Showing 162001 words to 165000 words out of 403653 words

Chapter 55 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

130

ce kawai zata buɗe fuskar mata, amma ta mance da yake an jima ba'ayi biki ba a kingdom ɗin. Kowa kuma yasan yadda bikin Jawad ya kasance cikin ruɗani da tashin hankali, so ba'ayi dik wasu al'adu nasu ba, dan haka ta mance da batun.

Cike da isa Akka ta ce. "To shikenan tun da Zunaira bata nan sai ku mayar da amaryar taku sai lokacin da kuka shirya nuna mana fuskarta Zunaira ta zo ta buɗeta". Ta kai karshen maganar tare da yunkurawa zata miƙe.

Innalilahi, kallon juna suka shiga yi, dikkansu tinanin ta yadda zasu dakatar da Akka ta yi hakuri ta ga Mahnoor suke yi. Uncle Jahiz ya fahimci momma ta shiga damuwa sosai a kan hakan, sai ya yi saurin riko hannun Akka dama suka kusa, cike da kalaman yaudara ya ce.

"Haba Akka na, to menene banbancin Sarina da Zunaira? Ai dikkansu kannen Jaish ɗin ne, dan haka ko ba Zunaira Sarina tana nan, sai ta buɗe mana amaryar ai".

Komawa Akka ta yi ta zauna, cike da isa ta juyo garesu domin ta sanar da su banbancin Zunaira da Sarina kwatsam idanunta suka sauka a kan uncle Abbas, aka ce idanun iyaye suna da kaifi a wajen da ake ƙoƙarin nunawa ƴaƴansu wani banbanci ko fifikon ko dai cin mutunci, ashe haka ne kuwa, ganin uncle Abbas yasa ta ji bata da kwarin gwiwar iya banbanta ƴaƴansa dana ɗan uwansa bayan kansu a haɗe yake.

Bata san abin da zai kawo masu rabuwar kai, dan haka sai ta ce. "Gaskiya ne babu banbanci, ke Sarina zo ki buɗe fuskar matan yayanku"...... Dik wanda ya ji maganar Akka a cikin parlon nan yasan ba daga cikin zuciyarta wannan magana ta fito ba, dik sun fahimci ganin idanun iyayen Sarina a wajen yasa ta danne bata faɗi banbancinta da Auta ba.

Wani irin takaici ne ya lulluɓe zuciyar Sarina, yanzu ace ita zata buɗe fuskar makiyarsu kishiyar Fanan? Gaskiya ko a iya haka an cuceta. Ita kuwa mammie ranta ne ya yi muguwar sosuwa, wato kenan ko a ina ƴaƴanta suna da banbanci da na King? Kenan ƴaƴanta ba koman komai bane ko a cikin dangi? Tin ba'a je ko'ina ba ana nuna masu su ba komai bane saboda ba babansu bane a kan mulki?.

A cikin zuciyarta ta furta lallai yazame mata dole ta tsaya tsayin daka domin mulkin kingdom of power ya dawo tsaginsu, ina ba zai taɓa yiwuwa su zama bayin wasu ba, dole suma su ci gashin kansu, ace har kakarsu da ta haifi ubansu da King ɗin tana ƙoƙarin ware ƴaƴan King daban dan shi ne mai rike da mulki, gaskiya ba zata yuwu ba.

Tabbas a nan Akka ta yi kuskure, kuma dayawa mata suna aikata irin wannan kuskure, sai kuga a gida an fi fifita ƴaƴan da ubansu ya fi abin duniya ko yake rike da wani muƙami, wannan babban kuskure ne wanda mun san kuskure ne amma muke aikatawa, Allah bai manta da talaka ba da ya barshi a talauci, haka zalika mai arziki ba wayau ya yi wa Allah ba da yasa ya bashi arzikin ba, dan haka ku daina irin wannan abin da kuke yi, wani ma zaku ga ko ubansu ne karami in dai yana da kuɗi to sai a nuna yafi kowa a gidan, ba'a yin haka wlh, hakan yana ɗarsa gaba da kiyayya a zukata, idan ba'a kiyaye ba sai shaiɗan ya shiga cikin lamurran, a haka ne sai ku ji ana cewa yaya ya kashe ƙaninsa ko ƙani ya kashe ƴaƴansa saboda abin duniya, dik ire iren wannan abin da kuke gani kamar ba matsala bane su suke hasasa waɗan nan abubuwa, dan Allah mu daina irin hakan ba abu bane mai kyau wlh, babu mai arzirtawa sai Allah, shi da yake talaka ai ba yin kansa bane, idan kuwa akwai mai bada arziki bayan Allah sai ku faɗa mun in ji!!!!!.

