Showing 249001 words to 252000 words out of 403653 words

Chapter 84 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

104

wajen domin su yi magana da warrios ɗin. Jikinta har kerma yake yi ta ɗauko wani katan laspeaker ta miƙa mashi domin ya yi magana. Karɓa ya yi kafin yasa hannu ya buga belt ɗin dake wajen mai sautin gaske domin ya samu attention na warriors ɗin.

Aikuwa yana bugawa gabaɗayansu suka juyo a kansa, kan kace me dik sun haɗu a gaban stage ɗin, da gudu master ya hauro sama shi ma da nufin ya dakatar dasu, shirinsa shi ne ya capke Ronnie da kokawa ya dakatar da su.

Ronnie ya fahimci hakan, dan haka sai da ya bari ya hauro yasa kafa da karfi ya takesa a kirji da karfi a in da ya yi baya baya ya ganganra kasan stage ɗin, ya faɗi ƙasa a gaban warriors, cike da bada umarni ta cikin laspeaker Ronnie ya ce da mayakansu na Robbot guda biyu da su kama master su jefa mashi shi a cikin prison na empeir ɗin. Tsalle Sweetie ta buga tare da cewa. "Good my bro".

Warriors biyu ne suka capki master suka wuce da shi, ga shi robbot ne bai isa ya gwada masu fin karfi ba, kuma Ronnie shi ne mutum na biyu bayan Black Tiger da aka shigar masu da su rinƙa bin umarninsa a cikin kwakwalwarsu, dan haka tin da ya ce su kai master prison ba makawa sai sun kaisa.

Attention ɗinsa Ronnie ya bayar a kan sauran warriors da sun haura sama da 3k a wajen, cike da bada umarni ya ce su yi maza su shiryawa yaki basu da isasshen lokaci an kawo masu hari. Sannan ya ware wasu warriors da zasu iya kai 300 ya umarcesu da su tattara mata, tsofaffi da yara, su tarasu waje guda, su basu karisa kada su bari wani abin ya samesu. Daga karshe ya wari wasu warriors ɗin ya umarce da idan yakin ya ɗauki zafi fiye da tunaninsu to fa su tashi jiragen eagle dromes na yaki su fara ɓarin wuta daga sama. Yana kai karshen wannan magana bai gama rufe baki ba suka fara jin rugugin tashin wuta daga cikin empeir ɗin.

Cikin ɗaga murya Ronnie ya ce ku je, daga haka ya riko hannun Sweetie da gudu suka sauko kasan stage ɗin suka nufi cikin empeir ɗinsu wajen Black Tiger kenan.

Wato idan ka yarda da Allah wlh cikin sauki zai kare ka daga sharrin dik wanda ya nufeka da sharri ba tare da kasan ya yi ba, kun dai ga aya a kan Floris, ta nufi Sweetie and Ronnie bayin Allah da sharri, to da yake su Allah kawai suka rike ga shi ya juyar mata da aniyarta a kanta, my people's me kuke tinanin yasa Black Tiger a cikin wannan hali? Ya kuke tinanin wannan yaki zai kasance babu Black Tiger? To mu dai bari mu je wani part ɗin mu dawo.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥

Zaune Auta take a gaban tabkeken s-p na gidanta da Smart ya mallaka mata, tana sanye da short army trouser mai shegen kyau da ya tsaya mata a iya gwiwa, sai kuma white shirt daga ta sama, ta yi shiru haɗe da buga uban tagumi tana tinanin Hoorain.

Manya manyan ƙosassun dolphin fish ɗinta suna ta wasa a cikin ruwan, sai fito da kansu waje suke yi suna taɓata dan ta zo su yi wasa amma taki kulasu, tana cikin damuwa, kun san dolphin idan ka saba wasa da su da sun ganka za su yi gaggawar fitowa saman ruwa, so ita a koda yaushe suka zo France ita da Jaish tana wasa da su sosai, ita ma tasa Smart ya saka mata su ɗan wasa, amma wannan karon sai ga shi taki kulasu, sai tsalle suke yi su fito su koma.

