Showing 138001 words to 141000 words out of 403653 words
daɗe kamar wani bosawa? Babu ko irin sunan love ɗin nan?".
Shiru ya ɗan yi tare da matsawa baya kaɗan ya fitar da ita daga cikin ruwan kenan, sannan ya rabata da jikinsa ya sauketa ƙasa a kan kafafunta.
"Hoorain baka bani amsa ba". Wannan karan murya a ɗan kasashe ta yi maganar.
"Na iya soyayya, sai dai ina tinanin abin da zai je ya dawo shiyasa nike ja da baya, bana san dik abin da zai iya jawo mana matsala da ni da ke".
"Ban gane nufinka ba". Cike da mamaki ta yi tambayar.
Gyara tsayuwansa da kyau ya yi, cikin nitsuwa ya fara warware mata komai dan gane da abin da yake jiwa tsoron yasa baya san zurfafawa a soyayyarsu, baya san sakin jiki sosai.
"Ke da kanki kin san ƴan uwanki ba zasu taɓa yarda da ni a matsayin masoyinki ba, ba zasu taɓa karɓata ba, sannan kin san matsayina da naki daban daban, ke kanki ina jiyewa zuciyata tsoron ki juya mata baya, na san daddynki ba zai taɓa yarda ya bani ke ba, kema kuma kin san da hakan, idan muka cigaba da soyayya na tabbata wahala zamu sha, and nasan ke ba zaki iya jura ba, idan kin ji wahala kaɗan zaki guji zuciyata ki barni a wahale, wannan shi ne kaɗan daga cikin abin da nike guje mana".
Tabbas ta fahimci dalilansa, sannan kuma ta gamsu dalilai ne masu karfi da dole zasu iya sanya shi ja da baya, tasan King ba zai taɓa yarda ba, bama azo ga King ba, ko guyson ba zai yarda ba, ranar iya ganinta kawai ya yi ta kusa da part na mayaka ji yadda ya tashi hankalinsa bare kuma ace ya ji tana san assistant commander? Tab ai babu wanda zai goya mata baya, ko Chuchu ba zata bi bayanta ba a wannan gaɓar.
Amma dik da haka sai ta kallesa ido cikin ido, cike da tsantsar makauniyar soyayyarsa ta fara magana masu zafa kamar haka.
"Tabbas dik abin da ka faɗa haka ne, kuma ka fini gaskiya, amma akwai kalma ɗaya da ka faɗa wanda ba hakan bane kuma ba zan lamunta ba!!".
Tattara mata hankalinsa a kanta ya yi yana sauraronta, cike da sa ran zata kawo masu mafita.
"Abin da ka faɗa ba daidai ba kuma shi ne cewa da ka yi idan na ji wuya zan juyawa zuciyarka baya, ka yi kuskure! Ban ga wata wahala da zata sa in juya maka baya ba a duniya, soyayyar gaskiya nike yi maka ba ta yaudara ba! Kada ka manta nasoka ne tin ban taɓa ganin kamanninka ba, tun da na taso a rayuwata bani da abin san kalla sama da kai, ka yarda dani, mu haɗa hannu zamu yi nasara! Na yi maka alkawarin a kai'na kuma dalilina dik ƴan uwana zasu canza su karɓeka a matsayin zaɓina hannu bibbiyu, ka mun alkawarin dik halin da zamu shiga ba zaka taɓa ja da baya a kan soyayyarmu ba?".
Ta kai karshen maganar tare da buɗe tafin hannunta ta miƙo mashi. Da yake jajirtacce ne babu tsoro a tatare da shi sai bai yi wani tinani ko ya damu ba, shi ma ya buɗe tafin hannunsa ya ɗaura a saman nata.
"Na yi maki alkawarin babu gudu babu ja da baya kome zai faru ina kan bakata na ina sanki!".
Ajiyar zuciya ta sauke, cikin sanyin murya ta ce. "Tabbas ba zan baka kunya ba, kuma na yi maka alkawarin sai dai a zare raina da soyayyarka a kirjina, ba zan taɓa san wani ba kuma ba zan taɓa yarda a haɗani da wani ba".
