Showing 390001 words to 393000 words out of 403653 words
nufi hanya fita dan ta gudu bedroom na Ronnie tana ƙoƙarin yin ihu sai dai voice ɗinta yaki fita sosai, a razane ta fara ƙoƙarin ɓalle kofar bedroom ɗin nata ta fita amma ina abin ya ci tura, ta gagara buɗewa, an datse kofar da karfin gaske, juyawa ta yi tana kallon yadda guguwar nan yake dinfaro cikin room ɗinta, gabaɗaya ilahirin jikinta ɓari yake yi, idanunta sun yi jajir saboda barcin da yake a kanta wanda bai isheta ba. Wasu irin muryoyi masu karfi ta ji a cikin guguwar ana magana da wasu yarukan da ko kaɗan bata taɓa jinsu a duniya ba, hankalinta ne ya kara tashi matuƙa.
Gadan gadan guguwar ya nufota yana dunkule waje guda yana fitar da kalar wuta daga cikinsa ga hayaki. Hannunta ta sanya ta kare fuskarta tare da furta lailaiha illah anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, hasbunallah wani'imal wakil. Lokaci guda ta ji an taɓa jikinta, a gaggauce ta zame hannunta daga saman face ɗinta tare da waro idanunta waje.
Nan ta yi arba da kyakkyawan face ɗin Ronnie yana tsaye, idanunsa dik barci, gashin kansa a watse kamar wani mahaukaci sabon kamu! "Sis lafiya kike ihu haka?". Ya jefa mata tambayar cikin muryar barci. A miliyan ta kai kallonta bayansa dan ta duba guguwar. Juyawa ya yi shi ma ya kai kallansa wajen, wayam babu kowa, INA GUGUWAR?. Windows ɗinma a datse suke gam. A tare suka dawo da kallonsu a kan juna.
Ɗan girgiza kai ya yi. "Akwai wani abin ne". Ya yi maganar idanunsa suna washewa daga barcin da yake yi. Haka kawai ta tsinci kanta da ƙasa faɗa mashi abin da ta gani da irin mafarkin da ta yi, sai ta ce mashi babu komai. Ɗan zubawa face ɗinta idanu ya yi yana kallon irin razanar dake a kan fuskar tata, sai kuma ya ɗan juyar da kallonsa izuwa in da ta kurawa idanu, a cikin zuciyarsa ya fahimci akwai wani abin, dole wannan ihun da ta rinƙa zundumawa wani abin ta gani, amma sai ya ce mata. "Muje ki kwanta in tayaki ki yi addu'a babu abin da zai faru In Sha Allah". Shi da yake bai san da batun Duniyar Shaiɗanu ba, sai ya zaci ko dai yayansa ne ya razanata ta hanyar magic, so yasan ba zai cutar da ita ba shiyasa ya ce su je ta kwanta.
Ba musu ta bisa ya rakata wajen bed, kwanciya ta yi tare da fara karanto addu'oi, shi ma addu'oin ya tayata karantawa waɗan da ya iya, ya shafa mata sannan ya ja mata bargo tare da miƙewa ya nufi bedroom ɗinsa dake manne da nata. Tana kallonsa bata iya ce mashi ko uppan ba, tamkar an ɗaure tongue ɗinta har ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyar da kallonta tana kallon windown, tamkar ba windown da ɗazun ya ruguje ba, to me yake faruwa da ita ne?. Ta jefawa kanta tambaya, ni kuma na amsa mata da kin fara shiga sabgar Duniyar shaiɗanu ne ta hanyar ƙoƙarin sauya masu Auta, dole su yi tattaki dan daka maki zazzafar warning, ai ke yanzu rayuwarki tana cikin gagarumin haɗari mai karfin gaske, dole ki dage da addu'a tare da fatan Allah ya raba Black Tiger da duniyar shaiɗanu, dan kuwa shi kaɗai ne zai iya tsaya maki ya kwaceki daga hannunsu, gara ki yi addu'ar ya fita daga makircinsu, idan ya fita, zai fitar dake kema!!.
