Showing 240001 words to 243000 words out of 403653 words

Chapter 81 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

110

fara aiki. Sannan kwana biyu tsakani akwai gagarumin Birthday party ɗinsa again, wato wannan birni akwai shagali idan abubuwa basu lalace ba a ranar partyn buɗe hospital.

A tinaninku su waye zasu yi nasara? Duniyar shaiɗanu zasu samu damar ganin ɗan autan nasu har su ɗauketa? Master zai cinwa burinsa a kan Ronnie and Sweetie? Waɗan can gungun mutane masu san kwace birnin zasu cinwa burinsu? Sweetie zata cinwa burikan da ta tsara wa birnin a ranar partyn? Mu je zuwa.

••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Su Sweetie sai da suka wuce har class ɗinsu, sannan Ronnie yasa suka juya kan motocinsu izuwa gida cike da kewarta.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






40




🔥🔥🔥🔥DUBAI.🔥🔥🔥🔥

Ɗago da kallonsa a kanta ya yi da nufin ya tsawatar mata ta cire hannunta ya yi aikinsa. Sai dai kash, yana ɗagowa suka kalli juna sai ya ji tongue ɗinsa ta yi mashi nauyin ya daka mata tsawan, gabaɗaya sai ya ji wani iri a jikinsa, tamkar an sanya igiya an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗin nasa ne, ido cikin ido suka kalli juna a kurkusa, kun san yana da matuƙar wahala ku ga juna ido cikin ido zuciyoyinku basu amsa da wannan kallo ba, so har cikin ransu suka ji wannan kallo ya ratsasu. Ai bata san time da ta zame hannunta daga saman wuyan rigar ba, sai dai ji ta yi ya sanya hannunsa ya yi kasa da rigar.

Shi kansa tin da yake dubata wlh bai taɓa mayar da hankalinsa a wani halitta tata ba sai a yau, a yau ɗin ma ba komai ne ya ja hankalinsa a kansu ba face tana zaune idanunta biyu, yadda ta zauna yasa gabaɗaya tula tulan nata sun tsastsaya cir, saboda babu bra daga ta ciki, so suna nan muraransu. Ga shi yadda ya ja wuyar rigar ta ɗan yi ƙasa sosai, hakan ya basu damar bayyana.

Wlh sai da ya ji gabansa ya faɗi, lokaci guda ya nemi natsuwarsa ya rasa, da kyar ya iya cire audigar, hannunsa ma sai ɗan kerma take yi, tamkar wanda zai yaɓa wuta, gabaɗaya sai ya ji shakkar sanya hannunsa a waje, kamar dai ba jarumi Ramish namu na amana ba, lokacin guda ya zama ɗan farinsa, har wata ƴar guntuwar munafukar zufa ce take keto mashi a gafe da gefen face ɗinsa, lokaci guda ya shiga cikin wani hali.

Ita ma dai cikin wani halin take, saboda yadda hannunsa ke taɓa fatar wajen gabaɗaya ya ruɗar da ita, sai wani mutsu mustu take yi tamkar wanda ake yi wa cakulkuli, da yake shi ma yana cikin yanayi sai bai fahimci tana mutsu mutsu bama. Da kyar ya gama mata, yana gamawa ya ɓallo maganninta ya miƙa mata, lokaci guda face ɗinsa ta sauya, gabaɗaya ilahirin jikinsa tsuma yake yi, a gaggauce ya juya ya nufi hanyar waje, ko tsayawa ta sha maganin a gaban idanunsa ma ba zai yi ba, yana miƙa mata adadin da zata sha cikin zafa ya wuce waje.

Bai zame ko'ina ba sai cikin bedroom ɗinsa, da alama dai abar tasu ta gado ce ta motsa. Ga shi shi kuma ba mijin aure ba tare ya rage zafi, sai ya kwanta yana ɗan juyi a saman bed ɗin nasa.