Hoorain kawai take tunani baiwar Allah, ta yi rama sosai, yau kwananta biyu a gidan nan tare da Smart and Pretty, sai dai ko kaɗan bata san a wace duniya take ba, ga shi tin da suka dawo Smart bai natsu ba bare har ya san halin da take ciki, baya zama saboda aikinsa, wani lokaci sai cikin dare yake dawowa,lokacin kuma sun yi barci. Ita kuma Pretty dama ba wani cika damuwa da abubuwa ta yi ba, bama zata fahimci halin da take a ciki ba bare har ta tausaya mata ko ta bata shawara. Ji take tamkar ta sanya hannu bisa kanta ta kurma ihu ko zata samu sauki, wayar da Smart ya bata wanda zata rinƙa kiransa idan tana buƙatar wani abin sai ruri yake yi ta ɗaura shi a saman kujerun dake kawayen da wajen, da alama ta yi nisan da bata ma jiyo ringin na wayar ba.

Guyson ne kuma yake ta kiranta, dan ya gaza samun kwanciyar hankali da sukuni, jiya ita ta kirasa da number da yake ta haddace numbersa, ta ce mashi ya dubi girman Allah ya je ya haɗata da Hoorain a waya, da farko yaki yarda, daga baya da ya fahimci zata iya cutuwa sai ya ce tabbas zai je koda dad zai jefashi cikin prison ne, to shi ne yake ta kiranta yanzu bata ɗaga ba hankalinta ya yi nisa.

A can cikin gida kuwa, Pretty ce tsaye a gaban dressing mirror na ɗakin Smart, bata san cewa bedroom ɗinsa bane, ta tashi daga barcinta kawai ta je ta afka cikin ɗakin a garin neman hanyarta na san fita waje ta duba Auta, ta san Auta tana yawan zama a wajen dolphins ɗin nan, sai dai bata iya fitar da kanta wajen ba, sai dai su je a tare da Autar, saboda hanyar yana da sarkakiya sosai.

Ganin kanta a cikin wani bedroom ɗin yasa ta fara kewaye a ciki tana zuba ƙauyancinta, taga bedroom ɗin ya fi nasu haɗuwa da ƙawatuwa sosai, ta ga abubuwan da bata taɓa gani ba, Allah ya yi zata zo France, dan suna rike da hannun juna ita da Auta a lokacin da Smart ya ja hannun Auta suka baro kingdom of power, sai Auta bata saki hannunta ba ta jata suka tafi a tare. Time da suka je airport Smart ya nuna ba zai tafi da ita ba, sai Auta ta ce ya kyaleta kawarta ce kuma suna san juna, dalilin da yasa ya zo da ita kenan.

Leke leke ta shiga yi mashi kamar ya aikata, kun san ita Pretty kifin rijiya ce, ba kamar Sweetie take ba, wayonta da sauki, ga bala'in tsoro ba confidence, sai shegen shagwaɓa da cin abinci. Amma idan baku manta ba ita ɗin gwana ce wajen iya fitina, bata ganin abu bata taɓa ba. Dan haka sai ta shiga yi mashi taɓe taɓe, dik abin da ta gani sai ta taɓa.

Cikin taɓe taɓen nata ne hannunta ya kai ta buɗe drawer mirror, tsautsayi dai baya wuce ranarsa, Smart yana rufe drawer da password, idan ya buɗe ya ɗauki abin da zai ɗauka, da ya tura drawer zata sake shiga password, so yau da ya tura drawer sai bata turu da kyau ba bare ta shiga password, hakan ya bata damar buɗewa.

