Showing 342001 words to 345000 words out of 403653 words
kiran, dan yadda ta ji ya ce sai da safen ya yi mata kama da wanda barci ta rigada ta ci karfinsa, so bata tsaya neman kiss na good night ba, gyarawa ta yi ta kwanta zuciyarta cike da tinanin kiss da ya bata. Saboda gajiyar hanya yasa tana kwanciya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. Tana yin barci bai fi da minti biyu ba sai ga guyson ya shigo cikin bedroom ɗin ya zo nemanta...... Ganin tana barci ya sa ya matsa dab da ita, addu'oi ya tofa mata kafin ya fice abinsa.
A ɓangaren Smart kuwa, yana barin bedroom na King ya wuce nasa, a gurguje ya yi wanka ya yi shirin kwanciya, rufe kofarsa da key ya yi ma saboda kada su zo su damesa, dan ya san Jaish zai zo, kuma yana kan tsini za'a iya samun matsala. Kuwa hasashensa gaskiya ce, dan kuwa Jaish ya zo nemansa, sai dai da ya ji kofar a rufe sai ya juya ya koma bedroom ɗinsa cike da damuwar menene yake damun ɗan uwan nasa. A daren wannan rana dai kusan rabin family ba barcin daɗi suka yi ba, cike da kunci da bakinciki wasu daga cikinsu suka kwana, har shi kansa King zuciyarsa tamkar zata fashe haka ya kwana. Momma ma dai hakan ce, Jaish cike da damuwa da tinanin san sanin abin da yake faruwa ya kwana, haka shi ma Jawad, abin dai sai shiru.
Washegari da safe, misalin karfe bakwai na safe, kiran gaggawa King ya aikawa da kowani members na family da ya hallara a cikin main parlournsa, aikuwa basu ɓata lokaci ba wajen hallara gabaɗayansu except Smart da kwata kwata ya ce ba zai sake taka kafafunsa a in da daddynsa yake ba har sai ya canza magana, kada ku manta kuma momma ta yi zazzafar magana a kan kada ya sake saka baki a kan bikin Auta, shiyasa ya yi banza da kiran daddyn nasa, ya ga massage ɗin kuma, yana kwance saman bed ɗinsa, wani ɓangare na zuciyarsa yana ta tinanin Pretty, dan da safe war haka a France tana ɗakinsa ne tana damunsa da zata sha tea ya je ya bata, yau dik sai ya ji babu daɗi da bata zo ta damesa ba, a ɗayan ɓangaren zuciyar tasa kuwa, bakinciki ne tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu!!.
Gabaɗaya family sun haɗe a main parlour, har da su Mammie, kowa ya natsu tsit yana jiran fara maganar King, Sarina burinta kawai taga Smart ya shigo cikin parlourn, dan a yunwace take da san kallansa. Fanan sai satar kallan Jaish da ya yi ƙasa da kansa yana tinanin zuwa ya duba Smart take yi, Khadijah and Zee suna part na Aunty MieMie. While ita kuma Aunty MieMie ɗin tana nan a wajen meeting da za'ayi. Gyaran murya King ya ɗan yi wanda ya janyo hankalin gabaɗayansu a kansa, natsuwa suka yi tsit dan sauraran abin da zai faɗa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kalli Jawad da Jaish ya fara magana a natse cikin bada umarni.
"Bakin Dubai sun sauka, ku shirya motocin zuwa tarbarsu a airport cikin ƙanƙanin lokaci". Ya faɗa tare da dawo da kallonsa a kan Auta dake zaune kusa da Chuchu ta kwanto jininta, dama ba komai yasa ya tattara ƴaƴan nasa dikka ba face yana san ne ya nuna masu cewa lallai ya isa da kowannensu, da alama kalaman Smart na cewa watarana zasu bijirewa maganarsa ta tsaya mashi a rai, shiyasa yake san kara nuna masu shi mai iko ne da su.
