Showing 51001 words to 54000 words out of 403653 words

Chapter 18 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

26

me kike faɗa kuwa? Mu bari sai da safe fa kika ce?".

Kai ta jinjina mashi alamar tabbatarwa da yes hakan ta ce.

"Amma lallai Rahilarh baki san me bakinki yake faɗe ba, kinfa san Omar tun yana karamin yake fama da ciwon ciki, kuma kin san yanayin tsananin azabar da yake sha idan ciwon nan ta tashi, ba godiya zaki yi wa Allah ba da yasa yau ciwon ta tashi har yake iya yin magana? Ai hamdala zaki yi ki kuma yi gaggauwar taimakawa wajen kiran Dr dan sauki ya fara samuwa, amma sai ki ce mu barshi sai da safe, Omar ɗin nawa?".

Momma dai bata wani damu ba, ta miƙa hannunta ta ɗauko wayarsa dake saman bedside drawer ta miƙo mashi tana ce mashi.

"Allah ya huci zuciyarka ranka ya daɗe, ga wayar".

Karɓa ya yi da sauri, yana rarrashin guyson, number Dr ya shigar dan ya kirasa ya zo ya duba mashi ɗan lelensa.

Sai binsu da kallo Momma take yi, guyson yana kara narkewa haɗe da kukan shagwaɓa.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



Babban Dr na hospital ɗinsa King ya kira, cike da bada umarni ya ce dik abin da yake yi ya bari ya yi maza ya zo gida Omar ɗinsa bashi da lafiya.

Cikin girmamawa Dr ya amsa da In Sha Allah ga shi nan zuwa yanzu.

Katse kira King ya yi ya hau rarrashin guyson babu kama hannun yaro, kun san irin wannan yanayi da zasu ga mutum ya yi kasa gane me yake yi mashi daɗi irin hakan sam babu daɗi, sai ka ji a takure kake a duniya.

Momma jiki dik a mace sosai, komawa ta yi ta kwanta tana tunanin meyake faruwa da ita ne haka?.

A haka Dr ya zo part na King ya samesu, da yake kowa ya san Drn King ne sai babu wanda ya tare mashi hanya, suka bashi dama ya shiga har tsakiyar parlon, sallama ya yi haɗe da dakatawa a wajen.

Kallon guyson da kyau King ya yi. "Tashi mu je Dr yana parlour ya duba mun kai".

Kai ya fara girgizawa, yana kuka ya ce. "Ni daddy bana san Dr ya dubani, ya tafi kawai".

"Meyasa to?". King ya jefa mashi tambayar.

"Bana san ya yi mun allura, ni dai gaskiya ya tafi zan ji sauki". Yana magana yana kara tsananta kukansa.

Lumshe idanunta Momma ta yi kamar mai jin barci, dama ita tasan idan ba Dr Raj ba babu mai iyawa guyson, Dr Raj ma sai in su Ramish suna nan ne zaku ga ya yarda ayi mashi allura, nan ma yana kwance jikin ɗaya daga cikinsu suna ɗauke mashi hankali sannan ake yi.

"Dr ba zai yi maka allura ba, i promised you that".

Kara ƙanƙame King ya yi yana faɗin a'a shi dai ba zai je ba. Ba yadda King bai yi ba ya ce shi dai a'a ba zai je ba, daga ƙarshe ya hakura ya ce da Dr ya tafi abinsa dan shi ma ya lura ba ciwon cikin guyson ɗin bane ta taso.

Haka Dr ya juya ya koma asibiti dan ya cigaba da yin aikinsa.

Guyson kuwa King ya cigaba da lallaɓa shi har barci ta ɗauke shi a nan, momma kam miƙewa ta yi ta basu waje, ta koma room nata.

Tana shiga ta ɗauki wayarta, wata number ta kira wanda aka yi saving da my happiness. Kwanciya ta yi a saman bed ɗin nata tare da shigewa cikin bargo.

Call ɗin ya yanke ba'a ɗauka ba, tana rike da wayar sai ga shi an biyo kiran nata. Cikin sanyin murya ta yi sallama. Baka jin me ake faɗa ta cikin wayar sai dai ita da ta amsa da lafiya alamar gaisuwa aka ɗaga mata.

