Showing 315001 words to 318000 words out of 403653 words
ɗin jikinsa da kallo ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, gudun kada ya ganota yasa ta yi saurin kawar da kallonta daga kansa, tasan kwararrun jami'ai suna amfani ne da motsi da kuma idanun mutum wajen gano mai laifi ko mai gaskiya, dan haka sai ta yi juriyar zare kallanta a kansa, ba wai dan bata sha'awar ta yi ta kallansa ba, saboda kowa ya gansa sai ya sake kallah. Dan kawai ta kare kanta kuma ta tabbatar da shirinta. TO ME TAKE SHIRYAWA KENAN? HAR DA WANI TA TABBATAR DA SHIRINTA!.
Shi kuwa binta da kallon tuhuma ya yi, yadda ya ga idanun nan nata bai yarda da ita ba, dole akwai abin da take shiryawa wanda bai sani ba, dan haka sai ya gyara tsayuwarsa a jikin door ɗin, ya harɗe hannunsa a saman kirjinsa da kyau ya cigaba da binta da kallon dan gane ina ta dosa. Gabaɗaya sai ta tsargu, ita kaɗai sai ta rinƙa sauke ajiyar zuciya tana ɗan dafe kirjinta, sai kuma ta rinƙa satar kallonsa ta kasan ido wanda dik yana kallonta, alamar rashin gaskiya dai ya tabbata kamar yadda yake zargi.
"Aesh". Ya faɗa ba tare da ya kawar da kallonsa daga kanta ba. Kin amsawa ta yi, dan tana ganin ko magana ta yi zai gane bata da gaskiya. Nisawa ya ɗan yi kafin ya juya, kamar bai gane komai ba ya ce. "Tin da ba zaki yi mun magana ba to na tafi, zan fita nan da 30 mins, zan dawo da wuri, pray for me". Ya kai karshen maganar tare da barin wajen ba tare da ya sake ɗaure idanunsa a kanta ba.
Wani irin daɗi ta ji da ya tafi, da gudu ta diro kasan bed ɗin tana sauke ajiyar zuciya, bukatarta kenan. Kai tsaye kofar ɗakin ta nufo domin ta leƙa shi, ya yi matuƙar kyau cikin wanna dressing ɗin, dama daurewa kawai ta yi ta ki kallansa, tin da ya tafi shi ne bari ta leƙa ta kallesa.
Sai dai kash, tana leƙowa suka yi four eyes, dan kuwa ba tafiya ya yi ba, ya ɗan yi baya ne ya tsaya a wajen tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana bin kofar ɗakin nata da kallo, kamar yasan zata zo leƙa shi. Ai suna haɗa ido bata san time da ta kurma ihu ba, saboda ya mugun bata tsoro, bata yi zaton zata gansa a haka ba, ga shi ya ɗan saki manyan idanun nan nasa sai ya yi kama da ya zarosu, hakan ya kara razanata. Abin gwanin birgewa gwanin ban dariya.
Da gudu ta juya ta koma cikin ɗakin tana cigaba da kurma ihu. Har da turo kofa zata murza key kamar wata mai aljanu. Hannu ɗaya yasa ya tare kofar ya hanata rufewa. Ai a miliyan ta saki kofar ta koma ciki, ta ji haushin da ya kamata zata leƙa shi, sam bata so haka ba.... Oh su Leesharh ana so ana kai wa kasuwa, wai ita mai amana, ta zage ba zata ci amanar Sharifat ba, to da alama soyayyar Ramish ne zai kasheta........ Suna yi ina shan maltina and exotic mai sanyi......🥱
Turo kofar ya yi ya dawo ciki. Tana tsaye a tsakiyar ɗakin ta yi ƙasa da kai tana kuka. Ko me na kukan kuma?. Oho mata dai. Tsayuwa ya ɗan yi na sakanni a bakin door ɗin, sannan ya taka izuwa ciki, mamakin kukan nata yake yi, amma kuma ya ji daɗi yadda ya gane cewa tana san kallon shi, in bata san shi ba zata rinƙa leƙosa tana san kallonsa idan yana waje ba. A gabanta ya tsaya kafin ya kai hannu ya riƙo hannayenta cikin nasa. Wani irin shock da ta ji ne yasa ta yi saurin ɗago kanta, while kukan nata ma ta ji ya tsaya cak.
