Showing 144001 words to 147000 words out of 403653 words

Chapter 49 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

139

ji.

"Ya isa haka, menene yake faruwa?". King ya faɗa yana kallon Jaish da har idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kawai dan ance Mahnoor ce matarsa.

Ransa a matuƙar ɓace ya zayyanewa King dik abin da yake faruwa, daga karshe ya rufe da cewa. "Ni daddy tun banga yarinyar ba i hate her, kuma bana san in ganta ma a rayuwata, ka ce da momma bana so ta mayar da ita in da ta ɗaukota in ba haka ba kome ya faru alhaki a kan wuyarku, coz i really hated her more than your expectations".

Kalamansa cike suke tab da gaskiya, tabbas ya ji ya tsani Mahnoor kuma baya san ganinta, kada kuga laifinsa, dik abin da zai faru bashi da laifi, ya sota ne a baya lokacin da yake matsayin Hamma wanda ko sunansa na ainahi bai sani ba, yanzu kuma yana amsa matsayinsa na Prince Jaish Zuhair Abdul Malik ne, kun san kuma babu ta yadda za'ayi ace Jaish ya karɓeta haka nan tun da dani da ku dik mun san halinsa a baya, kunga kuwa abu ne da ba zai yiwu ya yarda ba duba da yanayinta.

King yana ƙoƙarin yin magana ya katsesa da cewa. "And why daddy zaka aurawa Jawad Jannat? Meyasa?".

A ɗan takaice King ya ce. "Coz he love her".

"Love". Ya maimaita kalmar yana dallawa Jawad wani irin kallon wanda idan ya yi wa su Chuchu shi na tabbata ko yawu ba zasu iya haɗiya ba saboda azaban tsoronsa. Izuwa yanzu Jawad ya fahimci da gaske ran ɗan uwansa a ɓace, kuma shi kansa ya ji ɗacin cewa da aka yi wannan ƴar kauye da Momma ta dawo da su ɗin ne matar ɗan uwansa, shi ya zaci ma wasu ƴan aikin momma ta je ta kwaso, amma kawai sai ace matan ɗan uwansa, ina gaskiya ko shi bai aminta da wannan ba, ransa ta sosu matuƙa, he feel he's blood brother pain, wannan ai ƙaskanci ne a ganinsa.

Lallai jikokin Akka sun rai'na capacityn Mahnoor sosai.........😅

Matsawa kusa da Jaish Jawad ɗin ya yi, wani irin tausayin ɗan uwan nasa ya ji, ɗan rungumosa ya yi yana ƙoƙarin kwantar mashi da hankali. King kuwa, waje ya buƙaci da su samu su zauna zasu tattauna. Da kyar Jaish ya yarda ya zauna a bakin bed ɗin daddyn nasa, sai huci yake yi shi ransa a ɓace ancuce shi da aka dangantasa da ita, an zubar mashi da kima.

Zama King ya yi a gefensu, sai da ya fara da rarrashin ɗan nasa, suka haɗu shi da Jawad suka taushi wannan zazzafar zuciyar, dan idan zuciyar bata sanyayya ba babu wata magana da zata iya shiga kunnensa har ya iya amfana da ita, hakan yasa suka fara da tausan shi.

Sai da suka tabbatar da ya ɗan huce, sannan ne King ya fara bashi labarin yadda Momma ta faɗa mashi komai dallah dallah da yadda aurensa da ita ya kasance, zaman da suka yi da komai da komai.

Tin da King ya fara magana basu ce ko uppan ba, suna binsa da kallo suna sauraro har ya dasa aya.

Da ɗan ɗaga murya Jaish ya furta. "That's not me dad! Not me! Gaskiya wannan ai sai dai a film ne kawai zai faru, me I can't do that, kawai dai they told momma what the want ne kawai, but isn't true, kuma ni i can't believe that, and i can't accept this nonsense, dik zan yi maganinsu ne". Cike da gaskiyarsa yake wannan magana.

