Showing 204001 words to 207000 words out of 403653 words
tinanin kenan dikka warriors na yayansa haka suke.
Kun san me ya gani yasa shi rufe kofar nan kuwa? Jack ne tare da wasu ƴan'matan biyu tsirara suna holewarsu, shi master da maza biyu, shi kuma Jack da ƴan'mata biyu. Tsabar Jack tantiri ne ma yana kan ɗaya yana rike da breast ɗin ɗaya.
Gabaɗaya Ronnie yasa me yake yi mashi daɗi, bayin Allah Ronnie san da yake krista ma yana kyamar waɗan nan laifuka ina kuma ga hasken musulunci ta ratsa zuciyarsa? Ai dole ya tsaneta sosai, musulunci ai ba wasa ba.
Dafe kansa dake tsananta sara mashi ya yi, da sauri ya juya ya nufi part ɗin Black Tiger a cikin ransa yana tsinewa Master and Jack, ƴan iskan banza takadirai kawai.
Bedroom na Black Tiger ya dawo, babu kowa a ciki, saman bed ya zauna tare da haɗe kai da gwiwonsa yana tinanin in da sweetie ta tafi, baya ma tinanin ina yayansa nasa yake, yafi tinanin Sweetie.
A daidai lokacin da yake tinaninta ita kuwa tana cikin wani irin hudu mai tsanani a wani ƙungurmin daji mai ban tsoro da ɗaga hankalin dik wani halitta mai rai, zaka saurara iya saurarawanka ba zaka taɓa iya jiyo sautin komai ba, babu wani motsi, duniya dik ta yi tsit.
Ɗaɗaɗaure take a jikin wani irin sarka mai kifiyoyi, a jikin wani bishiya aka ɗaureta wanda kasar wannan bishiya wutace sosai take ci, turiri da numfashin wutar yana azabtar da ita matuƙa, gabaɗaya jikinta ya ɗauki zafi rau, tin tana iya daurewa har ta fara ruwan hawaye, ga shi ta juya gabas da yamma gudu da arewa sam sam babu alamar kowa, duhun dake wajen yasa ta gaza iya gane a ina ma take, ta gaza gani gabanta.
Sosai ta yi tsananin tsorata, ga wutar sai ƙara ci yake yi yana haurowa sama, jikinta har kerma yake yi tana haɗa wani irin uban zufa mai ban tausayi. A yau dai ta gama saddakarwa mutuwa zata yi, dik namar jikinta har ya fara laushi, hankalinta a tsananin tashe yake baiwar Allah. Sai dai kuma dik da wannan azaba ko kusa ko alama bata ji kamar zata janye kudurinta a kan canza zuciyar Black Tiger da ta yi niyyar yi ba, sai ma ƙarin kwarin gwiwa da Allah ya bata.
••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥
Lokacin guda haske ya gauraye wajen, gabaɗaya idanunta ta datsesu da karfi saboda ganin wannan haske ya kashe karfin ganinta. A hankali ta sake waro idanunta domin ta ga daga ina wannan hasken ya fito?.
Ba daga ko'ina ya fito ba face daga saman kan toliyar scepter King ɗinsa, kunsan kansa da ɗanyar gold aka yi ta, to ita ce ta bada wannan haske sosai. Ganin hasken scepter ɗin yasa ta fahimci shi ne ya zo. Cike da balai'n tsoron ganin face ɗinsa ta ɗago idanunta da suke jajir kamar wuta ta ɗaura kallanta a saman face ɗinsa.
Sai da ta ji gabanta ya yi wani irin mummunar faɗuwa na ganin yadda face ɗinsa take a ɗaure tamau, ta sha jinin jikinta ta kuma razana matuƙa, har kerma jikinta ya fara yi. Sunan Allah ta fara ambata a cikin ranta tana addu'ar Allah ya sake bata nasara a kansa yanzu ma kamar dai ɗazun, dan tana san fara yi mashi nasiha tare da faɗa mashi girman Allah ko zata samu wannan bakar zuciya ta ɗan ragu, dan haka sai ta fara neman Allah ya kareta tin ma bata fara nasihar tata ba.
