Showing 303001 words to 306000 words out of 403653 words

Chapter 102 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

109

numfashinta ya fara komawa daidai. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya duba time a diamond watch dake manne a hannunsa. 9:40pm. Nisawa ya yi kafin ya yi ƙasa sosai da murya, cikin natsuwa ya ce. "Aesh are you okey now?"..... Kanta na daga manne da chest ɗinsa ta gyaɗa mashi alamar e. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Thank god, but menene yake damunki haka?".

Kai ta girgiza alamar ita ma bata sani ba, sannan ta ɗan yunkura zata bar jikinsa. Cikin gaggawa ya yi ƙoƙarin hanata yana faɗin. "Ba zaki fama ciwon naki ba idan kika tashi?"....

(Kun ji mun Ramish da iskanci, kawai dai ka faɗi gaskiya, ba wani ba zata fama ciwonta ba, dama ni tin daga yanayin sleeping dress ɗinka nike zarginka da uhm uhm na yi shiru saboda su maman Sultan, amma da na faɗi wani abin, bazaki fama ciwonki ba idan kika tashi, kai Ramish ɗan duniya ne, bariki da kasuwa yaseen 😅)

Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e ba zata fama ba...... Ba tare da ya sake yin magana ba ya saketa. Miƙewa ta yi da kyar ta koma ta jingina bayanta da jikin kujerar motar tana jan numfashi a hankali hankali. Sorry ya yi mata kafin ya ce bari ya tada mota su koma gida da wuri dan ta kwanta ta huta. Kai kawai ta iya jinjinawa, dan ji take yi tamkar an ɗaure mata tongue ɗinta.... Kunna motar ya yi idanunsa a kanta ya fara driving, dik fa wannan damuwa da ya shiga bai san ya yi ta ba.

Kai tsaye gida ya wuce da ita yana tinanin lokacin cigaba da yin bincikensa ya yi, yakamata ya kama masu nikaf yanzu, yakama Leesharh ta bashi haɗin kai wajen bashi amsar waɗan nan tambayoyi da yake da buƙata da sauran evidence da suke hannunta, sai dai ya so kaita hospital duba da family Dr ɗinsu wato Dr Raj baya nan, amma bala'in kishinsu na jinin Modarawa yasa ba zai iya kaita ɗin ba, dama dai Dr Raj na nan ne, dan haka ya gwammaci ya wuce da ita gida ya je ya ɗan dubata da kansa........... Ramish namu na amana, zaka yi bayani, wlh akwai case tsakanin Leesharh, Ramish and Sharifat, ga Abbie a gefe wanda shi already yasan yarsa na san Ramish, sannan ya rigada ya basa, kuna tinanin su King Badeen zasu yarda Ramish ya auri bare ya bar Sharifat? Kuna tinanin Mama zata aminta? King Zuhair zai bari? Uhm abu ne da kamar wuya, dama dai ba'a san da batun Sharifat bane kila iya mama da King Zuhair su zame barazana da shamaki tsakaninsa da Leesharh, amma an san da batun Sharifat ai har su Abbie shamaki zasu zame tsakanin Leesharh da Ramish, akwai case ba babba kuwa.

Da yake yana sharara gudu sosai sai suka isa gida cikin ƙanƙanin lokaci, yana tsayar da motar a garaje ya juyo da kallonsa a kanta da nufin ya yi mata magana kenan sai ya ji saukar numfashinta irin na mai barci, ƴar ƙaniya ta ji wuya har ta yi barcin dole. Shiru ya zubawa kyakkyawar face ɗinta idanu wanda tun da yake da ita bai taɓa kare mata kallo irin haka ba. Zuciyarsa ce ta furta wow, shi kansa ya shaida ta haɗu, amma girman kansa ba zai bari ya yardanwa zuciyarsa da ta haɗu ɗin ba. Sauke kallansa ya yi izuwa saman kirjinta, lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tinano mashi yadda ya ganta tsirara a wancan ranar, take ya tunano yadda yaga tula tulanta muraran a fili.