Cigaba da tausan shi suka yi, King ne ya ce. "Sorry son, ba mommarka ta ce we should give her one week zata gabatar mana da yarinyar ba? So calm down, after one week sai mu ce we can't agree with her idan muka ganta, that's all".

Girgiza kai ya yi tare da miƙewa tsaye. "No dad, ba zai yiwu ba, babu wani one week da zata yi, yanzu zata bar gidan nan, for what reason zata ce matata ce? Ni nace ina san in yi aure ne? Did I say so?". Ya kai karshen maganar tare da nufar waje.

King bai dakatar da shi ba, dan ya fahimci lallai yau ran ɗan nasa a matuƙar ɓace yake, saboda Jaish bai taɓa yi mashi magana a irin wannan sigar ba, bai taɓa ɗaga murya fiye da nasa haka ba, kuma ga dikkan alamu Jaish ya manta a gaban King yake ma, dan har da ficewa tin basu gama magana ba, a bisa dokansu Jaish ya cancanci hukunci a kan abin da ya yi yanzu na suna magana da King ya tafi, dik da yake matsayin daddynsa sarki fa sarki ne mai cike da isa da izza a ko ina yake.

Ni kuwa na ce ba a ko'ina yake ba, ina da ja a kan wannan magana, domin kuwa a gaban momma dai baby yake zama, babu wani sarauta a wannan waje idan yana............. To dai saboda sirirkina ne na yi shiru, amma da kwance mashi zani a kasuwa zan yi....😅

🔥🔥🔥

Amma sanin halin ɗan nasa yasa bai ce komai dangane da hakan ba, sai ma ya ce Jawad ya bishi ya rarrashesa kada ransa ta cigaba da ɓaci. Da sauri Jawad ya miƙe ya bi bayansa. Shi kuma King parlournsa ya fito dan ya yi breakfast ya tafi fada, yau sarkin hatsi zai fitar da zakka daga runbum kayan hatsi na King izuwa ga talakawan dake cikin kingdom da kawaye.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A yau momma ta tsara Ibrahim kawun Mahnoor zai koma Nigeria, sai dai zai koma ba tare da ya sanya Mahnoor ko Mahreen a idanunsa ba, dan kowa yasan yadda dokan kingdom of power yake, dik da yake kawun Mahnoor yanzu matsayin matar Prince take, bashi da damar ganinta a saukake haka, idan ba ita ta buƙaci ganinsa ba to ko ya so ganinta ba za'a bashi dama ba har sai ta buƙata, kuma sun shiga ɗakin gyara ma abinsu. Ko momma ɗin ma bai samu damar gani ba, ta dai turo a faɗa mashi nan da sati ɗaya (wato idan King ya aminta da Mahnoor kenan) nan da sati ɗaya ya sanar da bappa zasu zo da tawagarsu su kawo masu kayan lefen Mahnoor da sadaki da komai da ake yi a biki, shi ne sarinta.

Sannan ta haɗa mashi uban tsaraba, yadika, shaddoji, atamfa, lace da arab abayas and jallabiyas, kayan abinci da makuɗan kuɗaɗe a kan ya kaiwa bappa a rabawa ƴan uwan Mahnoor sai sun zo nan da sati guda In Allah ya ɗorasu a kan King.

Tawagar mota guda ta ɗaga a kan a kaisa airport, ya samu gata albarkacin Mahnoor, dan kuwa private jet aka ɗaga ta ɗaukesa zuwa har birnin Jimeta Yola.

Yana san ganawa da ƴaƴan nasa, amma babu dama, haka ya hakura dan bai ga fuskar tambayar ina suke bama, saboda warriors da suka kai saƙon Momma garesa bai ga fuskar ya masu magana ba, tsoro ma suma bashi, da wuri dole ya amshi komai suka wuce airport.

Yana zuwa baifi da minti 10 ba jirginsa ya ɗaga sai Nigeria.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

UNCLE JAHIZ🔥

Sai da ya tsaya Zee ta ci abincin nan sosai ta ƙoshi, sannan ya ce ta tashi su je ya kaita wajen ƴaƴansa ta yi wanka ta shirya anjuma su je kallan Khadijah.