Jim ta ɗan yi kafin ta sake cewa. "Lafiya ta lou kawai dai ina jin jikina dik a mace ne yasa voice ɗina ta yi haka".

Shiru ta ɗan sake yi alamar tana sauraran abin da ake faɗe, can sai ta ce. "No ba barci nike ji ba".

Shi ma King ganin guyson ya yi barci yasa ya kwantar da shi haɗe da ja mashi bargo ya miƙe ya sauko kasa daga saman bed ɗin.

Waje ya nufa. Bai zame ko'ina ba sai room ɗin Auta, dama kunsan baya yin barci har sai ya yi mata addu'a.

Ya sha madarar mamakin ganin bata can, har ya mance da ana dinner, fitowa ya yi zai nufi ɗakin mommarta ya dubata a can sai ya tina da ai ana dinner su Jawad, dan haka tana can, bai so ya kwanta ba tare da ya yi mata addu'a ba, amma ba yadda ya iya, sai kawai ya juya ya nufi part ɗin Akka domin ya ganta kafin ya kwanta.

Already yar tsohuwa ta yi barci, dama in baku manta ba ba koshin lafiya ne da ita ba tin ɓacewar Spender.

Ganin already ta yi barci yasa ya matso a hankali ya tofa mata addu'a tare da rage mata gudun A.c, sannan ya fito ya koma room ɗinsa.

Ya sha madarar mamaki a lokacin da ya shiga bedroom ɗin nasa, kara waro idanunsa waje ya yi domin ya tabbatar wa kansa abin da yake gani gaskiya ce ko karya.

Babu guyson babu labarinsa, mutumin da aka bari yana barci, da sauri King ya karisa gaban bed ɗin dan ya tabbatar.

Tabbas da gaske ne Omar baya cikin ɗakin, to ina yake? King ya jefa kansa wannan tambaya.

A hanzarce ya juya ya nufi part ɗin Momma dan ya duba ko ya koma can, a tunaninsa kila da ya shiga ɓangaren Akka ne guyson ya wuce ba tare da sun haɗu ba.

Shi kuwa guyson yana tsaka da barci ne ya ji ana ta ambatar sunansa, tin yana jin abin da ɗan nesa nesa har ya fara jin hakan a kunnensa, abin kamar a mafarki kamar kuma a gaske, ba muryar kowa yake ji ba kuma face muryar Auta, tana kuka tana kiran sunansa.

Hakan yasa ya farka a firgice, har zufa sai da ta wanke mashi face ɗinsa, ya tsorata sosai na hakan. Kamar zai yi kuka ya fara goge zufar dake face ɗinsa da tafukan hannunsa.

Kamar daga sama ya sake jin sautin muryar Auta a kunnensa tana kuka tana kiran sunansa.

Ba ƙaramar razana ya sake yi ba, sai a lokacin ya tuna yau fa tun da rana bai sake haɗu da ita ba, tin da suka haɗu wajen ɗakin da Chuchu take ana mata ƙunshi, tuna hakan yasa ya yi saurin saukowa kasa daga saman bed ɗin.

Kai tsaye ya nufi waje da nufin ya je room ɗinta ya dubata. Dai'dai zai gifta ta wajen part ɗin maman su Yah Ramish sai ya tuna ai ana dinner, dan haka Auta tana can.

Kamar walkiya haka ya hango wani inuwar mutum kamar na Auta ya fito daga part ɗin maman Yah Ramish ya nufi hanyar dake wajen na fita waje.

Da sauri ya bi bayanta yana kwala kiran sunanta. Yana zuwa wajen kofar ya yi mamakin ganin a buɗe, yasan wannan kofa ba'a buɗeta fa.

Amma sai ya danne ya fito waje ta side ɗin. Wayam babu kowa, tsayawa ya yi yana ƴan waige waige a wajen, babu ko alamar motsin wani halitta, ya ɗan yi mamaki, amma sai ya ce gizo ne kawai saboda ita ce a ransa yasa yaga kamar inuwarta ne.

