Showing 393001 words to 396000 words out of 403653 words
jikinta har zafi ya yi saboda wannan tinani da damuwa game da tashin hankali!.
Da yake tana da alkunya ita, sai ta ji ba zata iya faɗawa Smart abin da mahaifinsu ya aikata a baya ba, dik da cewa ta san yasan sarakuna wannan al'adarsu ce, so ba wani abin bane a wajensu, amma ta ji nauyin hakan matuƙa. Bata ma san Smart kam ya fita sanin komai ba!!.
Ita kuwa Mama sai ƙoƙarin banƙaɗo dalilin da zai sa ace Smart ba ɗan King bane take yi, dik ta damu kanta, ba yadda za'ayi ta ci burin ɗanta Ramish ya gaji karagar mulki za'a wani ce mata ga wani ɗan da zai gaji ubansa ba nata ɗan ba, gaskiya ba zata yarda ba!. Rashin sani ya fi dare duhu, Allah sarki har ta ban tausayi, ya zata ji a lokacin da za'a ce mata Ramish ba mallakinta bane?!!.
Mummyn Chuchu dai yanzu ta cire rai da mulki baiwar Allah, da farko tana sa rai, amma yanzu tin da bayan Ramish ga Smart shikenan sai ta hakura ta fawwalawa Allah lamuranta.
UNCLE ABBAS PART. Bakaramar rikici ake bugawa a tsakanin Mammie da Aliyah ba, dik kuma rikicin a kan King Zuhair ne, sun yi sunyi tsafinsu ya gagara kama shi, Aliyah ta yawace bokaye daban daban amma kowannensu amsa ɗaya yake bata shi King Zuhair ya fi karfinsu, ba zai tsafu ba, bama King kawai ba, ƴaƴansa gabaɗaya nan gani nan bari ɗumaman mayya, shiyasa kuka ga da suka yi niyyar tsoratar da guyson ya zage aljanar tas, to jinin Zuhair sun fi karfin wani sihiri ya taɓasu, shiyasa suka kasa cusawa Smart soyayya Sareena, saboda ya fi karfinsu.
A yanzu kwakkwaran shiri suke shiryawa mai zafin gaske wanda suka ɗaukarwa Queen Zarina alkawarin zasu salwantar da jinin mutum ɗaya daga cikin ƴaƴansu ko ƴan uwa domin ta yi masu bakin sihiri a kan jinin King Zuhair, to dama kun san ZARINA tana kullace da kingdom of power, aikuwa ta yi gaggawar aminta da wannan shiri, ta kuma rattaɓa alkawarin zata yi masu aiki, yanzu Mammie tana cikin zulumi da damuwa matuƙa a kan waye zata sadaukar da jininsa ga Zarina? Ba zata iya bada jinin Sareena ba, saboda sheɗancinsu ɗaya, Sareena tana bin abin da take so, kuma ƴaƴa biyu gareta, yanzu dole ta sadaukar da jinin Fanan muddin tana son cikar burinta!!! Uhm ana tashin hankali ba kaɗan ba a Kingdom ɗin nan.
Sareena kuwa tana can har da zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda uncle Abbas ya faɗa mata cewa ya bada aurenta ga Smart, sai murna take yi, har da wani cewa yanzu lokacin cin uban dik wanda ta gani a part ɗinsa ne, dan shi ɗin mallakinta ne ita kaɗai, sai tsantsara kwalliya take yi zata je wajensa, wai fa ba shi zai zo hira ba, ita zata je wajensa, dik da a tsorace take da shi, amma tana da kwarin gwiwa a kan yakininta, ta yi imanin ba'a jin daɗi sai an sha wahala, kuma ta yi imanin yanzu babu abin da zai yi mata tin da har ya karɓi aurenta hakan na nufin yana sonta, bata san cewa shi bai ma san wainar da ake toyawa ba!!.
