Showing 108001 words to 111000 words out of 403653 words

Chapter 37 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

66

kina shan wahala".

Wani irin daɗi ta ji ya ziyarceta a ranta, tabbas bata cire ran Hoorain zai sota ya kuma bayyana mata soyayyarsa ba a yanzu.

Jinjina mashi kai ta yi alamar ta bashi dama, ai tin kafin ta gama zayyana ta bashi damar ya ɗauketa cak sai saman kirjinsa na zakunan mazajen nan, ya riko hannun Pretty suka kutsa cikin dajin, suka koma in da suka fito, wato wajen da ya gyara ya tanada dominta, waje mai cike da yanayin soyayya da nishaɗi.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangare guda kuwa, Sadauki kusan hauka ya yi a lokacin da ya kawo masu ziyara bai samesu a wajen ba, yau a karon farko sai da ya durkushe gwiwowinsa a ƙasa, dik da ba'a iya ganin face ɗinsa sai idanu, yau sai da tashin hankali ta bayyana acikin idanun nasa mai firgitarwa.

Cike da tashin hankali da damuwa ya fara kewaye arear wajen yana nenan ta ina zai gansu? Damuwarsa ma yadda Auta take da ciwo a ciki bata warke ba, hakan ta kara ɗaga mashi hankali sosai, jikinsa har kerma yake yi yana tsuma. Ya ɗauki a kallah mintuna 30 yana kewaye a yankin yana nemansu, dan gani yake suna nan a wajen basu yi nisa ba.

Wani irin damuwa ya ƙara shiga a lokacin da ya yardanwa kansa basu nan, basu wannan yankin kwata kwanta sun yi nisan zango, ga shi babu wata makama da ya gani wanda zai iya hasashen meyafaru da su? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne kawai kalaman da yake ta maimaitawa, ya shiga damuwa na wuce misali.

Da kyar ya iya jan kafafunsa ya kutsa cikin dajin da ya je ya cigaba da nemansu a can ko Allah zai sa ya gansu.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

After some minutes, rana ta take sosai, zaune Pretty da Auta suke a saman dutse kusa da wata bishiyar gwaiva, hannunsu rike da ganyen ayaba mai ɗan faɗi, gasassun kifi ne a saman ganyen ayabar wanda Hoorain ya kawo masu, ga kayan fruits a gefensu, basu san daga ina ya samo kifin ba, su dai ya ce masu su yi zaman jiransa yana zuwa, shi ne ya dawo masu da kifi gasassu kuma ya sake tafiya ya barsu ya ce yana zuwa.

Sai rarraba idanu Auta take yi tana jiran taga ta ina zai ɓullo, ta gaji da jiransa, dik bayan second ɗaya kara ɗaukin san ganinsa take yi, bata gajiya da shi, a kullum tana san taga tana a tare da shi.

Ita kuwa Pretty tinanin kifin kawai take yi, kunsanta ita da ci akwai amana, sai tinanin kifin take yi, ya bata sha'awa, ta yi mamakin ganin irin gashin da ya yi masu, tana da yakinin a wajen wancan wuta da ya kunna mata dan jin ɗumi ɗazun nan ya gasa masu, ya kamo kifin a kogi kenan ya gasa a can.

Gajiya da gafara sa bataga kaho ba Auta ta yi, dan haka sai ta miƙe tsaye, a hankali ta ce. "Pretty zauna ki jirani ina zuwa".

"Ina zaki je ki barni?". Ta jefa mata tambaya.............. "Ke dai ba zan yi nisa ba kuma ba zan wani jimaba, ina zuwa yanzu".

Jinjina kai Pretty ta yi tana cigaba da gutsirar kifinta tana kaiwa baki abinta sarkin ci kawai, har yanzu dai bata canza hali ba a fagen ci.