"Zunaira!". Ya ambaci sunanta. Da sauri ta ɗago daga jikin Chuchu, cike da respect ta amsa da na'am dad. "Anjuma by 2 za'a ɗaura aurenki da yayanki Abdussalam, shi ne taran jama'ar da kika gani a gidan nan, abin ya zo cikin gaggawa ne, dan haka ki shirya". Ya kai karshen maganar tare da juyo da kallonsa a kan su Momma. Da farko ya ce ba za'a faɗawa Auta ɗin ba sai an ɗaura auren, amma da Smart ya yi mashi waɗan can kalaman sai ya ce bari ya sanar da ita ya gwada masu shi ke da iko da su, kun gane irin abin ai?!!.
Wani irin zaro ido da Auta ta yi, tsabar rikicewa da shiga tashin hankali bata san lokacin da ta zamo daga saman sofa ta zube gwiwowinta a kasa ba, a kiɗime ta fara faɗin. "Dad Hoorain fa? Shi fa nike so dad, wlh Yah Abdussalam yayana ne kawai, Momma ki faɗawa dad, Akka please ki faɗawa dad cewa Yah Abdussalam yayana ne kawai, small dad ka faɗawa dad ina san Hoorain ka ji?". Cike da tashin hankali take sambatun, ba komai ya girgizata har yasa ta fita hayyacinta ba face tasan King magana ɗaya yake yi, yanzu ya rigada ya yi kenan, wannan abin yasa ta kusa zaucewa, surutu kawai take yi ba tare da tasan me yake faɗe ba!.
Wani irin tsawa da King ya daka mata a kan ta natsun masa ne yasa bata san lokacin da ta zabura ta miƙe ta faɗa jikin guyson tare da kankame shi gam ba. Cikin kakkausar murya King ya ce. "Na rigada na gama magana, ƴan awanni kaɗan suka yi saura!!".
Dik cikin parlourn nan babu wanda bai razana da ganin yadda King ya ɗauki zafi sosai ba! Dayawa daga cikinsu sun tausayawa Auta, mussamman ma Chuchu da tini hawaye sun gama jiƙe mata fuska, ita ma Fanan hawaye ya jiƙe eyelashes ɗinta sharkaf saura su zubo, Aneesa ma dai idanunta sun yi jajir alamar ta tausayawa sister tata.
Cikin kiɗimawa Auta ta fara faɗin. "Daddy mutuwa zan yi idan har ka aura mun Yah Abdussalam, wlh nasan zan mutu ne kawai, Yah Omar ka faɗawa daddy zan mutu". Ta faɗa cikin wani irin murya mai tsananin rauni dake taɓa zuciya. Miƙewa tsaye King ya yi, dik jikunnan dayawa daga cikinsu ya mutu, mussamman ma uncle Jahiz da yake ganin kamar suna da ƴancin yin abin da suka ga dama, kun san shi ma renon masu jajayen kunnuwa ne, so sai yake ganin kamar King ya tauye mata hakkinta ne. King kuwa ya fusata sosai, sai yake ganin ja in ja da shi da Auta ta fara yin nan kamar zancen Smart ne ya fara tabbata, nan fa hankalinsa ya yi mummunar tashi!.
"Hoorain kike so ba?". King ya faɗa murya ƙasa ƙasa. Da sauri ta fara gyaɗa mashi kai alamar e shi take so, take su momma suka fara jin daɗi har da sauke ajiyar zuciya, dan suna ganin kamar zai aminta da batun ne.......... "Tabbas ba zan hanaki aurensa ba, tin da shi kike so to bismilla gaki ga shi". Wani irin daɗi da ta ji har bata san lokacin da ta zabura ta raba jikinta da na guyson ba, sai dai kalaman King na karshe sun sa ta ji tamkar duniya ya tsaya mata cak, gabaɗaya brain ɗinta ya dai'na iya tariyo mata komai, cak ta yi na wucin gadin..