Wani irin bargon farinciki ne ya lulluɓe zuciyarsa, ya ma rasa abin faɗe, sai dai kawai ya yi shiru yana jin wani sanyi tana ratsa zuciyarsa.
"Yanzu meyakamata mu yi?". Cewarta kenan. "Gida zamu tafi yanzu, hanya zamu ɗauka, gobe zamu iya isa".
"Har na ji bana san mu koma yanzu, kamar mu kara kwana biyu a nan, wajen akwai daɗi sosai". Cike da yaranta a word ɗinta ta yi magana.
Kai ya girgiza tare da riko hannunta da kyau a cikin nasa, ƙasa ƙasa ya ce mu je. Bata yi musu ba ta bi bayansa suka tafi wajen Pretty, har lokacin sai barci take zubawa.
Kamar zai tambayi Auta su tafi da Pretty ko su barta a wannan dajin tun da ta faɗa mashi a nan suka sameta. Sai kuma ya ji ba zai iya tafiya ya barta ba, tin da suka ganta haka bata da kowa kenan, dan haka su tafi da ita kawai.
"Jirani ina zuwa, ki tashi Pretty kafin na ɗauko dokina". Yana kai karshen maganar ya sake hannunta, bai jira amsarta ba ya wuce da sauri izuwa ɗan baya da su kaɗan.
Ita kuma ta wuce ta tashi Pretty daga barci, yana dawowa suka hau saman dokin da dik wani abin da zasu buƙata, wajen da suka yi faɗa da damusan nan ya koma ya ɗauki takobinsa, sannan suka kama hanya, Auta a gaba Pretty a tsakiyansu shi a baya, ba komai yasa yaki saka Auta a tsakiyansu wato kusa da shi ba face kaucewa sharrin shaiɗan.
Auta ta manta da tana jin yunwa, haka suka kama hanyar nufar Kingdom of power..... To sai dai mu ce Allah ya kaiku lafiya.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥
2:30am.
Dare ta tsala sosai, ko'ina ya yi tsit, dik wani na kirki yana cikin gidansa, banda kukan karnikan Ramish su bisho dake tashi babu wani abin da zaka ji.
A hankali karan Acn ɗakinta yake tashi. Kasancewar bata da nauyin barci ko kaɗan hakan yasa in abu ya motsa a kusa da ita tana ji kuma yana farkar da ita, dama dik wanda ya yi zaman gidan yari da wuya ya iya nauyin barci.
Ta yi nisa cikin barcin da take yi cikin kwanciyar hankali, yau tana farincikin ta amayarwa masu nikaf kunan da ya daɗe yana babbaka ranta, yau ta samu sai'da da salama, har ta ji bata taɓa yin barci mai daɗin wannan ba.
Can a tsakar kanta ta ji kamar an taɓa mata kofar ɗaki, dik da tasan ba ita kaɗai take kwana a ɗakin ba, amm tasan yau Sharifat bata nan, kuma da wuya ta dawo cikin wannan daren.
A karo na biyu ta sake jiyo an mai da kofar nata an rufe tamkar wani ne ya shigo ya rufe, kamar a mafarki ta ji ana datse keys na kofar wanda tun da suke daga ita har Sharifat babu wanda ya taɓa datse wannan kofar da keys ɗinsa.
Hakan yasa ta zabura ta miƙe zaune, ɗakin duhu bakin kirin, dan yau ko lamp dama bata kunna ba. Wani irin ɗan motsi ta ji kamar alamar tafiyar jami'i a yakin sunkuru, ko kaɗan bata tsorata ba, dan ba ƙaramin abu yake tsoratata ba ita.
Cikin dabara ta laluɓa ta sauko kasa daga saman gadon, tamkar wata hawainiya ta fara taka kafafunta ta nufi switch. Unexpect ta isa wajen ta kunna wutar ɗakin, nan take haske ya gauraye ko'ina.
