Showing 3001 words to 6000 words out of 403653 words
rami, hasken dake fitowa daga cikin sai da ta ɗan dishashe mashi gani, amma dik da haka bai girgiza ba.
.................Ba komai ya haifar da wannan haske ba face hannun Sweetie, da yake da magic ya turata cikin ramin so tana tafiya ne bisa sarrafawarsa, hakan ya haifar da tafiyar tata a hankali hankali take yinsa, lokacin da zai rufe ramin ta daina ganin komai ta faɗa cikin wuta da kifiyoyin nan sai ji ta yi hanunta ya sake a in da ta nuna bakin ramin da tafin hannun nata tana yin alamar Ronnie dake tsaye ya taimaketa kada ya bari ta faɗa cikin wannan bakin azaban.
Wannan nuna tafin hannun nata da ta yi shi ya haifar da wani irin hasken gaske da ya fito daga tsakiyar siraran jijiyoyin tafin hannun nata. Hasken kuma ya hana ramin komawa ya rufu.
Tashin sense, me kuke tunani? Kenan Sweetie ma tana da magic ne ko me?!!.
Zantukan babansa ne kawai suka dawo mashi cikin kunnuwansa a in da yake ce mashi. "Tabbas a duniyar neman Spender da zai yi zai haɗu da ƴar baiwa mai baiwa irin tasa, idan ya yi wasa ita ce zata zama ajalinsa, in kuma ya bi komai bisa tsari shi zai cinye game ɗin".
Tuna wannan magana yasa zuciyarsa ta aminta da tabbas Sweetie ce wannan ƴar baiwar, domin tun daga kan yadda ta kurawa idanunsa kallo babu tsoro daga nan ya ji a jikinsa tabbas tana da baiwar irin nasa, bai kara tabbatar da hakan ba sai yanzu.
A maimaikon ya yi amfani da dark magic ɗinsa ya kasheta kawai, sai ya fito da ita a cewarsa bai ga wani halitta da ya isa ya ja da shi har ma ya yi nasara a kansa ba, dan haka zai ƙaryata maganar babansa, a zuciyarsa ya raya zai barta a cikin empeir ɗin ya ga ta yadda za'ayi ta zama ajalinsa, yarinyar da bata wuce ya murkusheta bane zata zama ajalinsa? So Funny, wonder should never end in this world. A ganinsa kenan, ya raina baiwar Sweetie, amma ku me kuke gani my people's? Me kuke tunani? Dan ya karyata maganar babansa nacewa zata yi ajalinsa zai barta da ranta ya ga ta ya zata yi ajalin nasa!.
Abin da yake tunani kenan fa, dan haka sai ya fitar da ita daga cikin ramin, ya kuma mayar da ramin ya shafeta kamar bata taɓa bayyana a wajen ba, har wani kyalli tiles na wajen yake yi kamar babu wani magic da ya taɓa wanzuwa a nan, ya saki Ronnie dake sankare, ita ma ya sake mata gaɓɓanta.
Kamar walkiya haka ya koma saman swan chair ya zauna tare da ɗaura kafarsa ɗaya a saman chair ɗin, ɗayan kuma yana ƙasa, ya ɗaura hannunsa ɗaya saman laps ɗinsa.
Da ido ta bishi da kallo har sai da ya zauna, sannan ta dawo da kallonta a kan Ronnie da yake kare mata kallo, ya ga ta rame, amma kuma ta kara wani irin kyau na musamman.
"Ronnie wannan ne yayanka ko? He's so handsome sosai, kamar ba mutum ba, ka ga jikinsa kamar na Robbot ɗin nan da suke aiki a gidan nan, yanayin fatarsu iri ɗaya kamar madara".
Tana magana tana zaro idanu irin like wow ɗin nan, ga mamaki sosai a saman face ɗinta, she was so surprised.
Wato ita kwata kwata abin da ya faru da ita ma bai bata mamaki ba, bata wani tsorata ba, hasalima kyansa yasa bata ga azabar da yake gabanta wanda har ya yi niyar ɗanɗana mata ba.
Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke tare da ɗan lumshe idanunsa kaɗan ya sake warosu a kanta, ya ji matuƙar mamakinta sosai, ya jinjinawa karfin halinta da rashin tsoronta.
Kallonsa take yi tana jiran ya amsa mata wannan shi ne yayansa Black Tiger ko ba shi bane.
Jinjina mata kai ya yi haɗe da ce mata shi ne.
Wari irin kara zaro idanu waje sosai ta yi, she was so surprised na jin hakan, a hanzarce ta mayar da kallonta kan Black Tiger, babu ko tsoro ta ce.
"Gaskiya yana da kyau sosai, kaga ɗan bakinsa ɗan karami kamar na Prettyna, amma yana magana ne ko bayayi? Dan naga bakinsa ya yi karami sosai". A ruɗe take maganar.
Kamar Ronnie zai ɗan yi murmushi sai kuma ya fasa tare da cewa. "Amma baki ganin mirror ko?".
Kai ta jinjina mashi alamar e. Harɗe hannayensa a saman kirjinsa ya yi kafin ya ce. "To ai kamar bakinki ma ya fi na yaya ƙanƙanta, jeki ga mirror a ɗakin ki ki gani".
Ya ce ta je ta ga mirror ne dan yana son ta fita daga ɗakin kada Black heard ɗin Black Tiger ta motsa ya ce ya fasa yi mata afuwa ya gana mata wani azaban. Sai dai kash, ita da bata san da wani izaya ba ai gaban mirror dake cikin ɗakin nasa ta nufa domin ta duba face ɗin nata.
Sosai Black Tiger ya yi mamakinta, wai ita bata san tsoro bane? Wata ɓangare na zuciyarsa ce ta tuna mashi cewa irin baiwarsa ke gareta fa, dan haka babu tsoro a jininta. Tashin sense, wlh akwai kura kuwa, Sweetie like black Tiger e kam akwai matsala, a cikinsu waye kuke tunanin zai kure wani? Shin da gaske kamar yadda babansa ya faɗa mashi ita ce zata zama sanadiyyar kawo karshensa da shi da zalincinsa ne ko kuma dai shi zai iya karyata maganar babansa ta hanyar barinta a cikin kingdom ɗin kuma ya zamana ba zata iya yi mashi komai ba? Waye kuke tunanin nasa tunanin zai zama gaskiya, baban Black Tiger ne ko kuma shi Black Tiger ɗin?! Muje zuwa, akwai game mai zafi a gaba.
Tana isa dai'dai tsakiyar ɗakin in da yake tsaye ɗazun kenan da nufin ta nufi gaban mirrorsa ta duba kanta. Wani irin kara ne ya fito daga jikin mirror tasa tamkar karar shigowar sako.
Slowly ya ɗago sharp romance eyes ɗinsa kai tsaye sai saman mirror ɗin masa, while ita kuma Sweetie ta dakata daga nufar wajen.
A hanzarce Ronnie ya kariso in da take, jikinsa har kerma yake yi saboda tsorata, da karfi ya fisgi hannunta ya nufi waje da ita, tsoro yake kada bakar zuciyar yayan nasa ya motso kuma.
Kamar aljani haka Black Tiger ya ɓace ɓat daga in da yake zaune, ya fito a gaban mirrorsa, wato tsafi fa ba abin da bata sanya mutum ya yi, Allah dai yasa mufi karfin zuƙatanmu kawai, amma matsafi abin tsoro ne.
Zubawa mirror idanu ya yi yana kallo kamar Tv, wani irin tambatsetsen jirgi ne mai girman gaske yake landing a Black Tiger international airport dake cikin birnin na Black world, jirgi ne har jirgi, girmansa ya wuci tunaninku, yanayin tsarin jirgin sak yake kama da FR-55, sai dai shi kan jirgin sak fuskar bakar damisa, da alama wanna tana ɗaya daga cikin manya manyan jiragen da Black Tiger yake alfahari da su, dan tsarinta daban ne.
