Showing 165001 words to 168000 words out of 403653 words

Chapter 56 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

134

mun"............. Tin da ta fara magana ya dawo da kallansa a kan wannan ɗan bakin nata da take turowa, gabaɗaya sai ya ji shi a network, wani irin kasala ne ya saukan mashi lokaci guda. Da kyar ya daure ya tako izuwa in da take.

Yana zuwa bai wani ɓata lokaci ba ya zauna a saman sofa yana sauke ajiyar zuciya. Zama ita ma ta yi kusa da shi, sai a lokacin ta ce. "Ina wuni baby?"........... "Sai yanzu za'a gaisheni my ƴan'mata?". Cikin zolaya ya yi maganar.

"To zumuɗin ganinka ya ja na manta da gaisuwar, amma yanzu na tina". Ta kai karshen maganar tare da ɗaukar cap ɗin cappuccinonta ta cigaba da kaiwa baki tana ɗan sipping....... Hannu ya kai ya ɗan ɗauki littafin nata ya fara dubawa.

Wani irin daɗin cappuccino nan take ji yau, dan baby ya zo. Unexpext ta ga ya sanya hannu ya karɓi cappuccino, a hankali ya kai bakinsa ya ɗan yi sipping, sannan ya cire, cikin nitsuwa ya fara kora mata bayani a kan karatun da bata gane ɗin ba, yana yi yana shan cappuccinon ɗin.

Sosai take fahimtar abin da yake faɗe, dan tana san karatun. Sai da ya tabbatar ta fahimci karatun sosai, sannan ya rufe littafin ya cigaba da ɗan sipping na cpn ɗin.

"Baby in kawo maka wani cappuccinon ne?". Ta jefa mashi tambayar tana dawo da kallanta a kansa. Kai ya girgiza mata tare da miƙa mata cup ɗin yana faɗin. "Wannan ma saboda ke na sha"....... Hannu ta kai zata karɓa hannunsu ya gogi na juna, nan take wani shock ta ratsa jinin jikinsa, har sai da ya ɗan furta ash ba tare da ya san ya faɗa ba, sai jin shagwaɓaɓɓiyar voice ɗinta ya yi tana faɗin.

"Sorry baby". Kai ya jinjina, ta wutsiyar idanunsa yake kallanta, kallansa kuma dik a kan tula tulanta da suka yi mugun tafiya da imaninsa. Sam bata fahimci yana kallanta ba, sai shagwaɓa ta hau zuba mashi tana kara jefa shi cikin saukin................

Kasa jura ya yi, out of control ya kai hannu ya janyota jikinsa, a take ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Ita kuwa ta zaci abin da ya saba yi mata ne na zaman da take yi a jikinsa suna hira, sai ta saki jiki har da ɗan ɗaura hannunta a saman kirjinsa ta sama kusa da shoulder ɗinsa.

A hankali ya sanya hannunsa a saman bayanta, dik bata kawo tinanin komai a ranta ba. Slowly ya zame mata hular kayan barci dake kanta ya ajiye a gefe, a hankali ya shiga shafa lallausan black hairnta. A wannan karan ji ta yi gabanta ya faɗi, amma bata yi ƙoƙarin hanashi ba, dan bata san ma me zata ce da shi ba.

Cikin dabara ya dawo da hannunsa saman........


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



26




Cikin dabara ya dawo da hannunsa saman wuyarta. Wani irin al'amari ta fara ji yana ratsata, zata tashi ya yi saurin maida ita ya kwantar, sai ya gyara mata kwanciya ma da kyau.

"Baby dare ya yi ba zaka koma bane?". Ta faɗa tana ɗago kanta. Bai yi mamakin jin maganar tata ba, saboda yaga tsoron abin da yake yi mata a cikin idanunta, shiyasa ma ta nemi ya koma bayan a baya kullum ita take damuwa da ya zo.

