Showing 198001 words to 201000 words out of 403653 words

Chapter 67 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

112

kuwa uncle Abbas sam baya san abin ta wuce haka, fatan abin ya tsaya a haka kawai yake yi. Gadan gadan cikin zafa ya nufi Hoorain ɗin again.

Ni da ku dik mun san a nan dai Hoorain ya tabka babban kuskure, ai ko zai shaki kowa banda Jaish dake matsayin yaya ga Zunaira, amma dai soyayya ce ta rufe mashi idanu, kuma idan kuka kwantanta abin da kanku zaku ga shi ma Jaish bashi da laifi, dan kowani yaya na gari zai tsayawa kanwarsa ce a koma inane, kuma shi dai Jaish ba soyayya yake yi ba bare muce yasan zafin da masoya suke ji, dikkansu dai cikin rashin sani suke, amma dai abin bai yi daɗi ba gaskiya.

Cikin zafa ya nufi sauka kan stage ɗin ya ƙarisa gaban Hoorain sai ji ya ji an rike hannunsa ta baya, cikin zafa ya juya dan yaga wanenen?. Yana juyawa suka yi ido huɗu da Aunty MieMie, ƙara ɗaure fuska sosai ya yi yana wani huci yana san kwace hannunsa, shi kuwa Hoorain yana tsaye a kan kafafunsa ya sunkuyar da kansa ƙasa zuciyarsa tamkar zata yi bindiga.

Cikin dakiya King ya ce. "Abbas kama shi ku tafi".......... Matsawa uncle Abbas ya yi yana riƙosa suka tafi, ba dan King ba da bai ga abin da zai sa yau ya kyale Hoorain ba.

Kallan Aunty MieMie King ya yi kafin ya dawo da kallonsa a kan commander Zafar, tsab King ya gama fahimtar soyayya ce take a tsakanin Hoorain da Zunaira, wannan bakincikin ita ta hana shi yin magana, dan ya fahimci Zunaira tana san Hoorain sosai, shi kuwa ko mutuwa zasu yi bai ga dalilin da zai sa ya bawa Hoorain Zunaira ba, dan bai shirya ganin yarsa a matsayin karamar bazawara ba, kowa dai yasan mayaƙa rayuwarsu babu tabbas, a kowani lokaci suna iya mutuwa, kuma ko da King ya ƴanta Hoorain ɗin ya zama ɗan ahali ba zai taɓa zama mai ƴanci da rayuwarsa ba, saboda ya riga ya tarawa kansa tarin makiyan da ba zai iya faɗa dasu domin ƙwatar kansa ba, dik in da ya je masu san ɗaukar fansa a kansa suna kewaye da shi, dan haka shi King yasan me matsalar, dole kuma ya dakatar da wannan soyayya cikin sauri tin kan abin ya yi nisa ya fi karfinsu.

Hmmm King a ganinsa soyayyarsu bata yi nisa ba kenan, my people's mu gaya mashi wannan soyayya ta fi shekaru 8 ne ko dai mu barshi su masoyan su nuna mashi karfin soyayyar dake zuƙatansu?.

Tsit fada ya yi kowa idanunsa a kan King, jiran word ɗinsa kawai suke yi, saboda babu wanda ya isa ya yi magana idan ba ya yanke abin da ya dace a kan wannan case ɗin ba.

Commander dai ji ya yi ƙafafunsa sun gaza ɗaukarsa, hakan yasa ya koma saman sofa ya zauna tare da sunkuyar da kansa ƙasa, domin shima ya rigada ya gane Hoorain ya fahimtar da Zunaira abin da yake ransa, idan baku manta ba dama commander yana hana shi kusantar Auta, ashe dik irin wannan yake gudun mashi, so yanzu ya fahimci soyayya suke yi da Auta, kuma ya fahimci King Zuhair ma ya fahimci hakan, Allah sarki yasan ko mutuwa Hoorain yake yi ba za'a taɓa bashi auren Auta ba, saboda ba kowa ma yake yarda ya bawa mayaƙa yayansa ya aura ba bare ita da take matsayin gimbiya, tab ai abune wanda sai in Allah ya ƙaddara akwai aure a tsakaninsu ne Allah zai kawo sanadi, amma kam akwai matsala.