Wani irin yawu ya haɗiya yadda kuka san ba lafiya ba, da alama abar tasu ta gado ta motsa kenan.

In faɗa maku abin da baku sani ba my people's, tin lokacin da yake jinyarta na wannan harbi da ta kare mashi, tin lokacin tula tulanta suka zauna mashi a ransa, dan kullum sai yaga tudunsu, daga karshe ya gansu muraran, amma bai bari kowa yasan sun birkita mashi lissafin ƙwaƙwalwa ba, nima saboda shegen bin kwakkwafina yasa na gano har na faɗa maku, dan haka kada ku bari yasan na faɗa maku......🥱

Ji yake yi tamkar yasa hannu ya yi kasa da zip ɗin rigarta dan ya ga koda iya tudunsu ne ko zai ji sauki, take wani ɓangare na zuciyarsa ta tina mashi a matsayin da suke yanzu shi da ita, kallan ɗan iska fa take yi mashi wanda kuma ba halinsa bane, kunga idan ta kama shi ya zuge mata zip ƙasa mekuke tinanin zai faru? Ai ko mutuwa yake yi bazata taɓa yardar ba halinsa bane. Tina hakan yasa ya hakura ya juya haɗe da buɗe side door ɗinsa ya fito, ba dan haka ba Allah saboda rashin kunyarsa sai ya zuge mata zip kasa ya gansu, amma yanzu neman wanke kansa a gareta yake yi, ba zai yi wani kuskure ba kuma.
Dik a gajiye yake. Cikin takun jarumta ya zago ta side ɗinta, kofar ya buɗe, cikin natsuwa yasa hannu ya ɗauketa cak ya fito da ita, da kafarsa ya take kofar ya mayar ya rufe, sannan ya nufi ciki.

Bata da nauyin barci sam, amma saboda azaban ciwon da ta sha sai barcin nata ya yi nauyi sosai, shi ma dik a gajiye yake, da kyar ya iya ɗaukarta da kyau. Bai zame da ita ko'ina ba sai cikin bedroom ɗinsa, kwata kwata ya mance cewa ba matarsa bace, ya mance ba ɗaki ɗaya suke ba, (saboda iskanci ba) sai da ya shinfiɗeta a saman bed ɗinsa sannan ya tina ashe ba bedroom ɗinta ya kaita ba. Siririn tsaki ya ja tare da cewa sai ya yi wanka zai mayar da ita nata bedroom ɗinta, a gajiye yake sosai, bari ya yi wanka ko zai samu karfi.

Wanka ya shiga a gurguje, sai dai da kyar ya iya yi saboda barci da ya ci karfinsa ga gajiya. A daddafe ya fito ya shirya cikin sexy sleeping dress ɗinsa masu matukar kyau da ɗaukar hankali. Yana zuwa ya ganta kwance saman bed ɗin nasa tamkar yadda ya barta, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kwanta a gefenta, a cewarsa bari ya ɗan huta kaɗan sai ya tashi ya mayar da ita bedroom ɗinta, sai dai kuma yana kwanciya barci ta yi awon gaba da shi, dan a wuya yake dama.

To my people's ya kuke ganin farkawarsu suga juna bed guda zai kasance? To ni dai na yanki gabas, bari in leƙa wani ɓangare in dawo.


🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

A hankali take dafa bango tana kuka ta nufo kofar fita daga bedroom ɗin, lokaci guda ta ji sansa na juyewa izuwa kiyayya, dan ya gwada mata zallar rashin imani da tausayi, baya kula da ita sai idan buƙatarsa ta taso, gaskiya Yah Jaish ya kai makura wajen san kansa da zalinci. Da kyar ma ta iya mayar da sleeping dress ɗinta jikinta, yadda kuka san mai koyan tafiya haka ta zama.