Wasu robobi ta gani a ciki kamar na zuba magunguna haka, tsabar fitina da kiran ajali wanda in ya kira dole a amsa sai tasa hannu ta ɗauki roba guda ɗaya, har da ɗan saka karfinta wajen buɗe robar da ta ɗauko. Tana buɗewa wani abu ya fita kamar hayaki haka, shakarsa ta yi a take ta saki robar ya faɗi ƙasa.
Lokacin guda jini ya fara gangaro mata daga hancinta da kuma hakinta, ji ta yi tamkar am shake mata wuya wuya da karfi, hannunta dikka biyu ta kai ta riki wuyar tata tana kwalalo idanu waje. Da kyar ta iya juyawa tana san barin wajen, sai dai ko motsa kafafunta ta ƙasa bare ta iya tafiya.
A take a wajen ta yanke jiki ta faɗa saman kirjinsa, dan yana tsaye a bayanta, da ta juyo ta fita a cikin hayyacinta ne yasa bata iya gane akwai mutun a kusa da ita ba. Shi kuwa dama ya fito daga wanka yana cikin dressing room yana shiryawa zai fita, to ya fito daga dressing room ɗin kenan yaga ta ɓalle marfin robar, shi ne ya kariso wajen ya tsaya a bayanta, ta cikin mirror dake gabansu yake kallan yadda jini ya fara zuba daga hancinta har izuwa bakinta.

Fararen kaya tas ne a jikinsa, da ta faɗa jikin nasa kaf ta ɓata shi da jini. Allah ya cecesa yana sanye da face mask a fuskarsa, dan shirin fita ya yi, da wlh a tare zasu mutu da ita, dan in ya shaki wannan chemical ɗin shi ma ba zai tashi ba, dama sai sun saka face mask, hand's gloves da wasu irin riguna na leda kafin suke buɗe chemical ɗin, kun tuna yadda suke aiki a wajen haɗa makamansa ko? To haka suke yi kafin amfani da waɗan nan shegun chemical, kisa suke yi nan take, ita kuwa da fitina da rashin sani ta je ta buɗe.

Sosai ta bakanta mashi rai, domin waɗan nan chemical ɗin suna da wahalar samu, shiyasa ma ya ɓoyesu a gida, wannan ɗan kaɗan ɗin da ta zubar mashi millions of dollars yake, chemical ne mai haɗarin gaske na haɗa nuclear mai karfi sosai, yanzu haka gabaɗaya ya tsastsaga mata kafa, saboda sake shi da ta yi ya faɗi ƙasa ya ɗan taɓa ƴan kafafunta.

Jininta a kafa ne ya fara zuba, lokaci guda ta sandare kamar wadda lantarki ya busar. Siririn tsaki ya ja ya rasa me ɗaya zai fara yi?. Daga bayansa muryar Auta ta katse shi da cewa. "Yah Omerish kaga Pretty? Yanzu na je ɗaki ban ganta ba". Da yake ya bawa kofar shigo baya ita kuma Pretty tana kwance a kirjinsa sai yasa Auta bata iya gane Pretty na ɗakin ba.

Ya lura da akwai shakuwa sosai a tsakanin Auta da Pretty, dan haka sai ya ce mata. "Jeki parlour ina zuwa". Ya yi mata hakan ne dan kada ta ga gawar Pretty hankalinta ya tashi, dama daga jiya zuwa yau ya fahimci tana cikin damuwa, daren jiya da ya dawo ya shiga bedroom ɗinsu, a nan ya sameta tana sambatu cikin barci, yau da safe kuma kafin ya shiga wanka sai da ya tsaya a jikin window ɗinsa ya zuba mata idanu tana zaune wajen dolphins, dama ya sa a ransa yau idan ya dawo daga office ya je ainahin gidansu ya dawo zai tambayeta me yake faruwa?.

Juyawa Auta ta yi ta fita hankalinta bai kai kan jinin kafar Pretty dake malale a kasa ba. Tana fita ya raba jikinsa da nata, da hannu ɗaya ya ɗagata izuwa balconynsa, saman ɗaya daga cikin kujerun dake wajen ya kwantar da ita.

Ita kuwa Auta parlour ta koma ta zauna tare da buga tagumi tana jiransa. A gurguje ya fito daga cikin bedroom ɗin nasa, rufe kofar ya yi dan ma kada ta Autar ta shiga taga gawar Pretty, bai tsaya bi ta kanta ba ya nufi waje yana ce mata yana zuwa. Ta yi mamakin ganin yadda yake tafiya tamkar zai haɗa da gudu, amma bata kawo wani mummunar tinani a ranta ba, tana san tambayarsa ya ga Pretty, sai dai kafin ta buɗi baki tuni ya sauka ƙasa.

