Showing 123001 words to 126000 words out of 403653 words

Chapter 42 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

98

su Annabi Musa, Annabi Dauda, Annabi Sulemanu, Annabi Isa (AS), duk daga zuriyar Annabi Ishaq (AS) suka fito, kuma sunan bani Isra'ila ya shafesu".

"Annabi Isma'il ba ya cikin zuriyar Isra'ila saboda shi ba ɗan Annabi Ishaq ba ne, kuma ba daga zuriyar Ya'qub yake ba. Dan haka Annabi Isma'il (AS) shi ne asalin zuriyar Larabawa waɗanda suka rayu a yankin Makkah".

"A taƙaice yadda zaka fi ganewa shi Annabi Isma'il (AS) ya yi rayuwa a Makkah, kuma an kafa al'adar ibadar Hajji tare da mahaifinsu Annabi Ibrahim (AS). Annabi Ishaq (AS) ya rayu a Palastine kuma ya zama tushen addinin yahudawa da kiristoci, ta hanyar zuriyarsa Isra'ila. Saboda haka dik wanda ba ya cikin zuriyar Annabi Ya'qub, ba a kiransa Bani Isra'ila, to kaga Annabi Isma'il (AS) ba shi da alaƙa da zuriyar Ya'qub saboda shi wani reshe ne na zuriyar Ibrahim (AS) wanda ya yi rayuwarsa a yankin Larabawa".

"Alqur'ani mai girma ma ya ya yi magana a kan, cikin Suratul Saaffaat, aya ta 112 zuwa ta 113, Allah ya bayyana cewa Annabi Ibrahim (AS) ya kasance asalin dukkan Annabawa, amma Allah ya sa zuriyarsa biyu daban daban, haka cikin suratul Maryam Allah ya bayyana Annabi Isma'il a matsayin manzo ga Larabawa, ka fahimta ko akwai sauran abin da baka gane ba?". Ta yi maganar tana kallansa.

Sosai Ronnie ya fahimci dik abin da ta faɗa, kuma hakan tasa ya kara ganin girman Allah matuƙa, ya samu karin ilimi, yanzu yasan cewa ga daga zuriyar da Annabi Isa ya fito, ashe da Annabi Isa da Annabi Muhammad dik kakanninsu guda ne, ɗaya dai ya fito ta gefen Annabi Ishaq ɗaya kuma ya Annabi Isma'il, amma dikkansu kakansu ɗaya ne wato Annabi Ibrahim, lallai Allah da girma sa hikima yake.

Ganin ya yi shiru bai bata amsa bane yasa ta ce. "Ko dai baka gamsu bane Ronnie?".

A hanzarce ya girgiza mata kai haɗe da faɗin. "Sosai na gamsu, jinjinawa girman lamarin Ubangiji nike yi shi ya ja hakan, amma kema ai kinsa ba zai taɓa yiwuwa ki yi wa mutum bayani bai fahimta ba ko? Dole ya fahimta dik toshewar ƙwaƙwalwarsa, magana cike da hujoji yadda yakamata, kai ke dai kin ji daɗi".

Ajiyar zuciya ta sauke, a nitse ta ce. "Kana burgeni Ronnie saboda son neman iliminka, kana san sanin dikkan abin da baka sani ba, ina addu'ar Allah ya kara buɗa maka ƙwaƙwalwarka, ka cigaba da bibiya kana tambaya ta dik wani abin da baka sani na, In Sha Allah idan na sani zan sanar da kai".

Jinjina kai ya yi alamar to, sai ya ji tamkar ya kwace dikkan ilimin dake kanta ya zuba a nasa kan, baya gajiya da neman ilimi shi dai a rayuwarsa.

Cigaba da jefa mata tambayoyi dangane da addini ya yi tana bashi amsa, haka suka kasance cikin farinciki har time da barci ya ɗauketa, kin fita daga ɗakin ya yi ya zauna yana ya kallanta cike da farinciki, Allah sarki har yanzu kuma bai san da ciwo a wuyarta ba.

