Showing 141001 words to 144000 words out of 403653 words
ta yi tana haki haɗe da sauke numfashi da karfi karfi. Har ta isa in da Abbie yake ba tare da ta sani ba, tana layi kamar wadda take a make. Tana isa dab da shi a lokacin ya sallame sallah ya miƙe dan ya je ya kunna wutar ɗakin yaga wanene ya shigo mashi ɗaki a irin wannan yanayi haka.
Yana miƙewa suka ci karo, a lokacin dik wani karfinta ya kare, tafiya ta yi zata faɗi ƙasa ya yi saurin rikota. Sai da gabansa ya faɗin jin cewa yarinya ce mace kuma kamar babu kaya a jikinta. Amma dik da haka ya yi ta maza ya rungumota a jikinsa gudun kada ta faɗi.
Da kyar ya iya riketa suka karisa gaban bed ɗinsa. Sosai ya zaro idanunsa a lokacin da wutar lamp ta haska mashi face ɗinta, a fili ta furta Leesharh da ɗan ɗaga murya.
Lokacin ta fara fita a hayyacinta, sam bata gane a hannun wa take ba, hankalinsa ne ya tashi bawan Allah, jiki na kerman mamaki ya kwantar da ita a saman gadansa. Ga bedsheets ɗinsa white color ne sosai, haka ya yi dama dama da jininta. Ɗan kawar da kallansa daga kanta ya yi duba da cewa babu sitira a jikinta, ya janyo white duv ɗinsa ya lulluɓeta da shi har saman kirjinta. Jikinsa dik ya ɓaci da jininta, dama white jallabiya ce a jikinsa.
Wajen phone set dake kusa da bedside drawer ya nufa, fili ne da aka yi sa domin ajiye waya, hannunsa har yana ɗan kerma wajen ɗauko wayarsa. Number zaratan samarin gidan nasa yake san kira ya ji menene yake faruwa a cikin gidan haka? Su zo su duba mashi me ya samu Leesharh? Waye ya yage mata kayan jikinta haka?.
Sai dai bai kai ga kunna wutar screen ɗin wayar bama bare aje ga call sai ganin ɗakin nasa ya yi ta gauraye da haske an kunna bulbs. A ɗan razane ya juyo ga switch na ɗakin.
Sanye take da sleeping gown tana tsaye a kan kafafunta, tsaresa da ido ta yi taba binsa da wani irin kallo wanda za'a iya fassara shi da kallan tuhuma. Ummie kenan.
Me kuke tinani ya kawo Ummie a dai'dai wannan lokacin? Abu kamar tasan da Leesharh a cikin ɗakin, ko da yake ɗakin mijinta ne, zata iya shiga a dik time da taga dama, ga shi kuma asuba ya kawo kai, dama za'ayi expect ɗin dik wata mace ta gari a irin wannan lokaci tana ga mijinta zata tashe shi sallar asuba ko?......🥱
From head to toe ta fara bin Abbie da kallo, abin ya yi matuƙar bata mamaki sosai, cike da zargi a idanunta ta mayar da kallanta a kan Leesharh dake kwnace a saman bed ɗinsa tana wani irin numfashi sama sama kamar zata sume.
"Omar, me zan gani kenan?". Ta faɗa tana zaro idanun, yau babu batun Abu Abdussalam, da ainahin sunansa Omar ta kirasa, mata duniya ne wlh.
Tabbas ya ji mamakin wannan suna da ta kirasa, yau sama da shekaru 30 suna a tare bata taɓa ambatar wannan suna ba sai yau, abin ya ɗan girgiza shi, nan ma wai hankalinsa bai kai ga kan abin da take zargi a ranta ba kenan, ya zaci ta tsorata ne na ganin Leesharh a cikin mawuyacin hali har ya ɗaga mata hankalinta, shiyasa har ta kirasa da Omar ba tare da ta sani ba, bai san babban bala'in dake tinkarisa ba.
"Lafiya kuwa?". Ya jefa mata tambayar cike da matsuwar san jin dalilin kiransa da ta yi da Omar ɗinsa. Amma fa bai yi mamakin ganinta a ɗakinsa a wannan lokacin ba, saboda ta saba zuwa, wani lokaci a nan take kwana, yau ta ce da Sharifat zata kwana shiyasa ta tafi ta bashi waje.
"Ni kake tambaya lafiya ma ko? Dama abin da kake aikatawa kenan? No wonder wani lokaci kake nuna cewa kafi san wannan shegiya tsintacciyar yarinyar a kan ƴar cikinka, ashe da biyu!!".
Ai Abbie bai san time da ya wani irin miƙe da kyau ya tsaya a kan kafafunsa ba, zaro mata idanu ya yi, ji ya yi tamkar an kwala mashi guduma a tsakiyar kai, da tsufarsa da mitumcinsa ne zata zargesa da abin da ko ɗansa ya kama yana yi sai ya ɗauki mummunar mataki a kansa, abin kyama, ya tsufa yana neman cikawa da imani ne zata nemi lalata mashi karshensa da banzan tinaninsu ma mata? Anya akwai hankali a kwakwalwata kuwa? Ya jefawa kansa tambaya.
A fili kuwa sai ya ce. "Ban gane me kike nufi ba?". Cikin kakkausar murya ya yi maganar.
