Showing 378001 words to 381000 words out of 403653 words

Chapter 127 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

103

ba, shiyasa take sonsu, dan haka cike da murna ta bar ɗakin ta nufi part ɗinsu. Su kuma suna shiga tsara tsarin yadda zasu yi da Pretty ba tare da kowa ya ganosu ba!! ME KUKE TINANIN ZASU SHIRYA MATA?.

---------------------------------------------🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Wasu irin shegun kaya Big Bro ya saya masu, kayane da basu taɓa ganin irinsa ba, kuma iri ɗaya ne ita da shi, komai nasu iri ɗaya tamkar tagwaye, har takalma dik iri guda, sai dai na Ronnie takalmar akwai ratsin baƙi kaɗan a ta kasa, nata kuma babu, amma ban komai iri ɗaya ne. Wani irin daɗi da ta ji bata san lokacin da ta daka tsalle ta haye jikin Ronnie tana dariya ba, shima rungumeta ya yi yana murmushi, kayan sun yi fitina ba kaɗan ba, gown ɗin nan nata ba'a magana.

Juyi da ita Ronnie ya fara yi a cikin ɗakin suna dariya gwanin birgewa. Lokaci guda kuma Ronnie ya dakata cak, a hankali ya sauketa ƙasa, saboda ya tina Floris, last year da ita aka yi shagali, yanzu kuma babu ita, take idanunsa da mood ɗinsa suka canza, wucewa ya yi ya sauna a gefen bed kusa da kayan. Sweetie sarkin basira ta gane me matsalarsa, ga kuma alkawarin da ta yi wa Big Bro na ba zata taɓa barinsa ya shiga damuwa ba.

Da sauri ta matso kusa da shi. "Lovely bro!". Ta kira sunansa da ɗan sauti. Shiru bai amsa mata ba, tin da take a rayuwarta bata taɓa yin rawa ba sai yau saboda shi, playing na music mai sauti ta yi a cikin tvnsa, sannan ta riƙo hannunsa a kan ya tashi su yi rawa. Da farko tirge mata ya yi, amma da ta ja shi da karfi sai ya miƙe, jikinsa a mace ya fara, amma da suka yi nisa take ya mance da damuwa ya saki jiki yau suka taka rawa tamkar ba gobe, ashe ita ma ta iya, yi ne kawai bata yi dama.

Dik abin da suke yi Big Bro yana kallansu, yana zaune yana shan green tea, ba karamin burgesa suka yi ba, sai ma indan suna tsaka da rawa Ronnie ya ɗagata sama ya ɗaura a saman wuyarsa, ta buɗe hannayenta kamar fanka ya fara juyi da ita suna sakin murmushi. Ronnie ya samu Sweetie ba kiba, ƴar caras sai ya yi ta ɗagata kamar ƴar tsana. Sosai suka sanyaya ran Big Bro yau.

Buga karfe 7 dai'dai da agogo ya yi ne ya dakatar da su da abin da suke yi, lokacin sallah ya yi kenan, sauketa Ronnie ya yi tare da manna mata sumbata a kumatu, sannan ya ce. "My only sis much love one in million". Sumbatarsa ita ma ta yi kafin su haɗu tare su tattare kayan nasu suka je suka shirya shi a wajen da ya dace, sannan ta shiga toilet. Shi kuma ya haye bed yana jiran ta fito!!.

AFTER SOME MINUTES.

Zaune suke a saman bed yana koya mata yadda ake amfani da waya, dan ya ce zai saya mata mai kyau, ta mai da hankalinta gabaɗaya a kan abin da yake nuna mata, cikin sanyin murya ya ce. "Sis ina san kin mun karin bayani a kan tsafi da kuma yadda yayana yake kwace ƴaƴa maza daga hannun iyayensu ya sanyasu a cikin sojojin yaki a renesu a matsayin warriors, iyayensu basu da ƴancin morarsu ko kaɗan, dik warriors ɗin nan namu da kika gani ta haya Big Bro ya tarasu". Ya kai karshen maganar tare da kashe hasken screen ɗin wayar ya ajiyeta a gefe, dan karatu zasu yi.

