Showing 93001 words to 96000 words out of 403653 words

Chapter 32 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

126

da mahimmanci, sannan kuma da kallo ɗaya ta yi masu ta ji yaran sun burgeta, sai ma taga kamar kannenta, saboda suma fafaren fata ne.

Rarrashinsu ta taya momma yi, sannan ta ce Fanan ta zo ta kama hannunsu su je. Sam Fanan bata san taɓasu, dan kada su saka mata datti a jiki, ita ma yanzu ta ji kyamarsu yakamata saɓanin ganin farko da ta yi masu, har da ɗan kawar da kanta wai suna wari, amma da yake Aunty MieMie ce ta ce ta zo ta kamasu su tafi sai bata musa ba, ta matso ta rike hannun Mahnoor kamar wadda ta rike kashi, haka ta wuce gaba suna rungume da juna suka rufa mata baya.

Da kallo momma da Aunty MieMie suka bisu da shi har suka fice. Suna fita Fanan ta yi saurin sake hannun Mahnoor tana wani kwaɓe fuska game da toshe hanci, a fili ta furta.
"Tab dik gidan nan ba ɗakin wanda ya kai ko kwatan ɗakin Auta a kyau da tsaruwa haɗe da kayan alatu na more rayuwa masu bala'in tsada da babu su a kasar nan, sannan ace waɗan nan ƴan datti kazaman za a kai can, gaskiya an cuci Auta".

Sarai Mahnoor ta ji abin da ta faɗa, saboda ita tana jin larabci, ita kuma Mahreen ta ji wasu bata iya jin wasu ba, to kun dai san Mahreen bata gani ta kyale, ta ji ance masu ƴan datti sai ta ce.

"Wlh mu ba yan datti bane, mun yi wanka, sai dai idan kece ƴar datti, da wani shegen idonki kamar na Hamma a wajen, wlh kin yi sa'a saboda Hamma zan ɗaga maki kafa, da sai kin ci dukan zaginmu ƴan datti da kika yi!". Cikin harshen fillanci ta yi maganar, hakan yasa Fanan bata gane me ta ce ba.

Tab da Fanan ta gane me kuke tinanin zai faru? Hajiya Mahreen manyan ƙasa, bata gani ta kyale, ni yanzu tsorona ɗaya Mahreen ta iya larabci ta kuma haɗu da Sarina! Kam bala'i wato akwai bidiri ba kaɗan ba, dan dai dik da a gidansu take wlh Mahreeh ba zata ɗauki cin fuska da walaƙanci ba.

Mahnoor dai bata ce komai ba, sai ƙoƙarin goge hawayenta da suka zubo take yi, dikkansu suna tafiya ne kankame da jikinsu, saboda suna ganin kamar zasu faɗi ƙasa, dan in baku manta ba a hawa na sama suke, ta elvator suka biyo, su suna ganin kamar zasu faɗi kasa yasa suka kame jikinsu waje guda.

Suna shiga parlon Auta Mahreen ta ƙanƙame Mahnoor tana ƙoƙarin sake yin kuka, dan ita bata taɓa ganin irin waɗan nan abubuwa ba, ga tsoron mutuwa ga rashin kunya kwando kwando cike da kai tab.

Ƙanƙameta Mahnoor ma ta yi suna jan kafaru, da kyar suka yarda suka karisa shiga bedroom. Ai suna shiga ihu Mahreen ta saki, sai ma da idanunta suka sauka a kan manya manyan teddys dake shirye saman bed da wasu a saman sofas dake cikin room ɗin. Ihu Mahreen ta rinƙa yi wai ɗakin aljanu aka kawota zasu kasheta. Ita ma Mahnoor tana san yin ihun amma tana jin kunya, sai ta danne tana ƙoƙarin rarrashin Mahreen.

Fanan da sun gana kulata har wuya, ranta ya bakanta sosai ne ta dakawa Mahreen tsawa a kan ta yi mata shiru ko kuma ta dalla mata mari yanzun nan. Ai banza Mahreen ta bawa ajiyarta ta cigaba da ihunta tana faɗin a mayar da ita wajen bappanta.