A gefe guda kuwa, Ummie tana nan tana shirya yadda zata samesa ta biya buƙatanta, wannan friend ɗinta mai kibar sai tsara mata yadda zata yi ta same shi take yi, harda bata shawarar ta bugar da shi da kwaya a cikin abinci ko ruwan sha tun da Sharifat ce mai kai mashi abinci, sai ta yi amfani da wannan damar ta zuba mashi kwaya, idan ya sha ta tinkaresa tsab zai yi abin da take so cikin fitar hankali ba tare da yasan ya yi ba(Auzubillahi). Aikuwa Ummie ta karɓi wannan shawara, har ta tsara ranar da zata aiwatar da wannan aiki.

Wlh a duniyarmu ta yau mata irin Ummie su suka fi yawaita, Allah jama'a mu ji tsoron Allah, budurwar zuciya! Ƴarta tana san mutum ita ma tana so dan jaraba, shi kuwa ko ɗaya daga cikinsu bai ga abin ɗaga idanu ya kallah ba.

A ɓangaren Leesharh kuwa, haɗiye maganin ta yi tare da komawa ta kwanta, zuciyarta cike tab da tinanin yadda suka kurawa juna ido cikin ido, lokaci guda tinanin Sharifat ya faɗo mata a ranta da yadda take nuna tsantsar kaunar da take yi wa Ramish. Auzubillahi minashshaiɗanirrajim ta furta tare da korar tinaninsa a cikin kwakwalwarta tana addu'ar Allah kada ya sake sanya mata tinaninsa a cikin kwakwalwarta, dan bata san tina abin da ƴar uwarta take mutuwar so. Daga haka ta datse idanunta gam tana ƙoƙarin tilastawa kanta yin barcin dole.

A ɓangaren shi kuwa, a wannan dare dai barci ta gaggaresa, dan yaga abin da bai taɓa gani a zahiri ba, hankalinsa ta tashi sosai, sai juyi yake yi a saman bed barci yaki zuwa, ga shi abin takaicinma shi ne yadda tunanin tula tulan nata suka tsaya ga idanunsa da ƙwaƙwalensa, wai a hakan ma iya tudunsu ya gani ba dukka ba, dik ya rasa sukuninsa. Idan ya yi yunƙurin tilastawa kansa mancesu ma, sai face ɗinta ta fara yi mashi gizo. Daga karshe dai siririn tsaki ya ja tare da miƙewa zaune, take ya fara kuncin rai kamar wani ne ya yi mashi laifi.

Miƙewa ya yi yana wani ɗaure fuska ya nufi toilet, abar ta miƙe zat taki kwanciya, dama ga yanayin kayan jikinsa ba masu rufin asiri bane, kana iya ganin halin da abar take ciki. Alwala ya shiga ya ɗauro yana kara kwaɓe fuska. Dadduma ya zo ya shinfiɗa tare da canza kaya zuwa Arabs jallabiya ya hau yin sallah ko zai samo saukin wannan jaraba.

Ita ma dai Leesharh barcin ne ya kauracewa idanunta, tambayoyin da ya yi mata ɗazun a kan masu nikaf shi e yake ta yi mata yawo a cikin kwakwalwarta.


🔥🔥🔥🔥BABYN BABY.🔥🔥🔥🔥

Kwance take saman sofa mai zaman mutum uku, ta tada kai da laps na Ammo, tana sanye da Negligee mai shegen kyau launin maroon color, ta ɗaura silky-c a kanta, sai tashin kamshi take, ta gama shirin yin barcinta tsab. Tana tsananin kewan babynta, yau tsawon kwanaki biyu kenan bai kawo mata ziyara ba, sai dai su yi waya, shi ma wayar baya wuce two mins sai ya ce mata zai sake kiranta ya katse, baya yin awa biyu bai kira ta ba, hakan yasa ta gane abubuwa ne zuka yi mashi yawa, amma tana cikin ransa, shiyasa baya iya ɗaukar awa biyu bai kira ba, idan ya kira kuma minti biyu ya ce zai sake kira.

