Showing 228001 words to 231000 words out of 403653 words

Chapter 77 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

18

bayansu da gudu.

Riketa sosai guyson ya yi yana ƙoƙarin kare mata kunamar. Obaid yana tsaye yana kallansu, a tinaninsa kunamar ba zata yi wa guyson komai ba tun da Mahreen ya sakarwa, sai dai bai ankara ba sai gani ya yi ɗaya ya sakewa guyson harbi a kafa, dai'dai lokacin kuma Omaid ya iso ɗin.

Azaban zafi yasa ya yi gaggawar saketa tare da tsugunnawa ƙasa yana ƙoƙarin riko kafar nasa. Ita kuwa yana saketa ta yanka a miliyan sai bedroom na momma.
Kusan a tare Omaid and Obaid ɗin suka zube gwiwowinsu a gaban guyson ɗin tare da kai hannunsu a kan kafar nasa, hankalinsu ne ya yi mummunar tashi, ga shi Jaish and Omerish suna gida, yau sun shiga uku, sun san idan brothers ɗin nasu suka samu labarin kunama suka saki ya cutar da guyson yau ba mai karɓarsu, dama Jaish ya jima da hanasu sake kunamar nan, amma basu dai'na ba.

Hankalinsu a tashe Obaid ya fara bawa guyson hakuri kamar zai yi kuka, Omaid kuma miƙewa ya yi tare da zura wayarsa a aljihun wandon sleeping dress ɗin jikinsa, sannan ya tattare karfinsa dikka ya ɗauki guyson cak, sai sorry suke ce mashi, kai tsaye cikin bedroom ɗin momma suka wuce da shi, tuni fuskarsa ta wanke da hawaye, rago a ciwo ba. Sosai yake kuka ga harbin kunama da balai'n zafi.

Abin mamaki, ko da suka shigo bedroom ɗin momma basu ga Mahreen ba, kuma tabbas nan ta shigo, sai dai ɓuya ta yi a wani wajen dan kada Obaid ya biyota ya kamata, ita bata wani damu da kunamar ya harbi guyson ba, ita dai ba ta samu ta tsira ba ai shikenan kuma.

Saman bed suka kwantar da guyson, a gaggauce Omaid ya fara ƙoƙarin cire mashi dafin kunamar, shi kuma Obaid ya ɗaura kan guyson ɗin a saman cinyarsa ya hau rarrashinsa yana goge mashi hawaye yana kara bashi hakuri da ya yafe mashi. Hankalinsu a tsananin tashe matuƙa.

Wlh Mahreen sai shirin Allah, haka kawai ta ja bawan Allah ya samu tsarabar harbin kunama, har wajen ya kumbura sosai, ita kuma ta gudu abinta, wlh idan aka bar Mahreen da su Obaid su kaɗai sun isa su tada kingdom ɗin nan, zasu tada zazzafar yaki wlh.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

SARINA.

Tana shiga parlon Jaish ta zare alkyabbar jikinta ta ajiye saman sofa, wai dan Smart ya kwaɗaitu da kyakkyawar surar jikinta...................... Yarinya, wai mu faɗa mata daga cikin masu jajayen kunnuwa masu yawo kusan tsirara ya fito ne ko dai mu yi shiru?.

Zuciyarta na shakkar tinkarar bedroom ɗin, amma burin da take da shi a kansa ya fi wannan yawa, san nan Mammienta ta kara mata kwarin gwiwa tare da ce mata yana shakar wannan kamshin perfume ɗin shikenan ba zai iya yi mata musu ba, dan haka sai ta ji ta kara samun kwarin gwiwar tinkarar bedroom ɗin tun da babu abin da zai yi mata.

A maimakon ta yi mashi sallama irin ta addinin musulunci ma sai ta wani kashe murya ta ce. Excuse me. Bata jira umarni ba ta turo kofar kawai ta shiga, tana ta faman yauki kamar hawainiya.

