Showing 372001 words to 375000 words out of 403653 words
wajenta abinsa, kafin ya je wajen momma sau ɗaya ya je wajenta sau uku, kun san zuciya bata da ƙashi, sai momma ta fara danasanin kai mashi su da ta yi, tana ganin kamar ya fi son mom ɗin tasa a kan ita da ta haifesa, bata san ba haka bane, shaƙuwa ce kawai, kada ku manta tun yana jajiriri fa, mom ɗinsa ita ta yi mashi komai, kunga kuwa dole ya fi shaƙuwa da ita, momma fa time to time take zuwa wajensa, a shekara sau ɗaya take zuwa idan ta samu damar zuwa Dubai gaisuwar azumi, kunga kuwa dole ya fi shaƙuwa da mom ɗinsa, amma batu na so da kauna ai baya haɗa momma da kowa, it kaɗai ce babu ta biyunta!!.
Zaune suke a parlourn momma, da momma da mom ɗin nasa suna hira, nan momma take cewa mom ta yi wa ɗan nata magana ya yi aure mata. Murmushi mom ta yi kafin ta ce. "Ai baya son yi, ta kyalesa sai time da ya yi ra'ayi, ga shi nan Heleena tana can tana haukar sonsa amma yaki kulata".
Jim momma ta ɗan yi, dan tasan Heleena da ake magana a kai, sai bata ce komai ba, dan kada ta ce wani abu mom ta ce bata son familynta.
A can gefe kuma King ya gama sanar da uncle Abbas cewa yana nemanwa Smart auren Sareena, dan sun dace, uncle Abbas kuma ya ce Allah ya basu zaman lafiya, wato ya bashi kenan, uhm yau ake yinta. SAREENA ZAƁIN KING GA SMART, HELEENA ZAƁIN MOM ƊINSA, PRETTY ZAƁIN MOMMA, wa kuke tinani zata zama zaɓin Smart kuma?........
Suna tsaka da hiran sai ga Sareena ta shigo cikin part ɗin, tana san ganin Smart ɗin ne, ta jima tana san ganinsa bata samu dama ba, shi ne ta daure ta zo part ɗin momma ko yana ciki, tana tsoron zuwa room ɗina. Yau dai tana sanye da abaya har ƙasa, sai dai da alama shegen shigar tata ta yi daga ta ciki.
A saman carpet ta zauna tare da ɗagawa su momma gaisuwa kamar wata ta Allah. Fuska ba ya bo ba fallasa momma ta amsa. Shiru ta yi tana tinanin me zata ce ne ta samu bayani a kan Smart, shin yana gidan ne ma ko baya nan, ta ƙosa ta ji. A daidai wannan lokaci mama Haulat ta shigo ɗauke da abincin Smart cikin wani luxury tray na alfarma.
Duba time momma ta yi, karfe 8:30 na dare, kallon mama Haulat ɗin ta yi. "Lokacin cin abincin nasa ma ya yi, bari mutuniyar tasa ta zo ta kai mashi"....... A saman table mama Haulat ta ajiye abincin tare da juyawa ta nufi waje. Jiki na ɓari Sareena ta ce. "Momma abincin Yah Omerish ne?". Kai Momma ta gyaɗa mata alamar e. A hanzarce ta miƙe, jiki na ɓari ta ce. "To bari in kai mashi momma". Oh ta samu dalilin zuwa in da yake!.
"A'a Sareena, Omerish bai aminta da kowa ya kai mashi abinci ba face Pretty, ko su Jaish ya ce baya so, ita kaɗai ya yardanwa, kuma kin san dokace ma ta wannan gidan ba kowa yake kaiwa Prince abinci ba sai wanda ya naɗa da kansa kuma ya amincewa". HAKIKA DOKARSU CE HAKA, BAMA ABINCI BA, BABU WANDA YA ISA ZUWA KUSA DA SMART A MATSAYINSA NA PRINCE MAGAJIN MULKI IDAN BA WANDA SHI DA KANSA YA YARDANWA BA KUMA KO ABINCIN DA ZAI CI SAI AN TANTACETA SOSAI, KO ITA PRETTY DA YA AMINTA TA RINƘA KAI MASHI ABINCI BA TA ISA TA KAI ABINCIN KAI TSAYE BA, DAGA KITCHEN SAI AN TANTACE KOMAI TSAB AN TABBATAR BABU WANI ABIN CUTARWA SANNAN TA WUCE TA KAI MASHI.