Ina kaunar addinina my people's, hakan yasa nake bala'in san part ɗin birnin Black world da kuma Sweetie, dan addinina, wayyo musulunci duniya ce jama'a, Allah ka kashemu muna masu yi maka bauta babu gajiyawa, kasa kalmar shahada ta zama kalmarmu ta karshe a duniya.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

KINGDOM OF POWER.

Alƙalamina ba iya nishaɗantarwa da faɗakarwa haɗe da ilmantarwa kawai ya tsaya ba, har da bawa ƴan uwana Sa'a da zai canza ya kuma inganta masu rayuwa, ba sai kin zauna kina ta bani bani bani, za'a yi taro a cikin dangi kece a baya dan baki da shi, miji ya gaji da baki kuɗin shiga ƴan uwa, kina zaune dirshan ba zaki nemawa kanki mafita ba. To Alhamdulillah Allah ya bamu ilimin sanin wasu abubuwa, dan haka na zaɓi sanar da mutane na dan ki fita daga jerin bani bani da kike ta famar ɗaurawa miji, kema ki nemi kuɗinki a dama dake, ko ke budurwace a gida zaki rinƙa yin saarki dan ki ragewa mama da baba wasu ɗawainiya, fatana dai kowacce ta kasance cikin farinciki a rayuwarta duniya da lahira, Allah yasa mu dace, bari in koya maku yadda ake yin sabulun wanke kaya, yana da riba sosai, zaku samu na kanku, kuma shi abu ne wanda ake saya kullum dan wanke dauɗa, a yadda komai ya yi tsada idan kika haɗa shi kika ɗan yi ƙasa da farashi wlh ba ƙaramin alkhairi zaki samu ba, ki jikan na kasa dake a dik abin da zaki sa a gaba sai Allah ya jikanki ya dafa maki kema, wlh zaki samu alkhairi sosai a wannan sabulu, makota zasu yi ta shigowa su saya hankalinki a kwance kina ajiye ƴan kuɗaɗenki ki huta da bin miji ya baki ya baki.

Ga abubuwan da zaki buƙata.

Sabulun wanke kaya yana buƙatar kayan haɗi masu wanke ƙazanta sosai, musamman sinadaran da ke yaki da maiƙo da datti. Ga yadda ake haɗa shi:

Kayan Haɗi. Caustic Soda shi wannan ana amfani da shi ne don samar da tushe (base) ga sabulun. Shi ne na farko. Sai ki samo soda Ash (Sodium Carbonate) Sai sulphonic Acid, wannan yana bayar da kumfa sosai. Sai STPP (Sodium Tripolyphosphate) sai Perfume don ƙamshi. Colorant Idan kuna son ƙara launi. Sai Ruwa don haɗin.

Yadda zaku haɗa.

Ki zuba Caustic Soda (10%) a cikin ruwa wanda ya danganta da yawan kayan haɗinki, sai ki barshi ya narke na tsawon awa 24.

Shi ma Soda Ash (5%) ki saka shi a nasa ruwan daban ya narke na tsawon awa 12 zuwa 24. Haka shi ma STPP (2-3%) ki narkar da shi a nasa ruwan kamar dai sauran na baya. Idan suka kai waɗan nan awanni sai ki ɗaukosu, soda ash zaki juye cikin caustic soda, ki gauraya sosai, sannan sai ki juye sulphonic acid, shi ma ki gauraya sosai, sai ki zuba stpp shi ma, a cikin babban waje da zasu samu space zaki zubasu ki haɗe fa. Ki zuba ruwan dai'dai da yanayin kayan haɗinki, idan kinga ya yi kauri sosai zaki iya kara ruwa.

Ki tabbatar kin juya sosai ya haɗe jikinsa ko in ce sun haɗe jikinsu. Sai ki zuba perfume and colorant, sannan ki rufe ki barshi na awa 24 kafin ki yi amfani da shi, idan kina son fitar da shi shape by shape zaki iya sayan shapes ɗin ki zuzzuba a ciki ki barsu su kame jikinsi.

