Showing 258001 words to 261000 words out of 403653 words

Chapter 87 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

100

da shekaru 20 basu taɓa kallan abin da ya wuce face ɗin Ummie ba, kullum tana cikin abaya da rolling veil, yau rana tsaka ya ganta da irin wannan shiga a part ɗinsu kuma daga cikin bedroom na Ramish?. Tabbas ko a iya haka Abbie yasan akwai waɗan da suka ganta da shigar barci wlh zai iya haɗiyar zuciya ya mutu saboda kishi, wani irin bala'i ne wannan Ummie take san ja masu?.

Gaggauwar kawar da kallansa daga kanta ya yi daga kallo guda, shi kansa taya Abbie ɗin nasu kishi ya yi, shiyasa ma ya kawar da kallansa tare da sa kai zai wuce yana mamakin wannan al'amari. Saboda rashin tsoron Allah da mutuwar zuciya sai cewa ta yi. "Bilal kaga Ramish ne?".

Ya ɗan yi mamakin jin tambayar tata, amma sai bai kula ta ba, sam bai bata amsa ba ya yi gaggawar wucewa. Har zai shiga cikin bedroom ɗinsa sai kuma ya fasa ya dawo ya shiga na Ramish dan ya duba lafiya? Wani irin bala'i ne Ummie zata fito cikin irin wanna shiga daga bedroom ɗinsa?. Bin bayansa da kallo ta yi shaiɗan yana raya mata ai babu wani banbanci a tsakanin Bilal da Ramish ɗin, tun da tana a kan tsini kuma bata ga Ramish ba kawai ta bi Bilal ɗin ta yi manege da shi. Tashin hankali.

Aikuwa saboda shaiɗan ya ci galaba ga zuciyarta sai ta bi bayan Bilal cikin bedroom na Ramish, zuciyarta na bugawa da karfi karfi amma haka ta daure saboda cikar burinta.............. . Yana fitowa daga balcony ya je leƙa Ramish a wajen kawai unexpect ya ga mutum tsaye a tsakiyar bedroom ɗin. Siririn tsaki ya ja tare da kawar da kallansa daga kanta tamkar bai ganta ba, ya zo zai wuce ta gefenta kenan muryarta ta katse shi da cewa. "Bilal magana nike san yi da kai".

Sam babu alamar zai dakata daga tafiyar da yake yi, saboda baya san ya sake ɗaura idanunsa a kanta, wanda ya yi ma bisa kuskure ne kuma yana fatan Allah ya yafe mashi, dan shi a matsayin uwa ya ɗauketa. Ganin ya bawa banza ajiyarta yana ƙoƙarin fita waje me yasa ta yi zafin namar juyawa, taku biyu ta kamosa a in da bata yi wata wata ba bata bari kanta ya kulle ba ta yi gaggauwar faɗawa saman faffaɗar bayansa har da sauke ajiyar zuciya.

Ai a wani irin haukace Bilal ya juyo, tsabar tashin hankali bai san time da ya tureta da karfi har sai da ta faɗi ƙasa da karfi ta buga kanta a jikin bango ba. Cikin zafa ya yi niyar sanya kafa ya taketa, amma sai kuma ya tina da Abbie da su Abdussalam, dan haka sai ya yi gaggawar zafin namar barin bedroom ɗin ya barta shanye a ƙasa, hankalinsa ya yi tsananin tashi sosai, har ciwo sai da ya ji kansa yana yi mashi.

My people's ganin reaction na Bilal mai ya tina maku? Ku duba ku ga yadda ƴaƴan King ke kyama da korar zina daga garesu, dubi yadda Bilal ya zabura ya harzuƙa daga fahimtar nufin Ummie, amma a haka ta sanya Ramish aikatawa, anya zai iya yafe mata kuwa?.