Shi kansa uncle Abbas ransa ya ɗan sosu, amma ya danne ya nuna kamar bai fahimci in da Akka ta nufa ba, shi ma uncle Jahiz ya ji wani irin, amma dik suka danne.

Miƙewa Sarina ta yi tana wani ɓata rai ta nufo Mahnoor. A kule ta sanya hannu ta janye hular alkyabbar baya kamar ma da mugunta ta yi abin. Dan yadda ta ja hular har sai da kan Mahnoor ya ɗan jinjiga.

Mummyn Chuchu ce ta ce. "Sarina menene haka? Haka ake buɗe fuska?".

Mammie ce ta tari numfashin mummy da cewa. "An kinsan bata iya bane, kinga ba'a taɓa biki a gidan nan da wayonsu ba sai bikin Jawad wanda shi kuma ba'a nemi kannensa na jini dan gudanar da komai ba, ina ga da yake amaryar yar gata ce kannenta ƴan gata akasa suka yi mata komai".

Wani irin gabaɗaya parlourn suka ji na jin kalaman Mammie, mamaki abin ya bawa King, shi kuma uncle Jahiz ya fahimci kamar abin da Akka ta yi mata ne ya bakanta ranta, momma kam da tasan komai ko kallo basu isheta ba, maman Aneesa dik rashin son zaman lafiyarta da izzarta sai da kalaman mammie suka ɓata mata rai, ga shi dai ba shiri take yi da kishiyoyin nata ba, amma da aka gasawa mummy magana sai ta ji zafi.

Dan haka sai izzar sarautar tata ta motsa. Cike da izza ta ce. "Ke saboda baki da hankali Umaima ɗin kike yi wa martani gatsau haka? Sa'arki ce ita? Shin dake ma ta yi magana ne? Ko kece Sarina? To maza ki bata hakuri kafin ranki ya yi mummunar ɓaci". Mama manya, mama harkar izza ba wasa, bata ɗaukar wargi ko ba a kanta ba.

Momma ta ɗan yi mamakin faɗar da mama ta tarewa mummy, dan sun san juna kar tu kar.

Ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya Akka ta kara yi, a kadarance ta ce. "Yauwa ku cigaba, ai na faɗa maku idan baku yi haka ba ba mata bane ku, ku cigaba da kyau".

Shi dai uncle Jahiz dariya ma abin ya so bashi, wai yau mama ce ta da tare wa kishi faɗa, tab abin babba ne.

Harara Mammie ta wurgawa Akka ba tare da kowa ya lura ba, a cikin ranta ta ce shegiyar tsohuwa idan baki yi hankali ba ni ce nan ajalinki. A fili kuma sai ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da cewa mummy. "Kiyi hakuri".

Wato akwai iyashege a kingdom ɗin nan, wlh matan King sun san kan duniya.

Jiki ba kwari Sarina ta bar gaban Akka ta koma mazauninta zuciyarta na tafasa, mammie ta ƙara jin ranta ya ɓaci, ta kara jin lallai dole ta mallaki kujerar kingdom of power ko ta halin yaya ne, da yanzu ita take da mulki a hannunta ai wane kaniyarsu su yi mata abin da suke yi mata ɗin nan.

Akka kuwa hankalinta gabaɗaya ta mayar a kan Mahnoor, like wow, she was so surprised seen her beautiful face, abin ta bata yi expecting ba, ita kanta ta shaida Mahnoor kyakkyawa ce, ga gyaran da ta sha, skin ɗinta har wani yellow yellow ya yi yana wani glowing, wlh komai sanin da ka yi wa Mahnoor ba zaka taɓa ganeta a yanzu ba, dan ta haɗu iya haɗuwa, ko makiyi sai ya jinjinawa haɗuwar da ta yi sai dai idan ba zai faɗi gaskiya ba saboda kiyayya.