Babu tausayi ko ɗigo a ransa ya nuna wutar da scepter ɗinsa, nan take wutar ta kara haurowa sama kusa da kafafunta dab, dama a rami ya hura wutar. Hankalinta ne ya kara tashi matuƙa, a ruɗe ta fara ƙoƙarin jan kafafun nata baya domin azabar ta yi mata yawa. Sai dai kashi a jikin itace take ɗaure, ba halin ta yi baya da kafafunta, babu space ta baya, dole ta bar kafafun nan nata su gasu.
Idanunsa a kan face ɗinta, babu alamar zai tausaya mata ya sake yunkurin ɗaga scepter ɗinsa zai nunata da shi. Cikin dakiya da kakausa kuma wahalalliyar murya ta ce.
"Kai kam baka jin tsoron Allah ne? Baka da tausayi da imani a cikin bakar zuciyarka ne? Meyasa kake san kashe mutane bayan kuma ba kai ka haliccesu ba? Ko baka taɓa tinanin cewa Allah zai tambayeka a kan ran da ka ɗauka bane? Me suka yi maka ka kashesu? Ko kai ka haliccesu? Ko baka san da cewa mamallakin rayukan zai tambayeka bane? Baka san akwai ranar tashin alkiyama ba ko? Baka san akwai ranar da kowani bawa zai fuskanci hukunci dai'dai da abin da ya aikata ba? Baka san akwai ranar da mulki, kuɗi, kyau, matsayi, ilimi, isa, taƙama, izza ba zasu tsinana maka komai ba ko? Baka san akwai ranar da zaka tashi matsayin ƙasƙantacce ko tufafi babu a jikinka ba?".
Dakatawa da yin maganar ta yi tana jin wani irin kuna da numfashin wutar nan take yi mata, tana ji a jikinta sosai. Fasa nunata da scepter ɗin ya yi, ya dakata yana jin maganganunta. Ganin ya dakata yasa ta ji kwarin gwiwar cigaba da magana, take ma ta ji zafin wutar ya gudu ganin yana sauraronta.
"Baka san wannan rana zata zo ba ko? Baka san akwai wata rana da zata zo da Ubangijinmu zai tara dikkan duniya waje guda ba ko? A ranar Alkiyama, dukkan masu mulki, sarakuna, shugabanni da azzalumai za su hallara a gaban Allah. A wannan rana, babu wani mutum da zai iya da'awar mulki ko iko, domin Allah ne kaɗai zai kasance da mulki da iko. A wannan rana Allah zai ce. Limanil mulku liyawm? Wanenen mai mulki a yau? Hasbunallahu wani'imal wakil. Babu wanda zai iya samun bakin amsawa Ubangiji wannan tambaya, wane mutum, Allah da kansa ne zai sake amsa tambayar da cewa babu wani mai mulki sai Allah subhanahu wata'ala. Wannan yana nufin cewa dukan iko da mulki na duniya wofi ne, sai wanda aka yi da adalci da tsoron Allah, shi ne kawai zai iya zama mulki mai amfani har ranar lahira. Kai da kake zalinci me zaka ce a ranar lahira? Ka tanadi abin faɗe ne?!!".
Ta jefa mashi tambayar tana wani irin huci sakamakon wannan wuta, ga kuma kululun bakinciki da ya tirnike mata zuciya. Da kyar ta ɗaura mashi da maganar bayan ta ɗan huta ta gama sauke numfashinta.
"Idan ma baka yarda da maganata ba to ka duba a cikin Alqur'ani, cikin Suratul Ghaafir, sura ta 40 aya ta 16. Allah ya ce
سورة غافر – آية 16
يَوْمَ هُمْ بَارِزُونَۚ لَا يَخْفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنْهُمْ شَىْءٌۚ لِّمَنِ ٱلْمُلْكُ ٱلْيَوْمَۖ لِلَّهِ ٱلْوَاحِدِ ٱلْقَهَّارِ
Fassararta
A ranar da za su bayyana gabaɗaya a gaban Allah, babu wani abu da zai ɓuya daga gare Shi. Sai Allah Ya ce. Wanenen mai mulki a yau? Sai kuma ya amsa da kansa dan babu mai iya amsawa, zai ce mulki nasa ne shi kaɗai, Allah shi ne malikyaumiddin, mamallakin ranan sakamako kenan"
"Kasan me ake nufi da tashin alkiyama kuwa? Kasan masifarta kuwa? Kasan balai'n da tashin hankalin dake cikinta kuwa? Na tabbata da bawa yasan balai'n dake cikinta da ba'a wayi gari da azzalumi ko guda ɗaya ba a duniya, kai koda sau ɗaya a samu wanda ya mutu ya dawo duniya ya faɗawa mutane musifar dake lahira da duniya ta tsabtata daga ƙazantar da take a ciki".