Tana sanya kanta cikin ɗakin ta ja birki a bakin kofar ta tsaya, lokaci guda cup ɗin hannunta ya suɓuce ya faɗi kasa ya tarwatse, gabaɗaya cappuccinon ya malale a ƙasa. A miliyan ta zaro idanunta gabaɗaya waje, tamkar zasu faɗo ƙasa, cikin wani irin karuwin murya ta ce. "Wow, handsome, gorgeous and sexy guy with sexy body". Babbar magana!!!.

Ba komai yasata yin wannan zabura da sambatun ba face Smart, kyakkyawa kuma kakkarfar surar jikinsa ya ruɗar da ita, ya fito daga wanka kenan yana sanye da bathrobe na Jaish a jikinsa, so bathrobe ɗin ta yi mashi gajere dan ya fi Jaish tsawo, bata gama rufe mashi cinyoyinsa ba, kun san mutumin da balai'n kyau, ga arab hairnsa a jike yana ɗigan ruwa, sajensa ta kara kwanciya luf, fuskarsa ta kara haske sosai, hakan yasa ya tashi kanta matuƙa.

Anya a jikokin Akka a mata ba Sarina bace ta yi gadon abar kuwa? Jarabar yarinyar nan dayawa yake.

Yana tsaye a gaban mirror yana shiryawa, Auta tana kwance a saman bed ɗinsa ta yi barci, shi kuma guyson ya tafi wajen momma tun ɗazun.

A hankali ya ɗago idanunsa ta cikin mirror ya yi mata kallo guda ya kawar da kallonsa, cigaba da abin da yake yi ya yi tamkar bai san da halittarta a wajen ba. Ganin hakan yasa zuciyarta ta saƙa mata ai ta matsa kusa da shi ya samu damar shakar kamshin perfume ɗin nata kafin ta cigaba da santin kyan jikinsa, har tinani take yi a ranta gata kwance a saman lion chest ɗinsa tana wasa da ɓul ɓul ɗin breast ɗinsa saboda jarababbiya ce ta karshe yarinyar nan.

Ta manta ma da batun ta ɓarnatar mashi da cappuccino, ta ɓata mashi ɗaki dan jaraba amma dik bata bi ta kai ba, cikin yanga ta fara taku tana jin faduwar gaba, amma haka ta daure ta isa gabansa.

A kusa da shi ta tsaya na ƴan sakanni, sai da zuciyarta ta tabbatar mata da ya shaki kamshin perfume ɗin, sannan ta kara matsawa kusa da shi, Sarina bata tsoro kuma bata da hankali my people's, ko da yake Mammienta ce ta ce mata in dai ya shaki kamshin shikenan ta yi mashi dik abin da take so bashi da bakin yin magana sai abin da ta ce kawai.

Dan haka tana ganin alamar ya shaka ta matsa dab da shi, yana ƙoƙarin zuba lotion a hannunsa dan ya shafa a jikinsa kawai sai ganin hannunta ya yi ta rike robar man, a tinaninta zai ɗago ya kalleta ne dan ta rike robar, sai taga akasin haka, bata san shi daban yake da kowa ba, ba komai yake ɓata idanunsa dan kalla ba.

"Yah Omerish ni yakamata in zuba maka man ka shafa ai, idan kana so ma ni zan iya shafa maka ai, tin da kai nawa ne". Cikin salon kirsa da kisisina ta yi maganar tana wani make murya kamar akuya mai jego.

Shiru bai yi kamar yasan da wata halitta a wajen ba, a ransa yana tinanin wai a cikin kannensa ne a ka samu fitsararriya mara kunya har haka? To me aikin Jaish kenan da bai gyarawa shegiya zama ba? Dama su Jaish haka kenan suka saki gidan kowa yana yin abin da ya ga dama basa cin kaniyarsu su gyara masu zama? Lallai da sake, dole ya sako tarbiya kuwa, dan ba zai ɗauki wannan iskanci ba, me banbancin kannen nasa da Heleena da ya ɗaurawa karar tsana kenan? Ai basu da wani banbanci, ya gyarawa Heleena da ba abin da suka haɗasu ma zama bare kannensa?