Fanan tana shirin kai wa bakinta bugu momma da Aunty MieMie suka faɗo cikin ɗakin, hakan yasa Fanan ta janye kudurinta haɗe da ɗaure fuska ranta bai so shigowar su momma ba, taso ne ta dallawa Mahreen mari ko guda ɗaya ne, dan ta ji bata sansu ko kaɗa.

Wai nace ba, a haka fa Fanan bata san Mahnoor matar abin kaunarta Jaish bace, bata san kishiyarta bace, da ta sani me kuke tinanin zai faru? Muje zuwa, akwai show fa.

Da gudu Mahreen ta saki Mahnoor ta yi wajen momma tana ihun a mayar da ita wajen bappanta, ita bata san wannan gidan na aljanu ne.
Aunty MieMie da tin fitarsu momma ta sanar da ita su wayesu ne ta hau rarrashin Mahreen haɗe da faɗa mata ba gidan aljanu bane.

Ai ina Mahreen ta ce bata san wannan magana ba, ita dai Jimeta kawai za'a mayar da ita.

"Momma ki je ki yi wanka ki ci abinci ki huta bari zan rarrashesu". Cewar Aunty MieMie da Mahreen ta ƙanƙame mata hannu.

Da yake momma a gajiye take sai ta amsa da to, sannan ta juya ta fita ta barsu da Aunty MieMie ta cigaba da rarrashinsu.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangaren Jaish kuwa. Yana shiga bedroom ɗinsa cikin toilet ya wuce, hakan yasa ko da Jawad ya shigo bai samesa a ciki ba.

A gefen bed ɗinsa Jawad ya zauna dan ya jirasa, saboda ya fahimci toilet ya shiga, yana zama wayarsa ta fara ruri alamar shigowar kira. Cirosa ya yi daga aljihun wandan kayan barcin jikinsa.

Jannawad shi ne sunan dake yawo a saman screen ɗin wayar, wato Jawad and Jannat su ya haɗe cikin soyayya suka bashi sunan Jannawad.

Miƙewa tsaye ya yi, ya so yin magana da Jaish, amma kuma dole ya tafi wajen Jannat, dan dama da kyar ya iya fitowa izuwa wajen Jaish, baya san yin nisa da ita saboda halin da take ciki. Bedroom ɗinsa ya nufa kai tsaye, a hanya ya ci karo da Sarina sanye da wasu shegun kaya na barci wanda kusan da su da babu dik ɗaya ne.

Riga ce doguwa wanda ta kai mata har ƙasa, ta kuma matseta sosai, sannan shara shara ce, daga gwiwonta izuwa kasa ta gaban ribar a buɗe take, akwai wata tsaga a wajen, dik wasu albarkatu na jikinta a waje, babban abin takaicin ma shi ne yadda rigar ya matseta ya fito da murarar surar jikinta.

Tana wani taunar chewing gum hannunta rike da hotuna guda biyu, daga ɓangaransu maman Yah Ramish ta fito, sai wani sakin murmushi take yi, kasancewar bata da fara'a hakan yasa ake zargin murmushinta a dik lokacin da ta yi shi, sai ta shirya mugunta take murmushi.

Wani irin ɗan iskan kallo da ya wurga mata ne yasa sai da ta yi tuntuɓe kafarta ya turguɗe ta faɗi ƙasa, babu komai a wajen da zai iya sanyata yin tuntuɓe, amma sai gata ta yi har ta kai ƙasa. Dik iskancinta da rashin kunyarta yau da kyar ta jawo yawu ta haɗiye a wahalce tana ɗan datse idanu. Dik kuma saboda wannan kallo daya dalla mata.

Shi kuwa ya rasa yadda zai yi da shegiyar yarinyar nan, idan ya ce zai daketa wlh tsab zai iya kasheta ko ya sumar da ita, kunnenta ya fi na ƙashi tauri, yarinya ana ga annabi tana rintse idanu, in suka biyeta wlh ba zata yi saura a wannan gida ba.

Tsabar tabbatar rashin kunya wai sai ta yi kasa da kai tana ɗaga mashi gaisuwa na rashin kunya, irin ita bata ga kamar ta yi wani laifi ba. Yadda kuka san ya dallawa jajir ɗin kumatun nan nata mari, takaici kamar ya take hegiya a kasar, a fusace ya bar wajen gudan kada zuciya ta ɗebesa ya yi mata one blow seven die.