Rinannun idanunsa da suka rikiɗe izuwa jajir ya sauke a kan face ɗinta. Ta ɗan tsorata ganin idanunsa sun sauya launi, hakan yasa ta kara jin tana san raba jikinta da nasa.

Ƙasa bata amsar maganarta ya yi, tamkar an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗinsa, sai kawai ya bita da kallo. Unexpext Ammo ta shigo cikin parlon tana faɗin. "Baby ba zaki hakura da karatun nan sai da safe ba kuwa? Dare ya yi yaushe zaki yi barci ba.............."

Bata iya ƙarisar da maganar ba ganin su biyu a parlon, ta yi mamakin ganinsa, da tasan yana nan ba zata fito ba. Kunyarsa ne ya kamata.
Sannu da zuwa ta yi mashi tana ɗan ja da baya. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kallansa, jinjin kansa kawai ya yi bai iya amsa mata ba, wai yana ɓoye halin da yake ciki kada ta gane.

Juyawa ta yi ta koma ciki tana mamakin yaushe ya zo gidan nan? Ko karar motarsa bata ji ba.

Ɗagowa daga jikinsa baby ta yi, a ɗan tsorace ta ce. "Baby zan je in kwanta dare ya yi"......... Lumshe idanunsa ya yi, wannan shagwaɓa tata ta kara ratsa shi sosai, sai ya ji ya zo har wuya.

Kasa shanyewa ya yi, a hankali ya matsar da face ɗinsa dab da ita. Zaro mashi idanu ya yi tana kallansa da mamaki. Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Can i kiss you my baby?".

Wani irin zaro idanu da ta yi tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa. A rikice ta ce. "Baby kiss kuma?". Muryarta na rawa ta yi maganar.

Kai ya gyaɗa mata alamar e kiss yake nufi. A wani irin zabure ta miƙe daga jikinsa, kafin ya yi wani yunkuri tuni ta watsa da gudu sai cikin ɗakin Ammo, tana shiga ta tura kofa tana sauke haki da sauri sauri. Sai da ta tsorata Ammo dake kwance a saman bed, a razane ta tashi zaune, dama bata yi barci ba, tana kwance tana tinanin wanda za'a iya alƙanta shi da lamarin su baby ɗin.

Ganin ta gudu yasa ya yi saurin miƙewa ya bi bayanta, dan ya santa da shiririta tsab zata faɗawa Ammo abin da ya ce mata. Yana turo kofar yasa kai ya shigo. Tana ganinsa ta saka yar kara tare da kwasawa a guje ta haye gadan Ammo tana riko Ammo da karfi.

Shiru ya ɗan yi yana kallanta, ita kam Ammo ta gama fahimtar komai, sai ta tuna kamar bata fahimta ba, ta riko jikar tata tana tambayar lafiyarta kuwa. Cike da shiririta ta fara ƙoƙarin faɗawa Ammon abin da baby ya ce mata. Sai dai bai bari ta faɗa ba ya yi saurin cewa Ammo.

"Ɗan bamu waje bari in yi magana da ita". Ba musu Ammo ta saketa tare da saukowa kasa. Da sauri ita ma ta sauko ta ƙanƙame Ammo tana faɗin sai dai su fita wajen a tare.

Ɗan jinjina kai ya yi tare da cewa Ammo ta je kawai kada ta damu. Wucewa Ammo ta yi da sauri ta rufa mata baya dan bata san tsayawa. Sun zo zasu fita ya damko baby ita kuma Ammo ta fice. Kuka ta saka mashi mai sauti tana faɗin ya saketa bata so.

Shiru ya yi bai saketa ɗin ba, kuma bai yi magana ba har tsawon mintina 5, sannan ne ya rungumota da kyau a jikinsa, murya ƙasa ƙasa ya ce. "Saboda na ce zan yi kissing ɗinki ne kike wannan kukan?".