Good 10 mins King ya ɗauka shiru yana binsu da kallo kafin ya ɗan yi gyaran murya, with sharp voice ya fara magana kamar haka.

"I think ka fahimci abin da na fahimta a tsakanin yaran nan ko Zafar?".
Dum dum commander ya ji kirjinsa ta buga, dan ya fahimci in da King ya dosa. Da kyar ya iya jinjina kai cikin girmamawa ya amsa da ya fahimta.

"Ba sai na faɗa maka hukuncin da ya dace da Hoorain ba, ka fi kowa sani tin da tare da kai aka kafa waɗan nan dokoki da hukunce hukuncen, dan haka ina mai baka umarnin da ka hukunta shi yadda yakamata, daga karshe ka datse alakar dake tsakaninsa da Zunaira bana san sake yin magana a kan hakan!!".

Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, haba King, wani irin zalinci ne wanna? Ta ya za'ayi kace uba ya hukunta ɗansa bayan kasan hukuncin yana da tsauri da tsanani sosai? Wannan babban zalinci ne wlh.

Tamkar commander zai yi kuka, idanunsa sun tsananta ja sosai, kansa a ƙasa cikin girmamawa ya ce. "Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, dan girman Allah ina neman alfarman da abawa wani daga cikin mayaka damar su hukunta Hoorain, ba zan iya hukunta shi ba".

Wlh dik taurin zuciyar Aunty MieMie na jinin Modarawa sai da ta ji zuciyarta ya karaya a wannan gaɓa, saboda abin da ciwo ace uba ya hukunta ɗansa hukunci mai azabtarwa, kuma dole ya yi yadda hukuncin take a rubuce idan ba haka ba dikka a azabtar da su, innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, wannan abin akwai taɓa zuciya.

"Amma dai kasan bana magana biyu ko Zafar?". Cewar King. A tinanin King fa idan ya sanya commander ya hukunta Hoorain to tabbas Zunaira zata fita a ransu gabaɗayansu, dan uba da ɗa ba wasa ba, shiyasa ya yi masu irin hakan, burinsa kawai ya yanke alakar Hoorain da Auta. Hmmm akwai matsala.

Shiru commander ya sunkuyar da kansa yana jin wani irin raɗaɗɗi na ratsa zuciyarsa, haƙiƙa bai taɓa yin danasanin zamansa da su King ba sai yau, ya ji da ace shi ba musulmi bane bai san girman Allah ba da babu abin da zai hana ya kashe kansa a kan ya yi wa Hoorain wannan hukunci, amma bashi da zaɓin da ya wuce ya yi mashi ɗin, dan haka sai ya miƙe jikinsa na kermar tashin hankali. Da kyar ya iya taka kafafunsa ya isa in da Hoorain yake tsaye. Guyson ne ya juya da sauri ya bi bayan uncle Abbas da ya fita da Jaish, dan kun san guyson akwai tausayi, ya ji bashi da kwarin zuciyar kallan commander Zafar a halin da yake ciki.

Aunty MieMie ce ta yi saurin juyowa ga King da nufin ta taushesa ta bashi hakuri wani ya hukunta Hoorain ba mahaifinsa ba. Sai dai tana ƙoƙarin buɗe baki King ya ɗaga mata hannu fuskar nan tasa babu alamar wasa, ya ɗaureta tamau kamar hadari, ya ɗaga mata hannu alamar ta yi mashi shiru.

Zuciyoyi dayawa sun karaya a cikin fada, dayawan jama'ar dake ciki sai da idanunsu ya tara ruwa mai ɗumi, dik mai imani sai ya tausayawa commander idan ya gansa.

Riko hannun Hoorain ya yi, jansa ya yi suka juya suka nufi hanyar fita, da kyar yake jan kafafunsa saboda rashin kwarin jiki.

Da kallo kowa ya bisu, warriors dake cikin fada kuwa daɗi suke yi suna faɗin Allah ya kama commander yau, ba ya iya hukunta ƴaƴan mutane ba, to yau abin ya juyo ta kansu ai shikenan shi ma ya ɗanɗani yadda iyaye suke ji a lokacin da yake azabtar masu da ƴaƴa.