Shi kuwa Kamran an kaisa part na baki, commander ya sanya tsaro a kansa sosai, sannan anbashi kulawa a matsayinsa na bakonsu, sun bashi abinci mai rai da lafiya, sun kuma tsaya mashi ya yi wanka ya canza tamkar ba shi ba, ya fito a ainahin yaron mammarsa, babu abin da yake ransa face tinanin Pretty, baya tinanin mammarsa kamar yadda yake tinaninta, saboda yasan mammarsa mace ce da zata iya tsayawa kanta a kowani hali, jaruma ce kuma sadaukiya, so Pretty kuma macece mai rauni da bata san kanta ba bare har ta san me duniya yake ciki, tinanin twins ne kawai a ransa, tsawon waɗan nan shekaru biyun bai taɓa yin minti biyu ba tare da ya tuna amanarsa kuma twin's ɗinsa ba, suna ransa tamkar yadda yake a ran Sweetie, kunga kullum tana tinaninsa, amma Pretty ko maganarsa bata yi, ko da yake ita yarinya ce da ba zaka taɓa iya gane cikinta ba, bata magana bare kasan ina ta dosa, waya sani ko tana tunasa bayyanawa ne kawai bata yi!
My people's, KAMRAN team, ina mai baku hakuri a kan abin da ya faru, kun san bana yin abu haka kawai sai da kwakkwarar dalili, na san kun ji zafin auren Pretty da Smart, amma nasan idan kuka ji dalilina da kanku zaku jinjina mun, tafiyar yanzu ta fara, kada ku manta yanzu muka gota tsakiya kaɗan, ina da dalilina mai karfi na yin hakan, amma kun kusa ji soon!! Ku yi wa KAMRAN fatan samun wacce zata kasance alkhairi a garesa, ba son rai'na bane nike raba masoyan nan, dalili yake sanyawa!! Amma kada ku damu a karshen page ɗin nan zan faranta rayukanku!......🙌💘
*CROWN OF JUSTICE*🔥🔥
Katafaren government house na ƙasar, zaune dattijo MUZAFFAR yake a saman wani dandatsetse kuma lallausan kushin mai bala'in tsada a cikin katafaren parlournsa, yana rike da wani littafin mai suna The Franklin scandal yana karantawa, yana cikin shigar manya-manyan malaman larabawa masu kima da mutumci, fuskarsa sanye da farar glass, ya sha rawani mai bala'in kyau na manyan malamai, farin balarabe ne tas wanda da ka gansa kasan mutumci da kima game da kyau haɗe da dukiya sun yi mubaya'a a wannan waje. Daga bakin kofa wasu zaƙwaƙuran securitys ne ke gadinsa, ya natsa cikin karatun da yake yi sai ji ya yi an yi mashi sallama.
Cikin sanyin murya ya amsa, murya mai cike da dattaku da kima. Wani security ne ya shigo cikin parlourn, with full respect ya ce. "Sir Prince Rishan ne yake neman iso"....... Gyara zamansa cikin natsuwa dattijo ya yi kafin ya ce. "Ka ce ya shigo"....... Sara mashi securityn ya yi alamar girmamawa kafin ya juya ya nufi waje. Yana fita bai fi five seconds ba sai ga Prince Rishan ya shigo cikin shigarsa ta alfarma irin ta ƴaƴan manya manyan sarakuna da ake ji da su. Zuba mashi idanun dattijo ya yi yana kallonsa har ya kariso, a saman kushin da yake zaune ya zauna, amma kafin ya zauna sai da ya duka kasa, dik wata sarauta ya ajiyeta a gefe ya tsugunna a gaban dattijo ya kwashi gaisuwa. Hannu dattijo yasa ya shafi lallusan gashin kansa kafin ya amsa gaisuwar.
Kusa da shi ya zauna, kallo ɗaya dattijo ya yi mashi ya gane cike yake da damuwa, dan haka sai ya rufe littafin dake hannunsa ya ajiye a gafe, sannan ya juyo da hankalinsa game da natsuwarsa a kan Prince Rishan. A natse ya ce. "My son akwai wata damuwa ne?".
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Papa akwai damuwa sosai ma, amma papa please meyasa baka san faɗa mun gaskiyar lamari a kan waɗan nan mutane biyu?". (Ude and Zarina yake magana) Dogon ajiyar zuciya Papa ya sauke kafin ya ce. "Rishan tono gaskiyar babu abin da zai kareka face bakinciki, koma menene ya rigada ya wuce, ka bar maganar, yanzu ina Rishma?".
