Showing 63001 words to 66000 words out of 403653 words
da ƙarfin alaƙar uba da ɗa, wanda baki ba zai iya misiltawa ba.
Uncle Jahiz ne da ya ga abin nasu ba mai karewa bane sai ya matso ya ɓanɓanre Jaish daga jikin King yana faɗin.
"Is okey yaya, Jaish lest go to ur mom room, I want to see her reaction a lokacin da zata ɗaura idanunta a kanka".
Ɗan ɗaure fuska kaɗan Jaish ya yi. "Uncle sai ka ce wanda ya ɓata tsawon lokaci sai yanzu aka ganesa? Tafiya fa nayi na je na dawo, kaga dad ma sai wani ƙanƙameni yake yi".
Tun da ya fara magana idanun King a kansa, sai yanzu suka fahimci Jaish fa bai san komai dangane da ɓacewansa na tsawon watanni ba, dan haka sai King ya ce Jaish ya je wajen mommarsa da wuri, ya ce mashi hakan ne kuma dan yana da yakinin zata rage damuwar da take ciki a halin yanzu idan ta gansa.
Aikuwa hakan ce ta faru. Lokacin da suka haɗu da momma a bedroom na King, hawaye masu ɗumin gaske ne suka fara kwaranya daga idanunta, tamkar ruwan sama mai ɗauke da albarka. A hanzarce ta sauko kasa daga saman bed ɗin King, da sauri ta kariso ta rungume shi da karfi, numfashinta yana cike da farinciki mara misaltuwa.
Ganin abin take yi tamkar a mafarki, shi kuma mamakin hakan yake yi, dik da yasan cewa Momma tana yi mashi fiye da haka idan ya yi tafiya ya dawo, to amma bata ruwan hawaye a kan tafiyarsa da dawowansa, yau sai ga shi tana hawaye, sai ƙwaƙwalwarsa ta fara bashi lallai akwai wani dalili mai karfi da yasa iyayen nasa suka yi mamakin dawowarsa, ƙwaƙwalwarsa ce ta tariyo mashi yadda King ya tarbesa, abin sai ya yi mashi some how haka.
Raba jikinta da nasa momma ta yi ta fara binsa da kallo, tana duba shi daga sama har ƙasa, kamar tana tabbatarwa idanunta shi ne ko ba shi ba.
"Kai ne Jaish, da gaske kai ne ka dawo gare ni, Allah mai iko, Allah mai kyauta mai kari!". Ta furta cikin muryar da ta ƙunshi da dukan ƙauna ta duniya.
"Momma nine mana, akwai wani abin ne?".
Zata yi magana idanunta suka sauka a kan uncle Jahiz dake bayansu, kai ya girgiza mata a kan kada ta faɗa mashi komai.
Dan haka sai ta rabu da shi a in da ta ce mashi babu komai. Ya yarda da babu komai ɗin, sai ya ce mata.
"Momma zan je in yi wanka, and then am feeling hungry".
Cike da kauna ta ce yanzu za'a kawo mashi abinci a bedroom ɗinsa, ya je ya yi wankan. Har ta ɗan samu sassauci a ranta.
Yana san tambayar ina Auta, sai dai tamkar an ɗaura tongue ɗinsa, ya ji ta yi mashi nauyi ya kasa tambaya, haka ya wuce bedroom ɗinsa ba tare da ya tambaya ba, sai dai cikin ransa tunanin Autar ce kawai.
Momma kuma ta koma saman bed ta kwanta.
••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
A ɓangaren mutanen fada kuwa, neman Hoorain aka shiga yi babu kakkautawa, a nan warriors dake bakin gate suka isar da sakon ai ya fita baya a cikin kingdom ɗin.
King ne ya umarci warriors guda huɗu da su bi bayansa cikin gaggauwa su sanar da shi King yana buƙatar ganinsa.
Sosai commander Zafar ya shiga tsananin tashin hankali na abin da yake faruwa, har wani irin kaiwa da komowa yake yi a cikin Kingdom ɗin, ya gaza zaune ya gaza tsaye, ya rasa sukuninsa, damuwarsa ɗaya a nan ita ce meyasa Hoorain zai fita daga kingdom of power? Ina kuma ya tafi?.