Tana ganin ya wuce ta bishi da matsiyacin harara tare da miƙewa tsaye, ta tsaya a kan kafafunta, hannunta dikka biyu tasa ta rike waist ɗinta da shi, kasa ƙasa ta furta.

"Ko uban me yasa ma ka warke daga ciwon son Jannat baka mutu ba bakin azzalumi? In dai Mammie tana shakar numfashi ta fetsar dik abin da kake so ba zaka taɓa samu ba, Jannat dai ta haramta a gareka, shi ma kuma Yah Rizwan ɗin da ya aureta ba zata taɓa zame mashi alkhairi ba, sai ya gwammaci mutuwarsa a kan aurenta, dan sai ta ɗanɗana mashi madarar azaba fiye da tunanin mutum, dan yanzu dab take da shiga sarrafawar Mammie na, dik sai kun gane baku da wayo, dik a tafin hannunmu kuke kanann marasa kunya!".

Cike da confidence take maganar, ta yi maganar ne bisa rashin sanin cewa Jannat Jawad ta aura ba Rizwan ba, kun san ita da Mammiensu basu da labarin abin da yake faruwa, Mammie na can part ɗinsu a kwance, ta yi karyar ciwo dan bata san ta zo cikin family ayi hidimar biki da ita, shi ne wai bata da lafiya, suna can suna shirya muguntarsu ita da ƴarta.............. Amma my people's me kuke tinanin Sarina take nufi da cewarta saura kaɗan Chuchu ta shiga karkashin sarrafawar Mammiensu? Anya ba wani abin a kasa kuwa?.

Hannunta ɗaya ta ɗaga izuwa dai'dai saitin face ɗinta, sannan ta naɗe yatsunta dikka ta bar iya na tsakiyar a tsaya, cike da iskanci da iyashege ta ce. "Fuck you, nonsense guy, zaka zo hannu ne yaro, soon kowa zai ɗanɗani kuɗarsa a cikin gidan nan, sai ma na auri Yah Omerish, a nan ne zaku gane baku da wayo, dan wlh har dad ma ba zan ɗaga mashi kafa ba, na godewa Allah da yasa Yah Omerish bashi da sauki dik ubanku zai ci, ni kuma in juya shi yadda rai'na yake so banzaye kawai, ni yanzu na wuce ajinku". Ta kai karshen maganar tare da fashewa da dariya kamar wata zararriya.

Sai kuma ta yi saurin toshe bakinta saboda tana kusa da part ɗin Akka ce, kada sautin dariyarta ya fita ya ja mata wata masifar, a hanzarce ta wuce izuwa part ɗin uncle Abbas, ko tsoron Allah babu bare kunya haka ta tsaga tsakanin waɗan nan part guda biyu, ta keta cikin warriors dake gadi ta nufi part ɗinsu da wannan ɗan iskar shigar nata, dik wani mayaki ya ganta sai ya haɗiyi yawu, sai dai takasance guba a garesu, dan sun san ko mutuwa suke yi ba samunta zasu yi ba, kallanta ma a sace suke yi, dan kamasu suna kallanta ma ba ƙaramin laifi bane, kuma sai sun karɓi tsastsauran hukunci.

Shi kuwa Jawad ransa a tsannin ɓace ya karisa part ɗinsa, sam baya san halin Mammie, dik ita take goyawa Sarina baya har ta lalace haka, ya rasa yadda zai yi da su, a yanzu yana takaicin a ce kannensa ne su ɗin.

Kwance ya isko Chuchu saman bed, tana kudundune a cikin bargo, jikinta ya samu sauki fa aka sallamosu daga asibiti suka dawo gida, amma yanzu jikinta da ɗumin zazzaɓi, ta kasa iya jurar rashin Auta, idan ta tinata sai kanta ya sara mata.

A gefen bed kusa da ita ya zauna, cikin sanyin murya ya tambayeta meyafaru ya ganta a cikin bargo bayan ya barta lafiya lou zata shiga wanka? Ya yi maganar yana kai hannun zai yaye bargon.