Ciki ciki ya amsa da tana gida, da alama ransa bai so amsar Papa ba sam. Wai menene gaskiyar da Rishan yake son sani?. Batu ne a kan mutuwar babansa wanda yake zargin kashe shi aka yi, dan shi bai samu damar ganin gawarsa ba, a lokacin da abin ya faru baya nan, kuma zarginsa gaskiya ya ce, dan familyn Thomas ne suka kashe shi, wato familyn Zarina kenan, ita ta yi poisoning na King Ranveer da hannunta, poison ɗin kuma daga hannun mahaifinta Thomas ya fito, so ita ta kashe sirikin nata, domin kawai Ude ya karɓi mulki ita kuma ta kwace, burinta kuwa ya cika, sai dai ta bar baya da kura, domin kuwa Papa ya san komai, ta so rufe mashi baki amma abin ya ci tura, shi kuma Papa yanzu abin da yasa baya son bayyana gaskiya saboda Rishan shi kaɗai ne, ba zai iya yaki da su ba, zasu cutar da shi ne kawai, dik da suna bala'in shakkarsa da tsoronsa, amma aka ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, Papa yana ganin kamar zasu iya cutar da Rishan and Rishma, shiyasa ya ki faɗa masu gaskiya, har yau Rishan ya gagara samu natsuwa, zuciyarsa tana faɗa mashi lallai dole ya nemo waɗan da suka kashe babansa. Kun san meyasa na baku wannan tarihi? Saboda a gaba kaɗan zaku tsinci kanku a alaƙa da wannan tarihi, bana son ina gaba in dawo baya shiyasa na faɗa maku a nan kawai, dan a gaba ba ɗauko tarihin daga farko za'ayi ba, za'a ɗaura ne daga kan in da Rishan ya tsaya!.
And Papa yana zargin da sa hannun Ude a kashe King Ranveer, saboda bai yarda Zarina kawai ta kaddamar da wannan aikin ba!. Lallaɓa Rishan Papa ya rinƙa yi har ya hakura ya daure ya sake suka sha hira da Papa ya mance da batun su Zarina, sai dai a karshe da ya tashi tafiya ya ce da Papa. "Papa zan kashe Ude tin da yaki komawa musulunci, kuma kasan hukuncin wanda ya yi ridda!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa zai fita.
Miƙewa tsaye Papa ya yi, sai da ya gyara alkyabbar jikinsa, sannan ya gyara glass ɗinsa kafin ya ce. "Kada ka yi saurin yanke hukunci Rishan, ka kara mashi lokaci zuwa nan da ko ƴan watanni ne, idan babu haske sai mu san hukuncin da zamu yi mashi, koba komai yayanku ne".
Kun san me my people's, wlh ba dan Rishan baya shiri da su Zarina baya taimaka masu ba, tabbas da babu wanda zai iya cinsu da yaki, saboda shi ɗin namiji ne kuma jarumi ne, tamkar yadda kingdom of power suke da commander Zafar, haka jarumtarsa yake, tsab Rishan zai iya kayar da commander, saboda commander Zafar ya tsufa, shi kuma sabon jini ne, amma Zarina saboda rashin wayo insert of ta kallaɓasa ya zama mai tsaya masu wai take faɗa da shi, ko da yake shi ma ba zai yarda ba, dan ya tsaneta tin kafin Ude ya aureta, tun yana yaro ya tsaneta sosai!.
Jinjina kai ya yi tare da cewa. "A kullum kai kake dakatar da ni Papa, kuma In Sha Allah ba zan taɓa gajiya da bin umarninka ba". Ɗan kara sakin fuska Papa ya yi haɗe da cewa. "ALLAH ya yi maka albarka Rishan, In Sha ALLAH kana cikin kariyar UBANGIJI babu abin da zai sameka, sannan zaka kasance cikin farinciki, na gode kuma na yi murna da har yau baka cireni a matsayin uba da ka ɗaukeni tin King Ranveer yana raye ba, ALLAH ya albarkaci rayuwarku, ka kula da Rishma sosai, ka tsaya da taka tsantsan".