Ƙasa sosai ya yi da murya kamar mai raɗa, cike da class haɗe da sigar rarrashi ya ce. "Aesh menene abin kuka kuma? Na yi maki wani laifi ne yanzu kuma?". Ya subhanallah, ai yadda ya yi magana yasa bata san lokacin da ta ji gabaɗaya ya kwance mata notikan ƙwaƙwalwa ba, ta ji tamkar ba'a duniya take ba.
Rasa abin faɗe yasa ta ce. "Ba kai ne kake ta kallona ba". Ita kanta tasan bata da dalilin yin kukan nata. "Da wani idanu kika kalleni har kika san ina kallanki?". Ya faɗa kamar mai raɗa. Irin wannan kallon nata mai kama da harara mai matukar tafiya da imanin nasa ta bishi da shi kafin ta yi ƙoƙarin kwace hannunta daga nasa tana faɗin. "Ni ban kalleka ba, kuma ka dai'na kallona". Ta kai karshen maganar tare da kwace hannunta da nufin ta bar wajen, tana ɗaure fuska, kamar wata maras gaskiya ta yi saurin kai hannu saman face ɗinta tana goge hawayenta, saboda tsabar karya na zuciyarta har da raya mata nadamar zub da hawaye a gabansa da ta yi, a gaggauce ta nufi toilet dan ma kada su sake haɗa ido.
Sarai yana lura da dik wani motsinta, ya tabbata yau bata da gaskiya, akwai abin da ta ɓoye mashi, amma koma menene zai gano ne, binta da kallo ya yi yana mamakin yadda idan tana tafiya surar jikinta yake motsawa cikin natsuwa da ɗaukar hankali. Sai da ta kurewa ganinsa sannan ya juya ya fita zuciyarsa na saƙa mashi abubuwa daban daban a kanta.
Shirinsa ya yi tsab cikin tsadaddun kayansa, sannan ya ɗauki car key da wayarsa ya fice daga gidan, tana tsaye a jikin window tana kallansa har ya fita, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, lokaci guda ta saki cool murmushi dan ta kalli yadda ya buɗe gate ɗin, kenan ta samu abin da take so. A gaggauce ta saki curtain na window ta dawo cikin bedroom ɗin, echolac ɗinta ta janyo daga cikin dressing room, jikinta na kerma saboda sauri, please call me hijab ɗinta dake saman bed ta ɗauka, a gaggauce ta nufo stair case, ko tura kofar bedroom ɗin ta rufe bata yi ba, kirjinta sai bugawa yake yi, fargaba kamar zai kasheta, har ta fara haɗa gumi.
Cikin sauri ta yi ƙasa, bibbiyu take tsallake stair case ɗin. Tana fitowa harabar gidan har da haɗawa da gudunta wajen isa wajen gate, kamar yadda ta ga ya yi haka ita ma ta yi wajen buɗewa, ta kuwa yi dai'dai, kaifin ƙwaƙwalwarta dai yana taimaka mata wani sa'in. Ta sha madarar mamakin ganin yanayin arear a zahiri, tsayawa ta ɗan yi wajen yin ƴan waige waige tana kallan hamshaƙan gidajen dake wajen, gaskiya sun haɗu iya haɗuwa. Ganin zata iya shekara a wajen ba tare da ta gaji da kallan ƙawatuwar arear da gidajen dake wajen bane yasa ta yi gaggawar jan echolac ɗinta ta kara gaba. Tana tafiya tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Ganin yadda take yi ne ma yasa Officers dake tsaron main gate suka tareta haɗe da tambayarta wacece ita kuma ina zata je?.