Tabbas ta damu saboda tana kewarsa sosai, amma kuma ta yi mashi uzuri saboda tasan tana cikin ransa. Yau tsabar kewarsa da ya yi mata yawa ma bata iya cin abincin dare ba, yoghurt kawai ta sha, ba yadda Ammo bata yi da ita a kan ta ci wani abin ba, amma taki, ta ce a ƙoshe take, Ammo ta fahimci tabbas kewar mijin nata take yi shiyasa take cikin wannan hali.

Shiru parlourn babu abin da zaka ji yana tashi sai kamshi da sanyi Ac, tv dake kunne ma ƙasa kasa yake magana ta yadda ba'a iya jin abin da ake faɗe a ciki sosai. Wayar baby dake kusa da ita ne ya fara ruri alamar shigowar kira. Ko bata dubaba ta san shi ne yake kiranta, dan ringintone na musamman ta saka mashi.

Cike da zumuɗi ta miƙe zaune tare da kai hannu ta ɗauki wayar, kamar yasan ta cika da kewarsa, miƙewa tsaye ta yi ta nufi bedroom ɗinta tana satar kallan Ammo ta ƙasar ido. Kawar da kanta Ammo ta yi kamar bata gansu ba, oh su baby ma wai yanzu idan za'ayi waya da baby sai a gudu daga kusa da Ammo, kai wannan yarinya ita ma tana yin san ranta fa.

Sai da ta shiga cikin ɗakin ta yi saurin ɗaukar kiran, yana gab da katsewa ta ɗaga. Faɗawa saman bed ɗinta ta yi tare da rungumo katuwar teddy ɗinta dake saman bed ɗin, ta kwantar da kanta a saman wata teddy tana turo baki, sai ta ji tamkar a saman kirjinsa ta kwantar da kanta. Shi kuwa tun da ta ɗauki wayar yake jiran ta yi magana, dan a ƙagare yake da san jin voice ɗinta, sun yi kewar juna.

"Hello baby". Ta faɗa tamkar zata saka mashi kuka. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke wanda sai da ta ji zuciyarta ta amsa. "Baby ina kewanka sosai fa". Still cikin shagwaɓar nan dai ta yi maganar. Nisawa ya yi, shi kaɗai yasan halin da yake ciki a wannan dare.

"Am so so sorry my baby, nasan dama dole kina kewata sosai, zan zo da safe In Sha Allah kin ji?". Yadda ya yi maganar kamar wanda yake cikin maye, voice ɗinsa ma bata fita sosai................. Sarai ta fahimci yana cikin wani hali ne, dan haka a matsayinta na mace ta gari, wato house wife material sai ta fara ƙoƙarin yadda zata ga ta kwantar mashi da hankali har ya ɗan samu natsuwa ko zai iya yin barci, Allah ya gani tana san mijin nan nata, ta yi takaicin ɓoye mata kansa da ya yi, da tabbas zata tsaya tsayin daga wajen nuna mashi soyayyar da zata sa ya mance komai, ba zata taɓa barin damuwa yasamu burgin zama a zuciyarsa ba, zata cikasa da soyayyar da koda an ɓata mashi rai a waje babu gurbin zaman wannan ɓacin ran, sai dai kash, ya ɓoye mata shi mijinta ne, yanzu dik abin da zata yi mashi ba zata yi wanda zai wuce tsakanin yaya da kanwa ba, saboda kada ya tuhumeta da cewa a ina ta koyi hakan kuma shi ba yayanta bane ya za'ayi ta yi mashi hakan? Kun gane me take gudunwa dai ai ko?.

"Baby meyasa ba zaka zo yanzu muga juna ba?". Cike da kula sosai ta yi maganar........ "Aiki sosai nike yi beb, amma da safe zan zo". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Tom shikenan". Yadda ta yi maganar sai ya ji kamar tana da wata magana a ƙasa, dan haka sai ya ce. "Akwai wata matsala ce?".