Shiru ta yi tana tinanin ina Pretty ta shiga kuma?. Can kunnuwarta suka tsinkayo mata wayar dake ruri a waje. Da sauri ta miƙe ta nufi waje. Filin dolphins ɗinta ta koma, wayar natan ne dai yake ruri. Tana zuwa ta ɗauka, guyson ne yake kiranta, a hanzarce ta yi picking tare da kara wayar a kunnenta tana faɗin.
"Hello Yah Omar". A maimakon ta ji voice ɗinsa sai jin muryar Hoorain ta yi ya amsa mata da Hoonaira. Ai bata san lokacin da ta zube ƙasa a wajen ba, tamkar zata kurma ihu saboda daɗi, har ta rasa abin faɗe ma.

Shi kuwa yana kwance a kan gadan jinya, da shi da Abbonsa dik suna gadan jinya, gara Abbonsa ma ya ɗan samu lafiya, ya farfaɗo yana iya gane waɗan da suke kansa. Shi kuwa Hoorain yana gab da mutuwa King ya samu labarin daga bakin masu tsaronsa cewa Hoorain zai iya rasa ransa a kowani lokaci daga yanzu, hakan yasa King ya ce a fitar da shi a kaisa hospital. Time da aka fitar da shi ranga ranga aka wuce da shi hospital, baya iya taka kafafunsa ma, sai ɗaga shi warriors suka yi. Jiya aka fitar da shi, yanzu a can guyson ya je ya kai mashi waya ba tare da sanin King ba.

Wai me ya faru a kingdom of power bayan tafiyar Smart ne?.

Cikin bedroom ɗinsa King ya nufa hankalinsa a tashe. Shi kuma Smart kai tsaye babban gate na kingdom ɗin ya nufa. Sun zo dai'dai wani waje dake kusa da fadar King ta biyu, idan baku manta ba na faɗa a baya fada gudu biyu ne a kingdom of power, so King baya amfani da ɗayan, saboda ainahi na mahaifinsa King Abdul Malik ne, to fadoji a da suna haɗe ne, sai ka shiga ta cikin ɗaya zaka je ɗaya, bayan hauwar King Zuhair mulki sai ya rabasu, aka toshe kofar tsakiyar aka buɗewa kowanne nasa kofar yana cin gashin kansa.

So sun zo giftawa ta dai'dai wannan fada na King Abdul Malik wani irin haske ne ya bayyana daga cikin fadar ya shiga cikin motar tasu, sarai Smart ya ga hakan, amma hankalinsa ta yi gaba wajen tuƙi, bai wani bi ta kan hasken ba, ita kuma Auta dama ta kifa kanta a kan gwiwowinta tana kuka, Pretty dake zaune kusa da ita a kanta wannan haske ya sauƙa, dama saboda ita ya fito, saboda Spender dake tattare da ita, dik yadda aka yi da akwai alakar Spender da wannan fada, ina ga yana daga cikin dalilin dayasa King Zuhair ya rufe fadar ƙin faɗawa mutane gaskiya ya yi, dik yadda aka yi akwai abin da ake ɓoyewa, amma lokaci zai warware mana komai.

Ba iya haske ne kawai ya fita daga cikin wannan fada ba, akwai abubuwa da dama da suka nuna alamar bayyanar Spender a wajen. Sai dai da yake Smart da gudu suka gifta wajen sai basu ga komai ba bayan wannan haske.

Akka dake cikin bedroom ɗinta tana kwance sai da ta zabura ta miƙe zaune a lokacin da su Pretty suka gifta wannan fada, a jikinta ta ji hakan, take ta ji jiri na ɗibarta, jikinta ne ya fara tsuma. A lokacin su uncle Abbas sun koma part ɗinsu. Wayarta Akka ta ɗauko, number King Zuhair ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka, a lokacin suna tsaye a tsakiyar bedroom shi da momma suna ƙoƙari neman Smart dan ya dawo.

