Showing 318001 words to 321000 words out of 403653 words

Chapter 107 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

75

kwari ta nufo bakin bed ɗinta da hijabin a jikinta, yau ko lunch bata yi ba saboda damuwa a kansa. Dik halin da take ciki kuma sarai yana sane, dan ya dasa mata Camera a cikin ɗakin, haƙiƙa ya ji babu daɗin kin yi lunch da ta yi, amma ya danne ya cigaba da harkokinsa.

Tana zama a bakin bed ɗinta sai ga dattijuwan ta kawo mata abincinta kamar yadda ta saba, haɗaɗɗen abinci mai rai da lafiya, sai tashin kamshi yake yi, tsohuwar ce mai girka mata. Sosai ta yi mamakin ganin lunch da ta kawo Leesharh bata ko taɓa shi ba, kamar yadda ta ajiye babu abin da ya motsa shi daga wajen, amma kasancewar Ramish ya ce ko word ɗaya kada ta yarda ya haɗata da Leesharh ɗin yasa bata tambayeta meyasa bata yi lunch ba? Sai kawai ta kwashi kayan abincin ta wuce ta fita bayan ta ajiye mata dinner ɗinta kenan. Dogon tsaki Leesharh ta ja bayan fitar tsohuwar, sannan ta dallawa kayan abincin harara tamkar su suka yi mata laifi. A dai'dai lokacin da take wannan abin sai da ta so sanya Ramish murmushi, saboda yana kallanta, dan dai bai iya murmushin bane da yau sai ya yi. A ransa ya ce ko me dinner ɗin ya yi mata take harararsa kuma? Yarinya sai faɗar bala'i!.

A fili kuwa cigaba ya yi da feshe jikinsa da daddaɗar perfume ɗinsa, yana shirye cikin kayan barci, kwanciya zai yi idan ya je ya bata drugs ɗinta ya dawo. Ita kuwa, gyrawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike da tinaninsa, tana jin tamkar ta tashi ya je bedroom ɗinsa ta sanyasa a idanunta ko zata ji sanyi. Amma girman kanta da rike amanar Sharifat yasa ba zata iya ba, a haka ta daure ta lumshe idanunta alamar barci take san yi, ba zata ci dinner ɗin ba kenan. Da kwanciyarta bai fi five minutes ba sai ga shi ya shigo bedroom ɗin bakinsa ɗauke da sallama ƙasa ƙasa. A hanzarce ta miƙe zaune idanunta a kansa, shi kuwa ya ɗaure angry face ɗinsa sosai, yana tafiya cikin natsuwa. Kai tsaye gaban bed ɗin ya nufo, bai ko kalli in da take ba ya hau ɓalle drugs ɗinta yana miƙa mata a kan ta karɓa ta sha.

Ƙin karɓa ta yi ta tsare shi da kallo, ya san me take yi wa dan haka sai ya zuba drugs ɗin a saman wani small plate dake wajen, sannan ya ɗauko ruwa ya buɗe mata bakinsa, ya ajiye mata su ready kafin ya juya ya nufi hanyar fita abinsa, wato idan ta ga dama ta sha, in kuma bata yi niyya ba sai ta barshi ko ohonsa, ai jikinta ne zai gaya mata. Anya ba dan ma babynsa yasa yake damuwa da ita ba kuwa?. To mu je dai zuwa.

Ganin fita zai yi yasa ta yi gaggawar miƙewa tsaye, muryarta na rawa ta ce. "Yah Ramish dan Allah ka tsaya ina san yin magana da kai". A tsorace ta yi maganar, dan tana fargabar abin da zai iya faruwa a tsayawarsa ko buɗar bakinsa. Tamkar ba da shi ta yi magana ba, ya cigaba da tafiyarsa. Ai a miliyan ta watsa da gudu ta tare gabansa, har sai da ya ji wani irin shock jin yadda ta yi gudun, ya ɗan ji fargabar kada ta faɗi. Meyasa ya damu da ita haka? Meyasa kuma yake kula da ita har haka? Meyasa baya san wani abin ya taɓata ko kaɗan ne? Akwai ayar tambaya fa a lamarinsa!.

