tsabtace wajen. Sannan ya ɗauko needle holder da zaren tiyata dan ɗinka wurin.

Ko kaɗan babu tausayi a ransa, haka ya ɗinke mata wajen tas ya kuma sanya plaster, daga nan ya tattare dik wasu abubuwan dake wajen ya mayar da su mazauninsu, ya ɗauki s-z ya matsar da shi kusa da shi, sannan ya zare hands gloves dake hannunsa. Ya yi amfani da s-z a hannun nasa dan tsabtaceta. Cikin kwanciyar hankali ya ɗauki remote ya kashe A.c dake ɗakin mai gabaɗaya.

Sannan ya cire coat dake jikinsa. Yana cirewa wani Robbot ɗaya daga cikin masu yi mashi aiki ya matso ya karɓi coat ɗin, shi kuma ya nufi waje da sauri cikin zafa abinsa.

A ɓangaren Ronnie kuwa, tun da ya yi wannan barci na dare jiya sai da rana ta take sannan ya iya farkawa. Da sunanta a bakinsa ya farka, a razane kuma. Sai dai kuma da kyakkyawar fuskar yayansa ya fara yin tozali ba ita ba.

Hankali a tsananin tashe ya ce. "Yaya where's Sweetie?".
Black Tiger yana zaune a gefen bed ɗin yana kallansa, yana sanye da kayan shan iska da suka kara bayyanar da kyakkyawar surar jikinsa, shi kuma ya kara haska kayan yadda yakamata.

Miƙewa tsaye ya yi ya bar wajen. Cikin Zafa Ronnie ya miƙe zaune a saman gadon, hankalinsa a tsananin yashe ya ce. "Please big bro where's Sweetie? Talk to me please and please". Hankalinsa a tashe ya yi maganar.

Black Tiger bai goge mashi tinanin kwakwalwarsa bane kawai saboda Sweetie tana raye, a tinaninsa ta mutu shiyasa ya yi niyar shafe mashi brain, ganin tana raye yasa bai yi hakan ba, ya ɗaga masu kafa.

Ƙasa Ronnie ya diro, da sauri ya bi bayan yayan nasa yana cigaba da bashi hakuri da ya faɗa mashi ina Sweetie take, har kuka sai da ya yi, ya cigaba da magiya.

Dik kaunar da Black Tiger yake yi mashi yaki faɗa mashi in da take har tsawon sati biyu cir, har zazzaɓi Ronnie ya yi amma Black Tiger yaki kula shi ya faɗa mashi ina yake, shi da ya yi mata aiki dai yana zuwa ya dubata ya canza abin da yakamata a canza, amma yaki sanar da Ronnie har sai da ta farfaɗo cikin ƙoshin lafiyarta, sannan ne ya faɗa mashi tana cikin wannan ɗaki.

Ɗakin ma a cikin bedroom ɗinsa take ta wata hanyar sirri da aka yi ta da da glass. Ni kam na ce ko ba komai Sweetie ta ciri tuta tun da ta shiga wannan ɗaki da iya shi da Ronnie kawai suke jinya a ciki, ɗaki na musamman, amma saboda Spender sai ga shi ita ma yau ya kasance a ciki, ɗakin da da ace mutuwa tana da magani to da tabbas za'a iya samun maganinta a cikin wannan ɗaki, saboda kwarewarsa a iya aiki.

Sai dai wani abin da baku sani ba, Black Tiger ya fahimci Sweetie ba zata bashi haɗin kai wajen mallakar Spender ba, dan haka ya fara tinanin zai yi mata aiki wajen zare tinanin kwakwalwarta ya sakawa wani daga cikin Robbot ɗinsa dan ya samu Spender.

Idan kuma ya yi mata wannan aiki to tabbas ba zata tashi ba, yanzu haka ya sanya a kowacce irin yanayi a shigo mashi da kayan aikin cikin kasarsa domin ya kaddamar da wannan aiki, saboda ya ga Sweetie fa ƴar a mutu ce, bata tsoron mutuwa bare ya yi mata barazana da shi ya ci galaba. Abu mai sauki kawai ya cire ƙwaƙwalwarta ya yi dashenta ga Robbot ɗinsa, sai dai kuma fa, in ya cire ƙwaƙwalwarta ya haura 30 mins bai yi saurin sanyawa robbot ɗin ba to zasu rasa tinaninta, dan kwakwalwar zata dai'na yin aiki kwata kwata......... Babbar magana. Akwai matsala fa.

Jin in da take yasa bai wani ɓata lokaci wajen kai kansa gareta ba, a lokacin ta kai sati da farfaɗowa, da yake ciwon ma ba wani babba sosai bane har ta samu sauki ba laifi, tana iya yin magana dik da ba wani sosai ba, kuma Allah ya taimaketa babu wani jijiya da ciwon ya taɓa.

Tana ganin Ronnie ta yi saurin miƙewa zaune, dama shi take dakon jira tsawon kwanaki, tun da ta farfaɗo bata ga kowa a ɗakin ba, dan Black Tiger ya daina zuwa tin da yaga ta farka.