SHIKENAN KIN HAƊA SABULUNKI, IN SHA ALLAH ZAKU RINƘA SAMUN SANA'O'IN DA ZASU RINƘA YI A CIKIN GIDA DAN TSIRA DA MUTUNCINKU WANDA KUMA JAMA'A ZASU SAYA, DAN DIK KAYAN AMFANI WAƊAN DA AKE AMFANI DA SU YAU DA GOBE ZAN KOYA MAKU, WAƊAN DA DOLE ZA'A SAYESU DA AMFANI.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





19



••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

KINGDOM OF POWER.

Zaune Momma, Mama Haulat and aunty MieMie suke a parlourn momma, mama Haulat tana zaune a ƙasa, Aunty MieMie da momma a saman sofa, babyn Khadija yana rike hannun momma, ya sha kwalliya cikin wasu irin kayan sanyi masu bala'in kyau wanda momma da kanta tasa uncle Taheer ya je shopping ya saya mata su, kayan baby dayawa ya sayo mata, yaro sai sakawa yake yana kara canzawa abinsa, har ya murmure, amma matsalar ɗaya shi ne bai samu nonon uwa ba, ko sau ɗaya bai ɗanɗana ba, Allah sarki.

Cikin sanyin murya momma ta fara magana tana kallan Aunty MieMie. "Raeesa kamar yadda na faɗa maki cewar wannan yarinya matar Jaish ce to hakan take, yau da safe na same shi a bedroom ɗinsa domin muyi maganar da shi, sai ya nuna mun shi wlh baya santa, hasali ma ba zai taɓa zama da yar kauye wadda bata yi karatu ba, ya nuna baya santa kuma ba zai taɓa santa ba, har da ce mun shi bashi da lokacin mace a yanzu, shi ma daddynku ya kafe a kan bayan santa, wai sai dai a warware wannan aure".

Ɗan zaro idanu Aunty MieMie ta yi, cike da mamaki ta ce. "Amma kuma momma menene laifin yarinyar nan da zasu ce basa sonta?". Allah sarki, ita Aunty MieMie ko kaɗan bata ji kyamarsu Mahreen ba, wato mufa Nigerians dik in da muke mun fita daban, jinin ɗan Nigeria musamman ɗan arewa ci wlh baya kyamar kowacce yare da kabila, zama muke da kowa da zuciya ɗaya, sai dai a nuna mana kabilanci da wariya, amma mu bana nunawa, kowa ɗaya muka ɗaukesa, lallai ya tabbata jinin Nigerians na gudu a jikin Aunty MieMie, jama'a ku tafa mata, bata bar gida ba baiwar Allah.

"Hmmm shi dai Jaish kin ji dalilinsa, wai saboda yar kauye, yar datti, ba karatu ce yasa baya santa". Cewar Momma kenan.

Ɗan siririn tsaki Aunty MieMie ta je. "To shi kuma daddy menene dalilansa na kinta?". Cewar Aunty MieMie.

Shiru momma ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. "Saboda kin san halinsa ai, wai akwai qualities da yake sanwa ƴaƴansa a matan da zasu aura".

"To yaga ita Mahnoor ɗin ne da zai ce bata yi ba?".
Kai momma ta girgiza mata kafin ta amsa da. "A'a bai ganta ba tukun nan, na dai ce ya bani sati guda zan kawota ya ganta, in ya ganta sai ya yanke hukunci".

Shiru suka yi Aunty MieMie tana tinanin mafita.

Katsesu momma ta yi da cewa. "To shi ne yanzu nike san mu yi shawarat ta yadda zamu haɗa mata dik wasu qualities ɗin da suka dace ta yadda idan ya ganta zai bada goyan bayan Jaish ya zauna da ita, ni bani da matsala ta ɓangaren Jaish, dan nasan ba zai saɓa umarnina ba, matsalar daddynku ya aminta da ita ne kawai, kunga idan aka raba auren nan magana ta domin Allah an cutar da yarinyar nan da iyayenta, bana jin kamar ko shekaru 15 ta cika, sannan dik bama wannan ba, Mahnoor ta dace a matsayin matar Jaish wlh, iyayenta sun yi mana halacci na wuce misali, bai kamata mu saka masu da sharri ba".

