Showing 276001 words to 279000 words out of 403653 words

Chapter 93 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

46

mai motsi a parlourn ƙasa bayan ya san dare ya yi, yau a gidan Auta zai kwana da su, dan jiya sun yi mashi complain a kan ba zasu iya cigaba da kwana ba tare da shi ba, suna tsoro, shiyasa ya ce wa daddynsa ya yi tafiya, amma yana tare da su, baya san kaisu gidansu kuma, dan baya san dad ɗinsa yasan ya je Kingdom of power ko ya haɗu da mahaifinsa, momma ta ce ya ɓoyewa dad ɗin nasa, dan ba ƙaramar dirama za'ayi ba, King zai ce a bashi ɗansa, shi kuma daddyn Smart kun san aikin da suke aikatawa da Smart a ɓoye wanda idan King ya ji ba zai taɓa yarda ba! Ko ita momma ta ji wannan aiki ba zata yarda ba!! So kun dai san daddynsa ba zai taɓa yarda ya koma kingdom of power ba, yanzu ita momma ta rasa yadda zata ɓullowa wannan al'amari, ita kanta yanzu tana san Smart ya dawo gareta tun da already yanzu King yasan yana raye, to burinta ya dawo kusa da ita tana jin ɗuminsa, ta kuwa san yayanta dai ba zai yarda ba, wlh akwai cakwakiya ba kaɗan ba, sai ma King yasan aikin da Smart yake yi tukunan, a nan ne za'ayi yaki kam.

Bugu ɗaya King ya ɗauka, dan a lokacin yana hira da momma ne a kan dawowar Smart ɗin, ya ce ya umarceta da ta dawo mashi da ɗansa kamar yadda ta ɗaukesa ta kai shi can, to hiran da suke yi kenan, ta yi ƙoƙarin tausansa a kan ya bari zuwa ɗan wani lokaci, a take ya gwada mata ɓacin ransa tare da ce mata wlh ko wata ɗaya ba zai iya bari Smart ya kara a can ba, dole ya dawo wajensa ya ji ɗumin ɗansa da ya rasa tsawon shekaru.

Da okey kawai ta amsa mashi, amma ta sha jinin jikinta, dan bata san da wani ido zata iya fuskantar mommyn Smart da sunan zata ɗauki ɗanta ba, Allah sarki, babban damuwarta ma shi ne su daddyn Smart ɗin Allah bai basu haihuwa ba har suka tsufa, sun ɗauki son duniyar nan dik sun ɗaura a kansa, kuna dai ganin yadda suke rayuwa, idan baka sani ba ba zaka taɓa cewa ba su suka haifesa ba.

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

"Good evening dad". Ya faɗa yana tako stair case a hankali cikin natsuwa. "Evening my love how was your day?". Da Alhamdulillah ya amsa kafin ya ɗan yi shiru yana cigaba da tafiya a natse.

"Dad where's momma?". Ya faɗa yana warware igiyar rigar barcin dake jikinsa, dan ya ji igiyar ta ɗan kama shi sosai, shi ne zai sukurkutata. "My son kowani lokaci mommarka kawai baka san yin hira da ni ne?". Cikin murya mai rauni King ya yi maganar, Allah ya gani yana bala'in san Smart fiye da tunanin mutum.

"No dad, ina san yin hira da kai mana, in the morning zamu yi hira sosai, but now give momma the phone I want to ask her something". Jinjina kai ya yi tare da miƙawa momma wayar ya miƙe ya nufi toilet, dama wanka zai shiga suka tsaya hira da mommar.

Kasa shi kuma Smart ya sauko parlourn akwai duhu babu haske, kai tsaye ya nufi switch dan ya kunna wutar...... "Hello momma". Ya faɗa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa da. "Son how was your day?". "Alhamdulillahi what of you?". .... Da Alhdulillah ita ma ta amsa mashi. Dai'dai lokacin ya kunna wutar parlourn haske ya gauraye ko'ina.

