Showing 18001 words to 21000 words out of 403653 words
a kan kayan.
A aljihun rigar ya ciro dalleliyar wayar Jaish, ya sha mamakin ganin wayar sosai, gata kamar sabuwa, bata ci screen ko ta lalace ba, sai dai bata kawo wuta, a kashe take.
A gefensu ya ajiye kusa da wallet ɗin ya cigaba da binciken aljihun, a nan ya samu passport, dama kun san da niyar yin tafiya Jaish ya bar gida, so ga passport ɗinsa da komai, amma ruwa ya jiƙasu har sun ɗan yayyege, sun kuma manne da juna babu halin bappa ya buɗe ya karanta.
Hakan yasa ya ajiye a gefe, cigaba da laluɓar aljihun ya yi har sai da ya tabbatar da babu wani abin da ya bari a ciki. Sannan ya ajiye kayan a gefe ya kai hannunsa ya ɗauko wallet da ya fitar da farko.
Da kyar ya iya ɓalle wallet ɗin ya buɗeta, sannan ya fara fito da abubuwan dake ciki, akwai takardarsa na ɗan kasa, ID cards da sauran muhimman cards.
Dik babu wanda bappa ya iya karantawa ya gane, saboda rubutun turanci ne a jikinsu, dibasu ya fara yi one by one yana binsu da kallo ba tare da yasan amfaninsu ko me zai yi da su ba.
Da yake yasan waya sai ya ɗauko na Jaish ɗin yana ta kallo, ya rasa ta ya zai yi ya kunnata, dan ya danna wajen kunnawa da ya sani na wayoyi amma taki kunnuwa, hakan yasa ya ji jikinsa ta kara sanyaya matuƙa, ya ga rashin amfanin bincikar aljihun tun da bai samu wani abin da zata taimaka mashi ba.
Daga karshe ya kwashi komai ya mayar in da ya fitar, ya ɗauki kayan ya mayar ya makalesu, ya dawo ya kwanta yana tunanin yadda zai yi da wannan al'amari, ya saba da Jaish sosai wanda rabuwarsu lokaci guda haka babu ko sallama zai iya haifar mashi da babbar matsala, and ya zai yi da Mahnoor?. Ya jefawa kansa tambaya.
A ɓangaren Nenne kuwa, murna kamar zai kasheta, tuni ta je ta kyankyasawa gwaggo ga abin da yake faruwa, sun yi matuƙar jin daɗin hakan, gwaggo har da wani bata shawara da ta ɗaura ɗamarar zaman gidan bappa a yanzu dan ta dawo da ƴancinta da ta rasa a baya, sannan ta tabbatar ta gallazawa Mahnoor har sai Inna ta ji ɗaci a ranta tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu.
Ba ƙaramin daɗi Nenne ta ji ba jin abubuwan da gwaggonta ta ce, dan haka ranta fes ta janyo doggin kafafunta ta nufo gidan bappa da su.
A hanya ta haɗu da Ibrahim da su Mahreen. Ko tsoron Allah babu bare kunya ta wani dakatar da zu har da cewa.
"Kai Ibrahim ina kuma zaka kai su?".
Bai tankata ba, ga dikkan alamu basa zaman lafiya da ita, ko kallon in da take ma bai yi ba ya sanya kai zai wuce ya cigaba da tafiya.
"Ba da kai nike magana bane Ibrahim? Nace ina zaka je da su?"
A harzuƙe ta yi maganar, irin ranta ya ɓaci ɗin nan, ya za'ayi ace tana mashi magana zai bawa banza ajiyarta yasa kai zai wuce?.
Still dai bai tanka ba, bai yi kamar yasan da halittar bil'adama a wajen bama, ya cigaba da tafiya hannunsa sarkafe dana Mahnoor.
"Ke Mahreen zo nan ki wuce mu tafi tun da ke kam nike da iko da ke!!".
Cike da isa da gadara ta yi maganar, irin Mahreen ƴarta ai dole ta bi umarninta. To kun san halin Mahreen ba sai na sake faɗa ba, yarinya ce da bata bin bayan rashin gaskiya komai ƙanƙantarta, dan haka sai ta ce.