Shi da kansa ya ce wa momma bayan Pretty bai yarda da kowa ya taɓa abincinsa da sunan zai kawo mashi ba, yana jin daɗin cin abinci da ita shiyasa ya ce ita zata rinƙa kawo mashi, saboda su ci a tare, kun san Pretty da shiririta da sakalci, idan suna cin abinci tana sanya shi nishaɗi da har ya ci abinci sosai ba tare da ya sani ba, yana mugu mugun son kasancewa a tare da ita, sai ta kai karfe 1 na dare a ɗakinsa, yana aikin bincikensa a kan familynsa, ita kuma tana zuba mashi shirme tana bashi nishaɗi, wani lokaci sai ta yi barci a bedroom ɗin nasa, sai ya kammala abin da yake yi zai mayar da ita nata ɗakin, a tare suke kwana da Mahreen a part na momma, to nan yake kaita idan ya tashi kwanciya barci.
Da momma ta ce to ya auri Pretty ɗin mana kawai sai abin ya fi bada armashi, sai cewa ya yi shi bai ce yana sonta ba ai, kawai dai yana jin daɗin kasancewa da ita ne, tana ɗebe mashi kewar Zunaira tana kuma saka shi nishaɗi.
My people's anya kuwa kun yarda da Smart? Wai tana saka shi nishaɗi! Ina team ɗin Pretty, kada ku yarda zai lallata maku ɗiya, in ba iskanci ba ka aureta ɗin mana, zaka wani ce nishaɗi take baka!.
Wani irin ɗaure fuska Sareena ta yi, ranta ne ya yi maki, kamar zata sake yin magana sai kuma ta yi shiru, ta zauna tana jin tamkar ta haɗiyi zuciyarta......... Tsabar sakalci irin na Pretty ko sallama bata yi ba ta afko cikin parlourn, tana sanye da sleeping dress white color, riga ne da wando dogo, ta saki gashin nan har baya, Momma ta yi ta yi da ita ta rinƙa ɗaura ɗankwali amma yarinyar nan taki fir. Tana turo baki ta zo ta zauna kusa da momma, sarkin son jiki har da kwantowa a jikinta tana shagwaɓe fuska. Momma tasan halinta sai cewa ta yi. "Yunwa kike ji ko?".
Kamar zata yi kuka ta amsa da e yunwa take ji!. "To ai ga abincin yayan naku, tashi ki je ki kai mashi sai kuci kamar da kuka saba". Cewar momma.. ita dai mom da bata jin larabci sai binsu da ido kawai take yi bata san me aka faɗa ba. Jin momma ta ce ta tashi ya ɗauki abincin Smart ne yasa Sareena ta gane e lallai wannan ita ce Pretty da ake ta magana, binta da kallo ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, saboda tsantsar madarar kyau da ta kallah, tasan babu abin da zata gwadawa Pretty sai rashin kunya wanda bata san cewa shi ma Pretty number ɗaya bace, sai dai idan ba'a zo ɓangaren ba!.
Ziciyarta ne ya cigaba da kara ƙawata mata kyan Pretty, tinani ta fara yi a kan me zata yi mata ta rabata da Smart, ya zamana ma ko inuwarsa ba zata sake gani ba, bama ta san wacece Pretty ko yar wacece ba, ita dai tin da ta ganta a part ɗin momma sai ta zaci ko daga cikin ƴan uwan momma na Dubai take!. Tana can tana tinane tinane bata san lokacin da Pretty ta ɗauki abincin Smart ta fita abinta ba, sai waigawa ta yi taga babu abincin kuma babu ita ma Prettyn. Siririn tsaki ta ja wanda ta manta a gaban momma take.