Ajiyar zuciya ta sauke, haƙiƙa ta yi farinciki na jin cewa zata je kallan ƴar uwarta, sai satar kallansa take yi, idan ya kalli face ɗinta kuma sai ta yi saurin kawar da kallanta.

Ɗakin Aneesa ya nufa da ita, a lokacin ita kuma tana ƙoƙarin fitowa hannunta rike da wayarta tana kallan hoton Yah Rizwan, Allah ya gani tana san bawan Allahn nan. Sanye take da sleeping dress, yanzu ta tashi daga barci, kamar wata aljana ta samu labarin Yah Jaish ya yi aure ne ta nufo waje, ko wanka bata tsaya yi ba zata je kaiwa Fanan gulmar.

Kai Aneesa duniya, da alama ƴaƴan mama ma ba baya ba a kaifin ƙwaƙwalwa, ga Ramish ga Aneesa, ko daga ina ta samo labarin Jaish ya yi aure kuma?. Maganar da iya King and Momma ne kawai suka sani, sai kuma Yah Jawad da aka faɗawa da safen nan, ko uncle Abbas and uncle Jahiz da suke matsayin uba a garesu ma basu sani ba, kai gaskiya Aneesa ta fara bani tsoro.

Zata fita shi kuma zai shigo, ɗan karo suka yi, baya ta ɗan koma tana ce mashi sorry haɗe da cewa. "Good morning my lovely second dad".

Kanta ya ɗan shafa yana amsa gaisuwar tata cike da kauna, Allah sarki koma dai me Aneesa macece mai fara'a ga iya ƴan uwanta kawai banda bare, a waje kana ganinta zaka san jinin sarauta ya ratsa jinin modarawa dake gudana a jikinta, kuma suna shiri da uncle Jahiz sosai.

"Daughter ga friend na kawo maki, ki tayata ta yi wanka ki bata kayanki ta sanya". Ya faɗa yana satar kallan Zee ta witsiyar idanunsa.

Da wani irin kallo mai kama da na ƙaskanci ta ɗan bi Zee da shi, ba dan uncle Jahiz ne ya kawota ba da bata ga dalilin da zai sa wannan ƙazamiya ta shigo mata room ba, sai wari ma take yi, ta faɗi hakan a cikin ranta, a fili kuma sai ta ɗan kwaɓe fuska, cike da izza ta ce. "Second dad wacece ita ɗin?".

Ya fahimci kyamar Zee take ji duba da yadda ta kwaɓe fuska, amma bai ga laifinta ba, dan haka suke, suna da tsabta basa san datti komai ƙanƙantarsa.

"Daughter tana da mahimmanci sosai ga rayuwata, ba kamar yadda kike tinani ba, ta wuce nan, ki kula mun da ita sosai, kada ki ji kamar ba ƴar uwarki bace, ki kalleta a matsayina kin ji?".

Ya yi mata hakan ne dan kada Zee ta fiskanci kyara da kyama a wajensu, yasansu sarai, idan ba haka ya bi da su ba wlh Zee zata yi kuka kasancewarta da su.

"Second dad ka ganta fa, a hakan ne take da mahimmanci a wajenka?". Cike da mamaki ta yi maganar. Tana yi tana ɗan hararar Zee da wannan idanun nasu na gado.................................... Jinjina kansa ya yi alamar tabbas tana da mahimmanci a wajensa.

"To amma second dad meyasa bata yin wanka, ka ji fa wari take yi". Ta sake jefa mashi tambaya.

Da yake da larabci suke yin magana, kuma sun zurfafa sosai sai yazamana Zee bata ji sosai, dama sama sama take ji, shi ma dan islamiyyar da suka yi kafin babanta ya rasu ne yasa take ɗan ji. So bata ji irin cin mutuncin da Aneesa take yi mata ba.

Satar kallan Zee ya yi kafin ya dawo da kallansa a kan Aneesa da ta turɓune fuska sosai.
"Daughter bata da lafiya ne fa, daga hospital ta tawo yanzu, please take good care of her, ni zaki yi wa kin ji my lovely daughter?".