To ni dai bari na yi tsokaci a nan na isar da sakona da nike san isarwa, babban kuskure ne ku ɗauki yarinya karama ku aurawa babban mutumin da kunsan ba zasu tsufa karfinsu ya kare a tare ba!!. Dik yadda aka yi iyayen Ummie kuɗin Abbie suka bi suka aura mata shi, dan ba sa'anta bane shi ɗin, nesa ba kusa ba ya tsere mata, yayan momma ne fa, daga daddyn Smart sai shi, kunga kuwa ba ƙaramin bane, momma ma ku duba shekarun Smart sai ku kiyaste nata shekarun, haba abin babu tsari wlh irin wannan aure, yanzu ga shi shi Abbie karfinsa ya kare ya tsufa, ita kuma a yanzu ne take da buƙatar namiji, kunga kuwa dole a sami gagarumin matsala, irin haka ne suke faɗawa zinace zinace da lesbian, kuga suna bin yara ƙanana sa'annin ƴaƴan cikinsu, wlh wasu iyayen ku ji tsoron Allah, ku sani idan kuka yi wa ƴarku haka dik halin da ta faɗa kuna da kasan zunubi a ciki, ku gudanwa ƴaƴanku faɗawa wannan halaka, masifa ce babba wlh!!!. To na isar da saƙona a ɓangaren Ummie, Allah yasa zaku ji kokena ku kuma gyara!!.

•••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Bedroom ɗinsa Bilal ya wuce yana huci tamkar zai haɗiyi zuciyarsa, rufo kofar nasa ma ya yi tare da murza key wai dan ma kada ta biyosa. Wayansa ya ɗauka cike da tashin hankali ya fara kiran number Ramish dan ya ji ko dai yana da masaniya dangane da abin da Ummie take nema. Sai dai kash, three miss calls ya bugawa Ramish amma bai ɗaga ba, a lokacin yana can yana zuba aiki. Jefar da wayar tasa a saman bed ya yi ransa tana kara zafafa ya shiga toilet dan yin wanka.

Ita kuwa Ummie, jiki dik ya yi mangaribar jemage ta miƙe tsaye, tana ɗan dafa bango tana layi ta nufi waje, mararta kamar zai fashe saboda ciwo na abar da ta tara, ta rasa ya zata yi da ranta.

A gefe guda kuwa Sharifat tana can tana neman Leesharh, dan ta je ɗakin da take jinya bata sameta ba. Har ɗakin Ramish ɗin Sharifat ta zo ko Leesharh na a ciki nan ma ta ga wayam, cike da damuwa ta koma bedroom ɗinsu. Wayarta ta ɗauka ta hau kiran number Ramish dan ta tambayesa ina Leesharh? Sai dai bai ɗauka ba, ɗaura wayar a saman phone set ta yi tare da kwanciya tana tinanin ina Leesharh ta tafi.

Can wani ɓangare na zuciyarta ya ayyana mata ai Leesharh tana tare da Ramish ɗinki. Wani irin zabura Sharifat ta yi ta miƙe zaune tana furta auzubillahi minashshaiɗanirrajim, dan zuciyarta ba zai iya ɗaukar wannan bala'i ba, kishi ne da ita nasu na gado, zata iya kashe Leesharh a kan Ramish, dan nata ne ita kaɗai.

(To nima zan iya kashe maltina roba goma a kan guyson, dan nawa ne ni kaɗai🥱😅)

Sai da ta ɗauki almost 5 mins tana ta nanata sunan Allah a ranta dik dan koran tunanin Leesharh na tare da Ramish, da kyar ta samu ta rabu da tinanin, sannan ta koma ta kwanta tana fatan Allah ya mallaka mata Yah Ramish ɗinta, haƙiƙa idan Sharifat bata mallaki Ramish ba za'a sami gagarumin matsala.

To my people's me kuke tunanin zai faru a gidan Abbie? Uhm muje dai zuwa.

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥

Cikin bedroom ɗinsa ya wuce rike da hannunta, a gefen bed ya zaunar da ita tare da ɗauko tissue paper, hawayenta ya share mata tare da yin shiru yana mamakin karfin hali irin na daddyn nasu, ace mutum kamar Hoorain ai bai cancanci ace King ya hana shi wani abin idan ya nema ba, wannan sam ba halacci bane, mutum tun tasowarsa yana yi maku hidima, ya sadaukar da ransa saboda kare rayuka, dukiya, martaba da kimar masarautarku, sannan shi ne zai zama abin walaƙantawa a gareku dan kawai ya fita a matsayin bawanku mai yi maku hidima?. Har King yana da bakin cewa Hoorain ya tara makiya ba zai bashi ɗiyarsa ya aura ba? To saboda su waye ya tara makiyan? Ba dik dan saboda kare rayukanku ya tara makiyan ba?.