"Amma ni Omaish jika ga Abdul Mutallab ina kalubalantarka da ka je ka karanta suratun Az-Zalzalah (الزلزلة) tana daga cikin surorin da ke cikin Al-Qur’ani mai girma. Tana da ayoyi takwas 8, kuma tana cikin Juzu’i na 30. Wannan sura ta yi cikakken bayani game da ranar tashin kiyama, in da ƙasa za ta girgiza da fitar da dik abin da ke cikinta, wato dikkan mutanen da suka mutu aka binnesu kenan. A wannan rana, kowane mutum zai ga sakamakon ayyukansa, komai ƙanƙantar su. Wannan sura tana ƙarfafa imani da ranar sakamako, kuma tana ƙarfafa mutane kan su aikata alheri domin gudun sakamakon munanan ayyuka, dan haka zan so ka karantata tare da fassararta dan ko ba komai bakar zuciyarka na tabbata sai ta ragu, babu wanda zai ji labari game da lahira zuciyarsa bata kaɗa ba, ko shaiɗan ubanku a zalinci shi ma hantar cikinsa kaɗawa take yi a dik time ɗin da aka yi batu kan lahira".
Ta ɗan dakata tana jan numfashi mai fita dakyar sosai kafin ya daure ta ɗaura da cewa.
" Bayan suratul Zalzalah akwai wasu surori da Hadisai da suka bayyana Tashin Alkiyama da Masifunta, ina kalubalantarka da ka karanta su dikka. A cikin Al-Qur’ani da Hadisai masu yawa, an yi bayani mai zurfi game da tashin Alkiyama, tsayuwarta, masifunta, da yadda za a yi hisabi kafin Allah ya raba hukunci. Daga ciki akwai suratul Az-Zalzalah wadda take magana a kan yadda ƙasa za ta girgiza kuma ta fitar da abin da ke cikinta. Sai suratul Waqi’ah surata 56 ta yi bayani yadda mutane za a rarrabe su zuwa rukuni uku a kiyama. Na dama sune Ahlul Janna wato ƴan aljanma, sai na hagu Ahlun Naar, ƴan wuta kenan, da waɗanda suka yi wa Allah hidima sosai As-Sabiqun. Sai suratul Takwir sura ta 81, ta yi bayani kan yadda rana za ta narke, taurari su faɗi, da kuma yadda dabbobi za su taru. Sai suratul Infitar, surata 82, ta yi bayani kan yadda sama za ta tsage, ƙasa ta zube, kaburbura su bude, kuma mutane su san sakamakon ayyukansu. Sai suratul Inshiqaq surata 84, ta yi bayani yadda sama za ta tsage kuma mutane su hadu don hisabi".
"Hadisai Masu Bayani Kan tsanani da tsaruwar Alkiyama, masifu da bala’o’in tashin Alkiyama akwai bukhari, hadisi mai lamba 4635, sai Muslim lamba ta 157, Annabi Muhammad (SAW) ya ce. Kiyama ba za ta zo ba sai rana ta fito daga yamma. A cikin Muslim again, a ranar Alkiyama, mutane za su tsaya tsawon shekaru 50,000 kafin a fara hisabi, shekaru dubu hamsin da, ba kuma irin shekarun duniya ba, wuce nan, sannan za'a sauko masu da rana dab kansu, wanda ya yi aikin alkhairi ya bi Allah da manzonsa zai kasance ne a ƙarƙashin inuwar alarshin Ubangiji. (Allah kasa muna daga cikin masu samun wanna ni'imar) Za a yi tambaya kan imanin mutum, ibadarsa, arzikinsa da yadda ya kashe shi, da iliminsa da yadda ya amfani da shi, idan aka yi maka wannan tambaya me zaka ce?"
Ta jefa mashi tambaya tana kallan yadda face ɗinsa yake kara rikiɗewa. Babu alamar zai iya buɗar baki ya yi mata magana, dan haka sai ta cigaba da cewa.