Zaune take saman sofa mai zaman mutun biyu, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, hannunta rike da cup da mai aikinsa ya haɗa mata hot tea mai kauri. Sanye take da sleeping dress, gown ne zuwa kyawawan cinyoyinta kusa da gwiwa, sai yar pant daga ta ciki, launin kayan pink color hakan yasa ta yi kyau sosai cikinsu, ga skin ɗinta luwai luwai, ta zubo gashin nan nata ta gaban saman shoulder ɗinta, kun dai san Pretty bata shiri da yunwa, shiyasa ta fito cin abinci abinta, ita kuwa Auta tana ɗaki sai gwada number Hoorain take yi baya ɗauka saboda ya karɓi alluran barci ɗazun, ya birkicewa commander a kan ta ne yasa commander ɗin ya ce a watsa mashi alluran barci ko kwakwalwarsa ta huta, shiyasa take ta kira ba'a ɗaga ba, har kuka ta yi.

Zuba mata idanu Smart ya yi yana kallan yadda take shan tea ɗinta a natse, bata ko ɗago kai ta kallesa ba, abincinta kawai take ci, wlh Pretty akwai miskilanci fiye da tunaninku, ba komai take ɗaga idanu ta kalla ba sai abinci ne bata yi mashi hakan. Wani irin faɗuwar gaba ya ji ganinta a cikin wannan shiga.

"Son baka jina ne?". Momma ta faɗi hakan har sau uku, amma bai ji ko ɗaya ba, saboda hankalinsa yana a kan Pretty, yarinya kamar wata aljana. Har momma ta katse kiran ta sake kiransa, jin karar wayar yasa ta ɗan ankara tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ya katse kiran ya kirata, har lokacin bai zare kallansa daga kanta ba, ita kuma tamkar bata san da mutum a wajen ba, tea ɗinta kawai take sha, ko irin ta ɗago kanta ɗin nan, ya ɗan yi mamakin ganin ta nuna tamkar bata san da mutum a wajen ba.

Karisawa ya yi tsakiyar parlourn, a saman sofa mai zaman mutum biyu ya zauna, cikin natsuwa ya sanar da momma so yake ya koyar da daddynsa cewa babu banbanci tsakanin talaka da mai kuɗi menene shawararta a kai?. Yana magana yana kallan ɗan bakin Pretty da take ta fama hura tea ɗin wai dan ya yi sanyi, ya yi mata zafi ne.

Daga ɗayan ɓangaren momma ta ce. "Wannan shawara ce mai kyau, amma dole da kanka zaka yi amfani, idan ba haka ba ba zaka taɓa iya juya zuciyar daddynka ba". ..... Da ɗan mamaki a tattare da shi ya ce. "Ni kuka momma? To meyasa ni?". Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa ta nufi waje dan ma kada King ya jiyota, kai tsaye rest parlourn ɗinsa ta nufa, saman sofa ta zauna sannan ta ce. "Saboda kai ne raunin daddynka, idan akwai wani abin da yake tsananin so to ya biyo bayanka gaskiya, dan haka dik abin da zaka yi mashi ko tarko da zaka kafa mashi ya kasance ka haɗa da kanka hakan ce kawai zata sa ya yi gaggawar saukowa har ya gane abin da kake so ya fahimta".

Shiru ya ɗan yi, ya fahimci abin da momma take nufi, amma dan ya tabbatar sai ya ce. "Momma I didn't understand".... Sarai tasan ya fahimci abin da take san faɗa, dan tasan yaranta da saurin ɗago abu, amma tun da ya nemi bayani dallah dallah bari ta yi mashi yadda zai fahimta.
"Ka samu ƴar gidan mutunci ƴar gidan talakawa ka kawo mashi da sunan zaka aura, ka nuna mashi idan ba ita ba zaka iya mutuwa, ta hakance kawai zai sa zuciyarsa ta sassauto tun da abin ya biyo ta kan sanyin idanuwansa.........."