Cigaba da yin kukanta ta yi bata yi magana ba, sai dai ta kwanta luf a saman kirjinsa....................... "To am so so sorry, ba zan sake faɗin hakan ba, saboda ba zan so hawayenki su sake zuba ba, ya isa haka kin ji?".
Stilll shiru bata kulasa ba, sai ma ƙara kukan nata da ta yi. Ɗan rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa can suka fito daga ɗakin, yana jin wani irin azabbabben yanayi a tattare da shi, amma ya daure saboda ya fin san farincikinta fiye da komai. A tinaninsa zasu samu Ammo a parlour, sai kuma yaga akasin hakan, saman sofa ya koma da ita a jikinsa ya zauna, rarrashinta ta cigaba da yi babu kakkautawa, tin yana jiyo sautin kukanta a hankali hankali har ya dai'na ji, a hankali saukar numfashinta irin na mai barci ya fara dokan dodan kunnesa, alamar ta yi barci kenan. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaga kansa sama ya jingina da jikin head na sofar, a hankali ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya.

Ya ɗauki 20 mins a haka kafin ya dawo da kallansa a kanta haɗe da sauko da kansa. Ai ina, ta jima da yin barci har barin ya yi nauyi. Nisawa ya yi tare da miƙewa da ita cikin dabara, ya ɗauketa cak sai bedroom ɗinta. A saman kyakkyawar bed ɗinta ya kwantar da ita, ya janyo mata bargo ya lulluɓeta izuwa dai'dai cikinta, a gaban bed ɗin ya tsuggun dai'dai saitin face ɗinta, kasa kasa kamar mai raɗa ya ce. "Rigimamma kawai, to yanzu ba ga shi kin yi barci ba?". Ya yi maganar yana kallan ɗan bakin nata.

A hankali ya dawo da kallonsa a saman kirjinta da gabaɗaya tudunsu suke a waje saboda yanayin kayan jikinta da yanayin kwanciyar da ta yi. A hankali ya ɗan haɗiyi yawu kamar wani da ya ga abin kwaɗa yi. Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya kai hannunsa jikinta, hannun nasa sai wani kerma yake yi. Wuyar rigar tata ya ɗan ja mata sama, sannan ya ɗan sunkuyo da kansa a kanta. Sumbata ya manna mata a baki. Ɗan motsawa ta yi kamar tana san farkawa.

A hanzarce ya miƙe kaman maras gaskiya, da sauri ya nufi switch na ɗakin, kashe mata wutar ɗakin ya yi, da sauri ya fice kamar zai kifa ƙasa. Bai zame ko'ina ba sai cikin motarsa, ko da ya shiga ya kasa jan motar ya tafi, ya ɗauki good 30 mins a wajen yana ƙoƙarin controlling na feeling ɗinsa kafin ya iya driving.

Da kyar ya iya tada motar da gudun gaske ya nufi gate, da yake gate ce mai amfani da na'ura, da kanta ta buɗe kanta ya danna waje da gudun gaske. Ammo tana tsaye a windown bedroom ɗinta dake fuskantar harabar gidan tana kallansa har ya tafi, sannan ta nufo ɗakin baby. Kamar yadda ya barta haka ta sameta, addu'ar barci ta zo ta yi mata dik da tana da yakinin ya yi mata, dan ya saba yi, sai dai bata san yau kansa ya ɗauki zafi bai yarda ba ya tafi.

Bayan ta gama yi mata addu'ar ne ta fito ta wuce nata bedroom ɗin, ta koma saman bed ɗinta ta kwanta cike da tinanika kala kala a ranta.......... ASUBA TA GARI.

🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥

"Haulat bani waje bari in yi magana da ita". Cewar Momma kenan, tana san ganawa da Mahnoor wanda bata yi hakan ba ko sau ɗaya, so yanzu tana san su gana. Zaune suke a bakin bed ita da Mahnoor ɗin, Mahnoor kanta a ƙasa.

Miƙewa mama Haulat ta yi cikin girmamawa ta ansa da to tare da nufar hanyar fita. Har ta kai tsakiyar ɗakin sai ta tsinkayo muryar momma tana faɗin. "Nan da 2 hours ki turo mun Mahreen".