"Tsafi wannan dogon karatu ne, zan ɗauko maka tarihinsa daga farko ne yadda aka yi ya wanzu a duniya, shi kuma raba uwa da ɗaya wannan babban kuskure kuma babban laifi wanda Allah yana iya yi wa wanda ya yi hakan mummunar hukunci ko ya aiko mashi da bala'i mai girma". Natsuwa ya yi yana sauraronta, cigaba ta yi da cewa.

"A cikin Al-Qur'ani mai girma ALLAH ya bayyana wahalar da uwa ke sha wajen samun ɗanta, wanda ke nuna girman soyayya da tausayin uwa ga ɗanta, dik wannan wahala ba zata taɓa tsanar wannan ɗa ba sai ma kauna da take yi mashi. Cikin suratul luqman sura ta 31 aya ta 14 Allah ya ce. Mun yi wa mutum wasiyya da mahaifiyarsa. Mahaifiyarsa ta ɗauke shi a cikin rauninsa da ƙari, kuma ta shayar da shi a cikin shekara biyu. Mun ce masa ka gode wa ni da iyayenka, zuwa gare ni makomar ku take, wanna yana muna maka girman uwa!!".

"Kazalika cikin suratul Abasa sura ta 80 aya ta 34 zuwa 36 Allah ya ce. A ranar da mutum zai guji ɗan'uwansa, mahaifiyarsa da mahaifinsa, matarsa da ƴaƴans. Mafi girman mutanen da zaka ji zafin rabuwa da su kenan, shi ne yasa ake kwatance da su. Wannan yana nuna cewa a duniya soyayyar uwa da ɗa tana da matuƙar ƙarfi, har yana da wahala a raba su. Rabasu ma shi ne karshen zaluncin da bawa zai yi wa mata!!"

"A cikin Bukhari Manzon Allah (SAW) ya ce. Lallai Allah yana jin tausayin bayinsa fiye da yadda uwa take jin tausayin ɗanta. Girman soyayyar dake tsakanin uwa da ɗanta babban abu ne da har Allah yake kwatance da shi Manzon Allah ma yake kwatance da shi. Wannan hadisi yana nuna irin ƙauna da kulawa da uwa take ma ɗanta, wanda idan aka raba su, yana da matuƙar wahala ga ita da yaron ma gabaɗaya".

"Kazalika cikin tirmidhi Manzon Allah (SAW) ya haramta raba uwa da ɗanta, ku ji fa haramtawa ya yi, har ya ce. Dik wanda ya raba uwa da ɗanta, Allah zai raba shi da ƙaunarsa a ranar Alƙiyama, innalilahi wa inna ilahir, kaga kenan abin babba ne sosai!!".

"Raba uwa da ɗanta abu ne mai matuƙar raɗaɗi, kuma addinin Musulunci ya hana hakan. Iyayen suna da haƙƙi a kan ƴaƴansu, kuma raba su ba tare da wani dalili na shari'a ba babban zalunci ne, gaskiya yakamata mu yi dik mai yiwuwa wajen dakatar da Big Bro daga raba ƴaƴa da iyayensu, idan ba haka wlh wata balai tana gab da afka mashi, saboda dik abin da ka ji Manzon Allah (SAW) ya haramta to ba kara mun abu bane". Ta kai karshen maganar tare da ɗago kallonta a kansa. Gabaɗaya mood ɗinsa ya canza, ya shiga damuwa jikinsa dik ya yi sanyi.

Cigaba ta yi da cewa. "Batu a kan tsafi kuma wani abu ne da Allah ya la'anci masu yi, ba abu bane mai kyau, bari in ɗauko maka shi daga farko, a cikin suratul Baqarah sura ta 2 ayata 102 Allah ya ambaci Harut da Marut, wasu mala'iku ne guda biyu da Allah ya saukar zuwa ƙasa a zamanin Annabi Sulaiman (A.S) domin su jarabta mutane da ilimin sihiri (tsafi). A lokacin mutane da yawa sun fara amfani da tsafi don cutar da wasu, musamman ma dan raba miji da mata, ko dan cimma wata mummunar manufa nasu. Allah ya aiko da Harut da Marut zuwa garin Babila wato Babylon a Iraki, domin su gwada mutane da basu ilimin sihiri, amma kafin su koyar da wani, sai su ce masa. Mu fitina ne, kada ka yi kafirci. Wato suna faɗawa mutum cewa. Wannan ilimi ba domin amfani da shi bane. Mu kawai jarabawa muke yi kar ka yi amfani da shi zaka fita daga addini!!"