Saukowa kasan dutsen Auta ta yi, sannan ta miƙi hanyar da take tinanin yana ta wajen. Tana tafiya tamkar mai tsoron taka ƙasa, saboda ciwonta idan ta yi sauri zai fama. Tafiya a hankalin yasa bai ji zuwanta ba, yana tsaye saman dutsen dake gaban wannan koramar, yana ƙarisa wanke takobinsa da bai samu ya yi ɗazun ba.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Tin da ta doso wajen ta hangosa daga nesa tsaye saman dutse, gabanta ne ya yi wani irin faɗuwa sosai, kirjinta ya bada dukan uku uku, bata san time da ta ɗaga kafarta da sauri wajen ƙarisawa garesa ba. Sam bai ji alamarta ba, ya bawa hanyar da take zuwa kuma baya yana karisa wanke wanke takobinsa da bai ƙarisa ɗazun ba. Ya kuma ɗauro alwala dan ya yi sallah.

A wani irin slow ta ambaci sunan cike da salon da bata san ta iya shi ba. "Hooooooooooraiiiiiiiiiiiiin" haka ta faɗi sunan.

Da karfi ya juyo domin ya ji abin ne kamar almara, kamar voice ɗinta kamar kuma ba nata ba, sai ya ji kamar mafarki kamar kuma gizo, hakan yasa ya yi saurin juyowa da karfi.

Juyowa da ya yi da karfi yasa kyakkyawar dark black curly hairnsa ya watse kamar wata mace kamar kuma wanda aka hurawa gashin iska ya watse haka.

Ya ilahi ya lilliahi! Mutuwar tsaye ta yi tana kallansa, kamar wadda aka zarewa rai, ta kame kam. Shi kuwa cikin zafa ya diro ƙasa daga saman dutsen, da wani irin gudun gaske ya nufota. Zaro idanunta ta yi tana mamakin me zai yi mata da ya nufota da irin wannan uban gudun kuma? Ga lafiyayyar takobinsa a hannunsa.

Ku me kuke tinanin zai faru? Yau dai ta ganshi babu hular yaki, ko ya kamanninsa take? Meyasa ya nufeta da gudu dan ta gansa bai rufe fuska ba, meyasa ta yi sumar tsaye dan ta gansa? To ni dai bari in leƙa Black world muga me suke ciki kafin in dawo muga me zai yi mata kuma mu ga ya kamanninsa yake da yake ɓoyewa tsawon shekaru, yau dai komai ta bayyana..........🥱

••••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••••🔥

A wani irin razane Ronnie ya juyo da kallonsa a kan yayan nasa. Wani irin razana ya yi ganin yadda Black Tiger ya ɗaure fuska tamau alamar babu tausayi babu imani.

Nan take wasu irin zufa suka fara keto wa Ronnie babu kakkautawa, shikenan yau Sweetie ta ja mashi yanka kazar wahala, watar azabarsu ce ta tsaya.

With her full confidence sweetie ta ce. "Ronnie kada ka damu, kwantar da hankalinka ka dai'na yin zufa, Big bro kana ɗagawa Ronniena hankalifa, kuma ni bana san hakan, ka dai'na kada rai'na ya ɓaci". Yadda ta yi maganar yadda kuka san uwar Ronnien ce take magana.

Ronnien da ya kusa sakin fitsari a wando saboda tsorata ne ya kara zaro idanu waje tare da juyowa gareta da kyau ya kuma saki hannunta da ya rike.

Sai dai kafin ya kai ga juyowa gareta da kyau Black Tiger ya juyo magic eyes ɗinsa a inda tamkar walkiya haka ya fisgota ta ƙariso gabansa. Cikin zafa rai a matuƙar ɓace ya sanya hannunsa ya yi mata wani irin mahaukacin damka a wuya mai razanarwa wanda sai da ta ji kamshi kamshin mutuwa.

Ta ɗauka wasa yake yi, bata san baya ɗaukar wargi ba, a tinaninta idan tana tsokanarsa ta wannan hanya zata iya samun damar shiga jikinsa har su fara aiwatar da plan ɗinsu a kansa, bata san shi ɗin tamkar dutse yake wanda huda jikinsa a shiga ba ƙaramin abu kamar yadda ta zata bane, in ta yi kokarin shiga jikinsa ya zo mata da karar kwana ma ai sai ta mutu ba damuwarsa bane.