"Nenne ni kam kawu Ibrahim zan bi, ina gidan Arɗo yau".
"Ban yarda da haka ba! Zo maza ki wuce mu koma gida". Cikin gadara ta yi maganar.
"Nenne wai idan mun je gidan me zan yi maki? Kawai in je in zauna?".
Kai ta gyaɗa mata alamar e, sannan ta ɗaura da cewa.
"Kwarai kuwa, ko ban isa in ce ki yi abu bane?".
Shiru ta ɗan yi tare da juyawa ta kalli Ibrahim da Mahnoor da suka ɗan yi nisa a tafiyar da suke yi, sun barta tsaye tana biyewa Nenne.
"Ni gaskiya Nenne ba zan koma gida ba, wajen ƴar uwata zan je, ke bakiga kuka take yi bane? Zan je ne mu rarrasheta, yau a gidan Arɗo zamu wuni!".
Tana magana tana turo baki na rashin kunya da kuma shagwaɓa
"Eyee ke da in nace ki je wajen gwaggo sai ki ce mun baki son zuwa ke ba zaki je gidan Arɗo ba, amma yanzu saboda munafurci ne har da cewa a can zaki wuni ko?".
Kai ta gyaɗa haɗe da cewa. "Yanzu ma saboda Adda Mahnoor zan je, ba dan ita ba ni Allah ya sawwaƙa in je gidan Arɗo".
Salati Nenne ta saka ta sanar da Ubangiji, sannan ta ce. "Kema yanzu kin koyi munafurci koh Mahreen? Wato Mahnoor ta koya maki munafurci da rashin kunya ko?".
Ɗan zaro idanu waje ta yi, cike da mamaki ta ce. "Adda Mahnoor da munafurci kuma?".
Kai Nenne ta gyaɗa alamar e haɗe da cewa. "Ko karya nayi ne?".
Kai tsaye Mahreen ta amsa da. "Wlh karya ne! Adda Mahnoor bata munafurcin kowa, nice ma nan kullum nike kawo mata gulmar Inna Rabi, kuma har faɗa take mun a kan in dai'na gulmar mutane idan basa nan, in ya zama dole na yi maganarsu to ya zamana maganar da zan iya maimaitawa a gaban idanunsu su ji ransu bai ɓaci ba zan faɗa, kullum sai ta yi mun nasiha, ai Nenne ke da wancan gwaggo mai ido kamar na aljanun ne ma kuke yin gulmar mutane, ba har zagin Inna kuke yi ba? Ai ina jinku dik abin da kuke............."
Bata kai karshen maganar ba ta yanka a miliyan ta bi bayansu Mahnoor sakamakon cabka da Nenne ta kai hannu zata yi mata.
"Mahreen ki dawo nan kada ki yarda ki bisu".
Nennen da ranta ya gama ɓaci, ta kawo har wuya ne ta faɗi haka, tana da bala'in son girma, amma sai dai bata san ta yadda zata bi da mutane su girmamata ba, yau ga shi ƴar cikinta ke gaya mata ita ce munafuka kuma ma gulmaciya, me ya kai wannan ciwo fisabilillahi? Alhaki ai kuykuyone, ga shi ta fara gani.
Ina kafa me na ci ban baka ba? Kafin Nenne ta dasa aya a maganarta ma Mahreen ta kurewa ganinta, kamar wata haske ta wuce fiwwww, yarinya mai saa mai kuma baiwar iya gudu.
Galala Nenne ta saki baki tana jin ɗacin maganganun Mahreen a ranta, karin ɓacin rai ma shi ne yadda Mahreen ta haɗe har da gwaggo ta zage, abin ya bakanta mata matuƙa.
Ta ɗan jima tsaye a wajen tana tunani, wucewar da Mairo ta zo zata yi a kusa da ita ta ɗaga mata gaisuwa ne ya fargar da ita ashe a kan hanya take tsaye.