Ƙara ɗaure fuska sosai ya yi, ya haɗe gerar sama da ƙasa, kwata kwata yaki yarda ya kalleta, with harsh voice ya ce. "Bani hanya in wuce!"....... Marairace fuska sosai ta yi, tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Ramish dan Allah ka yi hakuri, na san na yi kuskure, amma na tuba ba zan sake ba!"........ Ƙara daure angry face ɗin ya yi, murya a kausashe ya ce. "Kuskure?! Da wani abin ya same ki shi ma zaki kirasa da kuskure ne?! Kin san risk da kika gefa kanki damu bakiɗaya a ciki kuwa? Kin san yadda ake farautar rayuwarki kuwa? Kin san halin da kike ciki kuwa? Kin san matsayin lafiyarki a wajena kuwa?!".

Tin da ya fara magana idanunta a kansa, bata taɓa ganin ya yi magana cikin zafa har haka ba, hasalima baya ɗaga murya a magana sai yau, da alama ta yi babban kuskure ne ba karama ba.
"Ka yi hakuri, wlh ba zan sake ba ko da sunan wasa?" Cikin marairacewa sosai ta yi maganar. Nisawa ya ɗan yi, yadda ta marairace murya tasa ya ji wani irin a cikin ransa. "Shin kin san mutanen da suka biyoki daga fitarki har izuwa in da kika je kuwa? Kin san rayuwarki tana gab da zuwa karshe a lokacin da muka isa gareki kuwa? Ko kin ɗauka na damu ne saboda ciwon da kika jama kanki na ruwa da ya dakeki?". Ya kai karshen maganar tare da kai hannu ya damkar rigar jikinsa, karfi yasa wajen tsaga rigar gida biyu, jifa ya yi da ita gefe tare da sanya hannun nasa ya yi mata nuni wide chest ɗinsa da gabaɗaya yankar wuka ne a wajen, sai dai ya sha treatment sosai, almost yanka 4 masu zurfi ne a wajen, ga ɗaya a saman shoulder ɗinsa wajen damatsan hannunsa. "Diba abin da kika ja mun, ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu wani maganar ake yi a kanki ba wannan ba, kin yi zatan saboda abin da ya faru a tsakaninmu ne yasa na ɗaukeki daga gidan uncle? To idan ma haka kike zata kin yaudari kanki, ina san ki san cewa a gidan uncle rayuwarki cike take da barazana, ko kin yi zatan ban san attacking ɗinki da aka yi a ɗakinku daren ranar bane? Dik ina sane da komai, that's the reason why na ɗauke ki daga gidan, amma dik baki yi tinanin komai ba kika sa kafa kika fita". Cikin ƙunan rai ya yi maganar!. Ta bashi haushi sosai!!

Wani irin zaro idanu ta yi a lokacin da ta ga yankar dake jikinsa, ta tsorata sosai, ashe yana kan gaskiya fushin da yake yi da ita, ashe ta tabka babban kuskure na fita da ta yi ba tare da izininsa ba, yanzu ta ja mashi ciwo, ta kuma ja dole ya canza masu gida, ta ja mashi abubuwa da daman da bai bayyana mata ba, ciki har da rasa abokin aikinsa da ya yi, sun kashesa, sun zo harbinza da bindiga ba tare da saninsa bane babban yaron nasa ya tare masa, harbin ta same shi Allah ya yi mashi cikawa, dik a bayanta da suka bi, da ita za'a kashe Allah yasa bai ajiyeta ƙara zube ba, dik motsinta yana sane da shi, lokacin da ta fita daga gidan watch dake hannunsa ta buga mashi alarm na an buɗe gate na gidan, Allah yasa bai yi nisa ba shi ne ya juyo ya dawo, dan in baku manta ba yana fita ba'afi da 10 mins ba ta fita ita ba, so bai yi nisa da ita ba, da yana nesa ma ai da ta jima da mutuwa. Shi da farko ma bai yi zatan ita ce ta fita ba, ya yi zatan ko wasu ne suka shiga cikin gidan, sai da ya juyo ya dawo, can ya hangota a hanya tana tafiya!.