My people's dik yadda aka yi Sweetie and Ronnie suna da alaƙa ta jini mai karfi gaske, saboda irin tsananin kaunar da suke yi wa junansu, sannan idan kuka yi duba da yadda Ronnie zai rungumi Sweetie, ya bata hot sumbata, ita ma zata rungumesa, amma ko kaɗan basa jin feeling ɗin juna, hakan ya nuna akwai jini mai karfi a tsakaninsu, Sweetie ta fi Floris kyau da komai da komai, amma meyasa Ronnie baya feeling soyayya a kanta sai a kan Floris? Blood is thicker than water gaskiya, dik yadda aka yi suna da alaƙar jini mai karfi, za dai muga ta ina wannan alaƙa zata fito gaskiya, ko da yanayin yadda na faɗi Ronnie zaku san yana kama da Sweetie sosai.
Da kyar barci ya ɗauketa, shi ma sai can wuraren asuba haka. Shi dai Black Tiger dik wannan bidiri da ake yi bai da labari, yana can hankalinsa a kwance yana barci, Sweetie na can tana mafarkin ya shanye mata baki!.
🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥
Fitowa ta yi daga cikin toilet ɗinsa ɗaure da towel a chest ɗinta, yanzu kwata kwata ta dai'na fita waje, kusan a cikin bedroom ɗinsa take wuni, saboda takunkumin da ya sanya mata, yana tsoratar da ita.
A maimakon ta sanya kaya anjikinta, sai ta faɗa saman bed ɗinsa haka nan tare da minginawa ta ƙudundune jikinta a cikin bargo, lokaci guda ta saki siririn murmushi tana kallon sama, yau wani irin nishaɗi na musamman take ji! Kamar ba Pretty tamu ta zamani ba!. Ta yi nisa a cikin halin da take sai ganin mutum ta yi a saman bed ɗin yasa hannun yana ƙoƙarin janyo bargon da ta rufe jikin nata da shi, ƙoƙarin hana shi ta yi ta hanyar juyawa, sai shi kuma ya matsa ya yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa.
Turo baki ta yi kafin ta ce. "Ni banaso, dan Allah kada ka taɓa mun bakina". Harara ya dalla mata kafin ya sanya hannu ya janye bargon kasa gabaɗaya, ya rage daga ita sai towel ɗin da ya haura sama gabaɗaya santala-santalan cinyoyinta a waje!.
Jan dogon numfashi ya yi tare da saukewa a hankali, hannunsa ya ɗaura a saman cinyar tata ya ɗan shafa tare da lumshe idanu alamar abin ta kai mashi karo!.
Me kuke kallah my people's? Na ce me kuke kallah a nan? Maza ku ware! Matarsa yake latsawa ba kowa ba, dan haka bamu san sa ido. Kwarai kun jini da kyau matarsa na ce!! Ya aka yi tazama matarsa, na san tambayar dake ranku kenan, ku bari idan lokaci ya yi zaku san yadda aka yi, babu wanda yasan matarsa ce sai ni, shiyasa nima na sanar da ku, ko momma fa bata sani ba wlh, ita kanta Prettyn bata sani ba, amma tabbas matarsa ce ta sunnah ma kuwa, ɗan rainin wayo shiyasa yake abin da yaga dama da ita, momma ta tambaya kuma ya ce wai ba haka ba, wai my people's a ina kuke har Smart ya mallaki Pretty baku sani ba? Gaskiya ba zan sake bari a yi maku rufa rufa ba, zan rinƙa buɗe maku kun ji ai!. Uhm King yana can yana nema mashi auren Sareena, shi kuma ya yi son ransa da ƴar babyn matarsa mai sakalci da shirirta, ga Mom ta tsaya nema mashi auren Heleena, dik ashe ya manna masu hauka ne, zaɓin Mommarsa ya ɗauka ya rabu da King and Mom, Smart ya cika ɗan halak mai son farincikin mahaifiyarsa mai kuma bin umarninta, ta umarcesa a kan Pretty kuma ya bi, surprise yake san yi mata mai zafi shiyasa yaki faɗa mata cewa matarsa ce, amma ya kuke tinanin King zai karɓi wannan al'amari? Shin zai yarda kuwa? Kada ku manta ya rigada ya karɓa mashi auren Sareena fa!.... QUEEN OF SURPRISE NIKE, yau ma na tashi kanku da batun auren Smart and Pretty, ko ya hakan ya kasance, amsar zaizo maku daga bakinsa a time da yake sanar da Mommarsa, uhm akwai kallo fa! Bala'i Pretty bata san cewa ita ɗin mallakinsa bace!!!.