A fili ya furta. "Tun da na fito waje kawai bari in bi ta nan in je wajen dinner ɗin in ga Auta kafin in dawo in cigaba da barcina".

Na'am ya yi da wannan shawara dan haka sai ya nufi wata cikakkiyar hanya da take wajen dan ya ƙarisa wajen dinner. Yana tafiya babu tsoro cikin nutsuwa da kamala.

Dai'dai zai gifta ta wajen wasu flowers dake shuke kusa da part ɗin uncle Abbas kwatsam ya hango mutum a tsaye a wajen. Ko tsorata bai yi ba, kamar zai wuce ma sai kuma ya tsaya ya ce.

"Wanene a nan?".

Shiru ba'a amsa mashi ba, ga kuma mutum a tsaye kamar dai macece, wajen da ɗan duhu duhu.

Hannu ya zura cikin aljihun jallabiyar jikinsa da nufin ya fito da wayarsa ya kunna light ɗinta domin ya samu damar ganin wacece a wajen!.

Kash babu wayar a aljihunsa, hakan yasa ya ji babu daɗi, cikin ɗan ɗaga murya ya sake tambayar wacece a wannan wajen?.

A karo na biyu ma ba'a kula shi ba. Ransa ya ɗan sosu a kan hakan, ya ji babu daɗi sosai.

Amma sai ya danne tun da bashi da light a hannunsa sai yasa kai ya wuce kawai. Bawan Allah mai hakuri.

Cikin nutsuwa yake takawa, ba zaka yi zaton yana taka ƙasa ba saboda yanayin yadda yake tafiya babu wata sauti dake fita. A hankali daga bayansa ya ji takun mutum alamar ana biyo bayansa kenan.

Kamar ba zai juya ba sai kuma ya juya domin ya ga wanenen?.

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, wata iriyar halittar macece halitta na matsafa, gata doguwa mai mummunar fuska, baki kamar waga, batada kyan gani bata kuma da fasali ko kaɗan, ga ban tsoro a fuskarta.

Sai dai ko kaɗan guyson bai tsorata ba, ko a jikinsa, sai ma kallon ƙasƙanci da ya wurga mata, cike da confidence ya ce. "Ke kuma daga ina?".

Wani irin lankwasa ta yi haɗe da murɗe wuya, ita nan shegiya, ranta ya ɓaci ne dan bai tsorata ba.

Ganin tana wannan lankwashe lankwashe bata da niyar yin magana zata ɓata mashi lokaci barci yake ji ne yasa ya sanya kansa ya cigaba da tafiya abinsa, ko ɗigon tsoro babu a ransa, kaman wanda ya saba ganin aljanu, har da jan ɗan siririn tsaki.

Cikin wata iriyar kakkausar murya wannan aljana ko ace matsafiya ta furta.
"Kai bil'adama maza ka zo nan".

Yadda kuka san bai san Allah ya yi ruwan halittarta a wajen ba, ya cigaba da tafiyarsa yana kara jan tsaki.

"Kai bil'adama ba nace kazo nan ba? Kada ka kuskura ka kara koda taku ɗaya ne, zaka mutu idan ka yi hakan!".................Ta yi maganar cikin murya mara daɗin ji, kamar muryar ƴan shaye shaye yanzu kuma. Ta yi maganar tare da ɓacewa kamar walkiya ta fito a gabansa.

Dakatawa ya yi da tafiyar da yake yi, a hankali ya ɗago da kallonsa a kanta, sai da ya bita da kallon up and down kafin cikin sanyin murya ya ce.

"Awww ke nan wai a haka aljana ce ko fatalwa ko? Dallah ni bani hanya na wuce hai, da wani shegen ido kamar kuliya ta faɗa tarko, ji wani muzurai da kike yi tamkar kwarton da soja ya kama a gidansa, kina wani taunan hakwara kamar wadda ta yi shekaru ashirin bata ci nama ba, na zabga maki mari naga karshen iskanci, kina wani huro hanci kamar ana hura balo balo kenan wai hegiya ko?"............... Ya kai karshen masifar tasa yana raɓawa gefenta zai wuce.