"Yayin da mutane suka cigaba da karɓar wannan ilimi, da yawa daga cikinsu sun yi amfani da shi wajen cutar da juna. Allah ya nuna cewa wannan ba nufinsa bane, kuma wannan ilimin bai fito daga Annabi Sulaiman ba. Annabi Sulaiman bai taɓa yin sihiri ba! Kuma bai koyar da shi ba, shayatu ne suka buɗe ƙofofin tsafi ga mutane, sannan Harut da Marut suka kasance jarabawa ga masu raunin imani".

"Amma a yau an canza maganar, mutane suna amfani da ruwayoyin israiliyat da suke cewa akwai Mala'iku guda biyu da suka bijirewa Allah har ya kawosu duniya, wanda nasan kai ma ka karanta wannan ruwaya". Ta yi maganar tare da dakatawa tana kallonsa. Shiru ya ɗan yi kamar yana tinanin shin ya karanta ne ko bai karanta ba?.

(My people's kun san me? Wlh rubuta sunan israiliyat yana ban wahala sosai😅 wani lokaci sai na zo rubutawa sai in saka ilsiyat😅 kai ko karanta sunan akwai wahala, israiliyat😅)

"Ka manta ko?". Ta jefa mashi tambaya, kai ya gyaɗa mata alamar e. "Ni ban manta yadda yake a rubuce a littafan yahudawa da kiristoci ba, bari in faɗa maka ko zaka tina. Cewa suke yi Harut da Marut sun faɗi wata jarabawa daga Allah, inda suka sauko duniya cikin surar mutume ba tare da izinin Allah ba. A ƙarshe, sun ci jarabawar, sun yi kuskure, sai Allah ya azabtar da su. Akwai labarai da ke cewa Allah ya zaɓi su su zaɓi azaba a duniya ko azaba a lahira, sai suka zaɓi su sha azaba a duniya. Wasu riwayoyin har suna cewa suna rataye a cikin rami a Babylon suna shan azaba har yanzu. Dan haka babu wani Mala'ika da ya saɓa maganar Allah, sai shaiɗan wanda girman kansa ya ja mashi, in short tsafi abu ne wanda Allah ya harabta shi gabaɗaya, ina fatan Big Bro ya dai'na". Ta kai karshen maganar tare da jan kumatunsa, ya yi shiru ya tsareta da kallo.

"Sweetie waye ya baki magic to ke?". Yadda ya yi tambayar ka rantse da ALLAH ba shi ya yita ba.
Ɗan zaro mashi idanu ta yi har sai da yaga kyallin idanun nata a idonsa. "Ni ma wlh ban sani ba, rana tsaka kawai na gansa, amma ina ga wanna ina zargin wani abin". "Kamar me kenan?!". Shiri ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Zan faɗa maka gaba, yanzu dai zo mu yi karatu, ina san ka koya mun wani karatu".

Gabaɗaya mood ɗinsa ya canza, saboda ya ji bala'i zai iya saukowa yayansa, ba zai iya jurar hakan na, so hankalinsa a tashe. "Jeki ki kawo books ɗinki mu yi karatun". Ya faɗa yana ɗauko wayarsa zai duba time, so yake ya ga ko lokacin yin dinner ɗinsu ya yi ne. Saura 30 mins su ci abincin, dan haka yana da lokaci koya mata karatu, idan suka ci abinci kuma bedroom na Black Tiger zasu wuce su je su takurawa rayuwarsa da hira!!.
======🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



59


Tattaro takardunta ta yi ta dawo kusa da shi ta zauna, ajiye wayarsa ya yi, dik mood ɗinsa babu daɗi, ya ji matuƙar damuwa a kan yayansa, hankalinsa ya tashi, haka ya hau koya mata karatu cikin natsuwa da fahimta yadda zai shiga kwakwalwarta sosai. Tana bala'in son karatu sosai yarinyar nan, ga ƙwaƙwalwar tata kuma akwai ja ba karya.