MY PEOPLE'S AKWAI GAGARUMIN MATSALA! ME KUKE TUNANIN YASA HOORAIN YA GUDU? KENAN YA ZAƁI DA YA BAR MAHAIFINSA CIKIN WAHALA A KAN SHI YA KARƁI HUKUNCI?.
==========================🔥
•••••••••••••JIMETA YOLA•••••••••••🔥
A yau ne bappa ya miƙa sadakin Mairo dan cikar burinsa. Katuwar bujumar saniya ya bayar a matsayin sadakin.
Tun safe Nanne take faman zazzaga masifa tana aikin aika mashi da tsinuwa da bakaken maganganun. Amma yadda kuka san an shuka dusa a gona, ko kaɗan bai nuna alamar kamar yasan da wata halitta ita wai Nenne a duniya ba, sai hidimar gabansa yake yi, nan da kwana uku za'a ɗaura aure dan Mairo ba budurwa bace, ta taɓa yin aure sai dai bata taɓa haihuwa ba, mijin nata ne ya rasu aurensu da wata biyu.
So ba wani bikin da za'a gudanar mai tarin yawa dan dikkansu ba yara bane kuma ba saurayi da budurwa bane.
Wunin yau a gona bappa ya wuni shi da Mahreen da Mahnoor, sun bar Nenne da shakan kayan takaici.
Tun da suka je gona da safe har yamma suka dawo, tun kuma da suka je Mahnoor bata furta ko uppan ba, tana dai zaune shiru.
Da kaga idnaunta zaka san tana bala'in jin barci, dan har sun ɗan kumbura sun yi jajir, jiya yadda taga rana haka taga dare, ta kasa yin barci, Jaish ne kawai a cikin ranta, tana manne da kayansa a kirjinta har wayenwan gari.
Da kyar ta iya gabatar da sallar asuba, tun da ta yi sallah kuma ta fito ta kama yin aikace-aikacenta tamkar yadda ta saba yi, bata ma jira sai Nenne ta zo ta yi mata tashin cin mutumci ba, sai ta koma ruwa kawai gwanin ban tausayi.
Yanzu haka tana zaune a cikin gonar nan gyangyaɗin barci take yi, sai barcin ya yi kamar zai ɗauketa sai kuma ta zabura ta farka kamar wadda aka razana.
Dik abin da take ciki bappa yana sane, ya dai yi shiru ne kamar bai ganta ba, bawan Allah bashi da abin faɗe.
Yanzu so yake yi ya samu Arɗo su yi magana a kan wannan aure nata, tabbas Arɗo zai iya warware wannan aure, dan matsayin alkalin kauyen yake, da ace mijin Mahnoor ɗin sun san shi, sun san tushensa, sun san asalinsa ne ya tafi bai dawo ba, to wannan addini ya bada damar a jira na tsawon shekaru biyar, wata mas'haban ta ce shekaru uku in bai waiwayeta ba sai a raba auren, amma basu san shi ba, basu san daga ina ya fito ba, mutum ne ko aljani dik basu sani ba, kaddara tasa aka aura mashi ita, daga baya ya ɓace daga ganinsu to wannan a musulunci wakkwaran bincike za'ayi domin a tabbatar da mutum ne shi ko aljani, idan kuma babu ta yadda za'ayi a bincika kamar dai shi Jaish ɗin to wannan alkali yana iya raba auren!.
To yau da daddare ya shirya zai je ya samu Arɗo su tattauna.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
Zaune take karkashin bishiyar mango, ta buga uban tagumi, a zahiri zaku ga kamar tana kallon bappa da Mahreen dake aikin cire kananan ciyayin da suke fitowa bappa wajen masararsa.
Amma a baɗini tunanin kyakkyawan mijinta take yi, ganinsa kawai take yi a idanunta yana yi mata gizo.
Kamar daga sama ta ji an ce............
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Kamar daga sama ta ji an ce. "Mahnoor".