Parlournsa ta fito, azabar da take ji yasa ta ji ba zata iya taka kafafunta har ta isa part na momma ba, dan haka sai ta ce gara ta shiga bedroom na mama Haulat ta kwana a can, zuwa da safe sai ta koma wajen momma. Parlourn gabaɗaya baibaye yake da duhu, wutar a kashe take. A haka take laluɓawa da yake tasan a in da ɗakin mama Haulat ɗin yake, sai ta nufi can, hawaye wani na bin wani tamkar an buɗe tap...... Da kyar ta iya gano kofar ɗakin, tana ƙoƙarin laluɓar handle na kofar ta tura ta shiga sai ji ta yi kamar daga sama an ɗauketa cak, ga shi cikin duhu ne, amma kuma dik da ba haske ta gane shi ne, dan idan zata ƙasa gane kowa ban da sanyin zuciyarta, shi ɗin na daban ne da ya fita daban ko a cikin duhu.

Sai dai a tinaninta abin da ya yi mata yanzu zai sake mai da ita ya yi mata dan azzalumi ne a cewarta, dan haka sai ta fara ƙoƙarin kwatar kanta. Bai kulata ba, ya cigaba da tafiya, sai mutsu mustu take yi, amma dik a banza, dan bata tashi sanin in da take ba sai da ta ji kanta a cikin ruwa mai zafi sosai. Ihu ta zunduma, a cikin duhun ta fara laluɓar abin da zata samu ta kama ta fita, ruwan ya yi mata zafi sosai. Sai dai bata iya taɓo komai ba, har shi bata ji motsinsa ba, yana sakata a cikin ruwan bata sake jinsa ba. Tsananta kukanta ta yi tare da fara faɗin. "Na shiga uku, momma wlh Yah Jaish zai kashe ni, wayyo bappana, dan Allah ku mayar da ni wajensa".

Tsabar ta birkice tana kuka haɗe da sambatu bata ji lokacin da ya janyota ya mannata da kirjinsa ba, shi ma ya tsunduma cikin ruwan. Sai da ta ji sanyayyar muryarsa yana faɗin. "Babu wanda zai mayar dake wajen bappan naki, kina nan tare da ni, ya isa haka kukan"......... Sai sannan ne ta gane ashe tana jikin mutum. Cike da tsoro ta sanya hannunta tamkar mai tsoron taɓa abu ta fara laluɓarsa cike da fargaba. Tabbas shi ne, ƙoƙarin raba jikinta da nasa ta yi tana kara tsananta kukanta, cikin sauri ya kara kankameta yana faɗin. "Ina zaki je kuma?". "Yah Jaish dan Allah ka kyaleni haka, wlh ba zan iya ba, zan koma wajen momma ne in ce ta mayar da ni wajen bappana".

Ƙara matsar da lip ɗinsa dab da kunnuwanta ya yi, cikin raɗa ya ce. "Ni na bada izinin a mayar dake ne? Ko kin manta ni nake da iko da ke ne?".
Shiru ta yi ta rasa abin cewa. Hannunsa yasa ya kara jawota jikinsa, cikin dabara ya ɗan yi ƙasa da hannun nasa a in da ya fara bubbuɗe mata kafafunta ruwa yana ratsata da kyau. Kankamesa ta yi saboda zafin ruwan, tana san kurma ihu amma tana fargaban abin da zai iya sake aikata mata, rufin asirinta dai ta yi shiru....... Shi kuwa, sai da ya buɗe mata kafafu ruwa ya ratsata da kyau, sannan ne ya hauro da hannunsa sama, saboda tsabar tabbatar rashin kunya sai ya sanya hannu a saman nipple ɗinta, a hankali ya fara shafowa, a kunnenta ya fara raɗa mata. "Wajen yana yi maki zafi ko? Na basu wahala ko?"........ Kai Jaish akwai tsaurin ido, kunyar rashin kunya, ko da yake ba laifinsa bane, dik kunyar mutum ya zo wannan ɓangare sai dai ace mashi karuwan master room.