Kuka ta saka mashi haɗe da yunkurawa ta miƙe zaune. Jikinsa ta faɗo tana faɗin................. "Yah Jawad yanzu da gaske sun ɗauke mun Autata? Ni dan Allah kace su dawo da Auta su ɗaukeni ka ji?".

Cikin salon rarrashi ya ce...... "Ki yi hakuri, dad ya tura rungunar mayaka guda sun tafi ɗaukota, nan da kwana biyu war haka Auta tana tare da mu In Sha Allah, yanzu dai sauko ƙasa in baki abinci ki ci kin ji?".

Kankame rigar sleeping dress na jikinsa ta yi, kanta ta fara dirzawa a saman kirjinsa, kamar zata haɗiye ranta ta fara faɗin. "Yah Jawad ba zan iya cin komai ba".

"Why?". Ya jefa mata tambayar yana riko hannayenta cikin nasa............. "Ban sani ba Auta ta ci abinci ko bata ci ba! A wani hali take ciki dikka ban sani ba, Yah Jawad wlh ina ji a jikina Auta tana buƙatar taimakona, tabbas tana cikin damuwa, domin idan bata cikin damuwa kirjina ba zai rinƙa bugawa da karfi a dik lokacin da zuciyata ta ambaci sunanta ba, wayyo daddyna na shiga uku nikam, nasan idan basu dawo mana da ita ba mutuwa zan yi".

Kuka take yi sosai, ya fahimci ta fara fita a hayyacinta, dan haka sai ya zage wajen ganin ya rarraheta sosai, jikinta ya kara ɗaukar zafi sosai, Allah sarki bata san shima cikin wannan tashin hankalin yake ba, damuwarsa ma shi ne Jaish ya samu labarin ɓatar tata, ya twins bro ɗin nasa zai ji a ransa? Wanna yafi ɗaga mashi hankali fiye da komai.

Ƙasa ƙasa ya yi da murya sosai, cikin salo mai jan hankali ya ce. "Jannat kina san zuciyata ta buga in mutu ne?".

Kai ta girgiza mashi alamar aa bata so....... "To meyasa ba zaki barni in ji da zafi biyu ba? Meyasa ke ba zaki saukaka mun ta ɓangarenki ba? Kina dai gani har yau number Yah Rizwan bata shiga, sannan kuma su Yah Ramish sun ki haɗani da shi a waya, kowa sai ya ce mun baya kusa ko ya yi barci, a jikina ina jin akwai abin da suke ɓoye mun dange da shi da basa san in sani, saboda rashin lafiyarki na daure ban ɗaga jirgi na je na same shi ba, sannan ga ɓatar Auta da ya fi komai ɗaga mana hankali, ki daure ki yi hakuri Auta zata dawo kin ji?".

Kai kawai ta gyaɗa mashi amma ba wai dan zata iya daurewa ɗin ba. Da ya fahimci in dai tana nan a cikin kingdom ɗin nan bafa zata iya daure rashin Auta ba, dan haka sai ya yi wa P.A ɗinsa sms a kan ya yi mashi booking flight zuwa Dubai gobe da sassafe, gara ya ɗauketa su je duba Yah Rizwan meyafaru tin da ya bar kingdom ɗin wayarsa bata shiga? Daga nan su ɗan huta a can har a gane Auta ko kuma raɗaɗin ya ragun masu sannan su dawo bayan kura ta lafa.

Yana turawa P.A ɗin nasa sakon ya ajiye wayar a gefen bed, sannan ya cigaba da rarrashinta, shi dai bai more aurensa ba, matsaloli sai faruwa suke yi tin kafin auren har kuma yanzu, amma dik da haka bai wani damu ba, saboda shi ma yana cikin damuwar da ba zai iya gudanar da wani soyayya ba a yanzu.

Da kyar ya samu ta hakura ya buƙaci da ta zo ya bata abinci a baki, bata yi wani musu ba ta yarda, dan balai'n yunwa take ji, rashin nitsuwa da kwanciyar hankali yasa ta kasa cin abinci. Amma da ya zauna yana bata ta ci sosai, hakan kuma yasa da ta gama ci da ƴan mintuna ta samu barci mai nauyi da daɗi ya ɗauketa wanda tin da aka fara batun aurenta rabonta da ta yi irinsa.