Kunsan da farko ita ma Heleena ta so ta kawo mashi iskanci ta rinƙa taɓa jikinsa, watarana kawai ya ware rana ɗaya ya ci uban hegiya daga lokacin ta haɗa malaman jikinta ta natsu, shiyasa kuka ga tana tsoronsa kamar ta mutu, bugu ta ci a hannunsa.

Yana tsaka da tinani unexpect ya ji saukar hannunta a saman hannunsa da yake rike da robar tana faɗin. "Yah Omerish bari ma kawai in murza maka man da kai'na". Tashin hankali, lallai Sarina ta wuce yadda ake tinani.

Sake mata robar ya yi ya zame hannunsa, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, a tinaninta aikin Mammienta ya ci, ta samu kan Smart, sai ta wani ji bargo mai sanyi ya lulluɓe zuciyarta. Kawo robar man kusa da ita ta yi, tana ƙoƙarin zuba man a hannunta da nufin ta murza mashi a jikinsa tana wani fari da ido unexpect ta ji lokaci guda ta dai'na gane komai, sai ta ji kamar bata duniya, irin mutum ya ji komai ya tsaya mashi cak, shi kansa robar man dake hannunta sai ganinsa ta yi a can tsakiyar ɗakin, wani irin jiri mai karfi ne ya ɗebeta ta tafi ta zube ƙasa.

Ba komai ya ja mata hakan na face wani irin mari da Smart ya ɗauketa da shi, tass kake ji, kunnuwanta gabaɗaya sun dai'na jin sautin komai.

Bai bari ta dawo cikin hayyacinta ba yasa kafa ya yi ball da ita sai da ta tafi ta bugu da jikin bango. Daga nan ta ƙarisa dai'na gane komai gabaɗaya. Taku biyu ya yi ya isa in da take, hannunta da ta sanya a saman nasa lokaci da ta karɓi robar man ya take da kafarsa, ga shi in da ya taka ɗin ta wajen kashi ne, hakan yasa ta ji wani irin azaba ya ziyarceta.

Da karfi ta kurma wani irin ihu mai sautin gaske, ɗauke kafarsa daga kan hannunta ya yi ya take bakinta da take yi mashi ihu da kafar tasa, take bakin nata ya fashe sai jini. Belt ya ɗauko daga dressing room na ɗakin, yadda kuka san wanda yake jibgar katan gardin namiji haka ya fara saukar mata belt ɗin nan a jiki.

Ihu ta fara kurmawa mai sautin gaske, ko a jikinsa tamkar wanda aka saukarwa da wahayin duka haka ya yi mata lilis har sai da ya ji zuciyarsa ta ɗan samu natsuwa, sannan ya dakata da dukan nata, dik ya fashe mata jiki, ga shi ba kayan mutunci bane a jikinta bare su ɗan saukaka mata zafin belt ɗin, ga belt ɗin da kauri, ta zanu ba karya.

Ga shi Jaish baya part ɗin bare su ji ihunta su kawo mata agaji, yana can hospital shi da Mahnoor, shiyasa Sarina ta daku babu wanda ya kawo kata agaji. Ihunta ya tashi Auta daga barcin da ya ɗauketa. A tsorace ta miƙe zaune a saman bed ɗin. Ganin zane Sarina yake yi yasa Auta ta fara ruwan hawaye.

Yau Sarina sai da ta kira ainahin sunan Mammiensu na yanka saboda jibgar da ta sha. Bakin bed Smart ya koma ya zauna, cikin kakkausar murya ya daka mata tsawa a kan ta tashi ta zo gabansa. Ai tuni tsawansa yasa ta dawo cikin hayyacinta, dan muryarsa a kaifafe take. Wai a haka ma Smart fa bai ɗauki zafi ba, ransa bai ɓaci ba, da ransa ya ɓaci ai sai dai wata ba Sarina ba, ace a cikin kannensa a samu mai irin halinsu Heleena kuma yana raye? Tab wlh dik sai ya gyara masu zama kafin ya bar kingdom of power.