Da okey mama Haulat ta amsa sannan ta fice waje. Dawo da kallanta a kan Mahnoor momma ta yi, hawaye bibbiyu ne a face ɗinta, da alama ta tina maraicinta yasa take wannan kuka. Janyota jiki momma ta yi ta hau rarrashinta, cike da kauna ta ce. "Kada ki ɗaukeni matsayin sirika, ki ɗaukeni matsayin uwa". Ta kai karshen maganar tana goge mata hawaye.

Shiru Mahnoor ta yi tana jinjina halacci irin na momma, zamanta da mama Haulat na satin ɗayan nan har ta koyi wasu abubuwa masu muhimmanci.

"A matsayina na uwa a gareki zan yi maki nasihar zaman gidan miji, ki nitsu ki saurareni da kyau, dan a bisa dokarmu a ɓangaren mijinki zaki kwana yau, nan da sati biyu masu zuwa zamu je jimeta, da naso mu je gobe, amma akwai wasu dalilan da yasa sai next two weeks, akwai saye saye da za'a kawo daga Dubai, sai mun haɗa komai zamu tafi, gobe ya yi kusa".

Jinjina kai Mahnoor ta yi tana sauke ajiyar zuciya, tabbas tana jin momma tamkar mahaifiyarta, tana kaunarta sosai ita ma.

Cikin sanyin murya momma ta fara magana kamar haka. "Ki dage da hakuri da biyayya.
Aure yana buƙatar hakuri da juriya. Ki kasance mai biyayya ga mijinki, kuma ki guji nuna rashin kunya ko rashin girmamawa gare shi. Ki kula da addua da ibada. Ki dage da addu'o'i don neman zaman lafiya da albarka a gidanku. Ibada za ta taimaka muku wajen samun kwanciyar hankali. Ki zama mai tsafta da ƙyalli, Haulat zata koya maki kwalliya sosai. Ki kula da tsaftar jikinki, gidanki, da tufafinki. Mijinki mutum ne mai jin daɗi idan ya ga matar da ke da tsafta kuma tana jan hankalinsa, yana da kyankyani ya tsani ƙazanta, a kan kanwarsa ƴar autarsu ya fahimci hakan, dan in ta yi kwalliya wuni yake yi yana yabonta baya gajiya, so yana san kwalliya sosai. Ki koyi maganar mai daɗi da ta dace da shi, dan yana san magana cikin kulawa. Ki guji faɗar kalamai masu zafi ko cin fuska. Kalaman kirki suna gina soyayya kuma suna rage duk wani rashin fahimta. Kula da sirrin gidanki da mijinki. Kada ki yi gaggawar bayyana matsalolinku na gida ga kowa. Kula da sirrinku zai taimaka wajen magance matsalolin cikin sauƙi. Kauna da kulawa. Dik da nasan yana da wuyar sha'ani kuma zai yi wuyar juyowa gareki, dik da haka ki nuna mashi soyayya da ƙauna, sannan ki kula da dangi da abokan arzikinsa. Wannan zai sa ki samu ƙima a gidansu. Hakuri, hakuri, hakuri, ki kasance mai haƙuri. Komai yawan ƙalubale, haƙuri yana da muhimmanci don magance su. Ki rike ibada sosai. Wannan yana kawo albarka a cikin aure. Kar ki yi gaggawa wajen yanke hukunci idan ya yi maki wani abin. Idan akwai matsala, ki nemi hanya mai kyau don magance ta kamar yin nafilfilin dare dan neman maslaha daga wajen Allah. Ki kasance mai ilmantarwa. Karatu da ilimi suna taimaka miki wajen zama mai cikakken basira a rayuwa. Na faɗa na kara faɗa maki, mijinki yana san kwalliya sosai, sannan na manta ban faɗa maki cewa shi mutum ne mai san zanen lalle a hannun mace ba, ko ni da nike mahaifiyarsa idan na yi lalle ya rinƙa magana kenan, ya kalla ya sake kallah, har hoto yake ɗaukar hannuna, Jaish mutum ne mai san lallaɓawa, tin yana karami haka yake, baya san a ɗaga mashi murya, sannan baya san yana magana ki yi magana, ki kula da wannan, baya san cin abincin a kan lokaci, hakan kada ya ɓata maki rai ki ɓata mashi shi ma, cikin ruwan sanyi da sigar soyayya da lalama zaki koya mashi cin abinci a lokacin da kika yi ra'ayi, yana da zuciya sosai, wannan gado ce, dik suna da zafin zuciya da saurin fushi, idan ransa a ɓace kada ki yi saurin kula shi, ki kyalesa na ɗan lokaci ya sauko, in ba haka ba ba zaku kare da kyau ba".......... Ɗan dakatawa ta yi tana mayar da numfashi.

