Showing 363001 words to 366000 words out of 403653 words
ya ɓoye mata, shi dai burinsa yayansa ya dawo hanyar tsira, shi ai ya ɗanɗani daɗin musulunci har sha'awa yake yi wa wani, Allahu Akbar, musulunci duniya!! Musulunci ya yi, wanda baya musulunci wlh an barsa a wahalarce, ya kuma bonu ya lallace!! Yanzu dai Ronnie ma ya shirya na shi plant ɗin, zai baza capacitynsa ba tare da saninsu ba. Sai dai shi kuma Ronnie ɗin abin da bai sani ba shi ne, DUNIYAR SHAIƊANU ba zasu taɓa barin Black Tiger ya yi aure ko ya yi soyayya ba sai dai wani ikon Allah, amma wlh babu batun so ko aure a tsarin da suka tsara mashi da sihirinsu tin yana yaro, sai dai mu musulmai mun san suna nasu ne Allah kuma shi ne the best planner, ya gama tsarawa Black Tiger dik wani abin da zai yi a rayuwarsa. A tsarin DUNIYAR SHAIƊANU manyan malamansu ma masu takewa mahaifin Black Tiger baya basu da ikon yin soyayya ko aure, dan sun ce mata rauni ne, su ba zasu taɓa yarda da abin da zai raunata zuƙatansu ba, mahaifin Black Tiger shi ne kaɗai aka amincewa da ya rinƙa tarewa da mace, shi ma ɗin kuma idan ya tare da mace har ta samu ciki ta haihu, to tana haihuwa za'a kashe uwar su ɗauki ɗan, dan a cewarsu uwa mace barinta haɗari ne, dan mata suna da zuciya mai rauni da tausayi sosai, so zata iya koyawa yaron rauni da tausayi. Ga dikkan alamu ita ma mahaifiyar Black Tiger kasheta suka yi. (Ni kam ma anya ba gawarta bane suka yi mutun mutuminta a cikin fadarsu na in da na ce maku sun cakawa mace wani dogon karfe tin dafa bakinta har ya fito ta gabanta? Kun tina wajen? Da alama tin da aka yi gunkinta ita ce matar shugaban nasu wato uban Black Tiger kenan)
Bala'i can, akwai cakwakiyar na gasken gaske. Amma my people's ya kuke gani idan Allah yasa Black Tiger ya musulunta, kuma yasan daɗin uwa ya fara neman uwarsa? Me zai faru?.
Uhm gaskiya musuluntar Black Tiger yana da matuƙar wahala, saboda ko da ya so su ba zasu kyalesa ba, dan ma dai yana cikin killacewar da babansa ya yi mashi ne, amma dik ranar da ya fito shikenan ya koma cikinsu, yanzu haka sai shirin yadda zasu samu su ɗaukesa suke yi, akwai kalubale mai girman gaske a gaban Ronnie da Sweetie, amma da yake Sweetie ba haka ta zauna ba, tana kai kukanta ga Allah tana faɗa mashi sunan Black Tiger a kowacce Sallah nata idan ta yi, da izinin Allah kuma Allah ba zai basu kunya ba!!.
Kai my people's kun ji Ronnie ko? Zai jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, wai ya yi wa Black Tiger and Sweetie wayo su kamu da san juna! shi ma fa ɗan duniya ne wasa wasa!!.
Yana tsaye ta iso in da yake, zagowa ta yi ta gabansa ta tsaya!. "Shi ne zaka ganni kamar baka ganni ba ka wuce ko?". Ta jefa mashi tambayar kamar zata saka mashi kuka. Shiru bai tankata ba, sai ma da ya ɗan kara ɗaure angry face ɗinsa. "Kasan me? Kome ka yi kyau yake maka, da ka ɗaure fuskarma ka kara kyau ne".......... KALAMAN RONNIE TAKE YI MASHI, DIK SHI YA KOYA MATA!!
Idanunsa a kan kirjinta bai ce ko uppan ba, kunga yanayin rigar tata, so yana iya kallan tudun tula tulanta. Yatsun hannunta ta kyasta mashi a saman face ɗinsa, nisawa ya ɗan yi tare da cewa.
