Showing 132001 words to 135000 words out of 403653 words

Chapter 45 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

71

samu matsala". Ya faɗa yana sauka daga titin sama izuwa na kasa.

"Kai Yah Bilal ka fara ko?". "To ya kike san in yi? Dole ce tasa ai".

Shiru ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. "Samu waje ka tsayar da motar sai mu yi magana ko?"...... Ba musu ya gangara gefen titi ya yi parking, sannan ya juyo ya kura mata ido.

"Menene next my lovely wife?". Ya faɗa. Dai'dai lokacin call ɗin Ramish ya shigo wayarsa, bai kai ga kawar da kallonsa a kanta izuwa kan wayar ba tasa hannu ta ɗage nikaf dake face ɗinta.

Ƙasa kawar da kallonsa ya yi, da ɗan karfi ya furta wow. Leesharh ta sha make up yau sosai, ta yi kyau matuƙa kamar ba ita ba, sai glowing take yi.

Har call ɗin Ramish ya katse yana nan yana kallanta bai yi magana ba.

Me kuke tinanin ya haɗasu a wannan dare da har yake ce mata my wife? Dama suna soyayya ne? Ko dai yau suka fara?.

"Yah Bilal mu je ka saya mun ice cream sai mu koma gida dare ya yi". A ɗan shagwaɓe ta faɗa.

Nisawa ya yi, maza anga kyau iya kyau har ya ji kamar ba'a duniya yake ba. "Wife kin yi kyau matuƙa sosai".

Siririn murmushi ta saki kafin ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa. Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta.
"A'a barni in kalli face ɗin matata da kyau". Ya faɗa yana zame hannunsa daga haɓar tata.

"Kai Yah Bilal ni fa kunya nike ji". Ta faɗa tana kallansa ƙasa ƙasa. Matsar da bakinsa dab da kunnenta ya yi, ƙasa ƙasa kamar mai raɗa ya furta. "Kin girma fa, komai ya ciko dai'dai yadda nike so, yakamata......."

Katse shi ta yi ta hanyar jiyowa garesa da sauri. Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da matsar da bakinsa saitin kumatunta, sumbata ya bata a lallausan kumatunta.

Lunshe idanunta ta yi tare da sauke ajiyar zuciya. Ƙara matsa dab da ita ya yi, kamar zai haɗe bakinsu waje guda, kamar mai raɗa ya ce. "Yau kam za'a bani dama ne ko dai za'a cigaba da hanani kamar a baya?".

(What?😳 Kenan ya saba kawo mata harin kiss? Tab akwai matsala, a warware mana wannan cakwakiya ko zan samu damar shan maltina mai sanyi.)

Tana kallan cikin idanunsa ta ce. "Yah Bilal ko da can baya ban taɓa hanaka na ai, kai ne dai kake ganin kamar ina hanaka".

Gera ɗaya ya ɗaga mata tare da kara matsawa dab da ita sosai, a hankali yasa hannunsa zai ɗan rungumota.

A karo na biyu call ɗin Ramish ya sake shigowa wayarsa. Ɗan ciza laɓɓansa kaɗan ya ɗan yi haɗe da janye jikinsa daga kusa da ita, ya koma ya mannu da jikin kujerarsa yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya ɗauko wayar, kamar ba zai yi picking ba, dan yasan wanenen Ramish, tsaɓ zai iya cankar a wani irin yanayi yake ciki da jin voice ɗinsa kawai.

Amma sai kuma ya tina in har bai ɗauki wannan call ɗin ba to Ramish zai fita nemansa ne, saboda sun san dik abin da ya sha kansu basa wuce miss calls biyu ma junasu ba tare da sun yi picking ba, shirunsu basu yi picking ba hakan na nuna suna cikin matsala kenan, kunga dole ya fita nemansa.

Hakan yasa ya ɗauki call ɗin tare da kara wayar a kunnensa yana seseta nitsuwarsa. Daga ɗayar ɓangaren Ramish ya yi cikakken sallama. Amsawa ya yi idanunsa a kanta, ita ma shi take bi da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa.