Riko wuyar rigarsa ta yi ta baya a in da ta yi sama da shi sannan ta wurgar da shi gefe tana wani taunan hakwara, ga wani lanƙwashe kasusuwan gaɓɓanta da take yi, sai wani murɗe wuya take yi tamkar taliya ƴar murji.

Haƙiƙa ya ji zafin wurgi da ta yi da shi, abin ya taɓa shi sosai, dan haka sai ya ciza laɓɓansa da karfi, kamar zai yi kuka ya daure ya miƙe tsaye.

A fusace ya ce. "Ke mushirika kuma shaiɗaniya! Zaki bani hanya na wuce ne ko kuma sai raina ya ɓaci na gwada maki karfin ikon Allah?".

Kamar wata walkiya sai gata ta bayyana a gabansa. Wani irin lankwashe wuya ta yi tana muzurai kamar wata kuliyar da ta shiga tarko, laɓɓanta ta shiga taunawa da karfi tana wani bubbuga kafafunta a ƙasa.

Guyson da babu alamar zai ji tsoronta ne ya ce. "Wannan hauka da kike yi kuma fa? Ke ni ina da abin yi, zaki bani hanya ne ko sai na gwada maki yadda ake murɗe kashin wuya, na murɗe taki na karye shege na jefar?".

Ta lura fa guyson bashi da tsoro ta wannan ɓangaren, dama kowa da abin da yake tsoro a rayuwarsa, kun dai ga shi rago ne ta fannin ciwo, amma ba haka yake gabaɗaya ba, baya tsoron ire-iren waɗan nan mushirikan.

Da manuniyar yatsarsa ya nunata. Cikin fusata ya ce. "Bani hanya na wuce shashasha kawai!!".
Ya fara fusata ne, ransa ya fara ɓaci, zuciyarsa tana tafasa, so yake ya je ya ga Auta ya dawo ya kwanta!.

Kin bashi hanya ta yi tana cigaba da tauna hakwara tana muzurai.

Hannu ya ɗaga da karfi, ya yi bismillah zai wanke shegiya da mari sai ya nemeta ya rasa, ɓat ta ɓace. Siririn tsaki ya ja tare da wucewa ya nufi dinner hall.

Ransa a ɓace ya cigaba da jan tsaki yana tafiya. Bai yi nisa da barin wajen ba ya ji alamun ana binsa a baya! Wani sirirn tsakin ya ja, ba tare da ya juya ba ya ce. "Ai sauri zaki yi mu jera kafaɗa sai ya fi, shashashu kawai".

Guyson fa yana da gaskiya, wlh ko aljani ne idan ka nuna kana tsoronsa ya dinga azabtar da kai kenan, amma idan ka nuna mashi kai ma shege ne mai ji da kanka, ka rike ayoyin Allah wlh ta kansa zai yi, tuni zai koma yana shakkarka!!.

Guyson bai sake juyowa in da suke ba har ya kai hall ɗin nan, dai'dai zai shiga hall ɗin ya juyo, wayam bai ga kowa ba. Tsaki ya sake ja tare da ƙoƙarin juyawa dan ya shige ciki.

A wani irin haukace aljanar ta bayyana a gaban idonsa, gashin kanta kamar bukkar shaiɗanu, idanunta kamar jini, bata da fasali sam, ta yi irin wannan bayyana ne dan su tsorata shi, so suke yi ya tsorata dan ya basu kofar da zasu shiga jikinsa su rikka sarrafa shi, aljani baya shiga jikin mutum haka kawai, sai bawa ya tsorata ya bashi kofa.

Wannan tsorata da mutum zai yi shi zai basu damar shiga jikinsa, idan mutum ya tsorata wannan firgita da yake yi dik wasu kofofi a jikinsa buɗewa suke yi, to hakan yake bawa aljanu damar samun kofar shi, jama'a sai a kiyayye wannan, arinka daurewa ban da saurin razana a kan abu, wannan razana da kuke yi yana bawa abubuwa da dama hanyar shiga jikinku, ciki harda sihiri idan aka yi wa mutum, bayan sihiri akwai jifa, dik suna samun kofa ce ga hanyar razana.