"Tin da Hoonaira kika zaɓa tashi ki je garesa, amma kuma ki shafeni a babin rayuwarki, ki cireni daga matsayin mahaifinki, ki kaddara baki taɓa sanina ba, nima na cireki daga jerin ƴaƴana, ki nemi wani uban, Obaid shi ne ɗan Auta na a yanzu, Zunaira ta mutu a rayuwata!!". Su ne kalaman da suka gigita ƙwaƙwalwar dik wanda yake cikin parlourn, dan kuwa babu wanda ya taɓa tinanin King zai tsani Hoorain har haka, ita kam Akka ko a jikinta, dan ita ce ma ta kara takawa King birki a kan batun, bai yanke hukunci ba sai da suka yi zama da ita da uncle Abbas, a nan ne fa ta ce wlh ba zata taɓa yarda Zunaira ta auri warrior ba, dan haka bata aminta ba, wannan dalilin yasa shi ma King ya kara tsananta a kan hukuncinsa. Amma my people's baku ganin kamar irin wanna tsana da King ya yi wa Hoorain akwai wata dalili mai karfi a ƙasa kuwa? Anya iya kasamcewarsa warrior ne yasa ya yi mashi mummunar tsana haka? Kai ina zargin da wata ƙullalliya a ƙasa.
(Ni dai a nawa tinanin fa to kada ku ɗauka gaske ne, a nawa hasashen na ce Allah yasa ba shi ne uban Hoorain ɗin ba😅 dan kun san sarakuna suna iya tarewa da kuyangunsu, matar commander Zafar kuma kuyangarsu ce, balai'n can, wannan fa hasashena ne, dan ina ganin akwai dalili kai karfi na tsanar wanna haɗi da King ya yi, amma ku kai dubanku kan yadda Hoorain tun tasowarsa fuskarsa a rufe bata bayyana ga kowa ba zaku gane dalilin hasashena!! Me dalili rufe fuskar? Meyasa King bai damu da ya buɗe fuskarsa ba? Kai akwai fa bala'i!!! Amma mu je zuwa bayan bikin!!! King fa hege ne😅😅😅 ba dai ruwana na yi shiru sirikina ne kada ya hana aurenmu da guyson nima in shiga uku!!🥱)
Ai tsabar tashin hankali Jaish da Jawad basu san time da suka miƙe tsaye a tare ba, uncle Jahiz uncle Abbas uncle Taheer suma a tare suka miƙe, kalaman King ya gigitasu. Momma kam ta kasa motsawa daga in da take, guyson ma dai ya kasa motsawar ne, dan ya ji abin da ya girmawa shekarunsa. Dik rashin kunyar Omaid and Obaid sai da suka ji zuciyarsu ta raunata a yau, Aunty MieMie tamkar wadda ruwa ya cinyeta.
Cike da tsananin tashin hankali da kiɗima Auta ta zabura ta diro ƙasa, ai tsabar ruɗu bata san lokacin da ta isa gaban King ba. Tana kuka tamkar ranta zai fita ta riko alkyabbarsa, muryarta da kyar yake fita ta fara faɗin. "Na shaga uku na boni na lallace, wlh daddy bana san Hoorain, ka fiye mun kowa da komai a rayuwata, kai ne sanadiyar zuwata duniya da har na san daɗi da rashinsa, ka yafe mun daddy, wlh ba zan sake yin maganar kowa ba sai na Yah Abdussalam, shi ne zaɓinka kuma zaɓina, na karɓesa hannu bibbiyu ina mai biyayya, daddy tin da nike da kai ko magana cikin ɗaga murya baka taɓa yi mun ba, amma a dalilin wannan magana har marina ka yi, tabbas ko zan rasa rai'na ba zan sake kaucewa maganarka ba, dan Allah ka yi hakuri ka yafe mun, wanenen Hoorain? Ban san shi ba daddy, momma ku faɗawa daddy ko zan mutu na yarda zan zauna da Yah Abdussalam, Mummy, mama, Yah Jaish, Yah Jawad, Aunty MieMie, daddy, small dad, Yah Omar, Yah Omaid ku faɗawa dad ba zan sake ba, ya janye kalamansa a kai'na, na shiga uku na lallace yau!.........". Da kyar ta iya kai karshen maganar, a wannan gaɓa kusan dikkansu idanunsu sai da ya ciko da kwallah. Guyson, Chuchu da Aneesa kam hawaye sharɓa sharɓa. Jawad yana san zuwa ya ɗagota, amma kuma bai isa ba, saboda tsarin gidan sarauta, in har ba King ne ya basu umarni ba to fa ko mutuwa take yi a wajen haka zasu daure su bita da ido.