"Bayan dikka wannan fa akwai hayewa gadar airaɗi, kafin nan akwai musifun kabari, kasan me siraɗi kuwa?. Annabi (SAW) ya bayyana cewa akwai wata gada mai tsananin siranta da ke kan wutar jahannama, wato gadar Siradi.
Wasu za su haye gadar cikin sauri kamar walƙiya, masu aiki na kwarai kenan, wasu kamar iska zasu wuce saboda tsabar kyan aikinsu, wasu kamar doki, wasu kamar tafiya a kafa, wasu kuwa za su fadi cikin wuta saboda zalincisu. Ga shi gadar tana da kaifi fiye da takobi kuma tana da duhu mai tsanani, kai da kake aikata zalinci me kake tinanin zai faru da kai idan baka tuba ba?". Ta kai karshen maganar tana ciza laɓɓanta da karfi saboda azaban zafin wutar ya kai mata makura.
Allah yasa kun samu karin imani a kan tunatar daku lahira da na yi.💘 Wlh a dik time da na tina lahira sai na ji gabaɗaya duniya ta isheni ta fita a rai'na, sai in ji gabaɗaya na rasa me yake mun daɗi, ranar haka nike wuni sukuku, my people's akwai aiki a gabanmu babba, wlh kiyama ba karya bace, tashin hankalin dake cikinta bawa ba zai iya ɗauka ba, dan haka ku kullu ɗamara domin neman gobe mai kyau, duniya dikka kyalkyali banza ce, ruɗin shaiɗan ne ma yake ƙawata maku duniyar, dan haka ku yi wa kanku kiyamul laili tin kafin dare ya yi maku! Allah kasa mu dace ka yi mana kyakkyawar karshe.
Ƙasa cigaba da yin magana Sweetie ta yi saboda azabar da ya isheta, ta gagara yin magana kuma.
Ga dikkan alamu maganganun Sweetie sun yi tasiri a ransa, saboda kuwa ya tsaya cak ya gagara motsawa, wannan ma a tunaninsa Sweetie tana magana ne a kan Annabi Isa, kun san shi suka ɗauka a matsayin Allansu, so ya zaci tana faɗa mashi Annabi Isa zai tuhumesa a kan zalincin da yake aikatawa ne, dan haka sai ya ji kalamanta sun taɓa zuciyarsa sosai, dama ai komai taurin zuciya sai dai in bata ji batu a kan Allah ba, dole ta yi laushi sai dai idan mamallakin wanna zuciya ya ki yarda ya saduda ne kawai.
Ita kuwa Sweetie a hankali ta fara ganin dishi dishi, kafin wani lokaci numfashinta ya ɗauke cak saboda wutar ta yi mata yawa. A daidai lokacin da numfashinta ya ɗauke a dai'dai wannan lokacin barci ya ɗauke Ronnie kwance a gadan Black Tiger. Bawan Allah aman da ya yi ta shararawa ta jijjiga shi matuƙa, jikinsa dik ya mutu shi ya haifar mashi da barci.
Allah kasa kalaman nan nata su kara tasiri a zuciyar Black Tiger ko dan ta yi nasara, Sweetie ta sha wuyar rayuwa wlh, tun daga forest fa, ga kuma makanta, kai ta wahala fa, ina maganar Allah ba wasa ba wlh, dole zuciya ta girgiza wai dan ma bai da sani a kan hakan, ma'ana bai karanta ya gani muraran ba, ai da yau bashi ba kwanciyar hankali bare barci. Ina matuƙar kaunar part ɗin BLACK WORLD, saboda addinina, Allah ka kashemu muna masu imani da kai.💘
🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥
In short, sati guda cur Zunaira ta yi a hospital a kwance kafin ta farfaɗo, a cikin sati ɗayan nan abubuwa sun faru wanda suka haɗa da kwanciyar commander Zafar a gadan asibiti, yanke jiki ya yi ya faɗi tin ranar da King ya umarcesa da ya hukunta Hoorain, suna isa bakin kofar ɗakin duhu bayan ya tura Hoorain ciki ya rufe kofar kawai sai ya yanke jiki ya faɗi, ranga ranga aka ɗaukesa zuwa hospital, yanzu haka satinsa ɗaya a hospital amma bai farfaɗo ba, doguwar suma ya faɗa, bawan Allah.