Wani abin da baku sani bama, da farko wlh Ronnie ya so ya yi amfani da shiga addininta dan su samu Spender ne, dan ya lura tana san addininta sosai, shi ne kuma rauninta, amma da yake Allah ba'ayi mashi wayo kuma ya so shi da rahma, sai ya dasa mashi kaunar addinin a ransa na gaskiya wanda zai ma iya sadaukar da ransa a kan addinin ba tare da ya ji komai ba!!.

Da gudu cikin tashin hankali Ronnie ya nufi Black Tiger domin ya bashi hakuri ya saketa. Sai dai bai kai ga ƙarisawa wajen ba ya tsaya cak ya kasa gaba ya kasa baya kamar mutum mutumi.

Ita kuma ya ƙara shaketa da kyau da kyau, tin tana iya ganinsa har ta fara gani dishi dishi. Babu imani babu tausayi ya yi wurgi da ita ta tafi ta bugu da jikin swan chair dake ɗakin nasa ta faɗi kasa.

A wahalce ta saki wani irin azabbabben kuka mai tsuma zuciyar mai imani ba irin black heart ɗinsa ba, shi ko kaɗan bata bashi tausayi ba. Bai bata damar ta yi ƙoƙarin jawon numfashinta ba ya sanke amfani da magic ɗinsa ya janyota gabansa tana zube a ƙasan, shi kuma yana tsaye kamar wanda aka sassaƙa, ransa a matuƙar ɓace ne.

Ko kaɗan bai ji kamar zai tausaya mata ba, kafarsa guda ɗaya ya ɗaga ya sauke mata saman wuyarta, ya taketa ba tare da kalli in da take ba. Wani irin bargon azaba ne ta ji ya lulluɓeta, da gaske niyar kasheta ya yi, hasashen Ronnie ya saɓa hanya da ya ce mata Black Tiger ba zai iya kasheta ba, ashe dai sai in black heart ɗinsa bata motsa ba, tsab zai aikata fin kisa.

Sweetie ta shiga gonarsa dayawa, dama kuma already ransa a ɗan ɓace yake sakamakon addaba mashi da duniyar sheɗanu suka yi, suna kutsawa cikin ruhohin tsafinsa suna birkita mashi lissafi, abin yana bakanta mashi, yana ta ƙoƙarin ya rufe dik wata hanya da zasu iya riskar ruhohin tsafinsa ita kuma ta zo zata kawo mashi wargi, shi ne ya tattare haushin waje guda dikka ya sauke a kan!.

Bai ɗauke ƙafarsa daka samar wuyarta ba har sai da yaga ta daina numfasawa ta ɗauke diff rai ya yi halinsan! Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Sannan ne ya ɗauke ƙafarsa tare da yunƙurin zai yi ball da ita ta fice mashi daga ɗaki, sai kuma ya tina idan ya yi hakan gawar tata zata tarwatse mashi a cikin ɗaki ta ɓata mashi waje, dan haka sai ya yi amfani da magic ɗinsa wajen ɓatar da ita, kafin kyaftawa da bismilla babu ita babu rabarinta, ta ɓace a wajen.

Sannan ya yi amfani da magic ɗinsa wajen dakatar da bugawar numfashin Ronnie, ya yi kamar ya sumar da shi, dan in ba haka ya yi ba yau zai iya kashe Ronnie dan ɓacin rai, saboda yasan ba zai bar shi ya kwana lafiya ba, a kanta zai hana kowa barci ya yi ta kuka, so gara ya yi mashi haka zuwa da safe ya tashesa, kafin nan kuma zai yi ƙoƙarin ganin ya shafe mashi tinaninta a babin rayuwarsa gabaɗaya, e lallai akwai aiki babba.

Team Ronnie ina kuke, me kuke tinanin zai faru? Za'a shafe kwakwalwar Ronnie, damuwata ɗaya shi ne ya batun musuluntar da ya yi? Kenan zai koma krista?😥💔

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, wannan yafi komai ɗaga mun hankali, bana san ya koma krista wlh............😥💔

To bari dai mu leƙa Dubai kila kafin mu dawo abubuwa zasu ɗan yi sassauci.