Katseta ya yi a hanzarce da cewa. "Kuma sai na aureta ɗin?"........ Ta jima tana san ya yi aure yaki yarda, da ta kawo mashi maganar ma sai ya sauya zance, to yanzu tana ganin dama ne ta samu wanda idan ta bari ya kubce mata bata san ranar yin aurensa ba kuma, dan haka zata iya yin komai dan ya aminta da wannan shawarin nata, cikin sanyin murya da tausasawa haɗe da kalamai masu kaifi ta ce. "A'a ba sai ka aureta ba ai, kuma zaka iya auren nata ma idan ya so daga baya in daddynka yaga yau an wayi gari da kafarsa ya taka ya je gaban talakawa ya nemi alfarmar su baka aure, ya gane ashe talaka yana da rana kuma yana da darajar da za'a je neman abu a wajensa wani lokaci, to kana iya sakinta idan buƙatarmu ta biya".

A hanzarce ya ce. "No momma, ban yarda da hakan ba, ban yarda na aurenta na saketa ba, ni auren ma ba zan yi ba, kawo wata shawara!". Ya kai karshen maganar yana kai kallansa saman cinyoyin Pretty, da yake rigar tata zuwa gwiwowinta ne, ga shi kuma tana zaune sai rigar ta ɗan yi sama kaɗan, lokacin guda ya ji wani abu a ransa.

"Okey to yanzu ka fara soyayyar karya da yarinyar, sai mu bi iyayenta a bayan fage mu faɗa masu idan daddynka ya turo a nema maka auren su ce ba zasu iya bashi ba, dan ma ya kara sanin talaka ma yana da abin da za'a iya nema a wajensa, su hanaka yarinyar kai kuma kace idan ba ita ba mutuwa zaka yi, daddynka zai sha fama sosai, yana tsoron ka mutu hakan zai sa ya yi learning lesson, daga nan zaka iya rabuwa da yarinyar ba sai an kai ga aure ba, please don't say no to me my son, wannan ita ce kawai shawarar ta hanyar da ya dace mu koyawa daddynka darasi mu kuma sanya ya yarda da Hoorain, na san zaka so farincikin Zunaira fiye da kowa a cikinmu".

Kalamai dai masu daɗi ta rinƙa zuba mashi, dik dan ya aminta, kun san uwa ta gari tasan yadda zata shawo kan ɗanta har ma ta yi mashi wayau, wanda ya haifeka ya wuci gaban tinaninka, sai dai ya ganka kawai.

Shiru ya yi yana tinanin maganganunta, tabbas tana da gaskiya, wannan hanya ita ce kawai zata sanya King ya yarda talaka ba abin walaƙantawa bane, dan watarana za'a iya zuwa neman wani abin a wajensa, sai dai shi kuma how comes zai yi soyayya abin da bai iya ba, bai taɓa yi ba, ya zai yi yanzu?.

Katse mashi tinani momma ta yi da cewa. "Ka amince ko my son? Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya". ...... Momma na kalaman yaudara my people's, har da addu'oi tun bai amsa ya aminci na, kawai dan tasa ya ji ba zai iya karyar mata da gwiwa yaki yarda ba, har da kara nuna confidence ɗinta, dik ta sare mashi gwiwa ta kashe mashi jiki har bai san lokacin da ya amince mata ba. Ai wani irin sanyayyar ajiyar zuciya da ta sauke sai da ya ji ransa ya yi sanyi shi ma, mahaifiyarsa ta yi murna saboda shi har tana sauke sayyar ajiyar zuciya, kai abin ya yi mashi daɗi, a ransa ya kudurta ba zai taɓa bata kunya ko yasa ta ji babu daɗi ba, In Sha Allah zai kasance mai sanyata farinciki kamar na yau.