Ban da sambatunta da shesshekar kuka babu wani abin da zaku ji yana tashi a cikin parlon, King yana tsaye tamkar wanda aka sassaƙa yana jinta, ƙoƙari yake yi ya danni zuciyar Modarawar, dan fa ya hasala matuƙar. Ganin kukan nata ya yi yawa, tamkar zata rasa ranta yasa Queen mother ta miƙe ta isa wajen, dan bayan Akka babu wanda ya isa ya tsoma baki a cikin wanna case ɗin ba tare da izini ba. Hannu tasa ta ɗago Zunaira, cike da sigar rarrashi ta ce. "Ya isa haka, shikenan ki yi shiru"....... A birkice ta fara tattaɓa hannun Akka tana faɗin. "Akka dad bai yafe mun ba, yaki ya yi mun magana, dan Allah Akka ki ce mashi kome yake so shi zan". ......... Hannu Akka tasa ta rufe mata baki. "Ya isa haka, ya yafe maki, Ke Rahilarh zo ki kamata ku je". Ta yi maganar tana dawo da kallonta a kan Momma......... UHM KING A KAN YA NUNAWA SMART YANA DA IKO DA ƳAƳANSA ZAI KASHE AUTA!! WLH SMART ƊAN DUNIYA NE, DA KALMA ƊAYA TAK YA TARWATSA ZUCIYAR KING YASA YA KUSA ZAUCEWA!!
Ai tin bata gama rufe baki ba Jaish ya matsa ya ɗauketa cak, cikin sauri ya juya ya fice da ita daga cikin parlon, sai yan zu ya fahimci ɓacin ran Smart, ashe abin da yake faruwa kenan........ "Dikkanku ku tashi ku je". Cewar Akka kenan, ta ce da su mummy su tafi. Ai a hanzarce dik suka miƙe suka fita, wannan ya zama izina ga su Aneesa, dama abin da yasa King ya tarosu kenan, dan ya zama izini a garesu, sun kuwa tsorata ba kaɗan ba, dan sai da suka zub da kwallah, dikkansu addu'a suke yi a kan kada Allah ya ɗora masu san wani bare face zaɓin mahaifinsu.
Da kyar suka shawo kan King ya hakura, sannan ya wuce fada dan tarban manya manyan baki, Abu Abdussalam da kansa ya tako har KINGDOM OF POWER ya zo wanna ɗaurin aure, abokan Abdussalam tawaga guda suma sun iso yau, abubuwa dai babu kama hannun yaro. Ita kuwa Auta tin da ta yi shiru ta dakata da wannan kuka ba wanda ya sake jin bakinta ta furta wani abin, ta zama ganganji kawai, dan ainahin ruhinta yana tare da Hoorain, Allah sarki yana can bai san me yake faruwa ba, da safe ya yi ta kiranta almost 10 miss calls bata ɗaga ba, dik ya bi ya shiga damuwa, amma haka ya yi shirinsa sosai, dan yau gidan ya kara cika, tsaro zai tsananta a kingdom ɗin, ga kuma baƙi, dole ya shirya ya fita da wuri, amma ya so ya yi waya da ita dan ya bata hakuri a kan abin da ya faru jiya, amma ba dama, haka ya shirya suka nufi masallacin King dan tabbatar da tsaron rayuka, sai tsokanarsa su Ansar suke yi a kan ya kara kiba, sai dai shi gabaɗaya tin da ya tashi baya cikin mood mai kyau, sai ya ɗauki abin a matsayin ko halin da ya shiga daren jiya ne silar mutuwar jikinsa, dan gaskiya bai taɓa shiga yanayi irin na jiyan nan ba, da ace lokacin da yake juyin nan ta zo kansa tsab zai iya yi mata fyaɗe, dan gabaɗaya a out of control yake!.