Kai ta gyaɗa tamkar tana a gabansa kafin ta amsa da. "E akwai maganar da nike san mu yi dama". ........ "Okey to faɗi ina jinki?". Yana magana yana pressing na laptop dake gabansa, alamar aiki yake yi sosai.
"Baby anya maganar a zahiri ba zata fi a waya ba kuwa?". Ta jefa mashi tambayar. Zame hannunsa daga kan laptop ɗin ya yi, cikin natsuwa ya ce. "Na baki dikkan attention ɗina a yanzu yi maganar ina jinki".
Hannu tasa ta ɗan toshe bakinta saboda dariyar da take guntsewa ya kusa kubce mata, da alama akwai abin da take ɓoyewa ne. "Talk now, am listening". Ya sake faɗa...... Juyawa ta yi ta gyara kwanciyarta, sannan ta janyo bargo ta lume a ciki, ta kara rungunar teddy ɗinta da kyau, sannan ta haɗe natsuwarta waje guda, cikin sanyin murya ta ce. "Dama baby a baya ka taɓa ce mun idan na samu wanda nike so in sanar da kai da kanka zaka yi bincike a kansa in ya cancanta sai ka aura mun shi ko?". A karshen maganar ta jefa mashi alamar tambaya tare da dakatawa domin tsammatan amsa daga garesa.

Lokaci guda ya ji kirjinsa ta yi wani irin bugawa dum dum da karfin, bai san time ɗin da ya zaro idanunsa waje ba, cikin tashin hankali ya ture table ɗin laptop dake gabansa ya miƙe tsaye, sanye yake da kayan barci masu zubin pjs a jikinsa. A hankali ya taka ya nufi gaban wasu curtains dake cikin bedroom ɗin, yaye curtains ɗin ya yi nan take wata kofar glass ta bayyana, tura kofar ya yi ya fito balconynsa, daga sama yadda yake kallan garin gwanin ban sha'awa, sai dai shi kallan takaici yake yi gimbiya baby ta kona mashi ransa.

Shiru ya kasa yin magana har sai da sake cewa. "Baby baka jina ne?"....... Sarkafewa voice ɗinsa ya yi, da kyar ya ɗan yi gyaran murya kafin ya amsa da. "Ina jinki". Kamar zata yi kuka ta ce. "Kana jina amma shi ne ka yi shiru?".
A wannan karan jinjina mata kai ya yi tamkar yana a gabanta, sannan ya amsa da. "Sorry yanzu ina jinki yi magana".... Fuskarta cike da ƙayatattcen murmushi ta cigaba da cewa. "To yanzu baby na samu wanda nike so kuma yake sona, yanzu haka ya zo nan gida kawo mun ziyara kazo ku gaisa..........".

Katseta ya yi cikin tsawa yana huci. "Waye ya bashi izinin ya zo gidan?". Yadda ya futar da words ɗin sai ya baka dariya, dan a harxuƙe ya yi maganar.......
"Baby ai kai kace idan na samu mai sona na kawo shi zaka aura mun, to naga ina son shi shiyasa nace ya zo ku gaisa da kai and kuma wlh yana......." Tsawan da ya daka mata cikin kakkausar murya ne yasa ta haɗiye sauran maganganunta, bata yi zatan zai ɗauki zafi har haka ba.

Cike da ɓacin rai da fusata a fili ya ce. "Ya jirani gani nan zuwa, sai na ji uban waye ya bashi izinin yin magana dake, kema wait for me tukun nan, bari na zo". Yana kai karshen maganar ya katse kiran ba tare da ya jira reply ɗinta ba....... Cikin zafa ya wuce ta ɗauki key ɗin motarsa, kamar ba shi ne ya gama cewa ba zai samu damar zuwa gidan yana aiki ba, tuni ya mance da aiki ya figi mota sai gidan Ammo.

Ita kuwa, yana katse kiran ta miƙe a zabure, lokaci guda ta ji tsoro ya kamata, yanzu ya zata yi idan ya zo? Ta jefawa kanta tambayar. Da gudu ta diro kasan bed ɗin ta nufi waje. Bata zame ko'ina ba sai wajen Ammo, a lokacin ta koma cikin bedroom ɗinta.