Bata ɓoye masu wacece ita ba, har da yi masu kwatancen Ramish, ta ce masu ita ce suka fita da shi rannan, Officers ɗin sun ganeta sosai, sai suka saussauta muryoyinsu a kanta wajen tambayarta ina zata je da ta fito yanzu? Kuma meyasa take tafiya take waige waige haɗi da sauri haka kamar zata faɗi? Lastly ina Ramish da ta fito ita kaɗai?......... Yau Ramish ta north gate ya fita, bai biyo ta main ba, shiyasa basu ga fitarsa ba. Murya na rawa ta hau basu excuse ɗin cewa Ramish yana gida ita kuma zata je gidan Abu Abdussalam ne duba ƴar uwarta Sharifat, ta yi maganar cike da fargabar kada ace sun ga fitarsa su gano karya ta yi masu su mayar da ita gida ko su kirasa a waya, jin cewa sun tambayi ina yake neman yasa ta yi zatan kila basu ga fitarsa ba, tin da tasan gate uku ne arear take da shi.
Da farko sun so su ɗan yi kokwanto a kan fitarta, amma da suka tina wanenen Ramish sai suka ji ba zasu iya ja da ita ba, kada yazamana shi ya ce ta tafi su kuma su kutsa cikin lamarinsa su ja wa kansu, dan haka sai suka bata hanya cikin mutumci har ma da ɗaga hannu su sara mata, ta ci albarkacin Ramish.
A hanzarce ta wuce, bata sake waigosu ba har ta yi nisa, dan tana tsoron waigowa su sake jefanta da wani tuhuma. Tafiya take yi ba tare da ta san ina ta nufa ba, har da saurinta gudun kada ruwan sama ya jiƙata, ta ga garin nata kara narkewa da hadari.
Tsawon good two hours tana tafiya, idan ta gaji sai ta zauna ta huta, ta yi tafiya mai nisan da har ta dai'na jiyo ƙamshin arear tasu. Daga karshe da wahala ta yi wahala kafafunta dik sun yi mata tsami sai ta nemi waje saman wani kujera da ake shiryawa a bakin hanya dan jiran ƙananan jiragen ƙasa masu kama da bus ɗin nan, a nan ta zauna tana mayar da numfashi, ga wani irin kishirwa da take ji, saboda tafiyar da ta yi.
Tinawa ta yi a ranta yau saura sati a fara azumi, lokaci guda ta ji zuciyarta ta buƙaci da sanin ina zata samu mafaka? Afkawa ta yi duniyar tinani dan nemanwa kanta mafita, bata yi aune ba sai ji ta yi ruwan sama mai karfin gaske ya kece kamar da bakin kwarya, juyawa ta yi gabas da yamma, kudu da arewa babu mafaka a wajen, sai dogayen bishiyoyi dake can nesa da ita, wani irin tsoro ne ya dira a ranta lokaci guda, sai ta ji tamkar ta koma, sai dai kuma ita kanta bata san ta wani hanya ta bi ta zo nan ba, tafiya kawai ta yi ta yi.
Wasa wasa ruwa na kara yawaita while gari na kara tsananta duhu, bata da mafitar da ya wuce ta zauna a wajen, dan babu mafaka a kusa. Tana ji tana gani train na farko ya zo ya tsaya a gabanta har tsawon mintuna biyu, a zaton drivern shiga zata yi, suna cika mintuna biyu kamar yadda yake a dokansu drive ya tasheta ya kara gaba. Kazalika train na biyu ma ya zo ya tsaya, nan ma bata iya miƙewa ta je ta shiga ba, dan bata da wajen zuwa. A haka tana zaune a wajen har train huɗu suka wuce, ruwan sama ya yi mata dukan gaske, ga shi ko kaɗan ruwan yaki tsagaitawa, bata san lokaci ba, dan babu abin duba time a hannunta.
Ganin ruwan nan bashi da niyar tsayawa kuma cigaba da zamanta a wajen nan ba zai haifar mata da ɗa mai ido bane yasa ta miƙe tare da jan echolac ɗinta ta fara tafiya tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tin tana iya ganin dai'dai har jiri ya fara ɗibarta, har lokacin ruwan sama bai dakata ba, nisa sosai ta yi daga in da take, a daddafe take tafiya kamar mai gocewar kashin kafa.