"Ke wai bakya jin tsoro ne a rayuwarki?". Zazzakar muryarsa ya daki dodan kunnuwanta.
Ɗan siririn murmushi ta saki wanda har sai da fararen hakwaranta suka bayyana.
"Menene kuma tsoro?". Ta yi maganar tare da gyara rigar jikinta da kyau. Sai ka ce dole aka sakata ta sanya rigar, ta biyewa Ronnie zai yi mata wayo bata sani ba, wato fa dik iliminka idan mutum ya rigaka zuwa duniya to fa wani abin sai ka sarara mashi! Yanzu dai ya nuna mata fifikon shekaru!.
Kasa yin magana ya yi ya tsareta da idanu yana kallon tula tulanta da suke tsole mashi idanu a maimakon face ɗinta.
Ƴan yatsun hannunta guda biyu ta sake kyasta mashi a saitin face ɗinsa tare da hura chewing gum da take tauna ta yi balo balo kenan.
Kamar wani maras gaskiya da sauri ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta yana wani ɗaure fuska irin ya basar ta kamashi yana kallonsu ɗin nan.
"Big bro, face ɗina fa zaka kalla mu yi magana ba wani waje ba, da ni kake magana ba da kirjina ba, wai nace ba, mema kake kallo a kirjin nawa? Ko dai............". Dakatawa ta yi da yin maganar ta kasa ƙarisawa sakamakon zaro mata kaifafan sexy eyes ɗin nan nasa da ya yi.
Wato wannan ƙaddarar tasa ta zama tacacciyar ƴar ikka, kuma yasan dik waye ya ja mashi hakan, dole ya ɗauki mataki, yarinya ce ta wuci dik yadda yake tunani, yanzu ya shiga uku tun da ta kama shi yana kalle mata tula tula, wannan zance ba zai tsaya iya nan ba, to wai ma me ya kaisa? Shi anya ba zai ɓatar da yarinyar nan ba kowa ya huta?.
Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da, ai ba zaka iya ɓatar da ita ba, ka manta ita ɗin kaddarar ka ce, zama da ita dole, wannan shi ne ba saki ba karin aure, mutu ka raba takalmin kaza in ji hausawa..............😂
Kai Hasbunallahu wani'imal wakil, wato ana wani iyashege a wannan gida.😂🥱
Zata sake yin magana tana ƙoƙarin huro chewing gum ɗinta ya ɗan sanya mata zarra ta hanyar matsar da face ɗinsa dab da ita yana zare mata ido. Ai a miliyan ta yi baya, ta tsorata sosai. Ɗan gocewa high heel na kafarta ya yi saboda baya da ta ɗan yi ba shiri, hakan yasa chewing gum da ta huro ya ɓata mata fuska, tafita ta yi ta zube ƙasa a saman gwiwowinta!. Wuceta ya yi da sauri ya sauka ƙasa, dan tana neman kawo mashi wani sabon al'amari.
Turo baki ta yi, a fili ta ce. "Allah ba zan barka ba, tin da ka sanya na faɗi kasa kuma na ɓata face ɗina da chewing gum sai na ɗauki fansa, ai a yarjejeniyarmu mun yi da kai ba zaka taɓa mun abin da bana so ba kuma ba zaka taɓa bari na cutu ba, amma da kanka ka cutar dani yanzu". ME KUKE TINANIN ZATA YI MASHI?.
Tana ƙoƙarin miƙewa Ronnie ya hauro sama da gudu yana faɗin. "Sister come and see our surprise, Big Bro ya yi mana surprised mai matuƙar kayatarwa, za'ayi shagali a ranar white Happy and Sad day ɗinmu, zamu fi kowa kyau".