Miƙewa ta yi ta nufi waje, a cikin ranta tana faɗin lallata kyan Pretty kawai zata yi shi ne mafitarta, zata ɓata mata fuska kaca kaca ya yi damage ta yadda kowa zai ji kyamarta. Tana fita ta nufi part ɗinsu Omaid dan su shirya wannan mugunta a tare, dan ta rantse ba zata bar Pretty ba.
Ita kuwa Pretty kai tsaye ta wuce bedroom ɗinsa, babu ko sallama ta afka ciki abinta, yana zaune a saman bed ɗinsa sanye da sleeping dress kalar na jikinta sak, dama shi ya saya mata tin a France, so su uku suka yi ankonsu, shi da ita da Auta, yana rike da wayarsa suna chat da Ramish yana jin ya lafiyar Auta a yanzu. Ta wutsiyar ido ya kalleta, tin ɗazun tinaninta ne a ransa, yana tina yadda zata kare da azumi gobe, anya zata iya yi kuwa? Bata fa shiri da yunwa, ga shi gaskiya girma ya fara zuwa, kirjinta sun cicciko, period kawai ya rage ta fara yi, dole ma ai ta yi azumi, sai dai za'a sha fama kam, bala'i tab zai fi kowa fama da ita, dan daga shi sai momma take jin maganarsu. Tin ɗazun yake ta tinanin mafita a kan azumin.
Ajiye masu abincin ta yi a saman carpet ta nufo shi, a gefen bed ɗin ta zauna tana tura baki.
"Bana ce ki rinƙa yin sallama ba? Kuma bana ce idan kin zo ki rinƙa gaishe ni ba?". Ya gefa mata tambayar yana cigaba da katsa wayansa.
Unexpected ta faɗo jikinsa tare da sanya mashi kuka tana faɗin. "Yah Omerish wai mama Haulat ta ce gobe za'a fara azumi babu ni babu cin abinci sai dare?". Tana kukan kuma dan iyashege tana tura hannunta a cikin rigarsa ta kasa, so take ta taɓa cibiyarsa, wai ita da yake yi wa faɗa a kan saka ɗankwali da yin sallama, shi ne ta kwanta a jikinsa take yi mashi wannan sakalci da iyashegen, Pretty sai shirin Allah wlh, dama abin da take ta yi wa kuncin rai kenan, shi ne taki faɗawa momma ta zo tana juyeshi a nan, dan tasan ya fi kowa biye mata a gidan!
My people's me kuke tinani idan Sareena ta zubawa Pretty acid a fuska? Dan dai kun san su Omaid zasu bata goyan baya, uhm
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
58
Tsaye yake cikin arabs jallabiya milk color, ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana aikin kai komo a cikin bedroom ɗinsa, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin tsananin tashin hankali gane da ciwo, tamkar ba King ɗinmu ba, ya rame matuƙa, ya yi wani irin haske sosai, sai idanu kwala kwala farare tas zaka gani, gabaɗaya a dabaybaye yake da damuwa.
Tsayawa ya yi a gaban windown room ɗinsa dake fuskantar harabar family part, kalaman Smart ne kawai suke yi mashi yawo a ransa, ta wani ɓangare na zuciyarsa kuma rashin Zunaira, ta ko'ina ba sauki, babban abin da ya fi ɗaga mashi hankali shi ne kamar yadda Smart ya ce sai ya faɗa mashi uwar Ramish, to abin tashin hankalin a nan ne shi ne allura ce take shirin tono jibgegiyar garma mai girman gaske, domin kuwa ba faɗar uwar Ramish ɗin ne matsala ba, matslar shi ne ya aka yi ya baiwa mama Ramish a matsayin ɗanta ita kuma bata san ba nata bane? Wannan shi ne ainahin tashin hankali da yake ciki, dan tono yadda aka yi ya bata Ramish babban bala'i ne ga gabaɗaya kingdom ɗin wanda sai ta shafi kowa da kowa, idan Smart ɗin ma bai yi hankali ba zata zama sanadiyar mutuwarsa ko na mommarsa or guyson, dama shi guyson a kan hanya yake, taimakon Allah yasa bai mutu ba yake fama da ciwon ciki mai zuwa dik shekara kenan, wannan ba karamar bala'i bace, gara ma sanin me yake a tsakaninsa da matar commander a kan wancan bala'i na Ramish, siririn da a ka rufe tsawon shekaru 30 amma Smart ko daga ina ya jiyo sirrin har ya bankaɗo shi?. WANNAN SMART SAI DAI SHIRIN ALLAH, YA TAYARWA DA DATTIJO HANKALI YA BARSA CIKIN CIWO DA AZABA!!