Kafin jirgin ta kammala sauka jikin tampatsetsan mirrorn nasa ya rabe kashi biyu, rabi yana cigaba da nuna mashi landing wanna jirgi, rabi kuma ya fara nuno mashi cikin forest in da wasu zaƙwaƙuran matasan warriors ɗinsa ke ta aikin haƙar ɗanyar gold, kai sai dai fa muce masha Allah, amma arzikin gold kam ba'a magana, Black Tiger yana da arzikin da ba'a taɓa yin mai irinsa a duniyar yanzu ba.
Dikkansu ya zuba masu idanu yana kallo har jirgin ta yi leading, wasu zaƙwaƙuran manya manyan Robbot ne suka fara kutsawa izuwa gaban jirgin, sai kuma wasu jiga jigan motoci masu ɗauke da sunan Black Tiger irin masu container a bayansun nan suka ɗan matso kusa da jirgin.
Wasu Robbot ɗin ne suka zo suka hau bubbuɗe bayan containers ɗin, empty suke babu komai a ciki.
Ana buɗe Fp na jirgin Robbot da suka matsa kusa da shi suka kutsa ciki. Wasu jiga jigan manya manyan caton masu ɗauke da hoton motoci a jikinsu waɗan nan Robbot ɗin suka fara fitowa da su daga cikin jirgin. Girman waɗan nan kwalaye sun wuci mutane su iya ɗauka sai dai Robbot ɗin. Yanzu fa kusan manya manyan ayyukan Black world dikka Robbot ne suke yi.
Wanna jirgi maƙare yake da kayan billions of dollars, gabaɗaya kayan kyara sabbin motoci masu rai da lafiya ne. INA MASU CEWA BLACK TIGER YANA BURGESU TA ƁANGAREN GYARA KASARSA DA TAIMAKAWA WAJEN GANIN YA KAWO DIK WASU SABBIN TSARE TSARE DA ZATA KAWO MASHI CIGABA? TO A NAN DAI KUN YI GASKIYA, BAKU FAƊI BA DAN KUN SO SHI TA NAN, DAN FA BA KARYA YANA IYA ƘOƘARINSA WAJEN GANIN YA GINA KASARSA, BURINSA SU FI KOWACE KASA CIGABA DA KOMAI DA KOMAI, MATSALARSA DAI WANNAN BAKAR ZUCIYAR TASA TA ZALINCI NE KAWAI, BAREMA RABA UWA DA ƳAƳA DA YAKE YI, ABIN AKWAI TAƁA ZUCIYA.
Kafataren companynsa na kyara motoci za'a kai waɗan nan kaya domin a fara haɗa motoci sabbi wanda babu irinsu a duniya, a kullun yana son yaga shi ya fara kirkiro abu in ya so daga baya saura ƙasashe su kwaikwayesa, wannan yasa ya yi dogon nazari kafin ya fito da tsarin motocin nasa.
A kallah containers sun kai 50 a wajen, amma sai da suka cika tab da kayan nan da Black Tiger aircraft ta ɗauko.
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke ganin dik abin da ya buƙata sun sauka lafiya, a hankali ya mayar da kallonsa a kan masu hakar gold, yadda yake kallonsu ya ɗan zare sharp eyes ɗin nan nasa sai ya baku tsoro, kamar ba idanun mutum ba, da alama magic eyes ɗinsa ya juyo ba na ainahin ba.
Wani daga cikin warriors dake hakar gold ɗin ne ya miƙe tsaye tare da ihu yana faɗin.
"Red gold, red gold!!".
Ɗan kara zaro idanun Black Tiger ya yi. "Red gold!". Ya maimaita kalmar.
Ga dikkan alamu ya ji daɗin samun red gold a karkashin kasan kasarsa da suka yi, red gold shi ne abu na biyu a tsada a duniya cikin Precious stones and mentals, yana da bala'in tsada fiye da tunaninku, ga balai'n daraja, ya fi normal gold tsada nesa ba kusa ba, samun wanna red gold ɗin a karkashin kasar birnin Black Tiger ba karamar nasara bace, a yanzu haka suna da dukiyar iya karawa da kowace kasa bare kuma ace sun kara samun arzikin red gold? Me kuke tunanin zai faru? Wani irin arziki kuke tunanin Black world ko in ce Black Tiger zai kara samu?. Duniya iya duniya wa Black Tiger fa my people's.