Gabaɗaya su King zuba mata idanu suka yi suna kallanta, a cikin zuciyarsa King ya ce. Dama shi yasan dik abin da Rahilarh zata zaɓa ba abin yasarwa bane, lallai ba shakka wannan yarinya ta dace da jaish.

Cike da matsuwa da san jin amsarsu momma ta ce. "Gwaggo (Akka) ya kuka ganta? Ta yi?".

Shiru Akka ta yi tana cigaba da karewa Mahnoor kallo, baiwar Allah mai innocent face. Kun san Akka fa babu ɓoye ɓoye, dan haka sai ta ce. "Wannan yarinya anya ba zata iya zama green snake under green grass ba kuwa?".

Ɗan zaro idanu suka yi gabaɗayansu, sai dai babu wanda ya iya tambayar Akka dalilinta.

Cigaba ta yi da cewa. "Yanayin fuskarta ya nuna shiru shiru sosai ce ita, kun san masu irin wannan fuskar munafikai sun fi yawa a cikinsu".......... Akka tamu ta amana.

Shiru parlourn suka yi, dan idan Queen mother tana magana ba'a katseta sai ta gama.

Hannu ta kai ta ɗan ɗago haɓar Mahnoor, abinku da kaka, ko kunya bata ji ta fara yi wa Mahnoor leke leke har da gane mata girman tula tulanta, tana yi tana magana kamar haka. "Ni jikokina dik lafiyayyu ne, dan haka suna da buƙatar cikakkun mata, sannan suna san komai ya ciko sosai, saboda gujewa zinace zinace dole mu bincika da kyau mu samo wadda zata iya ɗaukarsu, dole na bincika masu komai".

(Nace yanzu kun gane qualities ɗin da King ya zage yake ta cewa sai mace tana da su sannan zai aurawa ƴaƴansa ita? Kun gane irin qualities ɗin ko sai an maku karin bayani? Su kansu sun san abin nasu na gado ne, to dai ga Akka ta buɗe komai mun ji irin qualities da ake nema😅🥱)

Tana magana tana sassaukewa Mahnoor alkyabbarta izuwa saman shoulder ɗinta.

(Kam bala'i, jama'a Akka duniya ce, a lallai gara ta duba masu, kai aima dole ta duba dan tasan sun yi gadon abin,🤭 tasan wanenen King Abdul Malik kakansu kenan, e dole ta duba aga Mahnoor zata iya ɗaukan Jaish ne ko yaya? Kai wlh wannan tsohuwa duniya ce.)

"Shekarunki nawa?". Ta jefawa Mahnoor tambaya. Momma ce ta yunkura zata yi magana, hannu ta ɗaga mata alamar ta yi mata shiru.

"Kada na ji bakin kowa a nan, bincike nike yi tukun nan"........ Tsit suka yi suna sauraronta.

Baiwar Allah kanta a ƙasa cikin sanyin murya ta ce. "Ban san takamaiman shekaruna ba, amma dai tsakanin 15 da 16 ne". Larabcin Mahnoor yana gargada,.bata kware sosai ba.

Jinjina kai Akka ta yi, sannan ta sake cewa. "Mahaifiyarki ta sanar dake abin da ake nufi da aure ko kuma ta barki a sake tana jiran ni in sanar dake? Kin san menene aure? Kin san yadda ake kula da miji? Kin san kalan mijinki kuwa? Kin shirya iya ɗaukarsa?". ........ Yau ga ikon god wajen Akka, tsohuwa zata buɗe komai fa.

"A'a bani da mama, babu kuma wanda ya taɓa faɗa mun menene aure". Tamkar zata yi kuka ta bada wannan amsa.

Cak Akka ta dakata da ƙoƙari cire mata alkyabba da take yi, da sauri ta dawo da kallonta a kan face ɗinta. "Ke marainiyace?". Murya cike da tausayawa ta jefa mata tambayar.

Da e ta amsa mata idanunta suna cikowa da kwallah, nan take Akka ta ji jikinta ya yi sanyi, Allah sarki suna da jin tausayin marayu sosai, haka zuciyarsu take, janyota jikinta Akka ta yi, sannan ta ce. "Ya sunanki?".