Ta rasa ina zata sa ranta, ta kwana ta wuni tinanin ina Ronnie yake, bata tinanin a in da take kamar yadda take tinanin a ina Ronnie yake. Shi ne yasa tana ganinsa ta yi gaggawar miƙewa zaune, shi ma da sauri ya ƙarisa cikin ɗakin.

Yau satinsa biyu da musulta amma ko sallah bai taɓa yi ba, dan bai san yadda ake yi ba, ita da zata koya mashi gata a kwance bai ma san ina take ba sai yau. Dan haka yasa bai yi ba sam sam, kuma a ƙagare yake da ta koya mashi ya yi ɗin, dan addinin ta ratsa zuciyarsa sosai.

Tsabar farinciki yana zuwa saman bed ɗin ya haye, cike da farinciki ya fara yi mata sannu yana kara bata hakuri, zuciya a karaye ya ce. "Sweetie yaya yafi karfinmu, ba zamu iya da shi ba, kawai ki barshi mu hakura". Ya yi maganar tare da riko hannunta yana murnar bata mutu ba.

Kai ta girgiza mashi, cike da kwarin gwiwa ta ce. "Bai fi karfinmu ba, kuma bai isa ya fi karfinmu ba, saboda mu Allah muka rike, da izinin Allah zamu canza yayanka, babu gudu ba ja da baya sai ya musulunta, dik azabtarwa da zai yi mana matuƙar ina numfashi ba zan janye kudurina ba".

Zaro idanun Ronnie ya yi sosai, cike da tsoro ay ce. "Sweetie kin ga abin da ya faru dake? Baki tsoron idan ya zo da ƙarar kwana ki rasa ranki?".

Ko a jikinta ta ce. "Tabbas idan na mutu a wannan hanya sai na fi kowa farinciki, a kan jahadi na mutu, a kan haryar isar da saƙon Allah da hidimtawa addini na mutu, dik wanda ya mutu a kan wannan hanyar ya yi shahada Ronnie, dik kuma wanda ya yi shahada makomarsa aljanna ce, dan haka babu gudu ba ja da baya, a da ina tsora ce da hakan, amma yanzun na kara samun kwarin gwiwar zan iya".

Sosai ya yi mamakin jin kalamanta, ya san da farko a tsorace take, to yanzu menene ya bata confidence har haka?.

"Kana mamakin menene ya kara mun kwarin gwiwa kenan ko?". Ta jefa mashi tambayar ne ganin cewa ya afka duniyar tinani.

Kai ya gyaɗa mata alamar e abin da yake tinani kenan. Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "Ba komai ne ya kara mun kwarin gwiwa ba face wasu abubuwa da na gano dangane da yayanka".

Like wow ya zaro idanu, a ƙagare ya ce. "Wani irin abubuwa kenan?". Ɗan girgiza kai kaɗan ta yi alamar ba zai gane ba kenan, sannan ta ce.
"Ba lallai ka fahimta ba, amma dai na gano cewa yayanka yana da bala'in saurin fusata, na biyu kuma baya saurin sauka idan ya yi fushi, na uku kuma tabbas bayan zuciyarsa fara ce, gaban ce aka dabaibayeta da bakar fenti, tabbas idan muka yi galaba a kansa mutane dayawa zasu ji daɗi su huta, ina da yakinin akwai abin da ya rikiɗar da shi izuwa bakin mugu....."

Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Ai na faɗa maki tsananin kaunar mulki ya rikeɗar da yaya izuwa mugu".

Kai ta girgiza mashi alamar a'a, sannan ta ɗaura da cewa. "Ba tsananin kaunar mulki bane ta rikiɗar da shi, akwai abin da ya saɓa, tabbas yana san mulki, amma bayanta akwai abu mai karfi da ya rikiɗar da shi, tabbas zan gano ko menene nan na da jimawa ba dan saukaka aikin mu". Babbar magana, amma me kuke ganin ya rikiɗar da Black Tiger izuwa azzalumi idan ba giyar kaunar mulki ba?.

"Sweetie zaki iya kuwa?". A tsorace ya jefa mata tambayar.

"In Sha Allah zan iya, samun kwarin haske da na yi a kansa ba ƙaramin taimaka mun zai yi ba, kaga yanzu zan san ta yadda zan gudanar da aikina a kusa da shi, zan san ta yadda zan guji ɓacin ransa da zai iya sakawa ya cutar da ni, sannan zan koyi yadda zan sarrafa ɓacin ransa a dik lokacin da Black heart ɗinsa zata motsa, yanzu ka koya mun yadda zan yi amfani da magic ɗina, dan shi ma zai taimaka mun wajen ganin na sarrafa Black heart na yayanka".

Shi kansa a yanzu ya samu kwarin gwiwa jin kalamanta, ya ji kuma kamar zasu yi nasara, dan haka sai ya ce. "Zan koya maki amfani da shi, amma yanzu dai ki bani wani amsa da tin last week nike ta san sanin shi, daga nan sai ki bani labari a kan bayyanar Imam Mahadi, sai ki koya mun yadda zan yi ibada".