Kin ɗago kai ta yi, dan tasan tabbas Hamma Faisal ne, voice ɗinsa ba zai taɓa ɓace mata ba.
Bai damu ba dan bata amsa mashi ko ya ɗago ta kallesa ba, sai ya nemi waje kusa da ita ya zauna yana ƙoƙarin sake yi mata magana haɗe da kai hannunsa kusa da face ɗinta da nufin zai goge mata guntun hawayen dake face ɗin nata.
Ai a miliyan ta miƙe tsaye daga kusa da shi yadda kuka san wadda aka kawowa wuta kusa da ita.
Mamaki ne sosai ya kama shi, bai taɓa tunanin zai zauna a kusa da ita ta guje shi ba, ita kuma auren da yake kanta take karewa mutuncinsa, tana daraja kanta, aurenta da kuma mijinta, so bata ga dalilin zama kusa da wani ba ko da ɗan uwan nata ne, bare kuma shi da ya taɓa santa a baya, babu wannan magana.
Miƙewa tsaye ya yi shi ma dan ya yi magana da ita. Sai dai bai kai ga buɗe baki ba da gudu tasa kai ta bar mashi wajen, dama lokacin komarsu gida ya kusa, sai kawai ta nufi gida wani irin zafafan hawaye suka fara zubo mata, ɗacin zuciyarta ya yi mata, yau da Jaish yana nan ai Hamma Faisal ba zai zo kusa da ita har haka har ya nemi yi mata magana ya nemi taɓata ba, gaskiya ta yi babban rashi matuƙa.
Da gudu Faisal ya bi bayanta, dik abin da ya faru a kan idanun bappa ya faru, ita kam Mahreen tana zaune ta buga uban tagumi, dik abin da ake yi bata da labari, ta shiga duniyar tunanin ina Jaish yake?.
Hmmmm Mahreen ma ta damu da Jaish haka bare Mahnoor da suka saba kwana ɗaki ɗaya, ya yi ta gwada mata soyayya, ai dole ta yi kukan rashinsa wlh.
Bappa ya kawosu gonar nan ne domin su rage damuwa, amma ina sai suka zo suka buga mashi uban tagumi suna kuncin abin da yake faruwa.
Tana shigowa cikin gida ta wuce ɗakinsu da gudu, a lokacin Nenne tana cikin ɗakinta, so bata ga shigowarta ba.
Kusan a tare suka shigo da Faisal ɗin, da yake hankali bata gama isarsa ba, sai ya bita har cikin ɗakin mijin nata, shi a dole zai rarrasheta.
Saman mattress ta faɗa tana cigaba da kukanta kamar wadda aka yi wa wahayin hakan.
A kan kayan Jaish da bappa ya bata ta kwanta tana jin kamshin jikinsa a jikin kaya, gani take kamar shi ne a wajen.
Kamar daga sama ta ji mutum a kusa da ita yana magana ƙasa ƙasa. Ai a zabure ta miƙe zaune, ido cikin ido ta kalli Faisal da yake dab gadan yana kallonta.
A miliyan ta miƙe tsaye, bata yi zaton ya biyota ba, tana san cewa ya fita mata a cikin ɗaki, amma kuma ta kasa yin magana, dan haka sai ta wuce ta raɓa gefensa zata fita waje.
Da sauri ya riƙo hannunta dan ta tsaya ya rarrasheta, Allah sarki, shi har yau har gobe yana santa bawan Allah.
Wani irin fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi da karfi, a zuciye cikin ɓacin rai haɗe da ɗaga murya ta furta.
"Ka sakeni Hamma Faisal!!".
Ya yi mamakin jin tsawarta a garesa, amma santa ya rufe mashi idanu da baya ganin laifinta, a baya ko ɗaga murya a magana Mahnoor bata yi, idan ma baka da nitsuwa ba zaka iya jin magana ba idan ta faɗa, tsabar yadda take magana a hankali ƙasa ƙasa cikin nitsuwa, amma yanzu rashin Jaish yasa ta fara faɗa.