"Ku shirya mana motoci zuwa hospital duba Zunaira, sannan ku ɗauki Taheer ma zuwa hospital". Shi ne abin da King ya faɗa kafin ya koma saman kujerarsa ya zauna yana jin wani irin kuna a ransa, wai Hoorain da Zunaira suna soyayya, wannan abin ya kona mashi rai matuƙa, har ji ya yi kansa na sara mashi.

Dik wannan abin da yake faruwa a cikin gida babu wanda yake da labari sai Mammien su Sarina and mama da suke da c.i.d, kun san suna da masu saka masu ido a lamarin fada, so har sun samu information a kan abin da yake faruwa.

JAISH kuwa kai tsaye part ɗinsa uncle Abbas ya wuce da shi, sai huci yake yi, wlh ba dan King ba yau bai ga abin da zai hana shi yi wa Hoorain dukan mutuwa ba. Tab yadda Jaish fusata haka kuna tunanin ko mutuwa Hoorain yake yi zai yarda ya bashi auren Auta kuwa? Hmmm akwai dai matsala.

A bakin bed uncle Abbas ya zaunar da shi yana tausan shi a kan ya yi hakuri. Hannu ya ɗaga tare da cewa uncle Abbas. "Second dad it is okey, zaka iya tafiya babu komai". Yadda ya yi maganar yana fitar da huci mai zafi zaka iya fahimtar har yanzu bai huce ba.

Kin matsawa daga kusa da shi uncle Abbas ya yi, dan ya fahimci komai zai iya faruwa idan ya tafi ya bar shi a haka. Dan haka sai ya zauna tare da shi ya cigaba da rareashinsa.

Shi kuwa guyson part ɗin momma ya wuce kai tsaye dan ya faɗa mata abin da yake faruwa, zuciyarsa ba zata iya ɗaukar hukuncin da King ya yankewa commander Zafar and Hoorain ba, abin akwai ciwo sosai, hukuncin ya yi masu tsauri sosai, ace uba ya kai ɗansa ɗakin duhu dan hukunta shi, bayan ya gama hukunta shi da kansa kuma zai jefa shi a gidan yarin masarautar tare da horo mai tsanani bayan na ɗakin duhu, wlh commander ba zai iya ɗaukar wannan musifar ba, dole su momma su saka baki ko za'a samu sassauci.

Yana ƙoƙarin shiga part ɗin momma ciwonsa ta tashi, wani irin azabbabben murɗa mashi da cikinsa ta yi ne yasa ya dafeta da karfi yana sakin ihu mai ɗan sauti kaɗan. Wani irin numfashi ya fara fitarwa da zafi zafi yana kara dafe jikin bango, a hankali ya fara jujjuyawa ko zai ga wani a kusa ya taimaka mashi, dan ko motsawa ba zai iya yi ba.

Dai'dai lokacin Mahnoor ta fito daga part ɗin Jaish cikin shiga ta girma wato ta matar Prince wanda mama Haulat ce ta ƙawata mata shigar, so zasu je gaishe da Akka ce ita da Chuchu, shi ne ta ce bari dai ta fara duba momma kafin su je wajen tsohuwa.

Chuchu na can suna sallama da Yah Jawad zai tafi office, sai aikin rungume juna suke yi kamar ba gobe.

Ganinsa ya dafe bango yana hawaye yasa Mahnoor ta yi saurin nufarsa tana tambayarsa lafiya kuwa?. Riƙo hannunta ya yi ya kasa yin magana, da hannu ya nuna mata part ɗin monma a kan ta taimaka mashi su je can.

Daddagewa ta yi tasa karfinta dikka zata taimaka mashi, gabaɗaya ya sake mata nauyin jikinsa saura kaɗan su zube ƙasa, da kyar ta iya kamewa ta iya ɗaukar nauyinsa, sai kuka yake yi sosai yana cigaba da dafe cikinsa da hannu ɗaya.