MEMENE WHITE HAPPY AND SAD DAY?
kalar fari shi ne fav kalar Black Tiger, wannan dalilin yasa ya sanyawa wannan rana sunan white Happy and Sad day, sau ɗaya suke shagalin wannan rana a shekara, rana ce da babansa ya mutu, kuma rana ce da a cikinta babansa ya karɓawa birnin Black world takardar zama ƙasa mai cin gashin kanta, wato rana ce da suka samu ƴancin kai! So ranar suna shagali da rana, da daddare kuma su yi kuka da jimamin mutuwar babansa, the whole ranar white clothes suke sanyawa, komai fari tas............ Wato babu kamar addinin musulunci fa my people's, wai ayi shagali da rana, da daddare kuma ayi kuka na jimami, kai jama'a Allah ka dawwamar da mu a cikin musulunci!!.
Miƙewa ta yi tana faɗin. "Menene white Happy and Sad day kuma?". Hannunta ya zo ya riko yana faɗin. "Muje ki ga kayan da Big Bro yasa aka kawo mana daga kasar England, idan kika gani zan faɗa maki menene white Happy and Sad day da irin shagali da kuka da muke yi"...... "Shagali da kuka kuma?". Ta tambaya cike da mamaki......... Wai shagali da kuka, dole kanta ya kulle...................... "Let's go zan yi maki bayani idan muka je bedroom". Ya kai karshen tare da jan hannunta, bayansa kawai ta bi mamaki kamar ya kasheta!!. My people's wannan rana ta W.H.S.D ɗin nan nasu fa ba ƙaramin gagarumin rana bane wanda kura zai tashi a cikinsa, uhm zamu sha shagali kuma mu sha kuka, kowacce shekara da Floris ake yi, amma wannan babu ita.............. 😥💔
-----------------------------------------------🔥
🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER.🔥🔥🔥
A yau jirgin momma ya ɗaga zuwa Dubai, tamkar Smart ya zuba ruwa a ƙasa ya sha haka yake ji, ya ji daɗin tafiyanta matuƙa, ta so tafiya da Auta dan ta kaita can ko zata huta ta ji sauki, amma King ya hana, saboda ya ƙasa samun natsuwa, yana cikin fargaba da tashin hankali, dan yana ganin kamar zai rasata ne kawai, saboda dik yadda kuke tinani abin ya wuci nan, Zunaira ta lallace ta rame, tamkar mai ciwon H.I.V, abin gwanin ban tausayi, uncle Jahiz sam baya san zuwa wajenta, saboda tana saka shi kwallah!.
Zaune take tare da Chuchu a saman bed a cikin part da aka kaita, sai ƙoƙarin janta da hira Chuchu take yi domin su samu ta ɗan saki jiki da su, sai dai ina, dik hiran da Chuchu take yi mata taki tofa ko uppan, kanta a ƙasa tana kallan yatsun hannunta da suke ɓulɓul a da, yanzu sun rame sosai, kamar ba nata ba!.
Dafata Chuchu ta yi tana faɗin. "Auta dan Allah ki ce wani abin mana! Tsawon awa biyu muna tare, ni kaɗai nike ta yin magana kinki ki amsani, kina son nima in kara ciwo a kan wanda nike ciki ne?". Cikin raunatacciyar murya Chuchu ta yi maganar, tamkar zata yi kuka, idanunta sun cicciko da kwallah, ta rame sosai ita ma, tamkar ita take jinya!.
Kanta a kasa ta ɗan girgiza alamar bata san Chuchu ta yi ciwo, amma bata iya yin magana ba. Kara matsawa kusa da ita Chuchu ta yi, ta buɗe baki zata yi magana kenan sallamar Abdussalam ya katseta. Sanye yake da arabs jallabiya dark ash, shi ma ya rame sosai, saboda ciwon nata. Ganinsa yasa Chuchu ta miƙe tana faɗin. "Zan dawo zuwa anjuma". Ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin.
A in da Chuchu ta tashi ya ƙarisa ya zauna, a hanzarce Auta ta ɗan ja baya tamkar wadda aka matsowa da wuta kusa da ita. Ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, cikin sanyin murya ya ce. "Zunaira ki faɗa mun dalilinki na guduna? Na tabbata yansu kam na ciwo bane! Dole akwai wani dalili, dan kin samu sauki"......... Kin yi mashi magana ta yi, sai dai har cikin ranta ta ji wani irin yadda ya kira sunanta, bai taɓa kiranta da Zunaira ba, kullum my wife yake cewa, da alama yau hakurinsa ya kare ne!.