Kuma shi King da yake wannan magana a gabaɗaya kingdom ɗin suna da biyun Hoorain da mahaifinsa ne? Yau da za'a kawowa kingdom ɗin hari ace babu tawagar Hoorain da mahaifinsa kuna tinanin kingdom of power zata kai labari ne? Wlh ko zata kai labari sai da taimakon su Ramish, amma dik da haka yau Hoorain da mahaifinsa sune abin walaƙantawa da ƙasƙantar a gaban al'umma dan kawai Hoorain ya kamu da son Auta wanda ba shi ya ɗaurawa kansa ba, gaskiya yana da kyau ya gyarawa kingdom of power ɗin nan zama su san cewa babu wata aya ko hadisi da ta banbanta matsayin talaka da mai kuɗi, sai dai ayar da ta banbanta tsakanin mai tsoron Allah da mara tsoron Allah.

Ganin ya yi shiru yasa ta yi tinanin shi ma zai ji kyamar talakawa ne, bata san shi ɗin cikakken mai amfani da iliminsa bane.

"Yah Omerish kai ma baka san my Hero ko?". Ta faɗa tana shessheka. Dawo da kallonsa a kanta ya yi, cikin sigar rarrashi ya ce. "Meyasa ba zan so abin da shalelena take so ba? Matikar bai saɓawa faɗar Allah ba tabbas zan zama mai goya maki baya my sweetheart". Ya kai karshen maganar yana janyota jikinsa. Zaro wayarsa daga cikin aljihunsa ya yi da nufin ya yi call sai ga kiran momma ya shigo.

Katse kiran ya yi ya sake kiranta, bugu ɗaya ta ɗauka, cikin natsuwa da girmamawa ya ɗaga mata gaisuwa. A maimakon ya ji ta amsa sai ya ji muryan King yana amsa gaisuwar tasa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Dama yanzu zan nemeka Dad"......... Daga ɗayan ɓangaren King ya ce. "A ina kake tun jiya muke nemanka a waya a kashe?".

Raba jikinsa da Auta ya yi, sannan ya miƙe tsaye ya nufi balconynsa dan ma kada Auta ta ji hiransa da King, dan ya sha alwashin ba zai ragawa kowa ba muddin suka kawo mashi tsaiko a kan abin da ba Allah bane ya haramta, su sun zaɓi kenan su yi wa yarinya auren dole su tabbatar da rayuwarta a cikin kunci da bakinciki? To shi bai zaɓi hakan ba kuma ba zai zaɓa ba, infact bai ga wanda ya isa ya hana Zunaira abin da take so ba matuƙar bai saɓawa shari'a ba.

Saman ɗaya daga cikin kujerunsa dake wajen ya zauna yana faɗin. "Ina Paris"...... Ta karfi King ya maimaita kalmar Paris kafin ya sake cewa. "To ka yi maza ka dawo in san ganinka". Jinjina kansa ya yi kamar yana a gaban dad ɗin nasa, sannan ya ce. "Dad menene batu a kan Zunaira and Hoorain?".

King daga in da yake tsaye ya wani haɗe rai tare da komawa bakin bed ya zauna, momma dake zaune a bakin bed already ne mamaki ya kamata na ganin ya haɗe rai, da kallo ta bisa tana san fahimtar me yasa ya ɓata rai haka? Kada dai ace Smart yana yi mashi wannan iko da ya saba, dik sai hankalinta ya tashi.

"Wannan magana ai na gamata, na bawa Abdussalam aurenta, kuma this coming Friday za'a ɗaura shi, dan haka bana da buƙatar sake tada wannan magana, dalilin ma da yasa na ce ka yi gaggawar dawowa kenan, saboda bikin"........ Shiru ya natsu yana sauraron dad ɗin nasa har ya kai aya a magana, sannan ya ɗan gyara zamansa tare da jan dogon numfashi, cikin sanyin murya ya ce. "Amma ita Zunaira ta ce Hoorain take so ba Abdussalam ba!......"..