Wani irin ƙasƙantacen kuma walaƙantatcen kallo ta bi Mairo da shi, bata amsa gaisuwar Mairo ba, sai wani kallon up and down da take binta da shi, ashe a wajenta Mahreen ta gaji irin wanna walaƙantatcen kallo da take yi wa mutane, wlh dik yadda kake ji da kanka idan aka yi maka irin wannan kallo sai ka ji kamar kai ba kowa bane, ka ji ka kaskanta ka walaƙanta, sam kallon bashi da daɗi.
Ganin haka yasa Mairo ta nufi kama kanta ta wuce, salum alum ta kama hanya, dama tasan Nenne bala'i ce, ta gaisheta ne kawai dan kada ace ta ganta bata girmamata ba.
"Ke zo nan?". Cewar Nenne.
Ba musu Mairo ta juyo ta dawo wajen ta tsaya, cikin sanyin murya ta ce. "Adda gani nan......."
Bata idasa maganar ba ta shanyeta dif sakamakon wani bahagon marin da Nenne ta sakar mata tasssss. Nenne bahaguwa ce, haka yaran Arɗo dikka suke lefty, harta Ibrahim bahagone, hakan yasa Mahnoor take bahaguwa ita ma, ta gada wajen mamarta, Arɗo shi ne ainahin bahago, so a wajensa suka gada.
A miliyan Mairo ta dafe ƙuncinta, take wasu zafafan hawayen suka faso idanunta a guje suka fara tsere a saman kumatunta, jikinta har ɗan kerma yake yi, hannun da ta dafe ƙuncinta sai rawa yake yi.
Tsabar masifa da rashin kunya irin na Nenne wai ƙoƙarin kara mata marin take yi, daga bayansu suka ji muryan bappa yana faɗin.
"Kada ki kuskura ki sake marinta". Cikin zafi ya yi maganar, ya jima bai zafafa a magana irin haka ba, tun maman Mahnoor tana nan, yau ransa a ɓace ne yasa ya zafafa.
Sanin halinsa da kuma jin ya zafafa yasa Nenne bata kara kai mata marin ba, dan tasan fa bappa ruwa ne ya daki babban zakara yasa ya yi sanyi.
"Jeki abinki Maryam". Ya yi maganar ne yana kallon Mairo da idanunta suke jajir, dan fa ba karya ta maru sosai.
Wucewa ta yi ba musu, dan tana da ladabi da biyayya. Shi ma bappa zuwa ya yi ya wuce Nenne tsaye a wajen kamar gunki bai ce mata uppan ba ya nufi hanyar gidansu Faisal, dan bappan Faisal ya aiko ya zo yana son ganinsa.
Bakinci ta kara taruwa ta yi wa Nenne kaho a wuya, ta rasa da wanne ɗaya zata ji! Wata zuciya ta ce mata ta bi bayan bappan ta je cikin mutane ta ci mashi mutunci ko zata huce haka nan. Wani zuciyar kuma ya ce ta bi bayan Mairo ta laƙƙaɗa mata ɗan banzan duka, hakan zai sa ran bappa ya ɗacaca sosai. Wani zuciya ya ce ta koma gida dik zasu zo ne su sameta tun da gwaggonta ta yi mata alkawarin zata murza kambunta, zata baza mulki a cikin gidan.
Tunani dai kala kala cike fal a ranta ta rasa madogara, sai zallar mugunta a bakar zuciyarta.
Daga ƙarshe dai da ta ga babu sarki sai Allah, sai ta shafawa kanta ruwan sanyi ta nufi gida tana ta wani kunkuni tana tsinewa bappan da bai san tana yi ba a cikin zuciya.
============🔥😥💔============
BLACK WORLD🔥
Shiru Sweetie ta kwanta saman bed ɗin Ronnie tana tunanin duniya, su kuwa suna church. Can tunanin kyan Black Tiger ya ratso mata ta cikin kwakwalwarta. Ai a miliyan ta tashi zaune tana ɗan sake fuska.
Can sai ta fara ganin shi a idanunta yana yi mata gizo, ta mutu a kan romance pink lips ɗinsa.
Zuro ƴan kafafunta kasan bed ɗin ta yi, sanna ta diro ƙasa, dan gadon yana da tudu sosai. Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi wajen glasses da ta gani kusa da tampatsetsan mirror.