"Ki yi magana kin ji? Ki kalleni a matsayin yayanki ba miji ba, ki faɗa mun damuwarki, ni kuma zan tsaya a wajen ganin na fitar dake daga damuwar"........... "So nike kawai ka sake ni, shi ne damuwata". Abin da ta faɗa kenan ba tare da ta ɗago da kanta ba, da kyar muryarta yake iya fita saboda kukan da ta sha. Wani irin zaro idanu Abdussalam ya yi, a hankali ya maimaita kalmar saki kafin ya ce. "Ai ko wata bare na aura ba zan saketa ba Zunaira bare ke da kike matsayin kanwata, ke da nike tsananin kauna tin kina yarinya, Allah ya mallaka mun ke ya cika mun burina kuma yanzu ki ce in sakeki? Tukun nan ma saboda me?".
Shiru ta yi mashi dan tasan ko zata mutu ba zai taɓa sakinta ba, aurensu ai babu saki, su a ƙaidar familynsu ma ba'a saki, babu wacce aka aura aka saka, ko bare suka aura nasa saki bare na gida, ai kun san wannan aure ba mai mutuwa bane!. Ganin ta yi shiru ne yasa ya kai hannunsa ya riƙo nata. Zabura ta yi zata kwace kanta ya yi gaggawar riketa da karfi, dan dole ta natsu bata iya kwacewa ba. Cikin taushi da tausasawa ya ce. "Zunaira please, ki tausaya mun, ki ji kan zuciyata, wlh ina sanki, kuma kome kike so zan yi maki, dan Allah ki faɗa mun menene yake damunki, Zunaira kalli yadda na rame fa saboda ke, please my wife, Yah Abdussalam ɗinki ne fa? Ko kin manta ne? Kin dai'na so na ne? Please kada ki bari zuciyar da bata san komai ba face sonki ta cutu, bata san komai ba sai begenki, please my wife help me and accept me as your husband, na yi maki alkawari zan sanyaki farinciki koda ni zan kuntata". Tamkar zai yi kuka ya kai karshen maganar.
Shiru ta yi idanunta suna zub da zafafan hawaye, take kalaman Hoorain suna ratso mata cikin brain ɗinta a in da yake ce mata. "Hoonairata kada ki yarda ki yi magana da wani namijin a bayan idona, ki rike mun amanar kanki, ke tawace ni kaɗai". Tina hakan yasa ta kai kallanta a kan hannunta da Abdussalam ya rike, take zuciyarta ya buga da karfi, ba iya magana da wani ba har hannunta ta bari ya rike.
Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi tare da kwace hannunta da karfi, da gudu ta miƙe ta fito parlour, ƙasa iya cigaba da tafiya ta yi, da ta so ne ta fita waje, amma sai ta ƙasa saboda jiri, bata gama samun lafiya ba, a tsakiyar parlourn ta zube gwiwowinta a kasa, rushewa ta yi da kuka mai sauti, cikin kukan ta fara sambatu kamar haka. "Am so so sorry my Hoorain, yau na karya alkawarin da na ɗauka maka, na bari wani namiji ya taɓani, ba zan yafewa kai'na ba har sai ka yafe mun, ni taka ce kai kaɗai, kai kaɗai kamar yadda kake nawa ni kaɗai". Cikin fitar hayyaci take wannan magana, sam bata lura da Chuchu dake zaune a saman sofa a cikin parlourn ba. Allah sarki Chuchu, ta kasa komawa family part ta bar autar ne, shi ne yasa ta zauna a parlourn tana jiran idan Abdussalam ya fita sai ta koma su cigaba da yin hiran.
A dai'dai wannan lokacin kuma King yana can suna kai ruwa rana da smart, ga tashin hankalin da yake ciki na ciwon Auta, ga zafafan questions da Smart ya jefesa da su. Yana tsaye a tsakiyar bedroom na daddyn nasa, yana sanye da sleeping dress, dan shirin kwanciya barci ya yi, while shi kuma King yaka zaune a saman bed ɗinsa, babu ko sallama Smart ya shigo mashi cikin ɗaki, kallo ɗaya King ɗin ya yi mashi ya kawar da kansa, a cewarsa yana fushi da Smart, a tinaninsa hakuri Smart ya zo bashi, sai dai bai san wata fitinar ce ma ta kunno kai ba.