Ya yi nisa cikin tinanin da yake yi sai magana take yi mashi tana zuba mashi ruwan albarka amma bai ji ta ba, hankalinsa ma ya koma kan Pretty da ta miƙe ta nufi kitchen dan ta gama shan tea ɗin. Sai da ya ga shigarta cikin kitchen ɗin sannan ya kawar da kallansa daga kanta, yana ƙoƙarin amsawa momma addu'oin da take yi mashi Pretty ta zumduma ihu tare da kwasowa a miliyan ta fito daga cikin kitchen ɗin.
Kai tsaye wajen shi ta nufa, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana ihu. Shiru ya yi yana ƙoƙarin gane a wani irin yanayi yake ne?. Da gudun gaske tigernsa ya fito daga cikin kitchen ɗin ya biyo bayan Pretty, tun da suke gidan bata taɓa sanin yana da zaki da kuma damisa ba, dan bata taɓa ganinsu ba, idan baku manta ba a sama gabaɗaya damisa da zakin suke, so basu cika saukowa ƙasa ba sai cikin dare, in baku manta ba a farko farkon littafin na faɗi hakan, so shiyasa Pretty bata taɓa saninsu a cikin gidan ba, gata mayyar tsoro, na tabbata da tasan da su a gidan ba zata yarda ta zauna ba, idan kuma ta zauna to fa ba zata yarda da fito waje ba, zata koma zaman ɗaki kan gado.

Wani irin tsalle tiger ya daka ya yi kansu zai yagusheta, dan ta je garin ajiye cup a saman table ta taka mashi bindi, bata lura da shi ba, shi ne ya biyo ta.

Ai a miliyan Smart ya rungumeta suka kwanta a sanan sofar sannan ya juya da ita ya zamana ita ta koma saman sofar shi kuma ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa ya tare mata damisan, hakan yasa damisan ya sauka a kansa.

Zubawa wuyarta idanu Smart ya yi yana kallan tsokan wajen gwanin ban sha'awa, idan baku manta ba suna da gurun wuya mai shegen ɗaukar hankali, aikuwa ya ɗauki hankalin Smart namu na amana. Ita kuwa ta datse idanu gam tare da kankame rigarsa ta wajen kirjinsa. Dirowa kasa tiger ya yi daga jikinsa yana wani girgiza, da karfi ya fara jan hannun Smart da bakinsa irin ya matsa ma bashi Pretty. Jan da tigern yake yi mashi ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka yana kallan wuyarta, komawa saman sofar ya yi ta gefenta ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, hannunsa rike da wayarsa momma na jin dik abin da yake faruwa, sai tambayarsa take yi waye mai wannan ihu amma bai ji ba, dan ya zare wayar daga kunnensa.

Tsalle damisan ya yi zai haye kanta Smart ya yi saurin riƙosa ya rungume irin alamar rarrashi, ita kuwa har lokacin bata motsa ba, kamar dai suma ta yi. Da kyar ya rarrashi damisan ya tafi, dawo da kallansa a kanta ya yi, yadda ta faɗa jikinsa ne kawai a ransa, a lokacin sai da ya ji gabaɗaya komai nasa ta ɗauke diff. A yanzu ma sai da momma ta katse kiran ta sake kiransa, doguwar numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, sannan ya katse ya kirata. Tana ɗagawa ta hau tambayarsa lafiya wacece take ihu haka. Bai ɓoye mata ba ya sanar da ita dik abin da ya faru.

Yana gama faɗa mata ta tari numfashinsa da cewa. "Shikenan ma mun sa yarinyar da zamu yi wannan aiki da ita, kuma ga shi Zunaira ma tana kaunarta, daddynku zai koyi darasi sosai, kuma yarinyar tana da natsuwa, ka kula da ita bari in binciko iyayenta, nasan mara galihu ce itama, dan Zunaira ta ce mun a daji suka haɗu da ita, bata da kowa, ni kuwa nasan ba zai taɓa yiwuwa bata da kowa ba, dan haka bari in fara bincike a kan iyayenta kai kuma ka fara kulla soyayya a tsakaninku"..