Yunƙurawa ta yi zata miƙe ta bar wajen, hannu ɗaya yasa ya mayar da ita ya kwanta tare da kai hannu zai warware towel ɗin, dik iskanci da rashin jinta ashe tasan suturta tsiraici, a miliyan ta sanya hannu ta damki towel ɗin nata tana ƙoƙarin zunduma mashi ihu. Cikin sanyin murya ya ce. "Kina buɗe baki zan kira Tiger, kuma ki cire mun hannunki daga wajen".
Shiru ta yi tana girgiza kai ta fasa yin ihun, saboda tsoron Tiger yasa ta zame hannunta daga rikon da ta yi wa towel ɗin, take idanunta suka ciko da hawaye. Banza ya yi da ita tamkar bai ga hawayen ba, cikin natsuwa ya sanya hannu ya warware towel ɗin gabaɗaya ya yi mata zindir.
Tsabar tabbatar duniyanci irin na Smart sai yasa hannunsa yana kewaye ƴan matasan tula tulanta yana kallon face ɗinta. "You toooooooooo small for me! Shekarunki nawa?". Ya yi maganar yana mai da hannunsa saman lipa ɗinta. Hawaye ne suka fara gangarowa a idanunta, kun san dik yadda mace take da san bayyana tsiraicinta wlh a lokacin da tula tulanta suke tasowan girma ta tsani a kallan mata su, amma saboda iskanci irin nasa, ya san da hakan sarai, kawai dan ya bakanta mata rai ne ya buɗe mata su.
"Mena yi maki da kike kuka?". Ya faɗa a ɗan kausashe. Wai a cewarsa yanzu zai reneta ne sai ta girma, amma kunga ɗan rainin wayo yana shanye mata baki, daga reno kuma ana ta...............🤫
Kai ta girgiza mashi alamar babu abin da ya yi mata.
"Baki da bakin yin magana ne?". Da kyar ta iya ce mashi tana da shi. "To idan na sake yi maki magana kika amsa mun da kai ba ki buɗi baki kin yi magana ba sai na yi maki irin ta jiya". Tana ruwan hawaye ta ce to.
Munahiki har cikin ransa yake jin sugar kallan surar jikinta, amma saboda iskanci wai renonta zai yi, gabaɗaya hankalinsa a tashe fa yake, dik abar ta motsa, har idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kamar wuta, yana wani ciccijewa. Uhm to malam Smart mun dai san komai! A dai'na wani shassha mana kamshi ana wani ɗaɗɗaure mana fuska.
(Kambalai kun san me na tina? Yadda haɗuwar Pretty and Heleena zai kasance, ga Sareena a gefe, yadda Heleena ke mutuwar son Smart anya akwai zaman lafiya kuwa? Ga shi su turawa mata ɗaya suke yi, idan Heleena ta san ya yi aure shikenan tasan ba zai kara wata mata ba sai dai idan kashe Pretty zata yi sai ya aureta, akwai badakala! Pretty dake son Kamran kuma shi aka bata ya kuke ganin wannan bidir zai faru idan tasan ita matar wani ba Kamran bane?!)
A gefe guda kuwa Zee ce zaune a main parlour na ƙasa a party ɗin Aunty MieMie, tana shirye cikin abaya mai shegen kyau launin dark purple, ta yafa mayafin a kanta, ta yi matuƙar kyau sosai. Tana zaune saman kujera mai zaman mutum uku, shi kuma Dr yana zaune a saman kujera mai zaman mutum biyu suna fuskantar juna. Sanye yake da ƙananan kaya masu kyau da tsada. Zee tana rike da baby Ahmad yaro mai wayo kuma bai lafiya, yana girma yana ƙara kyau kamanninsa da familyn Akka yana ta kara bayyana! Ya fi kama da uncle Jahiz sosai, sai dai banbanci yanayin zanen face ɗin baby Ahmad sak Korean face ne, kazalika yanayin haskensa, ya fisu haske nesa ba kusa ba!.