Sun yi nisa cikin karatun da suke sai jin voice ɗinsa ta yi ya ce. "Sis ranar kin ambaci yayana da sunan Fir'auna, kin ce zalincinsa kamar na Fir'auna wanenen shi Fir'auna ɗin?". Shi dai a dame yake, yana san a ce ga abu guda ɗaya da yayansa yake yi na kirki, amma babu, kome zalinci yayansa yake yi. Shiru ta ɗan yi tana tinanin a yaushe ta ce wa Black Tiger azzalumi Fir'auna kuma? Lallai ba shakka Ronnie yana kaunar yayansa sosai, wato dik abin da aka danganta yayansa da shi baya manta wannan abin.

Can ta tuna a ranar da yake kona mutanen birnin da wuta, tabbas a wannan rana ta kirasa da azzalumi Fir'auna kawai, still a ranar da ya ce zai konata ita ma har ya kaita daji ya ɗaure, ba shakka a wannan rana ma ta kirasa bakin azzalumi kuma Fir'auna, lallai Ronnie, wato bai manta ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Ɓacin rai yasa na kirasa da wannan suna, amma ba haka bane, zalincin da yake yi ne ya bakanta mun rai"........ Yana rubuta mata wani note ya ce. "Okey Fir'auna azzalumi ne kenan? Shiyasa kika danganta shi da yayana?". Ya kai karshen maganar yana ajiye pen dake hannunsa, kai my people's Ronnie yana da very very good hand writing, wlh rubutunsa ba dai kyau ba!!.

"E gaskiya Fir'auna azzalumi ne sosai, yayanka yana kwace yayan mutane ya mayar da su sojojin yakinsa dan ya tara runduna mai razanar da zuƙatan manyan masarautu, ya kuma yaki dik masarautar da yake so saboda karfin sojojin yaki, shi kuma Fir'auna yana kashe dik wani yaro namiji da za'a haifa a Masar, dan baya son a samu wani namiji da zai girma har ya kwaci mulkinsa, bokayen fadarsa ne suka shaida mashi da za'a haifo wani yaro daga cikin banu Isra'ila wanda zai tsigesa daga kan mulki ya mulki kasar, wannan dalilin yasa fir'auna yake kwace yaya maza yake kashesu, amma da Allah ya tashi nuna mashi shi Allah ya sha gaban tinanin ɗan adam, sai yasa fir'aunan da kansa ya reni Annabi Musa ɗin har zuwa girma, kuma ya yi sanadiyar hallakarsa, so yayanka bai da zalunci kamar na Fir'auna, ka kwantar da hankalinka, shi kuskuren da yake in da yake kwace ƴaƴa maza ya rabasu da iyayensu ya mayar da su warriors dan kawai ya zama mai karfin iko a duniya!!".

Shiru ya yi yana kallon ɗan bakinta. "Har yanzu baki faɗa mun wanenen Fir'auna ɗin ba ai! Ni yanzu ban san waye shi ba da har yake kashe ƴaƴa maza!". .......... Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce.

"Fir'auna yana ɗaya daga cikin manyan sarakunan Masarawa, kuma Alqur'ani ya ambaci shi sau dayawa a matsayin mai girman kai da zalunci. Ya kasance mai mulkin kama karya wanda ya zalunci banu Isra'ila, yana da'awar cewa shi ne UBANGIJI. Amma a ƙarshe, ALLAH ya kunyata shi kuma ya hallaka shi a cikin ruwa. Ba'a taɓa tantirin ɗan iska biyun Fir'auna ba, kuma daga kansa ba za'a sake ba!! Fir'auna yasan gaskiya amma yake take sani, bakin munafuki ne azzalumi!, karfin mulkinsa ya wuci yadda kake tunani!!!".

"Fir'auna yana da ƙarfi sosai a lokacin da yake mulki. Alqur'ani ya bayyana wasu abubuwa da ke nuna ƙarfinsa. A cikin suratu Zukhruf, sura ta 43 aya ta 51 ALLAH ya ce. Fir'auna ya ce. Ya ku mutanena! Ashe ba ni ne mai mulkin Misra ba, kuma ga waɗannan rafukan ruwa suna gudana daga ƙarƙashina? To shin ba kwa gani ne?"