"Ina kake Bilal?". Ramish ya jefa mashi tambaya.

Shiru ya ɗan yi yana tinanin abin faɗe, basu saba yin karya ba, hakan ya ja ya rasa abin faɗe.
"Ina zuwa gida yanzu". Ya faɗa yana san katse kiran.

Katse shi Ramish ya yi da cewa. "Ka faɗa mun in da kake in zo in sameka yanzu". A hanzarce ya ce. "A'a ba sai ka zo ba, ina hanyar gida yanzu".

Shiru Ramish ya ɗan yi, can kuma sai ya ce. "Ka dai san bana magana biyu ko?". Jinjina kai Bilal ya yi alamar e tamkar yana gabansa haɗe da cewa e haka ne.

"To ina kake zanzo yanzu".

Zaro idanu Bilal ya yi, sai ya ji kamar an kwaɗa mashi guduma a kansa, hankalinsa ne ya tashi, Ramish ya zo ya samesa a nan ai ya shiga uku, me zai ce mashi ya rabu da shi kenan?.

Zare wayar daga kunnensa ya yi, ba tare da ya sake yi wa Ramish magana ba ya yi saurin katse kiran, a hanzarce ya tashi motar.

"Yah Bilal lafiya?". Ta jefa mashi tambayar tana kallan wayar dake hannunsa.

"Sauke nikaf naki, sorry ba zamu iya tsayawa sayen ice cream ba, gida kai tsaye zamu wuce, gobe muna da taro, idan mun taso daga taron zan saya maki ice cream ɗin in kawo maki". Ya kai karshen maganar tare da kunne mota.

Da gudun gaske ya figi motar tamkar zai tashi sama, har sai da ya bata tsoro.

A can gida kuwa. Ramish yana tsaye a parlournsu, daga shi sai sexy short, babu riga a jikinsa sai white singlet mai kyan gaske, yana tsaye a jikin windownsu dake fuskantar harabar gidan, hannunsa rike da cup and his phone.

Shi ma Ramish yana da zanen letter R a damtse hannunsa da ya zana kamar yadda Bilal ya yi zanen B a wuyarsa, yanayinsa ta nuna yana cikin damuwa sosai, saboda abubuwa sun sha kansa matuƙa, ga shi gobe zasu yi wannan taro da yake sa ran kafin taro ya kama masu nikaf kenan, sai dai har yanzu bai samu wata makama da zai iya kamasu da ita ba, babu ma wanu abin zargi da suka bar mashi, abin dai ya sha gaban tinani, dik yadda aka yi su ma shegu ne.

Ya yi shiru yana kallan harabar gidansu kamar mai tinanin wani abin, bawan Allah damuwa ta yi mashi yawa, bai san ya taron gobe zata kasance ba.

Ba tare da ya juyo ba, cikin nitsuwa ya ce. "Daga ina kake a cikin wannan dare bayan kasan halin da muke ciki?"............ Kamar wani aljani, ko yaushe ya ji yo takun sahun Bilal?.

Bilal da ya shigo yanzu ne ya ɗan fara kame kame kamar wani maras gaskiya, dama kamar yasan zai sami Ramish a wajen yasa ya shiga parking space ɗinsu ta kofar baya ba tare da kowa ya gansa ba, dik dan gujewa ƴan gidan kada su gansa.

"Meyasa kaki yarda in zo in sameka a in da kake? And meyasa ka katse kirana ba tare da mun gama magana ba?". Ramish ya sake jefa mashi tambaya a karo na biyu ba tare da ya jira ya amsa ta farko ba.

Shiru ya kasa amsawa, dan bai san me zai ce mashi ba, ga shi dik in da suke zuwa dama a tare suke tafiya bare ya yi mashi wani karya.