In short a yau da misalin karfe biyu na rana dai'dai bayan saukowa daga sallar azahar ne dubban jama'a suka shaida da ɗaure auren ABDUSSALAM OMAR BADEEN tare da amaryarsa PRINCESS ZUNAIRA ZUHAIR ABDUL MALIK a kan sadaki na zallar zinari da ya haura darajar 100 million, kowa ya shaida wannan ɗauri aure da aka yi da misali karfe biyu dai'dai, jama'a sai murna suke yi, tabbas Momma ta yi murnar da ya kasance ɗan yayanta Auta ta aura, amma tawani ɓangaren ta yi tsananin bakincikin da ya kasance ƴarta bata samu zaɓin ranta ba. Ƴan uwa sai murna suke yi, yau King ya yi kyaututtukan da bai taɓa yin makamantansu ba, uncle Abbas, Uncle Jahiz dik sun yi tarin kyaututtukan da baki ba zai iya faɗarsu ba, duniya ta amsa da wannan biki, jikokin the most powerful King Badeen sun mallaki juna, ƴan uwa sun yi matuƙar murna ban da guyson da shi yasan komai. Shi kuwa Smart yana cikin bedroom tun da Momma ta yi wannan furuci shikenan bai sake fita ko parlour ba, a cikin bedroom ɗinsa yake sallah, tsawon sati ya ɗauka yana ƙoƙarin danne zuciyarsa a kan iyayen nasa, shiyasa ma yaki fitowa, dan yasan idan har zuciyarsa bata kwanta ba ya fito to fa zai iya tabka babban aiki, zaman sa lafiya ya zauna a ɗaki kada ya ja zuciyarsa ta ɓatawa momma rai!.
Hidima ta kara tsauri, sai kai komo ake yi, manyan baki daga sassan duniya daban daban sun halatta, harda manyan sarakuna daga Nigeria, masu mulki da sauransu, almost good one week aka ɗauka anata shagulgula, ita dai Auta ta zama tamkar kurma, bata uhm bata uhum-uhum, tazama abar tausayi, dik yadda aka jata haka take bi, taki furta ko word ɗaya. Hoorain ya yi kiran duniyar nan har ya gaji, sai ya ce ko dai shagalin biki ne ya yi mata yawa bari ya barta zuwa ɗan lokaci!!.
Yau za'ayi dinner, tin da su Aunty MieMie suka fara shiryata take zaune shiru bata ce ko mai ba, Allah ne kaɗai yasan me yake a cikin zuciyarta.... Anyi aladun larabawa daban daban wanda ya shafi girma da sarauta, anyi al'adar Henna Night wato laylat al-henna. Wannan rana ce na farinciki inda ake taruwa dan sawa amarya albarka, ana waka, rawa da annashuwa. Family mata da ƙawayen amarya ne ke halarta. Ana yawan amfani da garwashi da turaren wuta, da wake-waken larabawa da duma-duma. Sai dai dik Auta binsu kawai take yi, bata yi ko magana ba, da alama zuciyarta ya rigada ya mutu, gangar jikinta ce kawai ta rage tana motsawa!.
Bayan Henna night sun yi Zafaf. Ana nuna dukiya ta amarya, riguna masu kyau, kayan ado, turare, da kayan ɗaki masu ƙyalli. Wannan yakan zama wani biki daban, ana gayyatar mutane su zo su kalla. Familyn King suna ajiye wa amarya and ango manyan gift boxes masu shaƙe da zinari da lu'u-lu'u dan ɗaukaka amarya su nuna girma ta family ɗinsu. Dik kafin dinner suka yi wannan fa. Bayan ankammala shi ranar Saturday da daddare sun yi Gaisuwa da Karramawar Sarauta. Ana gudanar da gaisuwar sarauta tare da masu manyan cikin gida, ƴan majalisar sarauta, da jakadu daga ƙasashe daban-daban. Kamar yadda manyan sarakuna da shuwagabannin suka zo daga Nigeria, to amarya da ango zasu je har fada su gaisa da su!. Su kuma zasu gabatar da kyaututtuka daga sarkin garin, ministoci, da shugabanni zuwa ga amarya da ango. Sai dai nan ma Auta bata ce ba zata bi Abdussalam ba, ta bisa, suna shirye cikin tsadaddun shirinsu na jikokin the most powerful King Badeen, alkyabbar da Auta ta sanya ma da lu'ulu'u aka yi duwatsun masu hasken bala'in dake jikinsu, cover shoes dake kafafunsu daga ita har Abdussalam dik sun kasance da duwatsun lu'ulu'u aka kawata kwalliyarsu wanda hakan yasa suke ta zuba kyalli suna ɗaukar