Ko mushirikai sun nufeka da sharri basa iya cin maka har sai sun turo wani abin da zai razanaka, kana razana ka firgita zasu samu kofar da wannan aiki nasu zai shi.

Razana ga mutane wannan wajibi ne idan mutum yaga abin tsoro unexpect, to amma ya zai yi ya kare kansa daga mugayen idan ya razana? Amsa a nan ita ce ambaton Allah, idan bawa ya razana ya yi saurin furta sunan Allah, hakan zai yi matuƙar kuɓutar da shi daga dik wata sharri, dan haka ku yi ƙoƙari sunan Allah ya kama bakinku ya zauna, kune da cin riba, Allah ya kiyaye ya kare dikkan musulmi bakiɗaya.

A wannan karon ya ɗan tsorata kaɗan, saboda unexpect ta bayyana a gabansa, ga yanayin yadda ta bayyana abin tsoro ne sosai.

Sai dai yana ganinta ya yi saurin furta. "A'udhu billahi mina-sh-shaitanir-rajim". Fassara. Na nemi kariya daga Allah daga shaidan, wanda aka la'anta

Sai. Allahu la ilaha illa huwa al-Hayyul-Qayyum......... Har zuwa karshe.
Ayatun Kursiyyu ita ce mafi girman kariya daga aljanu da shaidanu.

Sai a karanta Surorin Kariyar

Suratul Falaq (Qul a'udhu bi rabbil-falaq...).

Suratun Nas (Qul a'udhu bi rabbinnas...).

Suratul Ikhlas (Qul huwallahu ahad...).

Sannan a karanta. Bismillahi alladhi la yadurru ma'asmihi shai'un fil-ardi wala fis-sama'i wa huwa Sami'ul-Alim.

Karanta Salatin Annabi (SAW). Yawaita salati kan Annabi (SAW) yana kawo tsaro da saukakawa bawa tsoro.

Guyson yana karanta waɗan nan addu'oi wannan mushirika ta ɓace ɓat. Guntun tsaki ya sake ja kafin ya ce. "Hakan ma bai yi aiki ba, sai ki sake shiri".

Yana gama faɗar haka ya shige cikin ball ɗin abinsa.

===================🔥

Momma ta jima tana wayar da take yi, daga karshe ta tufe da batun Jaish, cike da damuwa take zayyanawa wanda take waya da ita ɗin damuwar da take ciki a kan ɓacewar Jaish.

Izuwa yanzu dik wata jarumtarta ta kare, hakurinta ya gaza, tunaninta ya tsaya, dannewa da take yi ta kai makura, zuciyarta ya kara tsananta ciwo, ta yi kuka a ɓoye har hawayenta sun kusa dai'na fita, zuciyarta na raya mata Jaish ya mutu ya bar duniya.

Tas ta gama zayyanewa wadda take waya ta ita halin da take ciki. Hakuri ta rinƙa bata tana rarrashinta har sai da ta tabbatar da ta ɗan ji sassauci.

Sannan ne suka yi sallama. Gabaɗaya barci ya kauracewa idanun momma, damuwarta ya dawo sabo a kan ɓacewar jaish, uwa kenan, tamkar ta san yana hanyar tunkarosu, sai tunaninta ya kara tsananta a kansa, ta kara shiga damuwa, zuciyarta ba bugawa da sunansa.

Ganin kwanciya ba zai haifar mata da komai bane yasa ta miƙe ta je ta ɗauro alwala.

Sallah ta zo ta fara gabatarwa domin neman Ubangiji da ya sassauta mata wannan hali da take ciki a wannan masarauta.

A ɓangaren King kuwa, lokacin da ya dawo part ɗin momma dan duba guyson sai ya iskota tana sallah.

Ganin babu guyson a ɗakin yasa ya juya ya fita, part ɗin mummyn Chuchu ya nufa. Dan yasan guyson yana santa kuma yana zuwa wajenta sosai.

Nan ma guyson

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login