Haƙiƙa King ya shiga tashin hankalin da bai san ranar fita ba. Batu a kan maman Hoorain wato matar commander wannan tabbas suna da alaƙa, kai tin ba yau ba, tin kafin King ya yi aure suke tare, bari in maku tarihin, sun sha soyayya nakin karawa, saboda matar commander uwarta baturiya ce ubanta balarabe, shiyasa ta fita daban a masarautar, sai dai kuma tana matsayin baiwarsu, King Zuhair ya kamu da sonta sosai, yadda kuka ga Auta ta so Hoorain, haka suma suka so juna, sai dai kash, King Abdul Malik ya ce ko mutuwa King yake yi ba zai taɓa aurar baiwa ba, ya haramta masu mallakan juna, wannan dalilin yasa suka kasance a tare a bayan fage, suka rinƙa sheke ayarsu har King Abdul Malik ya fitar mashi da mata, wato da Mummyn Chuchu da Mamansu Aneesa, bai yi gardama dik da cewa baya sonsu ba, dan shi ai yana tare da wacce yake so a ɓoye.
Aka aura mashi su, ya cigaba da kasancewa da matar commander har ita ma ta yi aure, tsantsar soyayyar da suke yi wa junansu yasa suka gagara rabuwa dik da suka yi aure, haka suka cigaba da rayuwa har shigowar momma rayuwarsa a wani zuwa Dubai da ya yi, already Mummyn Chuchu and maman Aneesa ba zaɓinsa bane, shiyasa kuka ga ya fin san momma sama da su, dan ita ce zaɓinsa ta biyu bayan maman Hoorain. Maman Hoorain da suka yi aure ba'a cikin kingdom of power suke zaune da commander ba, amma dik da haka suna da wajen da suka ware wanda suke haɗuwa ita da King dan holewarsu.
A takaice lokacin da ya auri momma ta fahimci yana daga cikin sarakuna masu tarewa da kuyangunsu, shiyasa ta yi ƙoƙarin canzasa, kuma ta yi nasara, dan ta canzasa a lokacin da bai taɓa zata ba, a lokacin momma har ta haifi Jaish, lokacin ita kuma matar commander ta haifi Hoorain bai wuci 2 years ba a duniya, a ranar da za'a haifi Hoorain anyi gagarumin yakin da a ranar ne aka kashe King Abdul Malik, lokacin da maman Hoorain da maman Aneesa suna naƙuda, ranar anyi tashin hankali sosai. Bayan komai ya lafa aka yi jana'izar King Abdul Malik kamar yadda yake a dokar sarauta, daga nan King Zuhair ya karɓi karagar mulki, momma ta yi nasarar raba shi da matar commander, tin daga lokacin kuma ya tuba ya zama adalin sarki mai mulki tsakani da Allah, sai dai matsalar da aka sake samu a ɗan gaba kaɗan kafin matar commander ta ɓata da kuma bayan ta ɓata, wannan matsala lokacin da zaku san shi bai ba, dan wannan matsala shi ne yake da alaƙa da Ramish da kuma yaudarar mama da King ya yi, WANNAN SHI NE GASKIYAR ABIN DA YAKE A TSAKANIN KING AND MATAR COMMANDER ZAFAR, TO YANZU A TSAKANIN KING DA COMMANDER WANENE AINAHIN UBAN MARIGAYI HOORAIN? KAM BALA'IN CAN!! UHM WANNAN CAKWAKIYA SAI SMART YA WARWARE MANA! DAN KO SHI KANSA KING ƊIN BAN JIN YANA DA TABBACIN HOORAIN ƊANSA NE KO NA COMMANDER, ITA KANTA MATAR COMMANDER ƊIN BANA JIN TASAN AINAHIN UBANSA, WANNAN SHI NE KWAMACALA. KU DAI MU CIGABA DA ZUWA, AI KWAMACALA MA TANA CAN GABA!!