Ya ilahi ya lilliahi, wani irin mahaukacin razana ta yi. Idanuwanta ne suka yi mata tozali da wani tsayayyen namiji cikin shigar ban tsoro, baka iya ganin komai daga jikinsa, from up to down gabaɗaya bakaken kaya ne a jikinsa, fuskarsa rufe yake da tactical mask, ba zaka taɓa iya gane wanene bane, kafafunsa na sanye da combat boots masu karfin gaske. Ga shi a tsaye a tsakar ɗakinta, ya rufe kofar ɗakin kuma da key babu halin gudu ta fita.
Sosai ta razana, da karfi ta waje baki zata zunduma ihu kamar walkiya haka ya wurga mata wani abu mai kamar da karfen star a baki.
Wani irin baya baya ta yi kamar zata faɗi, dan dolenta ta haɗiye ihun da take yunkurin kurmawa, jinine ya fara bulbula daga bakinta, alamar abin ya fasa mata baki. Ganin hakan yasa ta fahimci komai, wato kasheta aka zo yi dan ta yi barazana wa masu nikaf.
Amm waye kuke tinani mai kwarin gwiwar da zai iya keta camarorin da suke kan titin hanyar ratsowa gidan Abu Abdussalam har ya iso, sannan ya keta dikka waɗan nan jiga jigan securitys ɗin ya shigo cikin gida, ya keta cameras dake cikin gida har da babban parlourn ya iso ɗakinta dik kuma babu wanda ya gansa? Anya wannan makashi ba daga cikin gida kuwa yake ba?.
Hannu ya sanya a wajen combat boots ɗinsa ya zaro wata karamar wuƙa mai bala'in kaifin gaske, ga shi har kwayar idanunsa baka iya gani, dan tactical mask idan ka sanya mutum ba zai iya ganin komai na face ɗinka ba sai dai kai ka gansa. So yau ko idanun bata samu damar gani na bare ta iya hasashen wanenen ko ta sa ran zata iya ganesa.
Ganin ya zaro wannan wukar yasa ta ƙara tsorata, da gudun gaske ta yunkura zata shiga toilet ta rufo kofar. Sai dai ina, bai bari ba, taku biyu ya yi ya damko gashin kanta. Da karfi ya fisgota da gashin nata ya yi wurgi da ita a saman bed ɗinta.
Sosai ta ji azaban jan gashinta da ya yi, amma haka ya daure ta shanye, da gudu ta yunƙura ta miƙe. Sai dai bata kai ga sauka gadan ba ya sanya combat boots ɗinsa ya take kirjinta da karfi har sai da ta bugu da jikin headboard na gadon.
A wannan gaɓar azaban da ya ziyarceta ya ja ta saki wani marayar kuka, ga shi bakinta sai bulbular da jini yake yi. Ta maza ta sake yi ta yi yunƙurin tashi zata gudu again tana dafe kirjinta, dan ya taketa a tula tulanta, kuka kunsan dole ta ji azaba over.
Kafafunta ya take da combat ɗin nan nasa, har cikin ranta azaban hakan ya ratsata, ta gagara yin kuka, ta ko'ina zogi da raɗaɗi take yi.
Matsawa ya yi kusa da ita, ya damko gashin kanta cikin hular kayan barcinta, sai da ya jijjiga kanta da karfi sannan ya bugata da jinin headboard na gadan, nan take goshinta ya fashe. Ko kaɗan babu alamar zai tausaya mata, babu imani a ransa, wuyarta ya sake shaƙowa da karfi, hannunsa na cikin Black gloves. Ya matse mata wuya da iya karfinsa.
Tuni ta fara jiyo kamshin mutuwa, tuni idanunta suka fara rufewa ta fara ganin duhu mai yana yana lulluɓe ko'ina, ta dafe kirjinta saitin tula tulanta, ko da zogin da suke yi mata kawai ya kyaleta ai ya isheta ba sai ya kara mata wani ba.