Lokacin da ya biyo bayanta ya so ɗaukarta tin time da ta fita arearsu, amma sai ya lura da wata black car dake biye da ita a baya, hakan yasa ya kira babban yaronsa da ya zo da wata mota mai tinted su bi wannan mota. Mutanen dake bibiyarta sun cigaba da binta suna san ta matsa daga idanun mutane su ɗauketa su aiwatar da nufinsu a kanta, shi ma kuma ya cigaba da binsu dan ya kamasu, abin da yasa bai yi gaggawar bayyana ya kamasu ba shi ne dan bai san su nawa bane, watakila bayan wannan mota akwai wani a ɓoye bai sani ba, hakan yasa suka cigaba da binsu da taƙa tsantsan. Lokacin da ta fita daga cikin mutane sai suka yi ƙoƙari kamata, amma sai suka ga kamar asirinsu zai iya tonuwa, wannan dalilin yasa sai suka yi yunƙurin harbinta daga ɗan nesa da ita kenan, a zuwan idan suka harbeta sai su gudu kawai, Allah yasa Ramish ɗin ya fita shi da yaronsa suka tinkaresu, a nan suka yi wannan faɗa har suka jijji mashi ciwo, suna tsaka da faɗar ne ɗaya ya zari gun zai harbi Ramish kenan babban yaronsa ya tare suka fasa mashi ƙwaƙwalwa, haƙiƙa Ramish ya ji zafin mutuwan yaron nasa, saboda sun haura sama da shekaru 7 suna a tare, sun saba kaman ƴan uwa.

Waiwaye adon tafiya🔥

Ina ranar da suka je wajen cin abinci a tare da shi har aka yi ta yi masu hotuna? Waɗan nan hotuna su suka baza media har masu nikaf suka san in da suke, a take suka tura mutane suka biyo bayansu, a nan ne suka rinƙa bibiyarsu har suka ga arear da suke, shi ne suka cigaba da gadin fitowar Leesharh ita kaɗai, sai a wannan lokaci Allah ya basu dama, to kun ji a ta yadda suka yi suka san in da suke har suka bi bayanta.

Ta shiga tsananin tashin hankalin da yasa gabaɗaya ilahirin jikinta ya fara kerma..... "Yah Ramish ka yi hakuri, kwata kwata ban kawowa rai'na akwai abin da zai iya faruwa dani dan na fita ba, ina mai baka hakuri kuma ina mai jajanta maka a kan rashin da ka yi". Tana magana idanunta suna ciccikowa da kwallah, haƙiƙa ta ji babu daɗi matuka a kan abin da ya faru, hannunta na kerma tana san taɓa ciwon nasa ta kara bashi hakuri, dik ta bi ta ruɗe kamar wata zararriya. Kan kace me hawaye sun fara zarya a saman face ɗinta, jikinta dik ya yi la'asariyar jemage. Yana tsaye tamkar wanda aka sassaƙa, bai sake ce mata komai ba. Hannunta na rawa sosai kamar wadda aka sanyawa lantarki, cikin tsananin damuwa ta ɗaura a saman wide chest ɗinsa, hawayen face ɗinta suna tsananta gudu matuƙa.