Hege Smart ya jefa King da kansa a cikin zulumi da tashin hankali shi kuwa yana can yana more rayuwarsa da Pretty, sai nishaɗi suke yi, ga King ya ƙasa zaune ya kasa tsaye, wlh tin da kuka ga King ya girgiza a kan batun Ramish, ba shakka ba karamar ɓarna bace zata bayyana, babban bala'i Smart yake son jijjigo mana wanda gara kowani irin cakwakiyar a littafin nan a kan wannan, tabbas King Zuhair and King Abdul Malik sun bar baya da kura, abin sai shiru, sai lokaci ya nuna mana kawai!!. ZAN BAKU MAMAKI FA, DAMA SUNANANE QUEEN OF SURPRISE, KU YI FATAN BAYYANAR KAMRAN LAFIYA KU DAI!!
----------------------------------------------🔥🔥🔥
"Azumi fa akwai lada, idan kika yi zaki samu lada sosai, kuma waye ya ce maki ana wahala a azumi?". Ya yi tambayar yana ajiye wayarsa a gefe, sannan yasa hannu ya rungumota da kyau. Kai ta shiga girgiza mashi. "Ni ko akwai ladan tin da akwai yunwa bana so, ni ba zan yi ba". "Ɗago kanki ki kalleni". Ya faɗa yana tattare dark black curly hairnta da ya zubo ta gaba ya tufe mata fuska, tattare mata ya yi ya tara a baya, sannan ya riko haɓarta da hannunsa ɗaya yana kallan face ɗinta, dik ta yi jaga jaga da hawaye!.
"Idan kika yi azumi zuwa dare zan saya maki su chocolate dayawa". Sarkin son zaki, kowa ya san halinta sha zuma ce......... "Ni dai kawai idan zaka saya mun saboda Allah haka ka bani to, idan kuma sai na yi azumi ne na hakura ka riƙe kayanka". Ta faɗa tana ƙoƙarin sake fashewa da kuka. .......... "To ya isa haka, yanzu mu je mu ci abinci kafin mu yi batu a kan azumi........." Bai iya ƙarisa maganar ba ya dakata sakamakon wani irin shock da ya ji na saukar hannunta a saman mararsa, a fujaje ya waro idanunsa sosai a kanta, turo mashi baki ta yi, ita a tinaninta jiran amsarta yake yi, bata ɗauki taɓa mashi cibiya da take yi a wani abu ba, sai ta ce. "Ni fa koma me za'ayi ba zan yi azumin nan ba, dan ba zan zauna da yunwa ba". Tana magana tana sake turo baki.
Nisawa ya ɗan yi tare da rakwafo da kansa kaɗan a kanta, kamar mai san raɗa mata magana a kunne, cikin dabara ya haɗe fuskokinsu tare da capke lips ɗinta na ƙasa ya fara tsotsa. Zaro mashi idanu ta yi wanda sai da tasa ya kara jin tsikar jikinsa yana tashi, hannu bibbiyu tasa tana ƙoƙarin tureshi ya sakar mata baki, shi kuwa ya kara riketa da kyau, tirgewa ta fara yi tana mutsu mutsu zata kwace kanta, ina ai yaki bata dama sai da ya yi kissing ɗinta da kyau, sannan ya saketa tare da jingina kansa da jikin headboards na bed ɗin. Ita kuwa kuka ta saka tare da barin jikinsa, hannayenta bibbiyu tasa ta fara goge bakinta wai yasa mata datti kuma yawunsa babu daɗi dan babu zaƙi ita ga sha zuma, zaki kawai take martabawa.
Bilhakki da gaskiyarta take kuka tana ta dirza ɗan bakinta wai tana goge in da nasa ya taɓa mata, sai tufar da yawu take yi, waje ta nufa da gudu, sam bai ji fitarta ba. Kai tsaye ta wuce wajen momma, tana zuwa ta faɗa jikinta tare da sanya mata kuka mai sauti, har lokacin mom tana wajen suna a tare.