After some hours. Almost 6 hours ana zuba ruwan sama, daga bisani ruwan ta rage zuba amma bata ɗauke dikka ba, irin yap yap yap mai ratsa jiki ya sanya mura ɗin nan shi ne yake cigaba da zuba. Tin daga farkon ruwan nan har karshensa a kanta ya kare, a yanzu an kai gaɓar da ba zata iya cigaba da jurewa ba, tafiya cikin duhun kai yasa har ta fita cikin jama'a bata sani ba. A dai'dai wannan gaɓa ta kasa iya cigaba da tafiya, kanta yana yi mata wani irin azabbabben ciwo mai tsanani, sai kakkarwa take yi, hakwaranta sai ba da sauti mai karfi suke yi, gabaɗaya ta takure ilahirin jikinta waje guda, ga wani irin jiri dake fisgarta da karfi karfi. Dai'dai kasan wani dogon karfen sadarwa wato internet, tana ƙoƙarin ɗaga kafafunta dan ta cigaba da tafiya, sai dai ina, ta kasa, tana ɗaga kafa bata san time da jiri ya fisgeta da karfi har ta saki echolac ɗin hannunta ta tafi gabaɗayanta zata kifa ƙasa ba.
Sai dai bata kai kasan ba ya yi gaggawar tarota ta faɗa saman wide chest ɗinsa. Kamar daga sama haka ya faɗo gabanta, yana sanye da waterproof jacket mai girman da ya wuce gwiwansa, ya sanya hular jacket ɗin a kansa, dik da yana sanye da face mask, hakan ba zai hana ka gane angry face ɗin nan nasa a yau ta fi ta kullum kasancewa a ɗaure ba, harta idanunsa sun yi jajir kamar bashi da lafiya, wasu zaratan maza guda biyu ne tsaye a bayansa dikkansu rike da umbrella, ɗaya ya rike mashi ne ya tare mashi ruwa, ɗayan kuma ya rikewa kansa a in da ya biyo bayansa dan su bashi tsaro. Ransa ya matuƙar ɓaci sosai, with his harsh voice ya bawa matashin dake bayansa umarnin da ya ɗauka mashi echolac ɗinta su tafi. Yana gama bada umarnin ya ɗan duƙa ya cicciɓeta sai saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya juya da ita.
Bata kara sanin in da kanta yake ba sai da ta farka ta ganta a cikin bedroom, ga wani irin ɗumi mai daɗi dake ratsata, tana ƙudundune a cikin duv mai laushin gaske. Lokaci guda ta ware hancinta ta shaki daddaɗa kuma niimanraccen kamshin dake kai komo a cikin ɗakin, slowly ta fara bin ko'ina na cikin ɗakin da kallo, while tana jin kamar jikinta ba mallakinta bane, dik sai ta ji gangar jikinta tamkar baya a tare da ita. Tana ɗago idanu sai kan drip dake ɗaure a hannunta, zaro eyesball ɗinta waje ta yi dan ta kara tabbatarwa da kanta haka ne. Lokaci guda ta ɗan nisa tare da cigaba da jujjuya eyes ɗinta dan ta tantace a in da take. Sai dai kuma, har ta gama iya kallanta bata iya cinkar a ina take ba, ɗan lumshe idanunta ta yi na ƴan mintunan da ba zasu gaza biyu ba. A hankali ta sake waro idanunta. Ai a miliyan ta zarosu waje ganin shi a tsaye a gabanta, blinking eyes ɗin nata ta yi two time kafin ta tsayar da kallanta cak a kansa, ta tabbata ba mafarki ko gizo bane, shi ɗin ne kenan.