Katse shi King ya yi da cewa. "Ni kuma Abdussalam nike so ba Hoorain ba". Shiru Smart ya ɗan yi, kamar ba zai sake tankawa ba, sai kuma ya ce. "Menene yasa baka san Hoorain dad?"...... A fusace King ya ce. "Saboda rayuwarsa bata da tabbas! Daga yanzu zuwa kowani lokaci zai iya mutuwa, ban shirya ganin rayuwar Zunaira a gantale ba! Dan haka na yi rantsuwa da girman Allah na kara yi ba zan bashi Zunaira ba, kada kuma ka sake mun maganarsu, dan na gama yanke hukunci, wlh a kan wannan magana sai dai Zunaira ta nemi wani uban!!!". Tashin hankali.

Haƙiƙa Smart ya fahimci dad ɗinsa ya ɗauki zafi dayawa, kuma a yadda ya yi wannan rantsuwa yake magana a fusace haka ya tabbata iya gaskiyarsa yake faɗe, and kome zasu yi ba zasu taɓa canza mashi ra'ayi, dan haka sai ya ce. "Okey dad, na yarda da maganarka, na yarda Zunaira ba zata auri Hoorain ba, but ina san ka saki Hoorain ya koma yadda yake rayuwa kamar da". Ya kai karshen maganar tare da ɗago idanunsa, unexpect ya yi arba da fuskar Auta tsaye a bakin kofar balconyn tana kallansa tana hawaye, bai yi zatan tana kusa ba, yanzu ta ji dik abin da suka faɗa da King.

Daga cikin wayar King ya ce. "Already ni na saki Hoorain, yanzu haka yana hospital yana jinya, idan ya samu sauki zai koma bakin aikinsa, dan mun yi yarjejeniyar hakan da mahaifinsa, ya mun alkawari Hoorain zai rabu da Zunaira har abada, shiyasa ma na sakesa".

Jinjina kai Smart ya yi zuciyarsa na ƙoƙarin pushing na fushinsa ya bayyana, shi kuwa yana ƙoƙarin danne zuciyar tasa saboda kada ya yi jayayya da mahaifin nasa, yana da ilmin addini sosai, so yasan rabo tana kisa, idan ya tsaya ya ce zai ja da dad ɗin nasu in Allah ya ƙaddara za'ayi wannan aure to suna iya rasa King ɗin, hakan ne kuma baya so, shiyasa ya sassauta zuciyarsa ya aminta da haka, gara mashi su bi wata hanya su saka King ɗin kaffara kawai a kan su yi ja in ja da shi su rasa shi na har abada, a kan batun aure da batun yara ba'a jayayya, idan ma'aurata sun rabu ba'a gardama a kan ƴaƴa, misali ace uwa ta ce ita zata rike uba ya ce abasa kayansa, irin haka ma Allah yana ɗauke ƴaƴan kowa ya raba faɗa, so a kan aure da yara ba'a ja in ja.

"Dad zamu yi magana anjuma". Yana kai karshen maganar ya katse kiran diff ba tare da ya jira amsarsu ba. Alama ya yi wa Auta da hannu a kan ta zo. Da ƴar gudunta ta tafi ta faɗa jikinsa tana sakin kuka mai tsuma zuciya. Rarrashinta ya fara yi cike da so da kauna. Cikin kuka ta fara faɗin. "Shikenan Yah Omerish kai ma yanzu baka goyan bayana? Yanzu ka koma bayan dad? Kai ma baka san my Hero?".

Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ya ce. "Kin yarda da ni?"....... Kai ta gyaɗa mashi alamar e ta yarda da shi. "To i promised you that In Sha Allah zaki zama mallakin muradin ranki, burinki zai cika wannan alkawarina ne, alkawari kuma kaya ne". Cike da gaskiyarsa ya yi maganar, babu wasa ko golaya dan ta yi shiru yasa ya faɗa mata haka.