••••••••••••••••••DUBAI•••••••••••••••🔥

Zaune Sharifat take a bakin bed ɗin dake cikin A&E room ɗinsu, ta buga uban tagumi tare da zubawa Leesharh dake kwnace a saman bed ɗin idanu tana kallonta, yau tsawon kwana uku kenan da Ramish yasa hannu aka saketa saboda ba wayarta bace, Bilal ne ya ɗaukota ya dawo da ita, Dr Raj yana kula da ita, shi ne Dr ɗinta, shi ma sai da Bilal ya sanya baki ne ya yarda yake dubata, da farko ya ce shi ba zai iya duba lafiyar wadda ba'a san asalinta ba, infact shi baya ma san ganinta, sai da Bilal ya umarcesa a kan hakan sannan ne ya yarda ba dan ya so ba!.

Tsawon wannan kwanaki ukun Leesharh bata san in da kanta yake ba, da farko ma Dr Raj ya ce ta mutu, sai daga baya suka iya jiyo sautin bugawar zuciyarta can ƙasa ƙasa kamar yana san dakatawa ya dai'na aiki.

Allah sarki ta ji horon manyan kai, sai da ta zaɓi mutuwa a kan hakan, a gaskiya Ramish mugu ne bashi da imani wlh, dama ga shi kullum yana maganar kada daddynsa ya yarda da kowa, kai gaskiya guy ɗin nan Ramish bashi da daɗi, ya azabtar da ita over.

Dikkan jikinta bandeji, an mammanneta ta ko'ina kamar wata pacin tayar mota, hannunta na dama ma ya samu karaya, wai a haka ma fa dan Bilal yana dakatar da Ramish ɗin, da ya jima da kasheta.

Sai kuka shafiat take yi hawaye bibbiyu, kwanaki uku Leesharhnta taki motsawa, tin tana sa rai har ta fara karaya, jikinta dik ya mutu ta fara tinanin ko dai mutuwa da gaske Leesharh ta yi basu sani ba?.

Yanzu kun gano daga in da Omaid and Obaid suka gado mugunta da iya horor da mutane ko?

Shi kansa Abu Abdussalam sai da ya razana a lokacin da Bilal ya dawo da ita, sosai ya yi wa Ramish faɗa a kan yi wa mutum ɗan adam irin wannan horo babu daɗi, ya ce ko namiji bai yarda ya sake hora shi kamar haka ba ballanta mace wadda ita sam babu gurbin wahalarwa a jikinta, ya rinƙa sassauta zuciyarsa gudun yin danasani gaba.

A ɗan fusace ya ce da Abbie. "Abbie danasani fa ka ce?!". "Kwarai danasani My son".

Kara ɗaure fuska ya yi kafin ya ce. "Babu wata danasanin da zan yi a rayuwata, dan haka ni ka dai'na faɗa mun hakan".

Da yake Abbie yasan halin kayansa sai ya koma sigar rarrashi. "Haka ne son, bana fatar ka yi danasanin nima, amma please ka rinƙa sassautawa, kaga macece fa ita, amma haka ka horata kamar ka riki kartin maza ƴan ta'adda".

Kansa a ƙasa ya jinjina tare da cewa. "Amma menene banbancin wanda ya so tasan bomb a wannan hall ɗin da ƴan ta'adda?".

Shiru Abbie ya yi, dan babu banbanci, gara ma ƴan ta'adda da sauki a kan wanda zai tashi bomb cikin wannan taro da sama da mutum 1000 zasu rasa rayukansu, har da makotan hall ɗin dik zasu iya kamawa da wuta su haɗa da mutanen dake ciki.

Miƙewa tsaye ya yi ganin Abbie ya rasa bakin magana. "Good night Abbie". Ya faɗa ba tare da jiran abin da zai ce ba yasa kai ya nufi waje. Da kallo Abu Abdussalam ya bisa har ya fice, ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaga hannu ya furta zafafan addu'oi kamar haka.

"Ya Allah ka shirya mun my son ɗina, Allah ka sassauta mashi wannan zafin zuciya tasa, Allah ka kara kare mun shi daga dik wata sharri, daga karshe Allah ƙasa ya kara zamtowa mai son na gasken gaske wato Allah ka haɗa zuƙansu shi da Sharifat na yi masu aure".