Jinjina kai Aunty MieMie ta yi, tabbas dik abin da momma ta faɗa gaskiya ne, bai kamata a yi wa Mahnoor wani abin da ba dai'dai ba, domin yarinyar ta kai dik wani matsayin da ake buƙata matar Prince ta kasance, ta cike dik wasu qualities, ilimin bokon ne dai kawai ya rage mata wanda shi dama ai ba dashi ake zuwa lahira ba, bai zama wajibi ba, rashinsa ba zai hanata zaman aure da kyautatawa mijinta ba, ta samu babban wato ilimin addini, dik wasu abin da ake koyarwa a bokon tushensu daga inane? Dik daga litattafan addini ne, dan haka Mahnoor bata da wata gazawa. Iya shege ne kawai irin na Jaish.

"Ranki ya daɗe zan iya yin magana?". Cewar mama Haulat dake binsu da kallo....... Jinjina mata kai alamar e Momma ta yi ba tare da ta yi magana ba.

"Ni a ganina tin da haka ne ai matsala ce mai sauki, sai mu gyarata, ta sha gyara sosai, a samu wanda zai fara koya mata karatu Kafin wani ɗan lokaci, ta goge ta canza, In Sha Allah zai sota, kuma shi ma mai martaba zai kaunaceta ya karɓeta a matsayin sirika".

Jinjina kai Aunty MieMie ta yi tare da cewa. "Wannan shawara ce mai kyau, sai dai kuma ina da kari a kan shawarar".

Zuba mata idanu momma ta yi alamar tana sauraronta kenan.

Cigaba ta yi da cewa. "Momma kada ki sake yi wa Jaish maganarta, tun da kin bawa daddy sati ɗaya, to a cikin wannan sati ɗayan kada a yi magana da kowa, mama Haulat ki gyara mana ita, sai ki fara koya mata wasu abubuwan da suka dace dan kauyancin nan da rayuwa kamar na dabobi ya fita a kanta, kun san idan nan da sati ɗaya aka kaita gaban daddy ya aminta da ita to a bisa doka daga ranar zata koma part ɗin Jaish, sannan zata zamana ita kaɗai alhakin kula da cinsa da shansa zai rataya a wuyarta, kun san yadda doka yake babu wadda zata sake kusantar abin da ya danganci cinsa, shansa da wasu privacy nasa ko?".

Jinjina kai mama Haulat ta yi, ita kuma momma still dai tana binta da ido bata furta word ba.

Cigaba ta yi da cewa. "Dole za'a haɗata da mama Haulat a part ɗin nasa dan ta tayata yakarsa, kun san halin Jaish da shegiyar murɗiya, mama Haulat ai ɗan ɗakinki ne shi kin san halinsa, dan haka ke zaki ɗaurata a hanyar da ta dace domin ta tabbata a matsayin matarsa ya kuma sota, dan haka wannan ragama mun rataya maki shi a wuyarki ko ya kika ce momma?". Ta kai karshen maganar tana tsayar da idanunta a kan momma.

Jinjina momma ta yi, sannan ta ce. "Tabbas wannan shawara ta yi, yanzu Haulat ki dage kafin nan da sati guda ki canza mun ita, ta yi kyau sosai, idan Allah ya ɗoramu a kan daddynsu muka yi nasara sai ki bita part ɗin Jaish ɗin kina cigaba da koya mata abubuwa da yi mata gyara, ban yarda da wata kuyanga da ta shiga lamarinsu ba face ke, da ke kaɗai na yarda a gidan nan, nasan zaki kula da su dikkansu biyu, kin san abin da yake so da wanda baya so, dan haka sai ki ɗaurata a kan hanyar da ta dace, wlh ina san Jaish da wannan yarinya, ban san dalili ba".

Cikin girmamawa mama Haulat ta karɓi wannan ragama da suka bata tare da tambayar ko akwai wani abin da za'a ƙara sanar da ita?. Aunty MieMie ce ta amsa mata da babu komai zata iya tafiya ta je ta fara aikinta daga yanzu, wato ta je ta ɗaukesu izuwa wajen gyara yanzu kenan, tare da Mahreen za'ayi masu komai dan a ragewa Mahreen ɗin ma wannan hauka da yake a kanta.