A ruɗe ta ce. "Yah Omerish how? Ta yaya zan mallaki Hoorain bayan daddy baya sansa, kuma ya yi rantsuwa da girman Allah ba zai bashi ni ba, sannan kowa a gida baya sansa, har Akka bata sansa, and nan da one week dad ya ce zai aura mun Yah Abdussalam". Tana magana zafafan hawaye suna bin kuncinta.
Ɗan jinjina kai ya ɗan yi kafin ya ce. "Haka ne dik abin da kika faɗa, and nasan abu ne mai wahala yiwuwar aurenku, amma In Sha Allah daddy da kansa zai sanya maku albarka a ranar aurenku, darasi zan bawa gabaɗaya familynmu ta yadda gobe ko da kuɗi aka basu ba zasu taɓa sake kyamar talaka ko na kasa da su ba".

Zaro idanu waje ta yi, cike da ƙaguwa na san jin abin da zai yi masu ta ce. "Me zaka yi masu da har zai sa su koyi darasi?". Hannu yasa yana share hawayenta ya amsa mata da. "Kada ki damu, ke dai keep praying for me". Ya kai karshen maganar yana duba wayarsa dake ruri alamar shigowar kira. Number momma ce again, kuma yasan dad ne, dan haka sai bai yi picking ba, saboda yana san ya ɗan yi tinani a kan irin lesson da yakamata ya koyar da familyn nan nasu, su san cewa mutum ɗan adam ba abin rainawa bane, da talaka da mai kuɗi dik Allah ne ya yi su..

Jama'a na ce mu jinjinawa momma, lallai ba shakka jinin momma ce yake gudana a jikin Smart, a gabaɗaya kingdom of power momma ce kawai bata kyama ko kyarar talaka, ita ce kawai ta ɗauki kowa dik ɗaya suke, ita ce uwar marayu irinsu Mahnoor, Zee, Khadijah and Mahreen, lallai ba shakka momma baiwar Allah ce kuma jininta ya fi karfi a jinin SMART!! Dan kunga shi ma baya gudun talaka bawan Allah!.

Pretty ce ta katse masu hiransu ta hanyar miƙewa zaune a saman kujerar da take kwance, kwata kwata Auta bata lura da ita ba tun shigowarta, dama a saman kujerar ya kwantar da ita, sannan ya wajen ya yi mata allurar da ya ceto rayuwarta. Sai dai kuma ya yi matuƙar mamakin ganin ta yi saurin farfaɗowa, yasan dai zata iya kai kwana biyu a sume kam, sai kuma ga shi ko awa biyu bata yi ba ta farfaɗo, abin da bai sani ba shi ne ita fa Pretty ko da bai yi mata wannan allura ba zata farfaɗo, saboda poison dake cikin chemical ɗin bai yi mata lahani ba dan ita ma akwai irin abin dake jikin Sweetie a jikinta, kuma ita ma hannunta yana iya yin magic, sau da dama tana ɓarin abu ta hanyar magic ɗin, amma rashin sani yake sakawa ta yi zatan kawai ɓari ta yi, bata san da shi a hannunta ba.

Da kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa a ransa yana mamakin tashinta a yanzu. Cike da kula da so da kauna Auta ta ce. "Pretty ina kika shiga ina ta nemanki". Tana aikin turo baki bata yi magana ba, miƙewa daga jikin Smart Auta ta yi ta koma wajenta dan ta ji menene yake damunta. Shi kuma Smart miƙewa ya yi yana faɗawa Auta zai je gidansu wajen mom sai kiransa take yi, yanzu ba jimawa zai dawo, daga karshe ya ce mata kada ta sare kuma kada ta bar Hoorain cikin kewa ta rinƙa kiransa a waya In Sha Allah kukanta zai tsaya. Da okey ta amsa mashi tana murna, har da sakin murmushi. Kai yasa ya nufi waje a ransa yana tina ta yadda zai yi ya yi maganin King, lallai ba zasu koma kingdom of power a yanzu ba, dole su dakatar da auren Abdussalam, sai after one month zasu koma, dole ya yi magana da momma dan su shirya komai a tare ta yadda ba zasu rasa King ba.

My people's kuna ganin shirin nan zai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login