"Cikin suratul Qasas sura ta 28 aya ta 38, Fir'auna ya ce. Ya ku shugabanni! Ban san wani abin bauta wa gare ku ba sai ni. To ya Haman! Ka hura mini wuta a kan tubali, sa'an nan ka gina mini hasumiya, dan in iya hawa zuwa ga UBANGIJIN Musa. Kuma lalle ne, ina ganin shi mai ƙarya ne, innalilahi wa inna ilahir rajiun!!. Wannan yana nuna girman kai da alfaharin Fir'auna da mulkinsa, har yana isgili da cewa zai hau zuwa ga UBANGIJI dik dan ya nunawa mutanensa karfin ikonsa da isa wanda zai yi amfani da hakan wajen tilasta masu su bauta mashi!!"

Cikin suratul Qasas sura ta 28 aya ta 4. ALLAH ya ce Lalle ne, Fir'auna ya yi girman kai a cikin ƙasa, kuma ya raba jama'arsa kungiyoyi. Yana raunana wata ƙungiya daga cikinsu, yana kisan ƴaƴansu maza, yana barin mata su rayu. Lalle ne shi mai ɓarna ne. Fir'auna ya bautar da Banu Isra’ila, yana tilasta musu aiki tukuru a matsayin bayi, zaluncinsa ma ba zai faɗu ba!"

"Amma da yake ALLAH gafurur rahim ne, sai ya aiko Annabi Musa (AS) da wahayi dan ya kira Fir'auna zuwa ga gaskiya, amma Fir'auna ya ƙi. Cikin suratul Taha sura ta 20 aya ta 24 ALLAH ya ce. Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle shi ya ƙetare iyaka, kada ka manta Fir'auna shi ya reni Annabi Musa ɗin har ya girma, shi ne ma yasa ya rai'na Annabi Musa sosai, sannan Annabi Musa baya iya yin magana saboda harshensa a naɗe take bata fitar da magana, cikin suratul Zukhruf sura ta 43 ayata 52 Fir'auna ya ce. Ko kuwa ni ne mafi alkhairi daga wannan wanda ba shi da kimar magana, kuma kusan ba zai iya bayyana magana ba?. Fir'auna ya raina Musa saboda ba shi da harshen da ke fita da kyau, har isgili yake yi mashi a kan maganarsa!!"

"Sannan Fir'auna ya kirawo bokayensa dan su fafata da Musa, amma Allah ya kunyata su. A zamanin Fir'auna sihiri ya kasance sanannen abu, kuma bokaye sun yi amfani da shi dan cin galaba kan Musa (AS). Fir'auna ya nemi su yi sihiri dan su nuna cewa shi ne mai iko, amma Allah ya nuna cewa sihirinsu ba komai ba ne.
"Cikin suratul A'raf, sura ta 7 aya ta 116 da117 annabi Musa ya ce. Ku jefa abin da kuke jefawa. Sai da suka jefa sai suka sihirce idon mutane kuma suka razana su, suka zo da babban sihiri. Sai muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa. Ka jefa sandarka. Sai ga shi tana haɗiye abin da suka yi ƙarya da shi".

"Cikin Suratul TaHa sura ta 20 aya ta 66 zuwa 69 ALLAH ya ce. A'a ku jefa. Sai ga igiyoyinsu da sandunansu suna ɗanɗanawa kamar su masu tafiya saboda sihiri. Sai Musa ya ji tsoro a zuciyarsa. Muka ce mashi. Kada ka ji tsoro! Lallai kai ne mafi rinjaye, ka jefa abin da ke hannunka, zai hadiye abin da suka aikata. Lallai abin da suka aikata sihiri ne, kuma ba zai yi nasara ba!!".

"Waɗannan ayoyi sun bayyana cewa Fir'auna ya dogara da sihiri ne, amma Allah ya kunyata bokayensa ta hanyar annabi Musa (AS). Kuma kaga dik iskanci da girman kan nan na fir'auna?". Ta jefa mashi tambayar tana kallonsa, kai ya gyaɗa mata alamr e, nisawa ta ɗan yi kafin ta cigaba da cewa. "Dik iskancinsan nan yana bala'in tsoron mutuwa kamar ransa, ka lura, dik mai aikata laifuka wlh bala'in tsoron mutuwa ne da shi, bawan ALLAH baya tsoron mutuwa! Amma fa a lokacin da mutuwar ta riskesa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login