Ta yi ƙasa da kanta tana jin kunyarsa, sai zuba mata love word yake yi babu kama hannun yaro, Zee ta faɗa dayawa fa!!.
A gefe guda kuwa, Mahreen ce rike da wayar Momma suna waya da guyson, ya ci sa'a yau momma ce ta bata wayar shiyasa ta karɓa, ba dan haka ba ta ce ta wuce class ɗinsa, kai Mahreen duniya, wai ta wuce class dinsa, ai Aunty Chuchu ta ce mata ai ita matar manya ce ba ta yara ba, to ita a tinaninta manyan a shekaru ake nufi, bata san Chuchu tana magana ne a kan babban gida ba, shiyasa ta ce ta wuce yara sai manyan kai, manyan kai a fagen kuɗi ake magana!! Kuɗi kuwa kowa ya san guyson akwaisu ba'a magana!.
Sai shirme take zuba mashi shi dai ko kaɗan bai damu ba, sai murmushi yake yi yana kwance a saman bed ɗinsa yana fuskantar celling, ya baro Auta and Leesharh a bedroom ɗinsu suna a tare.
A gefe guda kuwa hira sosai Aunty MieMie da Khadijah suke yi, Aunty MieMie tana san yi mata wayo ta faɗa mata wanenen daddyn Ahmad, dan tana zargin uncle Jahiz ɗinsu, amma Khadijah ta ce mata bashi bane, shi ne nan take son nuna mata fifikon shekaru ta yi mata wayau!.
A can gefe kuwa, gabaɗaya manyan cikin fada sun hallara sakamakon diran wani bako sabon fuska da basu sani ba, da alama matafiyi ne da hanya ta biyo da shi ta nan, dik a jigate yake yi, daga ganinsa ya sha wahala, magana yake yi da harshen da basa ji, kun san nace maku Kamran yana da yare wanda suke magana da shi da Mammarsa, to da shi ya yi ƙoƙarin yi masu magana da Fada, ko kaɗan bai yi turanci ba, dan ya manta yaushe rabonsa da turanci, tun rabuwarsa da su Pretty tsawon almost 2 years yanzu ake magana, ya sha bakar wahala a wajen neman su Pretty, shi yanzu ma ba babansa yake nema ba, Pretty yake nema, dan ya nemi babansa har ya gaji bai iya sanin in da yake ba, dama kuma mammarsa tasan ba zai taɓa iya ganewa ba, shiyasa ta yi mashi ɓaddakama, dan tasan idan ya doshi in da babansa yake, to fa ba shakka ko shi Kamran ɗin bai gane ba babansa ya gane ɗansa, ita kuma ba zata so hakan ba, dan bata shirya rasa shi ba, bai san tarihin babansa bane shiyasa ya nemi zuwa in da yake, matsa mata da ya yi yaki cin abinci zai kashe kanshi a banza yasa ta yarda ya je, amma ba wai dan ya haɗu da baban nasa, kawai dai ta rabu da shi lafiya. MAMMA FA TA IYA MUGUNTA YASEEN!!.
Tsawon shekaru biyu yaro na shan azaba yana wantagaririya a hanya, har ALLAH ya jefosa kingdom of power.
Idanun King a kansa babu ko kyaftawa, gani yake kamar ya gane wannan fuska dik da cewa ya canza, ya rame saboda wahala, ya yi duhu, amma kamanninsa ya dawo, dik askin da mammarsa ta yi mashi gashi ya sake fitowa fiye da na da a wajen, so kamanninsa sun bayyana.
"Sarkin gida ku ɗaukesa zuwa ɓangaren baki, ya ci abinci ya huta zuwa gobe sai mu san me ya kawo shi". Cewar King da tin da ya fara maganar har ya dire aya bai zare kallansa daga kan Kamran ba. "Commander kasa a kula da shi sosai zuwa gobe". Ya sake faɗa still kallansa a kan KAMRAN sosai, har mamakin irin kallon da King yake yi mashi KAMRAN ɗin ya yi, sai dai kuma!.