Sosai ya ji daɗin wanna karuwa da suka samu, sai dai babu ko ɗikon alamar canji daga face ɗinsa da zai sa ka fahimci ya ji daɗi, yana nan yadda yake kamar hadari.
A hankali ya juyar da idanunsa daga magic eyes izuwa ainahin sharp eyes ɗinsa. Kamar walkiya haka ya ƙarisa bakin wanna daular bed ɗin nasa duniya guda. Zama ya yi da alamar nazari ya shiga a kan yadda zai kara bunƙasa kasarsa, yadda zasu ci moriyar wannan red gold ɗin.
P-R-I-N-C-E-S-S T-E-E-M-A💘🔥
___________💘🔥______________
A bangaren Sweetie and Ronnie kuwa, yana jan ta bai dakata a ko'ina ba sai a room ɗinsa.
Suna shiga ya saki hannunta yana sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya sha da kyar, ko da yake kusan hakance da kyar suka sha.
Ita kuwa room ɗin nasa ta fara bi da kallo tana mamaki ganin kusan komai dake room na Black Tiger irinsa ne a nan, hakan na nufin Ronnie fa ɗan gata ne na karshen kasasheshe.
Ganin ba shi take kallo bane yasa ya miƙa hannu ya janyota ta faɗo jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Da sauri ta ɗago kai tana kallon face ɗinsa, while shi ma ita yake kallo babu ko kyaftawa, an jima ba'a haɗu ba, ya sha kewarta matuƙa.
"Ronnie meyasa baka je wannan ɗaki da yayankan nan ya ajiyeni ka dubani ba? Ka barni ni kaɗai sai wani mugun mutum da yake zuwa tambayata wai ina Spender? Idan ban gaya mashi ba sai ya yi ta azabtar da ni yana bani wahala, ranar har maciji ya saka mun........".
Ta dakata da yin maganar tana sauke numfashi tana ƙoƙarin fara kuka.
Bai iya ce mata ko uppan ba saboda har lokacin yana ganin kamar Black Tiger bai kyaleta bane, yana ganin kamar zai zo ya rabasu.
"Wani ɗaki wannan mugun ya kaini, ɗakin babu hanya kuma dik in da ka juya sai kaga kanka, (kewaye yake da mirror kenan) a wannan ɗaki ya sakani sai ya turo mun wani bakin maciji mugu, dik ta in da zan gudu sai in ga babu hanya sai dai hoton fuska zan gani, ga macijin shi kuma yasan hanyan sai ya yi ta bina, ina ta ihun sunanka kuma baka zo ba.............".
Tana kai karshen maganar ta fara ruwan hawaye masu ɗumi, wato kenan dama azabtar da ita Black Tiger ya rinƙa yi da ya ɗauketa, ya yi ta razanata, Allah sarki wlh razana tafi zahirin mugunta cutarwa da wahalar da zuciya, wani ma idan yana da karamar zuciya mutuwa zai yi idan aka razanar da shi, Allah gara a maka azaba direct a kan ayi ta razanaka da ababen ban tsoro. Wato Black Tiger ainahin bakin mugu ne da babi mix wlh, yasan sirrin mugunta da azabtarwa.
Hannu Ronnie ya kai ya fara goge mata kwallar dake idanunta ba tare da ya yi magana ba, saboda shi dai yasan Black Tiger baya yafiya, bai taɓa yafewa kowa ba a rayuwarsa, ya kware wajen yi wa mutane azaba da wuta, so sai yake ganin kamar zai zo ya raba shi da ita.
"Ronnie ka yi magana mana". Ta faɗa yanayin voice ɗinta a shagwaɓe sak na PRETTY yau kuma.
Jinjina mata kai ya yi, can kasan makoshinsa ya furta. "Zan yi magana Sweetie, amma ba yanzu ba, for now dai kyaleni ki yi shiru".