Wai irin ya nuna ransa ya ɓaci sosai ɗin nan kuma yana fushi da shi shi ne har da wani cewa Smart ɗin. "Meya kawoka room ɗina?". Ya yi maganar yana wani ɗaure fuska. Shiru Smart ya yi yana cigaba da binsa da kallo.
"Idan ba zaka yi magana ba ka fice mun daga ɗaki". Ya faɗa yana nuna mashi hanyar fita. Man ma shiru Smart ya yi, maganganun momma na ta yi mashi yawo a kunne in da take cewa tana san su yi magana amma tafiya Dubai ya zo da sauri, dan haka idan ta dawo zasu tattauna a kan matar commander, kada ya kula kowa a gidan, ya kasance a ɗaki kamar yadda yake. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Meyasa ka cika san kanka da zalinci ne dad?". A sanyayye ya yi maganar!.
A hanzarce King ya zaro idanu yana kallansa. "Omerish ni kake cewa ina da san kai'na da kuma zalunci? Ni kam anya baka shan wani abin kuwa?"....... Idanunsa kar kan dad ɗin nasa ya ce. "Dama shi mara gaskiya a kullum cikin hargagi yake, dad baka da gaskiya, kana da zalinci da son kai, baka san zaluncinka ya tonunwa duniya shiyasa kake ƙoƙarin hahhaura abubuwa a kan wasu".
A zabure King ya zuro kafafunsa kasan bed ɗinsa, yana zaro ido kamar an tare ɓera a tarko ya ce. "Zaluncin me na yi Omerish? Dan na aurawa Zunaira wanda ya dace da rayuwarta shi ne na yi zalunci?". Ya kai karshen maganar yana miƙewa tsaye, yana wani furkaki!.
"Dad ni fa ba ɗaya nike da sauran ƴaƴanka ba, kai kanka kasan da hakan, kasan cewa yaran momma gifted ne, shiyasa kake jansu a jikinka fiye da ƴaƴan kowa saboda baka san su ja baya da kai har su fara tinanin akwai abin da kake binnewa, kasan da cewa ko da iya Omaid and Obaid aka barka sai sun tona ɓarnar da kake yi cikin ƙanƙanin lokaci bare kuma ni".
Kara firgita King ya yi yana zazzare idanu. "Omerish ya tabbata yanzu kam da gaske akwai abin da kake sha!". Ya faɗa yana nufosa. "Dad babu wani abin da nike sha, yanzu ni ba wannan ne ya kawoni ba"..... "Batun Zunaira ne ya kawoka ko? To Zunaira matar aute ce, sai ka zare bakinka a cikin maganar ta". Cewar King!!
Kai Smart ya ɗan girgiza. "Ba'a banza makiya suke kirana da Smart ba, tun da har makiyana suka yarda ni Smart ne yakamata kai ma daddy kasan ni ba irin saura bane, ba shakka batun Zunaira yana daga cikin abin da ya kawoni, amma bashi ne the best ba, the best shi ne so nike ka faɗa mun wacece uwar Ramish?! Dan dai kasan Aleezarh (Mama kenan) ba ita ta haifeshi ba!!".
Tamkar kwayar idanun King zasu fito su faɗi ƙasa, lokaci guda wani irin gumi ya wanke mashi fuska, a rikice word ɗinsa suna harhaɗewa ya ce. "Idan ba Aleezarh ce ta haifesa ba kai ne uwarsa? Wai Omerish anya kana da hankali kuwa? Lallai ba shakka Rahilarh ta mun cuta da ba zan taɓa mantawa da shi ba, ta mayar da kai mara hankali ma.......". Ƙasa ƙarisa maganar ya yi saboda tsawa da Smart ya daka mashi. "Ya isheka haka dad! Kowani lokaci