Sannan ciwon guyson yaki sassautawa har sai da Dr Raj ya bar Leesharh ya tsallako ya taho kingdom of power da kansa domin shi ya saba da yi mashi dik abin da ya dace. Kwana uku da kwanciyar guyson ya yi dirar mikiya a kingdom of power ɗin, a ranar da ya zo a ranar ya shawo kan matsalar, amma har yau bai koma ba yana nan, Bilal ya ɗauko wasu Drs suna kula da Leesharh a Dubai
Tin ranar da Auta ta dawo Mahnoor bata sake haɗa ido da Jaish ba, dan baya zama kwana biyun nan, tin asuba yake fita, baya dawowa wani lokaci sai karfe 12 ko 1 na dare, shi ma aikinsa ta sako shi a gaba.
A ɓangaren King kuwa, babu gudu babu ja da baya a kan hukuncin da ya yanke a kan Hoorain da Zunaira, dik da commander yana asibiti hakan bai hana shi jefa Hoorain a ɗakin duhu ba, saboda kun dai san yadda zuciyarsu take, ina da tabbacin a cikin kaso ɗari da wuya a samu kaso ɗaya na sarakuna da zasu iya bawa mayaƙa ko bayinsu auren ƴaƴansu, abu ne wanda baya yiwu sai wani nufi na Allah.
Lets cut the story saboda labarin dake gaba mai muhimmanci ya fi na baya yawa, dan wlh ainahin rikicin bai fara ba, so nike in haɗa kan familys ɗin waje guda, idan baku manta ba na faɗa maku family's daban daban ne ko? To so nike in haɗa family's waje guda, sannan kowanne ya komawa ahalinsa, a nan ne za'a fara ainahin cakwakiyar, masu yawan damuna a kan ban juyo story a kan Kamran ba, to Kamran yana nan, shi ma shugaban wani ahali ne na daban, bayyanarsa kuwa zai zo da ruɗani da cakwakiya, dan kusan shi ne key na buɗe bakin zaren dikkan waɗan nan cakwakiyoyin, soon zai dawo cikin labari da bazata na ban mamaki. (Amma bari matarsa Pretty ta kara girma😅 dan yana dawowa sai aure😅 kada ku manta mom twin's ta bashi aurenta fa, matarsa ce, saura mammarsa ta yarda kawai mu sha biki ko ba sadaki🥱 ƴan special grp zaku biya mashi sadakin ko?)
To masu matsawa a kan Pretty and Sweetie ƴaƴan King Zuhair ne na ce sannunku, wato kuna nufin King ya auri mom twin's kenan ko? Amma fa kun iya hasashe, to muje dai zuwa, yanzu zamu buɗe babin surprise, get ready, bari in fara tashin kanku a cikin pages na kwanaki nan, an sha gwagwarmaya a pages ɗin baya, na week ɗin nan kuma bari mu sha surprises, gaba sai ayi cakwakiyoyi, let's go.
So lets cut the story kaɗan a nan. Tin da Zunaira ta dawo gida take yi wa momma kuka a kan ta taimaka tasa baki daddynsu ya kyale Hoorain, ita ta yarda a rabata da shi amma dan Allah a barmata shi ya shaki iskar ƴanci, a yafe mashi hukuncin da ya hau kansa.
Momma ta tsausayawa Auta matuka, amma babu yadda zata yi, domin a kan batun Hoorain King zai iya saɓawa kowa, momma ta same shi da maganar daren jiya, warning sosai ya daka mata tare da rantsuwa da girman Allah ba zai taɓa bawa Hoorain auren Zunaira ba, kuma idan suka matsa mashi tabbas ran Hoorain suke yi wa, saboda a kan wannan magana zai iya sanyawa a kashe Hoorain mai gabaɗaya kowa ya huta. Tashin hankali.
Dik wasu masu karfin gwiwar tinkarar King su yi magana da shi sun kasa iya shawo kansa a kan wannan magana, kai in takaice maku Queen mother da kanta sai da ta sararawa King a kan wannan batu, domin ya ɗauki zafi fiye da tinaninku, Akka dan dolenta ta kyalesa, uncle Jahiz ya yi iya yinsa a kan King ya duba ya yafewa Hoorain, sai dai ina, ya ce wlh ba zai yiwu