Sai da ya ji wani irin shock a jikinsa jin yadda ta taɓa shi. Slowly ta ɗago da kallanta a kansa, while shi ma ita yake kallo. "Sannu ka ji? Ni na tsani kaina, ban san meyasa a koda yaushe nike aikata irin waɗan nan abubuwa ba, kwata kwata bana amfani da ƙwaƙwalwarta da tinanina, kullum sai na aikata abin da zan zo ina danasani, na shiga uku na, wai menene yake bibiyar rayuwata haka ne? Shin na yi wa wani laifi ne? Wani zunubi na aikata?". In out of control take surutan nata, tana magana tana kara tsananta kukanta...... Lokacin guda tsananin tausayinta ya mamaye zuciyarsa, hannu yasa ya riko hannunta dake saman kirjinsa, muryarsa a ɗan sarke ya ce. "Ya isa haka, komai da ya faru ya rigada ya wuce, je ki yi dinner ki sha magani sai ki kwanta ko?".

Kai ta fara girgiza mashi tana wani irin kuka irin wanda zuciyar mutum yake a kusa ɗin nan.. "i can't eat anything Yah Ramish, na tabka babban kuskure, ni ban san menene ma ya shiga kai'na ba, ni mahaukaciya ce kawai wanda bata da tinanin kanta, kullum cikin jefaka a cikin masifa nike, na tsani kai'na". ..... "Aesh! Stop saying all this, ke yarinyar kirkice mai zuciyar zinari, dik abin da kike aikatawa rashin samun ishasshen ilimi ne da kuma ƙarancin shekaru ga rashin natsuwa da kwanciyar hankali, amma tabbas ke yarinyar kirkice, ke ɗin jaruma ce, ba kowace mace zata iya kwatanta abubuwan da kika yi ba, cikin mata dubu da wuya a samu goma da zasu iya abin da kika yi, mahaifinki fa suka kama, amma dik da haka kin jure kin ce ba zaki yi masu aiki ba, Allah zai kula da babanki, In Sha Allah babu abin da zai same shi, zai dawo gareki cikin aminci". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar.......... "A'a Yah Ramish, ni mahaukaciya ce kawai, kuma zan tabbata a haka tin da bana tinani da ƙwaƙwalwata". Tana magana tana girgiza kai, tamkar wadda ta zauce, ta fita a hayyacinta sosai!.

Ya lura da ta ruɗe dayawa, dan haka sai ya jata a jikinsa tare da ɗaukarta suka koma bakin bed ɗin, cikin sigar rarrashi ya rinƙa lallaɓata har ya samu ya shawo kanta ta natsu, da kansa ya janyo mata dinner ɗin ya ce ta ci, bata musa mashi ba ta fara ci kamar yadda ya buƙata. Binta da kallo ya yi yana jin wani irin yanayi a tattare da shi har ta kammala cin abincin, ta ci sosai saboda tana jin yunwa matuƙa, and tin da ta fara cin abincin kanta a ƙasa, taki yarda su sake haɗa idanu. Bayan ta kammala ya bata magani ta sha, sannan ya umarceta da ta kwanta sai da safe. Ba musu ta kwanta, ya rufa mata bargo kafin ya miƙe ya nufi waje. Har ya kai tsakiyar bedroom ɗin ya tsinkayo voice ɗinta tana faɗin. "Yah Ramish forgive me please, i made a big mistake that word can't explain, na tuba ba zan sake ba".

Ba tare da ya juyo in da take ba ya jinjina mata kai da to, sannan ya ce. "Have a wonderful sleep and sweet dreams". Yana gama faɗa ya yi waje da sauri. Shiru ta kwanta tana tinanin irin balai'n da ta rinƙa jefasa a ciki, yakamata a yanzu ta tsaya mashi ne, ta taimaka mashi dan ya kama waɗan da suke farautar rayuwarsa. Da wannan tinani a ranta barci ɓarawo ya saceta sai sauke ajiyar zuciya take yi.
In short a cikin kwanaki biyu sun samu fahimtar juna da jituwa, sai dai dikkansu sun ɗan ja baya da juna, shi saboda abubuwa ne da suka yi mashi yawa, ita kuma saboda kare amanar Sharifat, dan ta ji a ranta kamar ta fara jinsa a cikin zuciyarta, shi ne sai ta ja baya da shi, tana gudun abin da zai rinƙa haɗasu waje guda, wannan tsohuwa dake kawo mata abinci ita ta cigaba da kula da ita, ko parlour bata fita, kullun tana ƙunshe a cikin bedroom tana kallo, wani lokaci ta yi karatun Alkur'ani mai girma. Wannan kenan a Dubai, bari mu leƙa KINGDOM OF POWER kuma mu ga me yake wakana.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥
52