Mahnoor ta bata amsa. Kwnatar mata da kanta a saman gwiwowinta Akka ta yi tana ɗan shafa bayanta, da ɗan ɗaga murya ta ce. "Princess Mahnoor mata ga Prince Jaish barkanki da shigowa familyn King Abdul Malik".

Haba wani irin ajiyar zuciya su King suka sauke, barema momma da ta fi kowa matsuwa da san jin amsar Akka, tun da ta kira Mahnoor da princess shikenan ta yi na'am da ita kenan.

Mummyn Chuchu ce ta rangaɗa masu guɗa, nan take suka hau farinciki mara misiltuwa. Sarina and Mammie bakinciki kamar zai kashesu, barema da suka ga fuskar Mahnoor, babu abin kushewa a tattare da ita, ga kyau kamar ita ta yi kanta, uwa uba ta fi Fanan kyau da komai nesa ba kusa ba, kai in short basu da wani abin da zasu nuna mata da shi, ta fi su komai, kamar Sarina zata haɗiyi zuciya saboda taya Fanan kishi.

Wato akwai cakwakiya wlh sosai.

Kallan su King Akka ta yi, cike da bada umarni ta sanar da su ta aminta da Mahnoor, suma tana basu umarni da su karɓeta a matsayin sirika. Cike da gimamawa suka amsa mata da sun karɓeta hannu bibbiyu ma kuwa.

Akka ce ta buƙaci jin yadda aka yi Jaish ya haɗu da marainiyar Allah da kuma me ya kaisa Nigeria?. Babu ɓoye ɓoye momma ta zayyana masu dik yadda aka yi. Sosai suka kara jin tausayin Mahnoor yakamasu, nan take ran Akka ya ɓaci ta ce wlh ita ba zata yafewa Nenne ba, dole su hukuntata azabar da ta ganawa Mahnoor, kun san basa yafe zalinci su ato.

A fili Sarina ta yi suɓul da baka wajen cewa. "Ashe ƴan gidan matsiyata ƴan kauye mara galihu ne ma". Bata san ta yi maganar ba har sai da taga kowa yana kallanta, sannan ne ta farga, da sauri ta miƙe ta nufi waje tana ɓata ran wai ta ɓata lokacinta a kallan ƴar gidan matsiyata.

Da kallo suka bita har ta fita, a nan ne King ya fahimci lallai akwai matsala idan har basu yi da gaske ba, dole ya zauna shi da momma su tsara yadda zasu kula da Mahnoor ba tare da wani abin ya sameta ba, idan ba haka ba zata fiskanci barazanar kanne miji.

In short a nan aka yi komai aka gama, momma ta buƙaci iznin zuwa Jimeta a kai kayan aure da komai da ake yi wa mace kafin a aureta. Akka da kanta ta bata izini. Suka gama tsara komai, sannan mummyn Chuchu da momma suka miƙe suka kama Mahnoor suka fita da ita, mama ma miƙewa ta yi ta basu waje. Mammie ce ta yi fitar karshe.

Parlourn ya rage daga King, uncle Abbas, uncle Jahiz sai Akka, tattauna suka fara yi a kan batun, dan su san ta yadda zasu tsara komai.

Mahnoor kuwa part ɗin momma suka wuce da ita dan su kara shiryata yau za'a kaita ɓangaren Jaish. Mahreen dai an barota a ɗakin gyara.

🔥🔥🔥BABY AND AMMO🔥🔥🔥

Zaune take a saman sofa tana fuskantar Ammo dake zaune a saman nata sofar, Ammo na kallan Tv ita kuma tana rike da cup mai ɗauke da cappuccino tana sha, center table dake gabanta wani ɗan madaidaicin laptop ɗinta mai shegen kyau da tsada ne a kai, daga gefensa wasu takardunta ne tana karatun exams, na faɗa maku tana bala'in san karatu, kuma Allah ya bata ilimin both side.