Mahnoor kuwa ta kasa kunne tana saurari yadda yakamata. Shiru ta ɗan tsaya na ƴan mintuna tana kallan fuskar Mahnoor kafin ta nisa ta ɗaura da cewa.

"Kin ji kaɗan daga cikin abin da yake so ta waje, sai ta ciki, ba zan ɓoye maki komai dangane da mijinki ba, saboda yanzu a ƴa na ɗaukeki ba sirika ba, burinmu mu shawo kan mijin naki ne, dole na fayyace maki komai dan mu yi nasara".

Jinjina mata kai Mahnoor ta yi tana kara kasa kunne ta saurara da kyau, saboda tana bala'in san Jaish, dik abin da zai juyo mata da hankalinsa a kanta to tabbas zata yi shi.

"Mijinki yana da sha'awa mai karfi wanda zance maki dikkansu haka suke, sai ki shirya, amma yana da dauriya sosai, sannan baya san mace mai shigar manyan kaya, i mean matar aurensa, saboda na karancesa sosai a kan hakan, dayawan lokuta yana san sayawa kanwarsa kananan kaya dan yana yi mata kallan yarinya, so yana san shigar manyan kaya, wannan zan sa a yi maki akwati set guda a wajen haɗa lefenki, so Haulat zata koya maki yadda zaki yi amfani da su".

Mahnoor da bata san me ma mommar take nufi ba a maganarta ta karshen nan, ai sai amsa mata take yi to kawai kanta a ƙasa.

My people's ku tafawa uwa ta gari, wato dik abin da ƴaƴanta suke yi tana sane tana yin recoding a ƙwaƙwalwarta, ashe ta san Jaish yana san lalle, kun tuna idan ya zo ya samu mama Haulat ta yi mata lalle sai ya yi ta yabawa? Ashe dik tana ganinsa, ashe ta iya karantar abin da yake so da wannan da baya so, gaskiya wannan ita ce uwa ta gari, ba tare da ƴaƴanta sun faɗa mata ga abin da suke so ba ta rigasu sanin abubuwan da suke so, wani lokaci suna son abu basu ma san son shi suke yi ba, amma tsabar kula irin nata ita ta gane hakan, wata uwar ko kasheta zaki yi yanzu ki ce ta kirga maki abubuwa goma da yaronta yafi so ba zata kawo maki su ba, kuma tana sansa ba wai bata sansa ba, wasu ne akwai rashin kula sosai wlh, irinsu ne ƴaƴa su yi ya aikata abubuwa tsabar rashin kula zasu ce basu sani ba, yanzu ku momma bata burgeku ba yadda take zayyano abin da ɗanta tafi so ba tare da shi kansa yasan da yana sansu ba? Abin bai ƙayatar daku ya yi maku daɗi ba? Ki karanci yaronki ki san me yake so ma ke zaki fi kowa jin daɗi da moresa, dan in kika san me yafiso fa wlh dik in da zai je sai ya dawo wajenki, dan zai ga kamar dik duniya ke kaɗai ce kika iya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login