Uhm my people's abin da baku sani ba a nan shi ne, da Kamran da Hoorain uwarsu ɗaya, Hoorain mahaifiyarsa ya taimaka a daji lokacin da ya je neman su Auta ba tare da ya sani ba, kuma babu wanda ya san KAMRAN da HOORAIN uwarsu ɗaya, harta commander bai sani ba, saboda KAMRAN a forest aka haifesa, da cikinsa ta shiga dajin, KAI MY PEOPLE'S YADDA KUKE TINANI FA BA HAKA STORYN YAKE BA, KU JIRA BAYYANAR GASKIYA KAWAI, DAN DIK YADDA ZAKU YI TINANI WLH IDAN BA NI NA WARWARE MAKU BA BA ZAKU TAƁA GANO BAKIN ZAREN BA, DAN A DABAYBAYE KUKE, KU DAI KAWAI KU JIRA, LOKACIN BAYYANAR GASKIYA TA YI AI, YANZU ZA'AYI TA ZAƘULOSU ONE AFTER THE OTHER! BA DAI KAMRAN YA BAYYANA BA? TO KU JIRA AKWAI BABBAR CAKWAKIYA, WAI KUN ƊAUKA A BANZA NIKE TA CE MAKU AKWAI BABBAR CAKWAKIYAR NAN NE? UHM NA CE UHM, ABIN SAI SHIRU KAWAI, KANKU ZAI ƊAUKI CAJI OVER.
Kamannin Hoorain King yake gani a tattare da fuskar Kamran shiyasa ya kura mashi ido yana ta kallonsa, da farko ma ya ɗauka Hoorain ɗin ne, shiyasa ya shiga ruɗani, sai da ya dawo hayyacinsa sosai ya iya gane cewa Hoorain ya fi Kamran haske nesa ba kusa ba, sannan Hoorain ya fisa kyau nesa ba kusa ba, Hoorain ya fisa tsawo. Dik cikin fada babu wanda ya lura da kamannin Hoorain a furkar wannan bako face King, shi kaɗai ya lura da wannan, da yake ma ba ganin face ɗin Hoorain ɗin suke yi ba, akwai waɗan da ma basu san shi a zahirance ba!
Miƙewa sarkin gida ya yi tare da cewa ya nufi in da bakon nasu yake durkushe a saman gwiwowinsa, dik ya galabaita sosai, umarni ya bawa warriors guda biyu da suka shigo da shi a kan su ɗaukesa zuwa ɓangaren baki matafiya. Basu ɓata lokacin wajen ɗaukarsa zuwa can ba, commander ya miƙe ya bi bayansu. Har yau har gobe commander yana kallan Hoorain a idanunsa, cutar bata sake shi ba.
Tsabar mugutan irin na King kuma ya ce ba za'a kaisa hospital ba, dan idan suka tsaya mashi cutar ta sake shi, ya gane da gaske Hoorain ya mutu to tabbas zai yi masu bore, zai dai'na kare rayukansu da dukiyarsu, shiyasa ya ce a rabu da shi ya cigaba da imagine ɗin har abada!.
My people's me kuke tinanin zai faru ne wai? Uhm true colorn King yana ta kara bayyana, ta bakinku ƴan special grp ko dai a kan King RAWANIN ZALINCI take ne? To ku je dai zuwa, gaskiya tana ta bayyana tana zaƙulo kanta!!. In da one tambaya! Meyasa Mammar KAMRAN ta ce idan ya kusanci babansa tamkar ya kusanci mutuwarsa ne? Meyasa ta ce wajen babansa ba in da zai je bane?.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
62
Momma gabaɗaya kanta ya shiga ruɗani, tinani a kan mahaifiyar Hoorain ya sakota a gaba sosai, dik tinanin da ta yi sai result ɗin ya bata cewa Hoorain ɗan King ne, dik yadda zata yi wannan amsa yake fito mata, gabaɗaya kanta ya ɗauki zafi matuƙa,