Hannunsa ɗayan ya kai saman kumatunta, yana rike da ƴar wukar, sai ya sanya wukar a tsakiyar yatsunsa, hakan ya bashi damar matse mata kumatu sosai har sai da ta ja wani irin azabbabben numfashi.
Bata iya ganin idanunsa, amma shi idanunsa kar a kan kirjinta, hakan yasa ya saki kumatunta ya mayar da hannunsa saman kirjin nata, da karfi ya matse mata tuka tulanta dan bakar mugunta, azaba yasa ta ji wani karfi ya zo mata ta fara ƙoƙarin kwatar kanta. Ganin hakan yasa ya ji a ransa yana da kyau ya keta mutumcinta kafin ya kasheta.
Wannan tinani nasa yasa ya zame hannunsa daga fatar wuyarta ya mayar wuyar rigarta. Da karfi ya ja rigar ya yaketa. Ko kusa ko alama ba zata iya kwatar kanta daga hannunsa ba, ga shi babu ko vest a ciki, haka ya yage mata riga, ya kuma yage mata wando, ya rage pant a ciki kawai.
Kafarsa da ya take nata da shi ya cire. Da hannu ɗaya ya damki kafafun nata ya jata a in da ta dawo tsakiyar bed ɗin, gabaɗayansa ya tafi kanta da nufin aiwatar da abin da yakeso. Dik jikinta ya yi wanka da jinin dake bulbula daga goshinta and bakinta, ko ƙwaƙƙwaran motsi bata iya yi, hankalinta ya fara gushewa, tana ji ya haye kanta haɗe da rabata da komai nata.
My people's waye kuke tinanin zai yi wannan aika aikan? Shin ina mazan gidan Abu Abdussalam da har wannan abin zai faru basu sai ba? Ko da yake part ɗinsu yana da nisa da nasu Ummie, amma koma wanenen wannan anyi mai karfin zuciya da kwarin gwiwa, tab wannan masifa haka. Mekuke tinanin zai faru? Allah sarki Leesharh, ko tsoro baya ji zai kasheta cikin gidan ministan tsaro na ƙasa gabaɗaya? Lallai akwai cakwakiya.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥
Ko tausayinta babu alamar zai ji, da karfin tsiya ya fara ƙoƙarin haike mata, kasancewar wandan jikinsa irin Armored leggings ɗin nan ne sai ta yi mashi wuyar ciruwa lokaci guda, ga shi ba zata yagu ba bare ya yageta.
Hakan yasa ya ɗan ɗaga jikinsa daga nata kaɗan, da zafa ya fara ƙoƙarin kwance belt dake jikin wandan dan ya yi abin da zai yi da sauri.
__________________🔥
Lokacin guda ya ga wani irin warkiya kamar shocking na wutar lantarki, ya kuma ga wani irin jiri mai karfi ya ɗebesa, daga haka bai sake gane komai ba, sai jin kansa ya yi ya faɗi a saman mattress ɗin rigijib kaman kayan wanki. Ba komai ya ja hakan ba kuma face, lokacin da yake ƙoƙarin cire belt ɗin wandasa ita kuma ta lura da ya bar kanta, hankalinta ne ya dawo jikinta, cike da kunan ran abin da ya yi mata, ga azaban da take ji, cikin dabara da jajircewa irin nata ta sanya hannu ta laluɓi lamp dake saman bedside drawer, da iya karfinta na karshe ta jawosa.
Shi kuma hankalinsa dik yana a kan yadda zai zare belt ɗinsa, Allah ya bata dama, da yake bata da hakkinsa sai ta shammacesa ta dakarkare ta maka mashi a kai. Wannan shi ne abin da ya faru.
Da kyar ta iya motsa jikinta ta miƙe zaune, shesshekar kuka take yi sosai, hannunta tasa tana tattaro rigar barcin jikinta dan ta ɗan sitirta kanta. Kamar gizo haka idanunta suka hango mata shi yana motsawa a saman mattress ɗin yana san tashi kenan, alamar ba suma ya yi ba dama, zafin buguwa ce nawai ya ji yasa ya faɗi kamar ya suma.