Tana zuwa ta sanar da Ammo wautar da ta tabba kuma ga baby nan zuwa. Siririn murmushi irin nasu na manya Ammo ta yi, cikin natsuwa ta fara faɗa mata yadda zata yi idan ya zo ta kwantar mashi da hankali har ya fahimci wasa take yi mashi, daga karshe ta gargaɗeta da kada ta sake yi mashi irin wannan wasa, domin zata iya sanyawa ya shiga wani hali, yanzu in da ya ɗauko mota a fusace ya biyo daren nan idan wani abin ya faru fa? Irin wannan wasa yana da kyau ta san lokacin yinsa. Sosai ta ji shawarin Ammo tare da yi mata godiya.

Suna tsaka da hakan suka ji wani irin horn da aka rinƙa bugawa a gate ɗin a haukace, da gudu baby ta diro ƙasa ta nufi waje, da kallo Ammo ta bita tana tausayawa rayuwarta, saboda already baby ya faɗawa Ammo ɗin dalilin da yasa baya san kowa yasan matarsa ce, saboda familynsa, shi ɗan babban ahali ne masu ji da karfi da izza, so yasan abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa su yi accepting baby a matsayin daughter in low ɗinsu ba, wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ya ɓoyeta, shi kansa ba shi da kwarin gwiwar iya tinkarar familynsa da ita a matsayin mata, tsawon shekaru ya rasa yadda zai yi, ga shi yana santa kamar ya mutu, ba zai iya rabuwa da ita ba, musamman mahaifiyarsa da yasan ko zai mutu ba zata aminta da marasa asali ba, ya auri baby tun bata wuci 10 years ba a duniya, amma har yanzu ya gaza samun kalaman da zai iya tinkarar familynsa da shi wajen sanyasu su aminta da ita. Uhm babbar magana!!.

Bedroom ɗinta ta nufa da gudu, tana zuwa ta haye saman bed tare da shigewa cikin bargo tana sauke numfashi da sauri sauri kirjinta na ɗan bubbuga mata da ɗan karfi karfi. Da karfi ya banko kofar bedroom ɗin nata ya shigo, har sai da yasa gabanta ya faɗi sosai, da ta yi niyar yin pretending kamar tana barci, amma turo kofar da karfi yasa ta zabura ta miƙe zaune tana zazzara idanu. Fuskarsa babu annuri ko ɗigo a kanta ya afko cikin ɗakin, ransa a matuƙar ɓace sosai, numfashinsa ma kama yake yi da mai huci. Cikin kakkausar murya ya ce. "Waye ya baki izinin yin magana da wani har ki kawo shi cikin gidan nan?".

Sosai ta tsorata da ganin yanayinsa, jikinta na rawa ta diro kasan bed ɗin, dik sai ta ji ta kasa yin magana. Cikin kakkausar murya ya sake cewa. "Ina mutumin yake and ina Ammo da ta barki kika kawo wani cikin gidan nan"......... Cike da tsoron abin da zai iya aikata mata ta amsa mashi da. "Baby to ba kai kace dama in kawo dik wanda nike so zaka aura mun ba?".

Hmmm a lokacin da ya yi mata wannan magana fa bata wuci 9 years ba a duniya, amma tsabar iyashege wai bata manta da zancen ba. Kuma shi cikin wasa ta yi maganar fa.
"Ina mutumin yake na ce?!!". Cikin tsawa ya yi maganar. Satar kallan kofar fita ta yi, kafin ya ankara sai ganinta ya yi ta watso da gudu zata nufi waje. Ai cikin zafa a miliyan ya kai mata capka a ciki. Ihu ta so kurma mashi saboda tsorata sai kuma ta danne, shi kuwa tsabar yana cikin ɓacin sai sai ya yi wurgi da ita a saman bed tare da kara

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login