"Yayanka baya kallanmu ko?". Ta jefa mashi tambayar cike da damuwa tare da addu'ar Allah yasa Black Tiger bai gansu ba, ta manta ne kwata kwata ta saki baki tana ta magana.

"Nan cikin ɗakinsa ne, kuma na faɗa maki yana iya kallan ko'ina a cikin birnin nan amma ban da cikin ɗakinsa, dan yana ganin wannan mallakinsa ne komai dake ciki sai da izininsa zai motsa".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙa godiya ga Allah da yasa a ɗakinsa suke, sannan ta ce. "Me kake san tambayata tin last week?".

MY BEST PART AGAIN💘🦋

"Kin san na faɗa maki ina kaunar annabi Isa sosai, to shi ne fa na duba cikin litattafan addinin Kiristanci wato Bible dan na duba tarihinsa da ƴan uwansa, a nan ne na duba tun daga kan Annabi Ibrahim wato daga tushensa kenan, tsawon sati ina bincike ina karantawa, sai da na zo kan ƴaƴan Annabi Ibrahim ɗin ne na rikice, abin ya tsaya mun a rai ina san sanin gaskiya".

Ko kaɗan bata yi mamakin jin maganarsa ba, kuma bata so ta ji me ya rikita shi ba, dan a tarihin Annabi Ibrahim akwai abin mamaki, tasan bai wuce batu a kan Annabi Isma'il da Annabi Ishaq bane, dama su tarihinsu yana da ban mamaki da ɗan rikitarwa, sai ka yi karatu mai zurfi zaka iya ganewa, shi kuma bai zurfafa ba dole ya ɗan rikice.

"Kin san me ya rikitar da ni?". Ya katse mata tinani ta hanyar jefa mata tambaya.

Kai ta girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba..
"Abin da ya rikitar da ni shi ne, ance Annabi Ishaq shi ne rushen bani Isra'ila, shi kuma Annabi Isma'il shi ne tushen larabawa, kuma naga dikkansu ubansu ɗaya ne wato Annabi Ibrahim kenan, to ina san ki babbance mun ya aka yi zuri'arsu ta banbanta bayan kuma iyayensu guda ne, basu taso dikka a matsayin tushen larabawa ba, ya aka yi bani Isra'ila suka fito a tushen larabawa kuma?".

Ɗan gyran murya ta yi, wuyarta ya fara ɗan yi mata zafi, saboda jimawa da ta yi tana magana, bata gama samun sauki ba. Abin mamakin kuma shi ne Ronnie fa bai samu damar ganin ciwon wuyar nata ba, sam bai gani ba, shi a tunaninsa ma zazzaɓi ko ciwon kai ya kawota wannan ɗakin, shiyasa kuka ga hankalinsa bai wani tashi sosai ba, da ya gani ai da tashin hankalin da zai shiga abin zai sha gaban tinani, sanin zai shiga damuwa yasa Black Tiger ya yi amfani da magic wajen rufa mashi ciwon ya hanasa gani.

Kuma da ya ga ciwon na zai sanyata yin surutu dayawa ba.

Cikin nitsuwa da sanyin murya ta fara faɗin.
"Haƙiƙa Annabi Ishaq da Annabi Isma'il Alaihimus Salam sun kasance ƴaƴan Annabi Ibrahim (AS) ne, amma sun bambanta ta fuskar zuriyarsu da yadda aka danganta su da al'ummomi. Ga bayanin yadda suka banbanta da dalilin da ya sa Annabi Isma'il (AS) ba a danganta shi da Bani Isra'ila ba ya kasance shi ne tushen larabawa".

Ɗan jan dogon numfashi ta yi kafin ta ɗaura da cewa. "Annabi Isma'il (AS) ɗan Annabi Ibrahim (AS) ne daga mahaifiyarsa Hajara, wacce ta kasance daga ƙasar Misra. Zuriyar Annabi Isma'il kuma ta yi ƙaura daga Misra zuwa yankin Makkah, inda aka kafa zuriyar Larabawa ta asali keman, wato Larabawan Adnaniyya. Annabi Muhammad (SAW) fiyayyen halitta kenan shi ma ya fito ne daga zuriyar Annabi Isma'il (AS)".

"Annabi Ishaq kuma, ɗan Annabi Ibrahim (AS) daga mahaifinsa Sahra, wacce ta kasance matar farko ta Annabi Ibrahim (AS). Zuriyar Annabi Ishaq ta ci gaba da rayuwa a yankin Sham (Palastine a yanzu kenan) daga cikinsu ne Bani Isra'ila suka fito, waɗanda suka hada da Annabi Ya'qub (AS) mahaifin Annabi Yusuf kenan".

"Wannan suna na bani Isra'ila yana nufin zuriyar Annabi Ya'qub (AS) shi Annabi Yaqub ɗim shi ne Isra'ila, ainahin sunansa kenan Isra'ila, waɗan nan ƴaƴansa goma shabin nan da suka cutar da kaninsu Annabi Yusuf su ne suka ci sunan bani Isra'ila, wato yayan Isra'ila kenan. Dan haka dik manzannin da suka fito daga cikin zuriyar Ya'qub, irin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login