Sam ta kasa iya miƙewa da kafafunta, da jan jiki a kasa ta iso gabansa, sai kerma jikinta yake yi, bakinta ya kumbura suntum saboda take ta da ya yi, gabaɗaya singalalin hannunta sun yi ruɗu ruɗu da belt ɗin, abin ku da farar fata, tini jikinta ya zama jajir kamar jan gauda.

A gabansa ta ƙariso tana kuka ƙasa kasa. Ko kallon in da take bai yi ba ya umarceta da ta yi mashi kneel down ta ɗaga hannunta sama, daga nan har wayen gari ba zata bar wajen ba, in kuma ta yi koda motsi ne sai ya kakkaryata, daga karshe ta rufe mashi baki tsit baya san ya ji komai ƙanƙantar sauti ya fita daga gareta.

Yau dai Sarina ta faɗa koma. Wayarsa ya ɗauko domin ya kira Jaish ya zo ya faɗa mashi wanenen uban Sarina a cikin familynsu? Dan a cewarsa uban nata ma yana da buƙatar a gyara mashi tarbiyarsa, dan bashi da tarbiya shi ma, saboda idan yana da tarbiya a cewarsa da zai bawa Sarina tarbiya yadda yakamata, dan haka daga ita har ubanta yau zai gyara masu zama, irinsu ne ke ɓatawa larabawa suna...... Tashin hankali, lallai Smart ya dame su King ya iskancin, kam bala'i uncle Abbas zai bawa tarbiya lallai akwai cakwakiya.

A lokacin da ya kira Jaish wayar tana cikin mota shi kuma yana cikin hospital ya je kiran nurses, so bai yi picking ba. Jefar da wayar a gefensa ya yi tare da miƙewa ya shiga dressing room domin ya shirya ya zo ya kwanta, sai lokacin da Jaish ya kirasa zai iya sanin hukuncin da zai yi wa Sarina, dan yanzu wannan duka da kneel down ɗin dik ba hununci bane, ta dai yi ne zuwa yasan ubanta sai ya san kalar hukuncin da ya dace da su.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Da kyar Jaish ya iya driving suka isa hospital ɗin, ko da ya kashe motar sai da ya ɗauko good 5 mins a zaune shiru ita kuma tana kwance a jikinsa, sannan ya buɗe kofar motar a hankali, kafafunsa ya fara zurowa wajen da ita a jikinsa ya fito, da hannunsa ɗaya ya tura kofar motar ya nufi hospital ɗin.

Har zai shiga sai ya lura da yanayin kayan jikinta, to kun san su da kishi ko da ba matansu ba bare matansu, hakan yasa ya fasa shiga ya juyo da ita, cikin motar ya mayar da ita tare da fita ya nufi cikin hospital ɗin shi kaɗai yana wani lumshe idanu yana kame jikinsa wajen guda, da kyar ma yake tafiyar.

A dai'dai wannan lokacin ne call ɗin Smart ya shigo wayarsa, Mahnoor tana ganin call ɗin har ya katse, shi kuwa nurses mata guda biyu ya je ya taho da su a kan su zo su dubata a ciki.

Suna isa wajen motan babban Dr ya biyo bayansu yana kwala kiran sunan Prince Jaish, dakatawa Jaish ya yi domin su gaisa, su kuma nurse ɗin ya ce su shiga su dubata a ciki.

Gaisawa suka yi da Dr, cikin girmamawa dr ya ce meyasa bai kirasu a waya sun zo gida sun dubata ba ya fito a cikin daren nan. Ɗan jinjina kai ya yi kafin ya ce babu komai su tara next time, daga haka ya ce wa Dr ya je kawai.

So shi kansa Dr ya sansu da kishi, dan ko Auta ce bata da lafiya Jaish baya bari namiji ya dubata sai dai bace, dan haka dik da Dr bai san wacece bace sai ya juya ya koma ciki, a tinaninsa ma Auta ce. Dr na tafiya ya koma cikin mota ya zauna yana jin tamkar ba shi ba, wani zazzafar abar ce ma take sake taso mashi, kamar ba lafiya ba.