Angry face ɗin nan nasa babu alamar wasa kuma babu walwala ko kaɗan, tamkar bai taɓa sanin menene sakin fuska ba, ya sha kunu ya murtuƙe, ko sannu bai ce mata ba, sai dai ya kai hannu ya fara ƙoƙarin cire drip dake manne a hannunta, dan ya kare. Sosai ta sha jinin jikinta, ta tsorata da ganin yanayinsa, muryarta na ɗan kerma ta furta. "Good afternoon Yah Ramish"...... Tamkar mutum mutuminsa ne a wajen ba shi ba, ya yi banza da ita, kamar bai ji ba. Sake shan jinin jikinta ta yi tana zazzare eyesball ɗinta kamar an tare ɓera a tarko. Bata yi yunkurin sake ɗaga mashi gaisuwa ba, saboda tasan confirm ya jita, amsawa ne bai yi niyya ba.
Zare drip ɗin ya yi ya ajiye gefe guda tare da juyawa ya nufi waje. Bayansa ta bi da kallo, daga kan yanayin sleeping dress dake jikinsa ta iya fahimtar yanzu dare ne ba rana ba, ta sha mamaki sosai na ganin cewa dare ya yi, ita da ta sume a tsakanin azahar da la'asar, bata ma san kwana ɗaya ya wuce ba, dan tin jiya ta sume, sai yau ta farfaɗo, dan ma Allah ya taimaketa ta samu kula daga hannun Dr Raj da ya dawo jiya, kuma gobe zai koma kingdom of power, wani dalili ya dawo da shi, ba dan kular da ta samu ba ai da ta ɗanɗana a jikinta. (Ina tantamar anya Leesharh bata da kara mun ciki kuwa? Idan ma ba ciki akwai aljanu a kanta gaskiya 😅 kai nama fi zargin cikin ne yake sakata yin abubuwa off head haka.)
Wasa wasa tsawon kwanaki biyu Ramish baya kulata, baya yi mata magana baya kuma amsa nata maganar, alamar fa ran maza ya ɓaci sosai, tin bata wani damuwa har abin ya fara taɓata, sai take jin tamkar a rami aka haƙa aka sanyata, dik ta fara fita hayyacinta, tinani kala kala ne cike a cikin zuciyarta, wani lokaci ta ce bari ta same shi ta bashi hakuri, sai ɓangare na zuciyarta ya ce mata waye nata ne shi ɗin da har zata ce dan baya yi mata magana kuma baya amsa nata maganar zata damu? Shin sun haɗa dangi ne? Mijinta ne? Ko ubanta ne? Uwarta ne? Ko yayanta ne? Waɗan nan tinane tinanen su suke sanyawa ta ji ba zata iya tinkararsa ta bashi hakuri ba, ga shi kuma zuciyarta ta kasa jurar rashin maganar nasa, tana jin kamar ta fasa ihu. Har jikinta ya warware shi yake cigaba da kula da ita, time na shan magani da ya yi zai zo ya bata, idan ya fita ba zata sake ganinsa ba har sai zai sake bata wani maganin. Ko abinci ba shi yake kawo mata ba, wata dattijuwa ce take kawo mata, kuma idan ta yi wa dattijuwar maga sam bata amsa mata, abin ya dameta sosai, ga shi ba gidansu da ta sani ya dawo da ita ba, wannan gidan kam ma gabaɗaya ta rasa gane kansa, ko ta leƙa ta window ba abin da take gani face pool dake ta baya da basket ball area da gine ginen dake waje, abin ya jefata a ruɗani sosai matiƙa.
Uhm bata san cewa ita ce kawai makaminsu guda ɗaya da suke da shi dan isa ga masu nikaf ba, tsaronta da lafiyarta abu ne mai matuƙar muhimmanci a garesu, shiyasa ma ya canza masu gida, ya kawota waje mai tsaro sosai, damuwarsa yanzu ta samu lafiya ya samu hujjojin dake hannunta ya fara gabatar da aikinsa.
Yau takama Friday, zaune take a saman dadduma bayan ta yi sallar isha'i, ta yi shiru tana askar, amma tinaninta dik yana a kansa, yau ta kai har kololuwa sosai. Good 30 mins ta ɗauka a zaune a saman daddumar tana addu'ointa kafin nan ta miƙe, jiki dik babu