Kai ta gyaɗa mashi amma rai bai so ba, dan yadda ta ɓata ran nan babu alamar zata yi na'am da Zee, ta yi mugu mugun rai'na class ɗin Zee, a cewarta ma ko a ƴar aiki ba zata ɗauki Zee ba, gaskiya kuma dik kuyangunsu mata ne masu tsabtar gaske.

"Allah ya yi maki albarka Daughter, anjima da yamma zan zo in ɗauketa kin ji?". Sake jinjina kanta ta yi tana cigaba da ɓata fuska.

Juyowa ga Zee ya yi, cikin harshen turanci ya ce. "Zee zan dawo da yamma in ɗaukeki, ki zauna tare da Daughter kin ji?".

Kanta a ƙasa tana ɗan satar kallansa ta amsa da okey sai ya dawo. Kamar ba zai tafi ba, alamar baya san rabuwa da ita, amma sai ya daure ya juya ya fita. Yana juyawa ta bi bayansa da kallo.

Kura mata idanu Aneesa ta yi tana kallan yadda take binsa da kallo har ya kurewa ganinta, sannan ta katseta da cewa. "Kyakkyawa ne uncle ɗina ko?".

Aneesa akwai iya shege wlh, cikin harshen turanci ta yi maganar ganin uncle Jahiz ya yi wa Zee ɗin magana da turanci, sai ta yi tinanin ko bata jin larabci ne yasa, kuma ta ganta bakar fata sai ta kara rai'na class ɗinta.

Jinjina mata kai Zee ta yi alamar yeah uncle Jahiz kyakkyawa ne. Wani irin kallan up and down Aneesa ta watsa mata kafin ta ce. "Haka ne kam, gaskiya kyakkyawa ne, amma kuma kada ki bari zuciyarki ta yaudareki a kan hakan, dan shi ɗin ba zai iya dai'daita kansa da kowa ba, amma menene a tsakaninku da shi da ya ce kina da mahimmanci a rayuwarsa? Dan dai nasan a familynmu gabaɗaya babu irinku koda na nesa ne!". Cike da shegantaka da rai'nin wayo ta yi maganar, tana wani binta da matsiyacin kallo.

Zee ta fuskanci kalaman cin mutuncin a juye Aneesa take aiko mata da shi, dan haka sai ta yi shiru bata sake amsa mata ba, amma tabbas ta ji babu daɗin hakan, a tinaninta Aneesa zata karɓeta hannun biyu tun da basu wuce mate a shekaru ba, sai taga akasin hakan.

Jin bata amsa mata bane yasa ta wuce gaba tana faɗin. "Ki karisa ciki akwai toilet, ki yi wanka, sai ki duba dressing room ɗina akwai wani part da na ware zaki ga a jikin glass ɗin na rubuta n-n, ki buɗe glass ɗin ki ɗauki kayan da suka maki a ciki, ni ina da abin yi". Ta kai karshen maganar tare da ficewa.

Bayanta Zee ta bi da kallo har ta fita daga cikin ɗakin, sannan ta dawo da kallonta a kan alatun dake makare a cikin ɗakin, one after the other ta fara bin komai na cikin ɗakin da kallo, ita kanta a yanzu ta yarda lallai su Aneesa ba sa'anta bane, sun wuce da class ɗinta, irin wannan Daula haka? Ga yaran gidan dikka kyawawa gaske, ƴan gayu, kamar su suka yi kansu, ga iya wanka da tsabta, sai balai'n shan kamshi da jiji da kai suka iya.

Da dai taga tsayuwa ba zai amfana mata kimai ba sai ta wuce ta nufi in da take zatan shi ne toilet na room ɗin, tana tafiya tana zuba ƙauyanci.

Ita kuwa Aneesa tana fita kai tsaye ɗakin kuyangun da suke yi mata hidima ta nufa, ko sallama babu ta shige ciki. Ƴan mata guda biyu ne suke zaune saman katan bed ɗinsu suna hira.