Ganin ta yi barci yasa ya ja bargo ya rufeta tare da matsar mata da pillow kusa da ita dan ta ji kamar shi ne a wajen, ya sauko kasa ya shiga toilet.

After some minutes ya fito ya shiga dressing room, cikin ƙanƙanin lokaci ya fito shirye cikin brawn and milk arabs jallabiya, dadduma ya shinfiɗa ya tada sallah dan neman saukin abin dake damunsa daga wajen Allah.

Sai karfe uku dare ta tsala, sannan ya sallame sallar tare da tsawaita addu'oi, bayan ya kammala ya miƙe ya hau shirya masu kayansu da zasu yi tafiya Dubai gobe. 4:00 dai'dai ya kammala, sannan ya ɗan kwanta kafin asuba ya ɗan rintsa.

A ɓangaren su Mahnoor kuwa, kwata kwata sun ki cin abincin da momma ta saka aka kawo masu, saboda basu taɓa ganin irin abincin ba, ga uban yawa, shake da tabkeken tray, nau'ika daban daban abincin sai wanda ka zaɓa.

Amma dik sun ki ci, sun takure waje guda sunki sakin jiki, wanka ma Aunty MieMie ta yi wa Mahreen da kyar da suɗin goshi, Mahnoor kuma ta nuna mata yadda zata yi ta yi. Sun ki rabuwa da juna, sunki hawa gado, sun zauna a ƙasa, ba yadda momma bata yi da su ba sun ki yarda, sun tsorata sosai ne. Mahnoor kayan Chuchu momma ta bata ta saka, ita kuma Mahreen kayan Auta, amma kayan Autar sun ɗan yi mata yawa.

Da momma taga sun ki cin abinci sai ta ce Aunty MieMie tasa kuyanga Zubaida ta dama masu fura da nono, shi kam ai zasu sha, kun san gidan sarauta ba'a rabasu da tsabtataccen fresh nono da fura ai, dan haka sai Aunty MieMie tasa aka haɗo masu mai rai da lafiya. Nan ne fa suka ɗan sha, Mahreen ta sha mai yawa, Mahnoor kuma saboda kunyarsa momma da take ji kamar ta nitse kasa yasa ta ɗan sha kaɗan ba dan ya isheta ba ta bari.

Da kyar suka yarda suka hau gadan Auta suka kwanta, momma tana zaune kusa da su har sai da suka yi barci sannan ta fita, ba komai ya hanata fita ba kuma face kada su yi ta ihu in ta fita, saboda sun ki yarda su hau gadan sai da ta hau a tare da su, sannan ne suka kwanta, da Allah ya yi barci ɓarawo ya sacesu sai ta fita.

Bedroom ɗin mama Haulat ta shiga dan ta duba babyh Khadija da yanzu yaro ya sha wanka, kyansa ta kara bayyana matuƙa, kamar ka sace shi ka gudu.

Nan ta isko shi da mama Haulat kwance saman gado suna barci, sosai momma ta ji kamar ta ɗaukesa su koma bedroom ɗinta, amma kuma wajen King zata je, Aunty MieMie dake biye da ita ce ta tambayi ɗan waye shi ɗin? Bata faɗa masu ba ta sanya hannu ta ɗaukesa.

Tana ɗaukarsa mama Haulat ta farka daga barcin da take yi a razane, Allah sarki mace mai amana, a tinaninta sace shi aka zo yi yasa ta yi irin wanna farkawa.

Ganin momma ce yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da risinar da kai ta fara kwasan gaisuwa. A takaice momma ta amsa mata kafin ta sanar da ita zata je wajen King da babyn amma zata dawo da shi. Cikin girmamawa ta amsa da to a dawo lafiya.

Juyawa suka yi ita da Aunty MieMie suka fita, daga nan Fanan ta wuce part ɗin Akka cike da al'ajabin ɗan waye momma ta kawo? A ina ta same shi?.
Suna fitowa parlon Aunty MieMie ta miƙa hannu a kan a bata babyn, tana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login