Takardu ne cike tab a cikin glasses ɗin, su handout, Bible, drama books, text books da dai sauransu, Ronnie akwai san karatu sosai, shiyasa yake da tarin takardu sosai.
Ƙoƙarin buɗe glass ɗin ta yi a tunaninta dan ta duba ko akwai hotunan Ronnie da yayan nasa, sai dai abin da bata sani ba shi kansa Ronnie ranarsa ta farko ce na ganin yayan nasa a lokacin da ta gansa.
Kasa buɗe door ɗin ta yi, dan komai nasa mai mahimmanci killace yake da securitys.
Sam bata ji daɗin hakan ba, dan ta so ta gansa. Gaban mirrorsa ta nufa dan ta ga kanta ko zata rage kewar Pretty da take ji.
Hannayenta dikka biyu ta sanya ta dafe saman glass na saman table ɗin mirror, ta zubawa kanta idanu ta cikin mirror tana kallon kyan da ubangijin talikai ya yi mata.
Tunanin yadda kamannin Kamran ɗinta zai iya kasancewa ne kawai ya faɗo mata a ranta, da shi take kwana take kuma tashi.
Kamar walkiya haka ta ga mirror yana ƙoƙarin darewa gida biyu, da farko ta ɗan tsorata, sai kuma ta dake tana cigaba da kallon mirror babu ko kyaftawa.
Kamannin face ɗinta a jikin mirror ne ya fara sauyawa izuwa wani kamanni na daban, still bata tsorata ba, sai kara zaro idanu da ta yi tana cigaba da kallon kanta.
A hankali ta cigaba da rikiɗa tana canzawa izuwa kamannin da bata taɓa ganin irinsa ba.
Wani irin haske ne ya bayyana ta cikin mirror wanda yasa ba shiri ta ɗaga hannayenta izuwa saman face ɗinta dan ta kare idanunta daga samun matsala ta dalilin wannan haske.
Buɗe tafukan hannunta da ta yi wajen ƙoƙarin rufe face ɗinta ne ya yi sanadiyar bayyanar nata magic ɗin ba tare da ta sani ba.
Bata ankara ba sai ji ta yi wani irin tsawan tarwatsewar mirror ya daki dodan kunnenta.
Watsa watsa mirror ya yi a ƙasa, karfi ne ya haɗu da karfi, fitar magic ɗinta yasa ya haifarta wannan, dan hasken nata ya haɗe da wannan haske da ya fito ta cikin mirror, kuma nata yana da matuƙar karfi na ban mamaki, shi ne sila.
A miliyan ɗari ta yi kasa da hannunta a in da ta waro idanu tana kallon yadda mirror ya yi watsa watsa, haƙiƙa a wannan karon ta jijjiga sosai, ba ita kaɗai kuma ta jijjiga ba, har da shi Black Tiger sai da ya jijjiga, dan kuwa fashewar mirror nan ba ƙaramar abu bace a wajensa, ba mirror ce kamar kowanne ba, bai taɓa zaton zata buɗe tafukan hannunta magic ɗinta ya fita ba, da bai yi ƙoƙarin razanar da ita ba.
And bugu da kari unexpect magic ɗinta ya daki saitin zuciyarsa, kafin ya farga ya kare kansa haskenta ya tarwatsa tasa da har ya ɗan yi baya kaɗan, ya ji hakan a jikinsa sosai, sai dai kuma, a take ya juya magic eyes ɗinsa ya kusar da raɗaɗɗin da ya ji.
Zuciyarsa ta bakanta sosai a kan hakan, ba'a taɓa wanda ya taɓa gigin yi mashi abu makamancin hakan ba, dan haka sai ya kudurta a ransa dole ya hukuntata ya kuma durkusar da magic dake jikinta.
Ita kuwa sai ƙoƙari take yi ta fahimci abin da ya faru da har ya kawo tarwatsewar wanna mirror haka?.
Ji ta yi ɗakin ya fara juya mata, sai ta fara ganin kamar fanka yake yi mata. Da gudu ta bar gaban mirror ta haye saman bed.