Ai bata san lokacin da wani irin karfi ya zo mata ba, a maliyan ɗari kamar wata walkiya sai gata ta diro kasan bed ɗin, kai tsaye kofar room ɗin ta nufa, a gaggauce ta fara ƙoƙarin ɓalle key ɗin ta fita, hannunta sai kerya yake yi, yaki tsayawa waje guda bare har ta iya buɗe kofar.
Hankalinta dik a kansa, kun san idan mutum yana tsorace haka abin yake, sai ji ta yi key ɗin ma yaki murzuwa ta buɗe.
Shi kuwa a lokacin ya farfaɗo, a zabure ya zaro idanunsa da suka yi jajir waje, ya ji bugu hege. Wani irin miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin ya yi yana zaro idanun kamar ma tare ɓera a tarko. Wayam bai ganta a saman bed ba, hakan yasa ya fara jujjuya jajayen idanunsa yana neman ta ina zai ganta.
Ita kuwa kerman da hannunta yake yi yasa kofar taki buɗewa, sai zaro idanu a kansa take yi karjinta tamkar zai fashe saboda bugawa, iya tsorata yau ta yi shi, cikinta ya gama ɗuran ruwa, har gudawa ta ji, kamar fitsari zai zuba mata take ji.
Ganinta a wajen kofa yasa a miliyan ya diro ƙasa daga saman bed ɗin, sai ƙoƙarin murza key take yi tana ihu ƙasa ƙasa dan voice ɗinta baya fita. Cikin zafa ya nufeta yana wani uban ɗaure fuska, sai huci yake yi alamar ransa a tsananin ɓace.
Yana isa dab da ita Allah ya bata sa'a ta ɓalle key ɗin kofar, yana ƙoƙarin damko gashin kanta ta danna waje a miliyan. A haukace ta fito main parlour na sama, har lokacin jikinta dik jini, bata san ina ta nufa ba ga duhun dare, dik kwayayen fitillu a kashe. A tinaninta ya biyo bayanta hakan yasa ta kara gudu sosai.
Dai'dai zata fita parlourn suka ci wani uban karo da shi yana shigowa. Baya baya ta yi ta faɗi ƙasa, da yake akwai duhu a parlourn hakan yasa baka iya gane wanenen, amma ita dik da tana cikin tashin hankali bai hana ta fahimci da Ramish ta yi karo ba, saboda kamshin perfume ɗinsa ya banbanta da na kowa a cikin gidan.
Shi kuwa ko a jikinsa bai nemi sanin da waye ya yi karo ba, sarkin yawon tsakar dare a cikin gida kenan, ba shi da aiki sai ya yi ta yawo har garden ɗin dake harabar gida yake zuwa da tsakar dare, ya zauna ya yi ta latse latsen waya, to ya fito yawon nasa ne yanzu ma suka ci karo. Bai bi ta kan wanda ya buge ba yasa kai ya tsallaketa ta wuce ciki.
Ita kuma da karfi ta tashi ta fice wajen. Bata zame ko'ina ba sai part ɗin Abbie cikin rashin sani, Allah sarki bata san ina ta dosa ba, gudun cetan ranta kawai take yi. A lokacin karfe 4:00 daidai ta buga, asuba ta kawo kai kenan.
Takuwa yi sa'a idanun Abbie biyu yana saman dadduma yana sallah. A haukace ta afka cikin ɗakin, har taso ta ɗan bashi tsoro, amma da yake yana gaban Ubangijinsa sai bai wani damu da sanin wanenen ya afko mashi ɗaki a haukace haka ba. Cigaba ya yi da sallarsa cikin nitsuwa, ita kuwa cikin rashin sani ga duhu yasa ta fara bin jikin bango tana neman gane ina ta shigo ne?.
Tabbas lamps na ɗakin a kunne suke, amma bata iya hango Abbie, saboda ɗakin yana da girma sosai, hasken lamp basa kaiwa in da yake.
Cigaba da laluɓe