Banza da shi ta yi tamkar bata ji shi ba, ba wai kuma dan raini ko wani abin ba, sai dai bata da abin faɗe, ya goge mata hadda kaf. Cigaba ya yi da shafasu abinsa, yana raɗa masu wasu sexy word a kunne wanda bai bawa kowa damar jin abin da yake faɗa mata ɗin ba. Ai bata san time ɗin da ta natsu tsit ba, kukan nata ma da take yi sai daga baya ta nemesa ta rasa, bata san lokacin da ya gudu ba, kalaman mijinta ya ɗauke kukan ba tare da ta shiryawa hakan ba, cikin ƙanƙanin lokaci yasa ta saki jiki da shi, ta kwanta shiru a saman kirjinsa tana sauraron hot words ɗinsa, har ɗan sakin murmushi ta fara yi. Uhm maza, maza sai shirin Allah, yanzu dai har ya yi mata wayo ta yarda da shi, shikenan ya samu abin da yake so, da abar tasu ta motsa hankalinsa a kwai yana da in da zai rageta.


•••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A can gefe guda kuwa, tattabaru biyu suna can suna nasu aiki, sai rarrashi Jawad yake yi dan ya karya alkawari, ance mashi iya romance ya zarce har izuwa babban sashe, dan haka Jannawad dai taki yarda, muma team ɗinta ba zamu yarda ba, ai iya romance kawai muka ce, me ya kaisa ga babban sashe idan ba rashin alkawari ba? Chuchu kada ki yarda.

Bawan Allah ya ɗan ban tausayi, ya dukufa da girmansa da kimansa, da mutuncinsa a gari, kowa daraja shi yake yi sai ga shi ya kwantar da kai yana yi mata karamar murya, burinsa kawai ta ce ta yafe mashi, gaskiyar Jaish da ya ce Jawad ya gama jan mashi mutunci a kan titi ya yi yaga yaga da shi, shikenan fa yanzu Chuchu tasan abin da suke da shi, kai gaskiya Jaish kada ka yarda, idan ka yafe mu ƴan team naka bamu yafe ba, idan kuma ka raba wannan aure King ya tsine maka kabi bola babu ruwanmu, ko ya kuka ce my people's.......😅🥱

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥


A ɗayan ɓangaren kuma sai dirama suke bugawa, hakuri iya hakuri guyson ya bata a kan dan Allah kada ta sanar da momma abin da ya yi mata, dik izzar sarautar nan tasu har dukar mata da kansa ƙasa ya yi yana bata hakuri, amma taki fir ta ce dole ya buɗe mata kofa ta fita, shi kuma ya gargame ya ce sai ta yafe mashi.

Faɗi yake yi. "Dan Allah kada ki je ki faɗawa su momma, zan buɗe maki nawa rigar nima ki rama ba shikenan ba?". Ya faɗa yana kallan face ɗinta. Kallon uku saura kwata ta watsa mashi kafin ta amsa da. "To ni ce maka aka yi ƴar iska ce? Ni ina da mutumci kuma ina da karfi, ba sakaliya irin ka bace". Ta kai karshen maganar tare da murguɗa mashi baki.
Marairace mata murya ya yi tamkar zai yi kuka, ƙasa ya kara yi da murya sosai kafin ya ce. "Ni dai please don't let anybody to know kin ji? Ki yafe mun ba zan kara taɓawa ba"...... Tsalle ta yi ta dire kafin ta ce. "Okey dama kana da niyar sake taɓawa kenan ko?".

A hanzarce ya girgiza mata kai kamar wani yaronta, bawan Allah yanzu ma fa kuskure aka samu ya taɓa ɗin ba halinsa bane, ashe bala'i ya taɓowa kansa bai sani ba. Harara ta dallah mashi kafin ta fara zagaye shi tana binsa da kallon up and down. "Shekarunka nawa ne?". Ta faɗa tana dawowa ta gabansa, irin ita babban nan. ...... "19 to 20 haka". Ya bata amsa a sanyayye, shi dai damuwarsa kada ta faɗawa su Jaish, idan zata tsaya a iya faɗawa momma shikenan bashi da wata matsala, amma idan su Jaish suka ji me za su ce? Kuma wlh yasan idan ba lallaɓata ya yi ba kowa a cikin kingdom ɗin nan sai yasan ya taɓa mata kirji ta ja mashi raini har wajensu Omaid, to wai shi me ma ya kaisa ne?.