A hankali Ramish ya juyo garesa, wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce.
"Me kake ɓoye mun my love". Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallan tuhuma, dan yanzu zuciyarsa ta rigata da kai point ɗin da ba zai iya ɓoye zargin da ya jima yake yi ba, ya daɗe sosai zuciyarsa tana ɗarsa mashi zargi a kan Bilal na ɓoye mashi wani abin, amma a koda yaushe ƙoƙarin kawar da wannan zargi yake yi domin yaga ya kori shaiɗan dake san rabashi da ɗan uwansa ya haɗasu faɗa.

"What do you think that I'm hiding for you?". A ɗan razane ya yi maganar, alamar kamar dai da gaske akwai wata a ƙasa.
"Ka fini sani Bilal, ka fini sanin abin da kake ɓoyewa". "Wai Yah Ramish lafiyarka yau kuwa? Shin na taɓa ɓoye maka wani abin ne? Tin tasowata har zuwa yau ba a tare muke yin komai ba?..........."

Cikin zafa da kunan rai ya ce. "Banda wannan lokacin Bilal, tin da muka taso tare muke yin komai amma banda yanzu!". Yadda ya yi maganar da alama ransa ya fara ɓaci, zuciyarsa ta fara raunata sosai, dan da alamar zarginsa tana san tabbata, idan kuma abin da yake zargi ta tabbata da gaske, magana ta domin Allah zai iya rasa ransa, saboda kowa yasan bayan iyayensa babu wanda yake kauna biyun Bilal, yana sansa kamar ransa, dole zuciya ta buga idan kuwa haka ne.

"Yah Ramish why are you talking like that? Talking out of control, and you're shouting like mad............".

Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata cak sakamakon wani irin tsawa da Ramish ya daka mashi a kan ya yi mashi shiru.

Taku biyu ya yi ya matsa gabansa, dama tin da ya fara bincike a kan masu nikaf Bilal ya zare hannunsa yaki taimaka masa, tare suke yin komai, amma a wannan karon Bilal yaki tayasa, hakan yasa zarginsa a kansa ya karu, sannan ga fita da Bilal ɗin yake yi shi kaɗai a yanzu, idan baku manta ba a ranar da Ummie ta je ɗakin Ramish nace maku Bilal baya nan, ya fita ko?. To kun ga kuma a tare suke fita, yanzu Bilal baya taɓa fita tare da Ramish, sai dai ya fita shi kaɗai, ga yawon dare da yake yi wanda a baya sam baya yi, baya zaman gida ko wajen aiki sosai yanzu, hakan ya kara ɗarsa zarginsa a zuciyar Ramish, sannan sai ya rinƙa kawowa Ramish wasu silly silly abubuwa da basu da amfani ya haɗa shi da aiki yasa Ramish baya aiki bincikensa yadda ya dace, hakan yasa ya ja lokacin bai iya gano gaskiya a kan abin da yake bincika ba, ga shi gobe taron da zasu yi ne. A takaice abubuwa dayawa ya ja Ramish ya fara zargin Bilal tun watannin huɗu da suka wuce.

Da karfi Ramish ya damki wuyar rigar Bilal, idanunsa sun ƙaɗa sun yi jajir, da alama yana out of control ɗin da gaske, jikinsa har wani kerma ta soma yi, yana gudun tsono abin da zai iya zame mashi narazana ga rayuwarsa, sannan kuma yana san tono gaskiya ko dan ya san ina ya dosa da suwaye yake tare.

"Ka faɗa mun me kake ɓoye mun". Cikin zafa Ramish ya yi tambayar haɗe da ɗan ɗaga murya.

Pretending................. Ƙoƙarin nuna gaskiyarsa Bilal ya yi, yana san nuna shi ba mai laifi bane kuma babu abin da yake ɓoyewa, hakan yasa ya dunkule hannunsa da karfi ya kaiwa Ramish duka a kirji. Cikin ɗaga murya ya ce.
"Wani irin abu ne wannan? Meyasa na zama abin zargi a gareka? Meyasa zaka ce ina ɓoye maka wani abin? Mekake nufi da kalamanka a kai'na? Ko kana tinanin ni zan iya cutar da kai ne?".