"Mahnoor na ji na sakeki, amma dan Allah ki daina yin kuka kin ji? Ki yi shiru dan Allah sai ki faɗa mun meyasameki, meyasa kike kuka?".
Raɓawa gefensa kawai ta yi zata wuce, domin kuwa bata san ya tsaya mata a cikin ɗaki.
Bata kai ga fita ba ta tsinkayo muryar Jumma yar Inna Rabi wato amarya tana yin sallama a tsakar gida. Ai da gudu ta ƙarisa fitowa waje.
Suna haɗa ido da Jumma ta karisa da gudu ta faɗa jikinta tana kara karfin kukan da take yi, rungumeta Jumma ta yi, dama abin da ya kawota kenan, Inna Rabi ce ta turota da tazo ta jajantawa Mahnoor ɗin, sannan ta rarrasheta, Allah sarki Inna Rabi tana kaunar Mahnoor sosai, dik yadda aka yi sun yi zaman amana da mamar Mahnoor sosai.
Wani irin mummunar faɗuwar gaba Jumma ta ji ganin Faisal ya biyo bayan Mahnoor ya fito daga cikin ɗakin shi ma, ga Mahnoor ɗin kuma tana kuka, abin ya yi mugu mugun bata mamaki, to me ya kai shi cikin ɗakin matar aure kuma? Jumma ta jefawa kanta tambayar.
Sai ta ji kirjinta ya buga, tasan mutanensu fa wasun su ba hankali ne da su ba, kada ace wani abin ya je ya yi wa Mahnoor da yasa take kuka haka tamkar ranta zai fita.
Koke kokensu ya ja Nenne ta fito daga cikin ɗakin, basu ga fitowarta ba sai dai suka ji murya tamkar saukar aradu ta daka masu wani irin uban tsawa.
"Uban me kuke tsaya yi mun a tsakar gida kuna wani yi mun koke koke na munafurci zaku hanani shaƙatawa".
Jumma uwar rashin kunya idanunta a tsaitsaye kar ta ce. "Kai dama idan za'ayi wa mutum kishi shakatawa yake yi kenan?".
Zaro idanu Mahnoor ta yi, ai bata san lokacin da ta dakatar da yin kukan nata ba, lallai Jumma bata san bala'i da ake yi a wannan gida a kan wannan kishi da za'ayi ba ne! Da ba zata yi magana ba!.
Fusata Nenne ta yi, ranta ya sosu da jin kalamar Jumma, sai dai ba halin ta yi mata komai, saboda su fa ba ƙaramin aikinsu bane yanzu idan ta daki Jumma mijinta ya zo ya ci uban Nenne ɗin, su mazansu sun iya tarewa matansu faɗa, kai ko yaransu ka daka ba zaman lafiya har sai sun rama.
So Jumma matar aurece a yanzu tana tsoron dukarta bata san ya halin mijinta yake ba, kila mai tsauri ne a kan iyalansa.
Jumma da ta ga Nenne bata kulata ba sai ta ja hannu Mahnoor suka raɓa jefan Faisal suka koma cikin ɗakin.
A saman mattress suka zauna, hannu Jumma tasa tana goge mata hawaye tana cewa ta yi shiru yanzu ai ta zo zasu yi shawara a kan mafita, dan haka ta yi shiru suyi magana.
Ƙoƙarin danne kukan nata ta yi, amma abin ya ci tura, ta kasa dannewa, dan hawayenta cigaba da fasowa suke yi.
Tun Jumma tana goge mata hawayen har ta rabu da su kawai, dan sun ki tsayawa.
Cike da tausayawa ta ce. "Mahnoor yanzu kukan ne kike yi fisabilillah?".
Kifa kanta a saman gwiwonta ta yi, tana jin tamkar an ɗaura zuciyarta a saman wuta mai cin bala'i ne, cikin kuka da ɗan ɗaga murya ta ce.
"Jumma bappa ya ce zai raba aurena da Hamma a aura mun hamma Faisal..........."