Amin ya amsa da shi tare da juyawa zai fita, har ya kai bakin kofa sai kuma ya juyo, ya yi mamakin ganin yadda Papa yake yawan kallonsa a kullum idan ya zo zai tafi. "Papa meyasa kake yawan cewa in kula da Rishma da kai'na?". Ya jefa tambayar cike da sa ran zai samu amsar da yake so, dan abin na damunsa ta yadda ko a waya ya kira Papa sai ya ce mashi ya tsananta kula sosai, abin ya fara ɗaure mashi kai.
Murmushi irin na manya Papa ya yi dik dan ya kwantar mashi da hankali kafin ya ce. "Babu komai, kawai ina so ne in tabbatar da amanar da King Ranveer ya bani na rike amanar sosai, dan haka ka kula, ba zan gaji da faɗa ba, dan amanace ku a gareni!!". Shiru ya yi tare da juyawa ya cigaba da tafiya, ko kaɗan bai gamsu da amsar Papa ba, ya dai yi shirun ne kawai, kuma hakance, Papa na ɓoye mashi gagarumin gaskiyar da yakamata ace ya sani, amma Papa ya dubi abin ta wata fuska ta daban shiyasa ya ɓoye!.
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥
Bayan wani lokaci.
Zaune Auta take a saman bed ɗinta ta yi shiru tana tinanin rayuwa, wasa wasa yau ta shafi almost 3 month ba tare da Hoorain ko jin sautin muryarsa ba, abin har ya fara zame mata jiki, yanzu ta fara yarda da Hoorain baya duniya, Leesharh tana bedroom ɗinta tana wanka, guyson ya koma kingdom of power saboda an buɗe school, dole ya koma.
Ramish baya nan ya fita, a yanzu ya yi nasarar capke mutane kaso 60 cikin ɗari na masu nikaf, sai dai dik wanda ya kama sun ki faɗa mashi wanenen mai turosu, ya azabtar da su har ya gaji, amma sun ki faɗa, sun ce su haya killers ne, idan sun karɓi contract ko kashesu za'ayi alkawari suke ɗauka basa taɓa tona asirin wanda ya sanyasu aiki, sannan su idan suka karɓi aiki fa ko mutum me zai yi sai sun kashe shi, ko duniya dikka zai basu idan sun karɓi aiki a kansa sai sun ƙaddamar.
Ba karamun ɓacin rai Ramish ya ji ba, ya sanar da Smart ga abin da yake faru, Smart ya ce mashi kada ya damu ya kashesu gabaɗaya a rage mugun iri a cikin al'umma, kuma idan ya kashesu kada ya sake saka hannunsa a neman wanda ya sakasu, ya bar mashi aikin dan matsalar daga cikin gida ta samo asali, wanda ya sakasu yana cikin kingdom of power, su kansu basu san ainahin wanda ya sakasu ba, dan haka ya bar binciken shi zai kama koma wanenen a nan, saura kaɗan ya tattara dik wasu hojjijinsa ya tinkaresu gadan gadan! Wannan ne ma dalilin zamansa a kingdom of power bai koma Paris ba, shi ne kuka ga ya yi shiru kamar babu abin da yake yi, uhm babban ɓarna yake yi masu ta karkashin kasa ba tare da sun sani ba,. BALA'IN CAN, WANDA YA SANYASU KUMA YANA KINGDOM OF POWER?! HOW TO?! KUMA WHO?. UHM AKWAI ABUBUWA FA!!.