(My people's yanzu na ce waye ya kawo maganar cutarwa a nan? Babu rami meya kawo maganar rami? Shin Ramish ya ce Bilal zai cutar da shi ne da Bilal ya kawo batun cutarwa? Ku tayani yin alkalanci a nan wajen.)

Da gudu Dr Raj and Yah Rizwan suka fito daga nasu bedroom ɗinsu jin muryar Bilal cikin faɗa yana magana. Innalilahi wa inna ilahir rajiun shi ne abin da suka furta a tare.

Zame hannunsa Ramish ya yi daga wuyar rigar Bilal, da hannu ɗaya yasa ya daki kirjin Bilal da karfi har sai da Bilal ya yi baya baya ya bugu da jikin bango. Duuuuuuuuuummmmmmmmmm

"You are lying Bilal! There must be something you are hiding for us, and you have to tell us what you are hiding today!!". Cewar Ramish kenan.

Bilal domin ya kare kansa ya kuma tabbatar da gaskiyarsa sai ya yi ƙoƙarin kawo abin da zai kawar da batun ya faɗa masu me yake ɓoye masu, sai ya yi ƙoƙarin yin faɗa da Ramish ta yadda hakan zai ja wancan zancen ta kau.

Da karfi ya nufi Ramish da nufin zai rama dukan kirjinsa da ya yi. Dr Raj da Yah Rizwan ne suka shiga tsakaninsu da gudu, sanya karfi Bilal ya yi ya bangaje Dr Raj da karfi har sai da ya faɗi a saman sofa. Yah Rizwan kuma ya taresa yana mai daka mashi tsawa a kan ya nitsu su bar shir men nan.

Yah Ramish dai yana tsaye yana binsa da kallo, mamaki ne ma ya kama shi, wai yau shi da Bilal ne a irin wannan yanayi? Wannan wace iriyar musifa ce? Su da suke san junansu tamkar su yi wa juna numfashi! To wai me matsalar ne?.

Ya jefawa kansa tambaya, jikinsa dik a mace sosai, sam baya san dukan Bilal, dan wlh idan ransa ya ɓaci za'a iya kwasan Bilal ranga ranga, shiyasa yake ya ƙoƙarin koran shaiɗan kada ya kaisa ya barosu, dan har yanzu yaki yardanwa da zuciyarsa Bilal mai laifi ne. Allah sarki zuciya, kun san dama da wuya ya iya karɓar wannan kaddara idan har ba yaga da gaske ido da ido Bilal ya cutar da shi ba.

Da sauri Ramish ya juya ya koma cikin bedroom ɗinsa, basu ankara ba sai ji suka yi ya banko kofa da karfi ya murza key, a cewarsa koma menene kamata ya yi ya binciko da kansa, a matsayinsa na babba bai kamata ya tsaya tambayar Bilal ɗin ba ma ai, kamata ya yi ya tsaya da kansa ya binciko gaskiya, zubar da girma ne ma ya tsaya sa in sa da wani, shi da yake da hanyar gane gaskiya, shi da Allah ya bashi ilimi da kaifin ƙwaƙwalwa! Ai bai kamata ya wani damu ba!.

Yah Rizwan ne ya ja Bilal suka wuce bedroom ɗinsa, Dr Raj kuma ya bi bayan yayansa Ramish. Sai dai ko da ya je sai ya tadda Ramish ya rufe kofa, har kamar zai yi knocking sai kuma ya tina halin yayan nasa, yanzu a banza zai ɓata lokacinsa dan Ramish ba zai sauraresa ba, hakan saya ya juya ya bi bayan Bilal dan ya je ya ji me ya haɗasu faɗane wai, su da suke kamar twin's................To harshe da haƙora ma watarana ai suna saɓawa bare ƴan adam malam Dr Raj.