Muryar Akka na kermar ta ce. "Zuhair dik yadda aka yi Spender ya dawo cikin Masarautar nan, ku yi gaggawar gano in da yake". Yadda take magana ya yi matuƙar ɗaga hankalin King, a hanzarce ya ce mata. "Ki kwantar da hankalinki Akka dole nema mu nemosa, gani nan zuwa kin ji?".

Da okey ta amsa mashi kafin ta katse kiran, hankalinta ya yi matuƙar tashi, dik yadda aka yi Spender abu ne mai tsananin haɗarin gaske kuma barazana ne ga al'umma shiyasa take shiga damuwa sosai,!.

Kingdom of power dai ya rikice.

A ɓangaren su Mammie kuwa, kuri da cika baki ta rinƙa yi a kan wlh ba zata kyale Smart ba, sai ta ɗauki mummunar mataki a kansa, dan haka dole su fara gagarumin shiri, ta yi rantsuwa da Allah ba zai daki Sarina a banza ba, uncle Abbas dai shiru ya yi yana jin surutan nata ba tare da ya ce uppan ba.

Ɓangaren su Khadija kuwa, ita dai Khadijah tana cigaba da kula da babynta babu wani damuwa abinta, yaro sai kara wayo yake yi yana rikiɗewa yana komawa jinin Akka sak, dik yadda aka yi akwai alaƙa ta jini tsakanin yaron nan da Abdul Malik family.

Ita kuwa Zee tana nan da wannan hali nata, ta koma bedroom ɗin mama Haulat a part ɗin Jaish da kwana, dan ta yi fushi ta sallami part ɗin surukarta mama, ta fa kamu da san Dr Raj, amma ta tsani uwarsa, kai wato akwai dirama a gaba fa.

Ita ma Fanan ta koma bedroom ɗaya a part ɗin Jaish ba tare da sanin momma ko yarjewarta ba, shi ma Jaish bai sani na, shi yana can ma garden a can ya kwana, yaki dawowa part ɗinsa, wai baya san kwata kwata su haɗu da momma dan tabbatar rashin kunya.

A ɓangaren shi kuwa Jawad yau kwanan zaune ya yi yana rarrashi, ita dai ta ce ba zata zauna da shi ba, sai dai kuma bata da kafar tafiya wajen mummyn nata. A can kuma mummyn nata tana can tana faman sallar dare tana rokan Allah da ya rabata da shaiɗanin da yake ƙoƙarin ruɗar zuciyarta dan kawai Smart ya bayyana a matsayin ɗan kin, shaiɗan na san ruɗarta a in da take ta jin rashin daɗin bayyanar nasa, ance zuciya bata da kashi, haka ne kuwa, domin kuwa ga shi nan dai mummy ma shaiɗan nasan kai ta ya barota, tsawon shekaru yana zaune da kowa da zuciya ɗaya da amana, bata ɗauki duniya da zafi ba, yanzu kawai abu na neman birkice mata.

Sai addu'a take yi tana karatun Alqur'ani mai girma, to fans ɗinta sai ku tayata da addu'a kada shaiɗan ya yi galaba a kanta.

Idan muka waiwaya ɓangaren Mahnoor kuwa, momma ta kira wayat Jaish har ta gaji ya ki ɗagawa, dan a cewarsa bai san me zai ce mata ba ɗan albarka. Haka momma ta tsaya Dr ɗinta mace ta yi wa Mahnoor dik abin da ya dace, ta kuma bata magunguna da suka dace sannan ta tafi, baiwar Allah ta ga bone ita kam.

Ita kuwa Mahreen sai dai shirin Allah, dan kuwa a cikin dressing room na momma ta laɓe tana ganin su Omaid suka rinƙa jigila da guyson suna ƙoƙarin gyara ɓarnar da suka aita. Da kyar suka samu suka iya cire mashi dafin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login