Sanye take da kayan barci masu kyau, rigace mai laushi sosai mai karamar hannu, sai wani ɗan madaidaicin wando da bai wuce singalalin kafafunta ba, bai kai har kasa ba. Wandan dai'dai da jikinta yake, shi kuma rigan yana da ɗan faɗi kaɗan, tana da dirarren jiki sosai kamar dai su Pretty tamu, sai dai bata da wani tsawo sosai, tsayinta dai'dai da shekarunta.

Tana sipping cappuccino a hankali hankali tana duba takardunta, kanta na sanye da hular kayan barcin jikinta.

"Baby ni zan shiga in kwanta, karfe 9 ta yi, yakamata kema ki kammala karatun nan da wuri ki je ki kwanta tun da gobe exam kuke da shi kuma da wuri zaku rubuta ko?". Cewar Ammo.

"E exam muke da, yanzu zan kammala, saura kaɗan ne". Ta kai karshen maganar tana ɗaura cup ɗin cappuccinonta a saman table ɗin kusa da laptop ɗinta, sannan ta ɗauki takardanta ɗaya da take dubawa ɗin, ƙwaƙwalwarta ya ɗan ɗauki zafi, ta ƙasa gane wannan karatu, tinani take yi ko dai ta kira babynta a waya ta ce ya koyar da ita ne, in ya so su yi karatun ta Whatsapp kamar yadda suke yi a dik sanda wani karatu ya gagara mata.

Ita kuwa Ammo miƙewa ta yi ta nufi dakinta tana yi mata sai da safe, da yake ɗakinsu daban daban, sai idan baby ta yi ra'ayi ne ta je ɗakin Ammo su kwana.

Wayarta baby ta ɗauko da nufin ta kira numbersa ta sanar da shi ya hau Whatsapp su yi karatu, sai dai bata kai ga kiranba kofofin hancinta suka jiyo mata kamshin perfume ɗinsa, hakan yasa ta yi saurin kai kallanta a bakin kofar shigowa.

Yana tsaye ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, kallanta kawai yake yi, sanye yake da wando three quter jeans white color, sai round neck polo shirts sky blue mai shegen kyau, ya yi kyau matuƙa, da alama fitan ba shiri ya yi, duba da yanayin dressing ɗinsa.

Zaro idanu ta yi, cike da mamaki mai ɗauke da farinciki ta miƙe tsaye, wani ƙayataccen murmushi ne ya kubce mata kafin ta ambaci baby.
Shiru bai amsa mata ba, ya dai kafeta da idanu, idan ka gansa zaka yi zaton gabaɗayanta yake kallah, amma bahaka bane, hankalinsa yana a kan kirjinta, da yake bata sa bra ba, and gasu masha Allah suna tsole idanun mai kallo.......... Anya baby ba barci ya ƙasa yi ba da ya biyo dare kuwa? To mutum dai shi ba karfe ba, kuma shi lafiyayyen namiji, ya kai 30 years, ya zayyi ba zai ƙasa barci ba ɗazun yaga kaya iya kaya? Kada ku ce na ce, tom gaskiya dai na faɗa.

"Baby daman zaka zo ne baka faɗa mun ba?". Cikin wannan shagwaɓa tata kamar ta Prettynmu dai ta yi maganar.

Ɗan gyaran murya ya yi saboda ya ga kaya har muryarsa ta sarkafe taki fita. "Babu zuwan a lissafina, dole ce ta sa unexpect ya shiga lissafina". Ya faɗa ba tare da ya motsa daga in da yake ba.

"Dole kuma baby?". Kai ya jinjina mata alamar e........ "To waye ya yi maka dole ka zo ɗin?". Nisawa ya yi tare da ɗan kawar da kallansa daga kan dukiyan fulaninta, (yau dai ban ce tula tula ba saboda an saka mun ido da wannan suna nawa mai albarka 😅🥱)

"Kece kika tilasta zuciyata zuwa, na koma na kasa samun sukini, zuciyata ta damu da san zuwa in ganki".

Wani irin murmushi ta saki. "Yes that is my baby, dama nima ina san ganinka"......... A ɗan takaice ya ce. "Meyafaru kike san ganina?".

Turɓe fuaka na shagwaɓa ta yi, kamar zata saka mashi kuka ta amsa da. "Wannan karatun ne yake bani wahala, na kasa gane komai, please kazo ka duba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login