Shiru ya ɗan jingina kansa da jikin kujerar motar yana jin mararsa tana ɗan murɗa mashi a hankali hankali, ba komai ya ja hakan ba kuma face jarabar tasa. Yana jin nurses ɗin suka yi mata dik tambayoyin da yakamata kafin su fita su je su kawo mata magungunan da suka dace, sannan suka yi masu sallama.

Kuɗi ya ɗebo a cikin motar tasa ya miƙa masu ba tare da yasan adadin da ya ɗeba ba. Godiya suka yi mashi suka juya suka bar wajen. Tamkar jira yake yi su tafi, suna barin wajen ya janyota jikinsa yana jan numfashi a hankali hankali. Ajiyar zuciya ta sauke tare da saƙalo wuyarsa, can ƙasa ta ce. "Yah Jaish mu koma gida, dare ya yi ina tsoro".

Jinjina mata kai kawai ya yi, sannan ya kunna motar yana ɗan shafa bayanta da hannunsa ɗaya. A hankali yake driving yana cigaba da shafa bayanta har suka isa gida. A yanzu ma ɗaukarta ya yi kamar yadda ya ɗaukota a farko suka fito. Tsabar yana cikin wani yanayi ko wayarsa bai ɗauka ba bare ya duba ko an kirasa, a cikin motar ya bar wayar suka nufi ciki.

Ni kuwa na ce tab yau Sarina ta shiga uku, ga shi call ɗin Jaish Smart yake jira kafin ya yanke mata hukunci, lallai yau zata kwana a durkushe a saman gwiwowinta, waye ya gaya mata kowa ake yi wa iskanci a tsira, uncle Abbas ma ta ja mashi za'a sake yi mashi tarbiya......... 🥱😅

Jaish bai sauke matar tasa a ko'ina ba sai a saman bed ɗinsu. Da kyar ya iya ƙarisawa da ita saman bed ɗin ma, sannan kwanta a gefenta yana sauke numfashi a hankali hankali.

Hannunsa yasa ya laluɓi remote daga cikin drawer kusa da bed ɗin, wutar ɗakin ya kashe kafin ya juyo gareta. Tin ma bai gama juyowa ba ta matsa ta shige jikinsa, ita ma dai tsabar tana san kasancewa da shi a cikin mota ta baro maganin nata, ta shige jikinsa tana tura hannunta saman kansa.

A hankali ya ɗaura hanunsa a saman mararta, can ƙasan maƙoshinsa da murya kamar wanda yake cikin maye ya ce. "Ya cikin naki?". Kamar zata yi kuka ta ce. "Bai yi sauki ba, mu je ka bani magungunana kila zai yi sauki".

(Wato fa mu ƴan Nigeria da gaske ne fa dik in da muke mun fita daban, wato sai mu koyi abu ma kuma mu fi wanda ya koya mana iyawa 🥱 Allah ya yi mana baiwa matuƙa, ga dai Mahnoor nan ta kware har tana san fin Chuchu dake koya mata soyayyar ma.)

Rungumota sosai ya yi. "Zan baki maganin, amma kafin nan nima bari in samu nawa maganin kin ji?". Kamar mai rokanta ya yi maganar.
"Baka da lafiya ne daman Yah Jaish?". Ta gefa mashi tambayata tana zame hannunta daga kan nasa

Kai ya ɗan jinjina mata kafin ya amsa da. "Yeah bani da shi, amma kece sila". Ya kai karshen maganar tare da haɗe bakinsu waje guda, sam bai bata damar yi mashi magana ba bare ta tambayi ya aka yi ta zama silar ciwonsa.

Hot kiss ya shiga bata babu kama hannun yaro, a hankali ya.......


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






37



Hot kiss ya shiga bata babu kama hannun yaro, a hankali ya kai hannunsa saman tula

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login