Ba kara mun shocked Ramish ya ji ba a lokacin da ya ji abin da yayan nasa ya ce, ya so ya faɗa mashi wani abin da zai kwantar mashi da hankali yasa ya ji sanyi a ransa, amma ina sai ma kara mashi zafin da ya yi ta hanyar cewa kada ya kuskura ya sake zuwa gidan King Badeen, dan baya son kowa ya zargi wani abin, sannan shi Smart ɗin a zuwansa wancan karon da ya kawo Auta basu yi rabuwar daɗi da kakan nasa ba, ya yi masu tas bai ragawa kowa ba, ya kuma ce masu in dai kannensa basu auri waɗan da suke so ba to su ce shi ba jinin King Zuhair bane!!! Har da ce masu ya yi ya yi masu alkawarin Zunaira zata rayu ne kawai da abin sonta, ba zata zauna da Abdussalam ba! Sannan kuma Ramish ma yana da wacce yake so, kuma bare ce, yaga wanda zai hanasu zama ma'aurata tun da su babu abin da suka iya sai son kai, to shi kuma zai gwada masu a cikin Rahilarh ya haifu, ba su yi rabuwar daɗi ba dai, dan King Badeen ya nuna kafewarsa a kan babu auren bare a cikin zuri'arsa, dik gida zasu dawo su yi aure, har da cewa shi ma Smart ɗin ya dawo gida ya zaɓi mata! Shi kuwa ya ce zai gwada masu shi ɗan yau ne. DA ALAMA SHIYASA YA AURI PRETTY DAN YA GWADA MASU SHI MA YA AURI BARE, KAI SMART ƊAN DUNIYA NE WLH!!
Wannan dalilin yasa ya ce wa Ramish ɗin kada ya kuskura ya je gidan King Badeen, dan yana zuwa zasu kama shi su yi mashi auren gida ne tin da Smart ya ce yana da bare wacce yake so, sannan yasa Ramish ɗin ya cire sim ɗinsa ya ajiye a ƙasa, yanzu yakin ya koma na cikin gida, bari a saita na cikin gida tukun nan, dama kun san idan kana son yin gyara to ka faro daga cikin gida, a nan ne zaka iya cin nasara, amma idan ka faro daga waje, kana gyara a cikin gida ana warware maka komai!.
To kun ji abin da ya faru a zuwan Smart gidan kakan nasu, a lokacin Momma tana gidan uncle Rahab abin ya faru, da ta dawo baban nata bai sanar da ita ga abin da yake faruwa ba, sai ya kira King Zuhair ya sanar mashi, nan King Zuhair yake sanar da shi cewa shi ma Smart bai barsa ba, ya fi karfinsa, abin da yagadama kawai yaron nan yake yi, nan fa ran King Badeen ya kara ɓaci ya kira uncle Muhammad wato daddyn Smart na Paris, dan shi kaɗai kawai a duniya Smart yake jin maganarsa bayan Momma.
Sosai King Badeen ya yi wa uncle Muhammad faɗa a kan irin tarbiyar da ya bawa Smart, yaro kwata kwata baya ganin girman manya, sannan baya da tsoro, dik wata barazana a banza!. Hakuri uncle Muhammad ya shiga bashi kafin ya ce bari ya kira Smart ɗin. Da ya kirasa sai dai a maimakon ya yi mashi faɗa sai ya ce. "Son me kaje kake yi wa tsoffin nan ka tunzurasu har haka ne? Daddynka ya kirani last week, yau kuma kakanku ya kirani, ka je kana goda masu iko ko? Kasan fa su sarauta ne, babu mai nuna iko a gabansu".
Kai tsaye ya amsa da. "Daddy tsoffin ne basa a kan hanyar da ta dace shiyasa nike mayar da su kan hanya, kasan ba zan yi abu mara kyau ba ai ko my lovely dad?". Kamar mai shagwaɓa haka ya yi maganar, ALLAH ya gani yana kaunar daddynsa over.
Murmushi daddyn nasa ya yi. "That's my son, nasan gyara kake yi shiyasa ma da daddynka ya kirani ban kiraka ba, dik yadda aka yi nasan basu aikata dai'dai, cigaba da dawo da su kan hanya my son, zan yi alfahari da kai, amma ka yi sauri ka dawo ka ji? Ina kewarka over"...... Da okey kawai ya amsa tare da cewa i love you dad, love you too shi ma ya ce, daga haka suka yi sallama. NA CE YANZU KUN GANE MAI KARA SANGARTAR DA SMART KO? KUN JI UNCLE MUHAMMAD WAI YA CIGABA DA DAWO DA SU HANYA, KAI WATO ALLAH KA BARMU DA IYAYENMU!!.
---------------------------------------🔥🔥🔥
Baki a ɗauke da sallama dattijuwar nan