A ɓangaren su Sharifat kuwa, Leesharh ta dawo daga unguwar da ta je cikin ƙoshin lafiya, ta yi wanka da sallah tana kudundune a cikin bargo saman bed, Sharifat bata a ɗakin, tana wajen Ummie ɗinta, dan Ummie ta ce ta zo su kwana yau a tare dan tana da magana da ita.

Shiru ta kwanta tana tunanin duniya, karfe 11 na dare ta buga, time ɗin na bugawa wayarta ya hau ƙara alamar shigowar kira. With her full confidence ta janyo wayar.

Ganin private number ya sa ta yi saurin sakin siririn murmushi wanda ya fi kama da murmushin ramakon gayya. Wayar tana gab da katsewa ta yi picking tare da karawa a kunnenta.

Shiru aka yi ba'ayi magana ba, a gadarance ta ce. "Hello wanene?".

Daga ta cikin wayar ta tsinkayo muryoyi guda biyu suna magana kus, kus, kus alamar suna shirya abin faɗe kenan. Da yake bata jin me suke faɗe sai ta ce. "Idan baku gama tsara abin da zaku faɗa mun tun kafin ku kirani ba me na kirana? Ai da sai ku bari sai kun gama tsarawa ko?".

Shiru basu amsa mata ba, cigaba da magana ƙasa ƙasa suka yi. "Okey ni ina da abin yi, idan kun gama shawartawa zaku iya sake kirana, dan nima yanzu jiran call ɗinku nike yi". Ta kai karshen maganar tana ƙoƙarin cire wayar a kunnenta da ta katse kiran.

"Kada ki kuskura ki katse mana call". Daga ɗayan ɓangaren aka faɗi hakan. Gabanta ne ya yi wani irin mummunar faɗuwar jin voice ɗin kamar na Bilal. Amma sai ta daure, kun santa da jajircewa, ta nuna kamar bata san masu kiran nata ba, cikin nuna isa ta ce. "Da yake wayarku ce ba sai ku hanani katseta in gani ba".

"Ke kin san da suwa kike magana kuwa?".

Siririn tsaki ta ja, har da wani wuwwurga idanunta sama da ƙasa ta yi masu kallon up and down kamar tana gabansu, a walaƙance ta ce. "A fagen iskanci ko da shaiɗan nike magana karshe kenan a dik wani zalinci ko? To ko da shi nike magana bai isa ya ɗaga mun murya ya faɗa mun ga abin da zan yi da wayata ba".

Da suka fahimci faɗa ta zo da shi, su kuma lallaɓata suke da bukatar yi, dan su suke nema a wajenta, sai suka sassauta murya, cikin nitsuwa aka canza murya, da alama wani ya karɓi wayar.

"Dik ba wannan ba, magana muke san yi dake, ajiye dik wani zafin kanki da tashen balajarki a gefe ki sauraremu".

Jin haka yasa ta amsa da. "Ina jinku".

"Kin san da cewa aikinki bai kare ba ko baki sani ba?". Ya jefa mata tambayar haɗe da yin shiru yana jiran amsarta........... "Zaka iya cigaba da magana, saboda ba zan iya kowace magana in amsa ba, idan ka gama faɗar dik abin da zaka faɗa sai in tattare in baku amsa guda". Ta yi maganar tana miƙewa zaune.

"Okey zaki iya yin dik abin da kike so, amma ina san ki sani mahaifinki na hannunmu, ko ki yi mana abin da muke so, ko kuma yau lahira ta yi bako, wlh a daren nan idan baki nemo mana masaniyar a in da su Ramish zasu yi wannan taro ba, tabbas zaki rasa mahaifinki".

Tin da take a rayuwarta bata taɓa yin dariya irin wanda ta ƙaƙalo dan dole a yanzu ba. Bushewa da dariya mai ɗan sauti ta yi. Shiru suka saurara suna jinta, har da rungumo pillow ta yi a kirjinta tsabar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login