Shi kuwa Ramish, bedroom ɗinsa ya wuce, white jallabiyar jikinsa ya cire, ya rage daga shi sai sexy short and singlet............ My people's wai meyasa Yah Ramish yake san sexy kaya kamar wani mai aure ne?...🤔

Short ɗin ta kama shi sosai, dai'dai irin........ Na dai yi shiru kada ace na cika saka ido.

Toilet ya nufa dan ya yi wanka ya yi shirin yin barci. Bilal kuwa baya nan ya fita.

After some minutes ya fito sanye da sexy bathrobe milk color a jikinsa, ya yi masifar kyau sosai. Mayukansa masu kyau da tsadaya shafa. Yana tsaka da gyara gashinsa ta cikin mirror ya yi arba da face ɗinta t............


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




E..…...............17


After some minutes ya fito sanye da sexy bathrobe milk color a jikinsa, ya yi masifar kyau sosai. Mayukansa masu kyau da tsada ya shafa. Yana tsaka da gyara gashinsa ta cikin mirror ya yi arba da face ɗinta tana tsaye a bakin kofar shigowa, ta kasa gaba ta shigo ciki ta kuma kasa yin baya ta fita waje.

Kamar bai ganta ba haka ya yi, ya cigaba da abin da yake yi har ya kammala, bakin bed ya wuce ya zauna, cike da class ya ɗauko wayarsa, number da yake san kira ya shigar, babu suna number, hakan na nufin ba'ayi saving ɗinta ba.

Kira ya danna tare da kara wayar a kunnensa, bugu ɗaya aka ɗaga call ɗin cikin sauri. Daga ɗayan side ɗin Sharifat ta ce. "Hello wanenen?".

Wannan wayar tasa Bilal, Dr Raj, Rizwan sune kawai suke da phone number, shiyasa Sharifat bata ma san wanene bane, wayarta kuma ba irin nasu bane da in sun kira zai baka suna da location ɗin in da mai kira ya kiraka haɗe da gajeran bayanai a kan mai kiran.

Shiru ya yi kamar na minti ɗaya. Yana jinta ta kara faɗin wanene? Bai yi kamar zai amsa ba, ta sake tambaya na uku, nan ma shiru. Ranta ne ya ɓaci, dama ga damuwar rashin lafiyar Leesharh, sai abin ya kara yi mata yawa, dan haka cikin faɗa ta ce. "Wannan wani irin iskanci ne a kira mutum kuma ba za'ayi magana ba? To koma wanenen kada a kara kirana".

Sai da ta kai aya a zazzaga masifar tata zata katse kiran ne ta tsinkayo sexy voice ɗinsa cikin nitsuwa ya ce. "Ki kawo mun cappuccino yanzu".

Ai tana daga zaune a bakin bed ɗin Leesharh bata san time da ta miƙe tsaye haɗe da ciro wayar daga kunnenta ba, bata taɓa zaton Yah Ramish bane. Innalilahi wa inna ilahir rajiun shi word ɗin da ta rinƙa maimaitawa babu kakkautawa, gabanta sai faɗuwa yake yi, ƙoƙarin tinano abubuwan da ta faɗa cikin masifar da ta zazzaga ta fara yi ko Allah zai sa ta tina komai ta ji ta yi zagi a ciki ko bata yi ba, yau ta shiga uku shi ne abin da zuciyarta yake faɗe.

Shi kuwa yana gama faɗar abin da ya yi niya ya katse kiran, a hankali ya maido da kallonsa a kan Ummie dake tsayen mashi a bakin kofa, kamar dai akwai muhimmin abin da ya kawota ɗakinsa, dan bata zuwa part ɗinsu sai dole.

"Zan iya sanin abin da ya kawoki nan?". Ya jefa mata tambayar tare da kawar da kallansa daga kanta.

"Da gaske ne wai ka saki Leesharh? And da gaske ne wai ba ita ta yi maka laifi ba?". Shi ne tambayar da Ummie ta jefa mashi, daga ganin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login