Ya yi mata nauyi sosai, amma haka ta daddage ta tallabosa da kyar suka nufi part ɗin momma. Allah ya taimaketa momma tana parlor zaune ita da Mahreen and Zee suna hira, momma kenan, mai farar zuciya, ta haɗe ƴan'matan dikka ta rikesu abinta, babu kyara ko kyama.

Suna shigowa cikin parlourn saura kaɗan su zube ƙasa gabaɗayansu, a hanzarce momma ta miƙe ta taresu. Kuka ya kara sakawa mai sauti yana nunawa momma cikinsa babu bakin yin magana. Wlh idan ciwon guyson ya tashi sai kun tausaya mashi, ba karamar wahala yake sha ba...... WAI MENENE DALILIN WANNAN CIWO NA TSAWON SHEKARU HAKA? AKWAI AYAR TAMBAYA GASKIYA, TO MUJE DAI ZUWA.

Gabaɗaya ya sakewa momma nauyinsa, saman sofa ta kwantar da shi tana tambayar lafiya tana kallan Mahnoor. Cikin natsuwa Mahnoor ta ce ita ma bata san me ya same shi ba, kawai ta gansa ne a bakin kofar shigo part ɗin.

Riko hannayensa momma ta yi tana tambayarsa meyake yi mashi ciwo. Cikin tsananin ciwo da azaba ya fara nuna mata cikinsa yana kara tsananta kukansa.

Da yake momma tasan irin azaban da yake sha idan ciwon ya tashi sai hankalinta ya tashi sosai. Wayarta ta ce Mahreen ta miƙa mata, dama wayar tana kusa da ita.

Ɗauko wayar ta yi ta miƙa mata tana kallan guyson ɗin.
"Ji fa, kato da shi ne yake yin kukan ciwo, Adda Mahnoor kalle shi fa, wannan anyi wawa gaskiya". Tana magana tana harararsa. Ko kunyar idanun mommarsa bata ji ba take yi mashi wannan iskancin.

Ɗan buge mata baki Mahnoor ta yi tana kallanta. Hannu ta ɗaura a saman bakin nata ta hau murjesa tana faɗin. "To me na yi maki zaki buge mun baki?".

Momma dai hankalinta baya a kansu, ƙoƙarin kiran number Dr Raj kawai take yi. Ta kuwa yi sa'a bugu ɗaya ya ɗauka, a lokacin ya bi bayan Ramish yana faɗa mashi Leesharh tana da buƙatar karin jini idan ba haka ba zasu iya rasata, an gwada jinin Bilal and shi Dr Raj ɗin dik jininsu bai yi irin nata ba, o negative take da shi, ashe shiyasa take da shegen janircewa da taurin rai, jinin sojoji ke gareta.

Dr Raj ya yi iya yinsa a kan Ramish ya tsaya a gwada jininsa idan ya yi a sanya mata ya ce ba zai bata jini ba, dan yana jin nau'in jinin nata yasan irin nasa ne, bama sai an gwada shi ba, amma dai ya ce ba zai bayar ba, a sayi sabo a saka mata ko kuma a nemo ƴan uwanta dik a in da suke su zo su bata, dan ta bada ranta ta cecesa ba wai hakan yana nufin shi sai ya tsaya mata a kan komai ba, ya yi abin da yakatama ya yi, shi yanzu ma ya fara zarginta ne, dan da ya zauna ya yi tinani ƙwaƙwalwarsa ta basa dik yadda aka yi tana da masaniya game da komai, ashe banza kwanaki ya saketa, ya yi kuskure, dik yadda aka yi ta san komai, wannan abin ya baƙanta mashi da yasa ya ji ya tsani zuwa in da take.

Tun da ya sanya kafa ya bar ɗakin da ya cire mara bullet bai sake waiwayarta ba, Dr Raj yake kula da ita karkashin umarnin Bilal, abin kuma da baku sani ba shi ne, kamar Bilal ne yake kara tunzura Ramish a kan Leesharh, saboda Ramish ɗin ya ja baya da ita. Amma shi Bilal abin da bai sani ba shi ne, Ramish yana amsa mashi dik abin da ya faɗa mashi da fatar baki ne kawai, ba wai dan yana ɗaukar hakan a matsayin gaskiya ba, in short da Bilal da Leesharh dikka yanzu suna a karkashin sarrafawar Ramish ɗin ba tare da sun sani ba, dik yasa masu question mark, dik bincike yake yi a kansu ta ƙarƙashin ƙasa domin ya gane gaskiyar abin da yake faruwa.