Nan take wani iska mai karfi ya banko kofar ɗakin ya shigo, tana ƙoƙarin juyar da kallonta izuwa wajen kofar ba zato ba tsammani ta ji saukar wani mahaukacin mari a kuncinta wanda bata ga hannun mutum ba, bata san daga ina marin ya fito ba.
Tun da take a rayuwarta bata taɓa jin wani abu mai bala'in zafin wannan mari ba, dik da magic dake jikinta hakan bai hana ta ga wani irin duhu ya gilma mata ba, har wani irin jiri mai karfi ne ya ɗebeta daga zaune, na ƴan sakanni ta gaza gane a wani duniya take, kunnuwanta gabaɗaya sun toshe bata iya jiyo sautin komai.
Gabaɗaya kwayayen fitillu masu hasken da suka kawata ɗakin ne suka fara ɗaukewa suna sake kawowa a lokaci guda, dai'dai lokacin da ta dawo cikin hankalinta take ƙoƙarin fahimtar me yake faruwa. Dai'dai lokacin chandelier ɗakin ta jijjigo daga sama ta yo kanta a guje.
Ihu mai sauti ta kurma tare da dirowa kasa daga saman gadon, sai wani irin haki take yi tamkar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi.
Ga mamakinta sai ta ga tana dirowa kasa chandelier ya fasa faɗowa saman bed ɗin, ya juya ya nufota da karfin gaske.
A juye ta nufi baya baya dan ta fita waje. Sai dai kofar room ɗin ya rufe kansa tun bayan shigowar wannan iska da ya jijiigo da chandelier.
Ihu take yi sosai dan bata taɓa ganin iska mai karfin wannan ba, ga shi dik in da ta yi sai chandelier ya bi bayanta.
Kurewa ɗakin ta yi a in da ta mannu da jikin bango tana cigaba da ihu.
Ronnie dake zaune saman chair a cikin katafaren church ɗinsu sai ji yake yi gabansa yana faɗuwa, sai ya ji zuciyarsa ta tsinke, kansa yana sara mashi, dik ya sara nutsuwarsa da sukuninsa, yana jin kamar wani abin ne zai faru da shi.
Idan Sweetie ta kurma ihu sai ya ji hakan a cikin ransa, amma sam bai kawowa ransa ita ce take cikin damuwa ba. Pastor na jawabi babu abin da kunnuwansa suke iya ɗauko mashi, idanunsa dai yana a kan pastor, amma baya sauraronsa.
Da wani irin karfi na ban mamaki wannan chandelier ya nufeta tsaye a jikin bango tana ihun neman taimako. Lokacin guda da chandelier ya kusa isa gareta ya riƙiɗe ya zama wani irin kaifaffen wuƙa mai dafin bala'in, hasken dake fita daga jikin wannan wuka sai da ya sanyata kanƙantar da idanunta.
Kan wukar ta zanen bakar damusa ce, hasken light blue ne yake fita daga dik wata kusurwa na jikin wukar.
Kai tsaye wuyar Sweetie wukar ya nufa, da karfi kuma. Wani irin razanannen ihun ta saki mai doɗe kunnuwa, bata da madogara, ba hanyar gudu, tana ji tana gani zata mutu.
Ganin cewa wuyarta wanna wuƙa ya nufa yasa ta kai hannayenta ta tare wuyar tata tana ihu, sai dai a wannan karon bata datse idanunta ba.
Tana tare wuyarta da hannunta unexpect taga wani haske ya fito daga cikin hannunta ya nufi wanna wuƙa, nan take wanna haske ya dakatar da wukar a dab kusa da ita.
Ya ilahi ya lilliahi, ai sumar tsaye ta yi tana kallon hannunta, her first time seeing that she has a unknowing magic, she was so surprised!.
Kamar wata wadda aka zarewa ruhi, ido ta kara zarowa tana ganin yadda hasken hannun nata yake tamkar light aka kunna, abin ya yi mugun ɗaure mata kai, tana son ta motsa hannun nata ko wani sassa daga jikinta amma ta kasa, dik sai ta ji jikinta ya yi mata nauyi sosai.
Kafafunta ne suka fara gaza iya ɗaukar gangar