"19 to 20 years? Ashe ma baka wani fini sosai ba, amma ya aka yi ni jaruma ce kai kuma rago? Kenan girman banza ka yi?". (Allah mai iko🤔 wani abu sai Mahreeh, shekaru 7 fa ya bata amma wai bai wani fita ba saboda shegen san girma.)

Kai ya girgiza mata a karo na biyu. "Ni ba rago bane, kawai bana iya jure rashin lafiya ne, kuma ciwon nawa yana da tsanani sosai ba yadda kika zata ba, ban da ɓangaren ciwo babu wani abin da ba zan iya yinsa tamkar jarumi ba". Tun da ya fara magana idanunta a kan kyawawan roman lips ɗinsa irin na Auta........ "Kai ko lips ma baka da shi, ji bakinka kamar babu saboda ƙanƙata". Tana magana tana binsa da irin kallon da take yi wa su Abu a kauye.

Shiru ya yi dan bashi da abin faɗe, tun da ance bashi da baki ai dole ya yi shiru....... "Buɗe mun rigarka nima in taɓa shikenan sai in yafe maka". Ta faɗa tana kai kallanta ƙasa, ita kanta abin ya yi mata nauyin da ba zata iya haɗa ido da shi ba idan zata aiwatar da hakan, amma saboda tarihin rayuwarta bata yafiya yasa ba zata iya haƙura ba sai ta rama..... Shi kuwa, wani irin sanyi ya ji a ransa, ko ba komai zata rufa mashi asiri idan ta rama, dan haka a hanzarce ya ɓalle butiran rigar ya cire mata, kanta a ƙasa taki ɗagowa saboda iskanci ya cika ƙwaƙwalwarta, kai wlh Mahreen sai kun sakata a addu'a, ni kam Princess Teema ta fi karfina!.

Zare white singlet dake ciki ya yi, ya rage daga shi sai short, sannan ya ce mata. "To ga shi na cire maki ki rama". Tamkar zai yi kuka ya yi maganar. Slowly ta fara kallansa daga ƙasa tana haurawa sama. Ƴar ƙaniya sai da ta ji wani irin mummunar faɗuwar gaba, kirjinta ya bada bugun dum!!! Dum!!! Saboda kirjin nasa da ta gani, a tinaninta bashi da karfi, sai kuma ta kalli yana da murɗaɗɗen jiki, ta yi mamaki sosai, amma fa ta kasa iya yin sama da kallonta, a iya kirjinsa ta tsayar da idonta, dik rashin kunyarta ta ji shakkar haɗa ido da shi at this moment.

"Taɓa ki rama to". Ya sake faɗa idanunsa a kanta, ko kaɗan bai ji burgesa da take yi a da ya ragu a ransa ba, sai ma karuwa ya yi, yana mugun san confidence ɗinta da tsayawa a kan maganarta idan ta yi. Babu kunya ba tsoron Allah ta ɗago hannunta na ta kerma ta nufi kirjinsa da shi da nufin ta taɓa ita ma ta rama. The way tana matsar da hannunta garesa, the way hannunta yana tsananta kerma, amma dik da haka ta danne, ta nufesa. Ya zuba mata idanu kawai yana jiran ta aiwatar da nufinta ya mayar da kayansa.

Tana gab da taɓa shi sai ta dakata tare da fashe mashi da kuka mai ɗan sauti. Ɗan zaro idanunsa kaɗan ya yi, a rikice ya fara tambayarta lafiyarta kuwa? Me kuma ya sake samunta?. Kin kula shi ta yi, ta cigaba da kukanta. Matsawa kusa da ita sosai ya yi ya hau rarrashi, yarinya sai kace mai aljanu, shi yanzu to me ya yi mata da take kuka.

Yana can yana tinanin me ya yi mata sai jin voice ɗinta ya yi tana cewa. "Saboda kasan ba zan iya ramawa bane yasa ka ce in taɓa nima, wlh to Allah ya isana kuma ban yafe ba.........". Cikin ɗaga murya ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login