Waɗan can guy da suka harba a hall ɗin nan da Ramish ya je ya gansu sai da ya razana matuƙa, domin kuwa ya sha ganin ɗayan guy ɗin a tare da Bilal several times, and akwai hotunansu tare da Bilal a wayar Bilal ɗin, hakan yasa Ramish ya kara tsananta zarginsa a kan Bilal matuƙa.

And kuma yaki bari Bilal yaga gawarwakin mutanen, hakan ma tana daga cikin aikinsa, lokacin da zai je h-q duba mutanen Bilal ya so su tafi tare, amma sai ya ce a'a zai je shi kaɗai, ashe kuwa gara da ya tafi shi kaɗai ɗin, dan yana ganin mutumin ya ce ba zai bari Bilal ya fahimci komai ba, dan in da gaske Bilal yana da masaniya a kan komai idan yasan wanda suka kashe mutuminsa ne to zai iya katsewa Ramish yunkurinsa na gane suwaye suke da sa hannu a lamuran. Shiyasa ya canzawa kowa a gidan yanzu, ya kuma dai'na bari suna samun damar haɗuwa da shi, yanzu haka tin safe Dr Raj yake san haɗuwa da shi ya rokesa da ya taimaka ya bawa Leesharh jini amma ya gagara samun damar ganinsa, kuma yana cikin gidan, ganinsa ne ya hanasu dama.

Sosai Bilal ya shiga damuwa a kan ɗauke mashi wuta da Ramish ya yi, yanzu haka tun jiya bai samu damar haɗuwa da Ramish ɗin ba, ya yi ya yi su haɗu abin ya gagara.

A ɓangaren Ramish ɗin kuwa, wlh jinyar kansa yake yi sosai, domin kuwa dik wasu bincike da zai yi mutanen da zai zarga suna da sa hannu a yunƙurin kashesa sai ya gansu a tare da Bilal, duniya yau Ramish ya rasa me yake yi mashi daɗi, ya shiga tashin hankali da kunci da bai taɓa shiga makamancinsa ba, tun daga jiya kirjinsa take yi mashi wani irin azabbabben ciwo mai tsananin gaske har yau, haka yake daurewa yana aiki.

Wani lokaci sai ya ji kamar ya dakatar da binciken nan domin fargabar abin da zai iya cin karo da shi, yana tsananin fargabar abin da zai binciko, zuciyarsa tana rawa a kan binciken nasa, sai ya ji kamar ya haƙura kawai, gara ya zauna da Bilal ɗin a haka bai binciko gaskiya ba sai ya fi mashi, amma kuma yana san sanin gaskiya ta wani fannin.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Cikin natsuwa Dr Raj ya yi picking call ɗin momma. Hankalinta a tashe ta fara zayyana mashi ciwon guyson ya tashi, ai yana daga zaune bai san time da ya miƙe tsaye ba, muryarsa a ɗan dishashe ya ce what.

A tinanin Dr ciwon Guyson zata ɗauki a kallah shekaru biyu ko uku kafin ta sake tashi, amma sai suka ga akasin haka. A hankali ya koma ya zauna tare da haɗe natsuwarsa waje guda, sannan ya ce momma ta yi gaggawan kiran likitoci da wuri so zo, lokacin yi mashi aiki kuma bata yi ba, dan bayan shekara ɗaya ake yi mashi, so da yin wancan aikin bai kai shekara ba yanzu, to me matsalar? Dr ya tambayi kansa.

"Bari in kira Jaish ko Jawad su yi gaggawar kiran Drs yanzun nan, idan Drs sun iso sai mu yi waya dan su duba mun shi su ji menene matsalar kuma". Cewar Dr. Jinjina kai momma ta yi tare da katse kiran ta dawo da hankalinta a kansa, a hankali ta fara tofa mashi addu'oi tausayinsa yana kara

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login