"To yunwa nike ji fa". Ta faɗa tana ɗan kwantar da kanta a wannan faffaɗar kirjin nasa na ƴan Wrestling ɗin.
Da sauri ya ɗago kansa haɗe da kallonsa a kanta.
"To hau saman bed ɗina ki zauna bari in kawo maki abincin ko?". Da kyar ya iya furta hakan.
Da okey ta amsa mashi tare da wucewa ta nufi saman luntsumemen bed ɗin nasa, har tsoron haurawa taji ya kamata, gani take kamar idan ta hau zata jita a sama.
Idanunsa a kanta, bai fita ba yana jiran ta haura bed ɗin sannan ya fice. Da yaga kamar ba zata iya hawa ba sai ya ce. "Ki hau babu abin da zai faru".
Da sauri ta juyo da idanunta a kansa, kai ya jinjina mata alamar tabbatarwa da babu abin da zai faru. Da sauri ta haye ta zauna, sai da ta ɗan lumshe idanunta ta sake buɗewa saboda daɗi da laushin mattress na bed ɗin, ga wani kamshi na musamman mai kwantar da hankali dake tashi a arear wajen.
Juyawa ya yi ya fice daga room ɗin, ita kuma ta fara bin ko'ina da kallo tana mamakin yadda komai yake a shirye tsab gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali, ga fitinannen kamshi mai sanya nutsuwa a zuciya, lallai yanzu ta yarda da zancen Floris da take ce mata Ronnie shi kaɗai ne kanin Black Tiger, kuma ɗan gata ne, a yanzu ta gasgata hakan matuƙa.
Shiru ta zauna tana sakawa da warwarewa a cikin kwakwalwarta har ya dawo cikin room ɗin hannunsa ɗauke da katon glass tray mai shake da kayan abinci tab a ciki, abubuwa kala kala wanda bata taɓa ganin makamantansu ba.
Saman glass center table dake tsakiyar wasu egg chair a can gefe ya ɗaura kayan abincin, a ɗakin Black Tiger swan sofa chairs ne, a ɗakin Ronnie kuwa egg chairs ne, sunanan kamar design na kwai ne a ka fafake cikinsu aka yi wajen zama, sun yi matuƙar tsaruwa sosai.
"Zo in baki ki ci sai ki yi wanka mu je ki rakani". Ya yi maganar yana kai kallonsa a kanta.
While ita ma shi take ta kallo, sai yanzu ta lura da ya rame kaɗan ya kuma kara hasken fata, kamar wanda ya jera kwanaki yana zazzaɓin dare.
"Ina Floris?".
Ta jefa mashi tambayar tana saukowa daga saman bed ɗin.
Sai a lokacin ya tuna yau bai haɗu da ita ba, ya je school ya rubuta last exams ɗinsa ya dawo, yana dawowa kuma wajen yayansa ya wuce domin ya gaya mashi ina Sweetie take, a kan haka suka samu matsala ya fita ɗakin a fusace, zaman da ya yi a cikin cineman part ɗin yasa ya samu sanyi a zuciyarsa da har yasa ya miƙe ya dawo wajen Black Tiger domin ya bashi hakuri sai ya sameta a ciki.
"Ya ka yi shiru baka bani amsa ba?".
Ta yi tambayar ne a kusa da shi, bai ga lokacin da ta sauka bed ɗin ba, saboda ya afaka duniyar tunani.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "I don't know where's she, amma nasan ba zai wuce she's in her room or Delisha room ba".
Yana kai karshen maganar ya miƙo mata hannunsa a kan ta kama.
Ba musu ta saka ƴan hannayenta saman tafukansa, har ga Allah tana jin daɗin kasancewa a tare da shi.
Kamata ya yi ya zaunar da ita saman lallausan duma dake shinfiɗe a wajen, sannan ya sauko mata da trayn haɗe da tambayarta me zata ci.
Zubawa abincin idanu ta yi tana kallonsu, bata ma san menene bane bare har ta