Wani irin rushewa da kuka da ta yi ne ya ja ta haɗiye sauran maganganun ta kasa amayar da su, saboda ba zata iya karisasu ba, wato yanzu ba kukan rashin Jaish ɗin ba ma take yi, kukan raba aurenta da shi take yi, Allah sarki abin ya haɗu ya yi mata yawa.
A lokacin kuma Faisal ya wuce ya bar gidan saboda Nenne, yana tsoron bala'inta, sai ya kama kansa kawai ya haƙura, kuma Jumma tazo yasan zata rarrashin mashi Mahnoor ɗinsa.
"Haba mana bappa, ina hakan ba zai yiwu ba, gaskiya kada ki yarda a raba aurenki da hammanki, ina da tabbacin In Sha Allah zai waiwayeki, ai so ba karya bane, tabbas dik in da yake yanzu haka yana tinaninki, ba zai taɓa jefar dake ba komai zai faru"............ Cewar Jumma!.
Wannan magana ta Jumma ta yi dai'dai da lokacin da Jaish ya ke ƙoƙarin kwanciya a saman katafaren bed ɗinsa, ya yi wanka yana sanye da three quter jeans white color and white singlet masu kyau, ya yi matuƙar mamakin ganin yadda gashin kansa ya yi yawa, sai dai bai kawo a ransa ya yi rayuwa a wani waje ne dayasa gashin ta taru sosai saboda rashin datseta ba, ya wanke kansa kawai ya gyarata da mayukansa masu kyau da tsada.
Sai dai fa wlh gashin da ta yi yawa ta yi masifar yi mashi kyau, shi kansa ya shaida ta yi mashi kyau, hakan ce ma yasa bai wani damu da yawan gashin ba, sai ya ji ma kamar zai iya barinsa ya cigaba da kashe mashi kuɗi kawai dan ya yi kyau matuƙa.
Rage gudun Ac ya yi, ya kwanta kenan sai ya fara tunanin ina wayarsa zai kira number Zunaira ya ce ta zo.
Kada ku manta wayar tasa tana hannnun Mahnoor. Miƙewa tsaye ya yi ya fara bincikar ina wayar tasa take?. Ko'ina ya duba bai gani ba.
A bakin bed ɗinsa ya koma ya zauna, shiru ya yi yana tunanin in da ya jefar da wayar tasa, ɗan lumshe idanunsa ya yi ya fara tariyo baya dan ya iya gano ina wayarsa take?.
Dai'dai lokacin King and Momma suka shigo cikin ɗakin, uncle Jahiz yana biye da su a baya, hakan ya dakatar da shi daga tinanin da yake ƙoƙarin yi na a in da ya jefar da wayarsa.
Ita kuwa Jumma cigaba da karfafawa Mahnoor gwiwa ta yi a kan Jaish zai waiwayeta, dan haka dik bala'in da za'ayi kada ta yarda a rabata da aurensa, dan shi kaɗai ne garkuwanta kuma gatanta bayan Allah kenan.
Ta yi na'am da zancen Jumma, dan haka sai ta ɗaura ɗamarar gayawa bappa ba zata iya rabuwa da Jaish ba, ta kuma ji daɗin zuwan Jumma, har ta ji ranta ya ɗan sanyaya.
Da kyar ta goge hawayenta ta kuma dakata da yin kukan, har da ajiyar zuciya. Jumma ganin ta yi nasarar dakatar mata da kukan yasa ta fara ƙoƙarin kawo mata hira masu daɗi da zai ɗebe mata kewa.
Cikin hiran nata ne ma ta sanar da ita tana da ciki har na tsawon wata biyu da sati biyu, sosai Mahnoor ta tayata farinciki, ta ji daɗin maganar matuƙa.
Haka suka cigaba da yin hira tana bawa Mahnoor shawarwar haɗe da kara mata karfin gwiwa a kan ta dage ta tsayawa aurenta, kada ta yarda a farraka mata shi.
Sosai Jumma ta so jin kwakkwaf a kan ko dai ita ma Mahnoor tana da cikin Jaish ne, ko kuma sun taɓa kwanciya, amma ina Mahnoor taki yarda da