Tashin hankali!!! My people's momma zata jijjigo babbar aiki, domin binciko iyayen Pretty ba ƙaramin abu bane,!! Kuma zai iya zama abu mara daɗi a garezu, akwai show, momma zata tono wani babban............ Na dai yi shiru amma akwai cakwakiya.

"Momma wannan yarinya ce karama and......" Katse shi ta yi da cewa. "Ai yarinyar ta fi, saboda ka ga ba aurenta zaka yi ba, idan babbar mace ce ka yi soyayyar karya da ita zata iya fara sanka da gaske, kaga in ka barta baka aureta ba kuma an cutar da zuciyarta, amma ita yarinya bata san soyayya ba, ko ka rabu da ita a lokacin da buƙatarmu ta biya lafiya lou ne"..

Ni kuwa na ce ba dai yaran yanzu ba, da sanin komansu ake haifansu ato, dan haka kamar Pretty ta san soyayya mana momma!.

Ya gamsu da zancen momma, amma sai ya ce ta bashi lokaci ya yi tunani ko zuwa gobe ne. A kan haka suka tsayar da zance, daga haka suka yi sallama. Katse wayar ya yi ya tura cikin aljihu tare da ɗan sunkuyo da kansa a kan Pretty, sai a lokacin ya fahimci suma ta yi, mayyar tsoro kawai.

Miƙewa ya yi ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa ya nufi switch, kashe wutar parlourn ya yi ya haura sama yana tinanin a kan zantukan momma..... My people's me kuke tunanin zai faru? Momma zata gano iyayen Pretty? Su waye iyayen nata? Smart zai yi accepting soyayyar karya da Pretty idan ya gama tunanin nasa ko ba zai yi ba? Muje zuwa, kada ku manta Pretty dai an yi mata miji, mom ɗinsu ta bada ita wa Kamran kafin ta ɓata ko? In kun manta na tina maku!!.

••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥

Ko kaɗan kalamanta basu huda zuciyarsa ba, babu sassauci a tattare da shi, ta kankame hannunsa gam tana yi mashi magiya, amma ina babu alamar zai sassauta. Sun kwashi good 30 mins a haka tana mashi magiya bai kulata ba, taki sakar mashi hannunsa, kuka take yi hawaye bibbiyu wai ko zai tausaya mata, amma ko kaɗan bai ji komai ba, kuma idanunsa suna kan face ɗinta fa, yana ganin yadda take kuka, amma ina zuciyar ta riga da ta bushe.

Ihu Ronnie ya kurma tare da matsawa kusa da su yana faɗin. "Please big bro for give them, Sweetie konasu fa ake yi". A rikice ya yi maganar cikin fitar hayyaci.

Kun san already kafin Sweetie ta rike hannunsa ta hana shi latsa laptop ɗin ya rigada ya shigarwa da Robbot ɗin umarnin abin da zasu yi, so ita Sweetie a tinaninta tun da ta rike hannunsa shikenan ba zai samu damar bada umarnin ba, bata san aikin gama ya rigada ya gama ba, ta tsaya tana yi mashi magiya already su kuma robbot suna aiwatar da aikinsu. Injuna na zamani suka yi amfani da su wajen haka ramin cikin ƙanƙanin lokaci, sannan suka hura wuta tamkar yadda ya umarcesu. Dik wanda ya bijirewa Black Tiger sai su kama shi su jefa shi cikin wanna balbalin wutar, yana ihu yana basu hakuri haka zasu jefa shi ciki gwanin ban tausayi.

Wannan ihu da Ronnie ya kurma abin da ya gani kenan ya razana shi ya tashi hankalinsa, sai jefa mutane cikin wutar robbot suke yi. Hankalin Sweetie idan ya kai miliyan to ya tashi, wai abin takaicin ma har da ƙananan yaran da basu suka yi mashi laifi ba, iyayensu ne suka bijire mashi, to uwa ta yi gabas ai dole ta kama hannun ƴaƴanta su wuce gabas ɗin da shi ko?

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login