A takaice ta ce. "Ina da bakuwa a ɗaki, idan ta gama wanka ku wanke mun toilet da P.Z, sannan ku bisa da toilet perfumes kamar kala goma haka, dan bana san in ji wani iska ya canza daga na kamshi da na saba shaƙa, ku kara gyra mun ɗaki, kada ku bari na dawo na ji wani abin in ba kamshi ba". Tana kai karshen maganar bata jira amsarsu ba ta yi wajen.

Sun risinar da kai suna ƙoƙarin ɗaga mata gaisuwa, amma ina har ta wuce ta fita abinta. Da kallo suka bita suna kara jinjina halin ƴaƴan King, yaran nan babu mai iya masu sai iyayensu.

Tana fita bata zame ko'ina ba sai room ɗin Fanan. Tana shiga ta isko Fanan na zuba barci, ta wani baje a gadanta tana barci cikin nitsuwa, kai ba ɗan'kwali arab hairn nan nata a watse har face ɗinta. Hayewa saman bed ɗin ta yi tana ɗan turo baki.

Ƙaramin pillow ta ɗauko, duka ta kaiwa Fanan a tsakiyar baya tana faɗin. "Aunty Fanan tashi ki ji wani labari".

Miƙa ta ɗan yi, kamar zata yi kuka, murya cike da barci ta amsa da. "Kai Neesha me kuma na yi maki fisabilillah? Ki barni in cigaba da barci na mana, jiya momma ta kawo mun wasu darty girls sun hanani barci, sai hauka suke mun"................... Gyarawa Aneesa ta yi, ta manna bayanta da jikin headboard na bed ɗin, sannan ta ce.

"To cigaba da barcin za ayi maki kafa kuwa".

Waro idanunta waje ta yi, cikin magagi ta ce. "Ban gane za'ayi mun kafa ba, me kike nufi?".

Cikin halin ko in kula ta amsa mata da. "Ina da tabbacin waɗan nan dirty girls da aka kawo maki daren jiya ɗaya daga cikinsu ce kishiyarki, renon kishiya kika yi jiya".

A zabure Fanan ta miƙe zaune, har ji ta yi barcin nata ya watse, tana zaro idanunta ta ce. "Wai me kike nufi? Ban gane kishiya ta ba?"........... Kunna wutar screen ɗin wayarta Aneesa ta yi, cikin halin ko in kula ta cigaba da cewa. "Na zo yi maki mummunar albishir ne, Yah Jaish dai ya yi aure, kuma waɗan nan ƴan kauye da momma ta kawo ɗaya daga cikinsu ce matar tasa..........."

Ai katse maganar ta yi ta ƙasa karisawa saboda wani irin capka da Fanan ta kai mata a wuyar rigarta, a haukace ta kai mata capkar, bata ma san ta yi hakan ba, kun san larabawa da balai'n kishi kamar me, tuni hankalin Fanan ya bar jikinta, har wani juyi taga ɗakin nata ya yi mata kamar fanka saboda tashin hankali, sai ta ji kamar kunnuwanta ne suka sharara mata karya.

"Ke Aunty Fanan, bafa ce maki na yi nice kishiyar taki ba, mai da wukar, ni mai kawo labari ne kawai". Ta kai karshen maganar tana zare hannun Fanan daga wuyar rigarta. Ta gama aikinta sai ta sauko kasa gadan ta nufi waje abinta. Wato wlh Aneesa yar ikka ce, kawai ta kawo labari ta tafi ta bar Fanan da tafasar zuciya.

Lallai ba shakka safiyar yau bata yi wa Fanan daɗi ba, kuma na tabbata ba zata taɓa manta wannan safiya ba, Allah sarki soyayya, ba laifinta bane.

Da gudun gaske ta yaye bargon da ta lulluɓa, ƙasa ta diro, wani irin kuka mai karfi ne ya zo mata, da sauti ta saki kukan tare da watsawa a guje sai waje. Bata zame ko'ina ba sai part na uncle Abbas wajen Mammie ɗinsu. Tana shiga kai tsaye bedroom ɗin Mammienta ta nufa.

Nan ta isko Sarina da Mammiensu zaune a saman bed, Sarina ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login