Miƙewa mama Haulat ta yi ya nufi waje tana yi masu addu'oi masu tasiri da ratsa zuciya.
Tana fita uncle Jahiz ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Zeezee tana biye da shi a baya, dama Aunty MieMie tana ƙoƙarin ɗaukowa momma zanjen babyn nan dake kama da shi ne sai ga shi ya shigo.

Dan haka cikin girmamawa suka gaisa. Saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna tare da umartan Zee da ta zauna a kusa da Aunty MieMie.

Kin yarda ta yi, ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai, ta ji sauki sosai jiki ya yi kyau Masha Allah, ita dai ta samu sallama, saura Khadija da mai keken napep ɗinsu da shi ma ya farfaɗo yana ta fama da nashi jinyar bawan Allah.

Zee na ƙoƙarin zama a ƙasa idanunta suka hango mata babyn Khadija dake hannun Momma, ai kuwa zubur ta miƙe, ita da bata san a ina take ba, bata san ba a gidan wargi take ba, bata san a gidan sarauta masu izza da ji da kansu take ba, sai ta miƙe a zabure tare da nufar momma da nufin ta kwace babyn.

Tsawa Aunty MieMie ta daka mata tana faɗin basa san shirmen banza, ita bata san a gaban wa take bane? Gaban princess Rahilarh take, dole ta nitsu ta jira komai sai an bata izini, su sarauta ba'ayi masu irin wannan wautar.

Shi ma uncle Jahiz dama ya buɗe baki zai dakatar da ita daga tinkarar momma ɗin ne sai Aunty MieMie ta rigasa, dan haka sai ya ja bakinsa ta datseta cif.

Allah sarki Zee, jikinta sai rawa yake yi, burinta ta karɓi ɗanta ɗan ƴar uwarta, yau sama da sari biyu kenan tana rokon da abata shi ta ga jininta, amma bata samu dama ba, ta tsumu da san ganinsa har ta gaji, kullun idan uncle Jahiz ya je dubasu sai ta yi mashi kukan ina yaronta, yau dai da aka basu sallama sai ya ce ta zo su je ta ga ɗanta, shiysa yanzu da ta gansa ɗauki yasa ta rasa nitsuwarta, ta rasa control ɗinta, kuma ya haɗu da bata san a gaban wa take ba, shiysa ta yi saurin miƙewa zata je ta karɓesa, shi kawai idanunta yake hango mata, sam bata ga su momma ba baiwar Allah.

Ai ƙasa komawa mazauninta ta yi, sai kawai ta tsaya a wajen cak tare da rushewa da kuka mai tsuma zuciya, dama a kusa take, kiris take jira ta fashe dama.

Da saurin uncle Jahiz ya miƙe ya nufota, cike da gimamawa ya fara faɗin. "Sarauniya momma ayi mana afuwa, na tabbata ɗauki ganin babyn yasa ta rasa control ɗinta, and bana tinanin tasan in da take shiysa dik ta yi wannan shirmen". Ya kai karshen maganar yana rike hannunta.

Baya kaɗan ya jata izuwa in da ta miƙe, cikin nitsuwa ya mayar da ita ya zaunar.

Momma da tausayin Zee ya gama narkar da zuciyarta ne ta umarci da su rabu da ita ta matso taga ɗanta, ai jini ba wasa ba. A tinanin momma Zee ita ce uwar ɗan.

Ai Zee tana jin an bata dama ta yi saurin miƙewa ta isa gaban momma, jikinta har rawa yake yi wajen kai hannu, tin ba'a miƙo mata shi ba ta karɓesa. Aunty MieMie ma tausayinta ta ji ya kamata, Allah sarki jini ba wasa ba, sai kerma hannunta yake yi ta rike yaron gam idanunta suna ciccikowa da kwallah.

Momma mace mai dattaku, hannu ta kai tana dan shafa kanta da yake Zee ta zube gwiwowinta a ƙasa gaban momma ɗin ne da ta karɓi yaron. Rarrashinta momma ta fara

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login