Zama mai matuƙar muhimmanci yau King yake gabatarwa tare da dikka wakilan fada ta dattawa a cikin zauren majalisar tattaunawar cikin fada, yau magana ce ta musamman wanda hakan yasa suka haɗu a zauren Majalisar tattaunawa dake cikin wajen. Sannan yana da manyan baki daga kasar Iceland, ya saukesu a masaukin baki na cikin fada, suna cikin meeting sai sun kammala zai saurari bakin nasa.

A cikin zaman da suka yi ɗin sun tattauna batutuwa masu muhimmanci sosai da abin da zai kara ciyar da mulkinsu gaba, abin da zai kawar da dik wani abin da zai kawo masu tangarɗa or tseko, sannan suka tattauna batu a kan zalincin da Queen Zarina take yi wa jama'arta, nan ma suka tsayar da matsayan yakarta su kasheta kawai a halin yanzu kowa ya huta, sai a canza tsarin mulkin masarautar tata izuwa ta addinin musulunci. Batu kan Spender ma ya ratso ta cikin tattaunawar nasu, sannan batu a kan cin amana ma ya ratso, saboda harta manyan wakilan fada ɗin ma yanzu King ya fara zarga, bcos yana mamakin yadda za'ayi su yi magana a tsakaninsu kuma ace Zarina ta samu labari, abin yana bashi mamaki, yanzu ya fara yarda da zancen Ramish na ce wa kada ya yarda da kowa har su uncle Abbas ɗin ma, dan haka ba komai ya tattauna da wakilan fada ɗin ba, ya bar wasu batutuwa a ransa da nufin zai yi shawara da Smart and Ramish.

A cikin wannan zama dai Aunty MieMie tana ciki, sannan Akka ma ta halacci zaman a matsayinta na Queen mother, yana da kyau Momma ta halatta ita ma, saboda ita ce ainahin sarauniya, matar da sarki ya fi so ya fi ji da ita ita ce babbar Queen ba wai uwargida ko ta tsakiya or amarya ba, babbar Queen yana ta'allaka ne a kan yadda sarki yake santa, ya kuma aminta da ita. So a matsayin momma na babbar Queen ya ci ace anyi wannan zaman da ita, amma King ya ce a'a baya da buƙatar hakan, saboda bala'in kishi irin nasa, yana daga cikin dokikin da ya zartar a kan kingdom ɗin, wato hana matansa fita, hana su zuwa fada, hanasu zuwa dik wani taron meeting.

A wannan zama dai King ya sakowa su commander Zafar zancen auren Auta, har da commander a taran, dan ya warware sosai, shi kansa Hoorain ya warware har an sallamesu, yana room ɗinsa yana karasa jinya manne da waya a kunne yana bayin ruwa wa flowernsa.

Wani irin faɗuwar gaba commander ya ji a lokacin da ya ji batun auren, amma sai ya danne, domin ya nunawa King ne Hoorain ya rabu da auta, a zahiri kuma ni da ku mun san ya kasa iya tinkarar Hoorain da batun su rabu ɗin, so ya barsu suna cigaba da soyayyarsu, ya shararawa King karyar sun rabu, to yanzu ga shi King ya zo da babban al'amari mai girma, wato auren auta. Shiru ya yi yana tina lion ɗinsa, Allah sarki maraya bawan Allah.

Shi kuwa King cigaba ya yi da cewa. "Jibi za'a ɗaura auren, abin ya zo ne ba shiri cikin gaggawa, dan haka a tsananta tsaro

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login