"Taya zaka gane abin da nike nufi, dama ai shi tabarmar kunya da hauka ake naɗesa, yanzu kai babu kunya babu tsoron Allah zaka hakewa ƴar yarinyar da ko Sharifat ta fita shekaru? Ko tsoron Allah baka ji! Dubi jikinka fa, dik jini, ko tausayin yarinya baka ji ba? Wlh ba zan yarda ba, wannan ƴar iskar karuwar sai ta fita gidan nan a yanzu". Cikin faɗa da ɗaga murya ta kai karshen maganar. Tana kaiwa karshe kuma ta nufosa gadan gadan.
Ƙasa magana Abbie ya yi, ya ji bala'in da ta fi karfinsa a yau, sai ya ji abin tamkar a mafarki.
Yana can yana tinanin sai gani ya yi ta yaye duv da ya lulluɓe Leesharh da shi tana zazzaga masifar.
"Shegiya matsiyaciya, yanzu zaki fita daga gidan nan dan ubanki, karuwa kawai, dama ai na jima ina zargin akwai wata a tsakaninku, ashe kuwa zargina gaskiya ce........." Ƙasa karisa maganar ta yi sakamakon ganin Leesharh tsirara da ta yi bayan ta yaye duv ɗin kenan.
Wani irin ihu ta kurma tare da ja baya. "Shikenan zancena ya tabbata, shikenan wlh ya tabbata, da gaske ne zina suka aikata". Kamar wata zararriya haka take maganar, ga shi cikin ɗaga murya.
Ganin zata tara masu family yasa ya daka mata tsawar ta yi mashi shiru. A tinaninsa tana jin maganarsa tin da bai taɓa yin magana ta ce a'a ba, sai ya yi tinani in ya yi tsawa zata yi shiru, bai san cewa a irin wannan point ɗin mata basu da saiti sam sam ba.
Aikuwa yana daka mata tsawa ta daka uban tsalle kamar wata mahaukaciya sabon kamu, ihu ta yi tare da wurgi da duv dake hannunta wanda ya rufe Leesharh, sannan ta haye saman bed ɗin kan Leesharh, hannu tasa ta fara kaiwa Leesharh bugu babu tausayi ba imani, tana dukanta tana aika mata da muggan zagi kala kala.
Leesharh da tuni dama ta sume ai bata jiyo komai, sai zaginta take yi a kan ta tashi ta fita mata daga gida, har da ikirarin yau sai ta kasheta.
Da Abbie yaga abin is getting out of hand, zata iya cutar da Leesharh, sai ya yi yunƙurin dakatar da ita. Ai ina kin sauraransa ta yi, ta ko'ina take kaiwa Leesharh duka babu kakkautawa. Ransa ne ya yi mummunar ɓaci, zuciya ta ɗebesa ya dalla mata wani irin mari mai gigitarwa.
Ihu mai sauti ta zunduma tare da dirowa ƙasa daga kan Leesharh, ta nufi waje tana faɗin bari ta kira su Ramish sai sun zo sun fitar mata da wannan shegiyar yarinyar daga cikin gidanta, kuma kowa ya zo yaga abin da suke aikatawa, har ƴan aiki sai ta kira.
Tashin hankali, my people's me kuke tinani zai faru kuma? Kuna tunanin ya rayuwar Leesharh zata kaya a gaba?. Anya zamanta a gidan zai yiwu kuwa? Abu Abdussalam zai iya wanke kansa a kan babu abin da suke aikatawa da Leesharh kuwa? Kada ku manta a irin yanayin da yake shi da Leesharh gabaɗaya, ni dai a gaskiya ban ga ta hanyar da zai iya wanke kansa a kan wannan ƙazafi da Ummie ta yi mashi ba, dan kuwa ga Leesharh tsirara, ga jini a jikinsa shi da ita, gata a ɗakinsa a kan bed ɗinsa, meya kawota ɗakinsa nasan shi ne tambayar da kowa zai fara yi idan ya zo kan wannan case ɗin, Abbie dattijon arziki, ya kuke tinanin zai ji idan Ummie ta kira su Ramish suka zo suka ji halin da ake ciki? Akwai babban cakwakiya da tashin hankali, part na Dubai ta kama da wuta, bari mu rarrafa wani part ɗin domin mu duba meke wakana.
••••••• KINGDOM OF POWER••••••••🔥🔥🔥
A wayewar garin yau tawagar Auntynsu Jawad zasu koma in da suka fito, ƴan England zasu koma haka ƴan Saudiyya ma, dik cikinsu babu wanda ya san da batun ɓatan Auta, King ya ce a ɓoye maganar a matsayin sirri, saboda fitar maganar zai zamana gazawace a garesu, kuma abokan gaba zasu ji daɗin anyi nasarar yi masu wani abin da bashi da daɗi, za'a rai'na yanayin tsaronsu tun da za'a iya shiga har cikin gida a saci yarinya, and bugu da ƙari fitar maganar zai sa a ce ga hanya mafi sauki na ladabtar da king wato a kwashe ƴaƴansa kenan.
A takaice dai fitar bayanin ɓatar Auta babban abu ne a garesu, dan zai sa su Jaish da ake ɓoyewa su sani, Akka zata ji labari, zai haifar da munanan abubuwa da dama, dan haka sirrinta shi shi ne ya fi komai a garesu, hakan yasa King ya sirrinta hakan.
Auntysu Jawad tayi farinciki sosai na jin aure ya koma kan Jawad, dan dik bata da matsala da su. Sai dai ta so haɗuwa da Rizwan kafin ta koma, amma ina bata samu dama ba, Rizwan yaki yin waya da kowa, yama kashe wayansa ne mai gabaɗaya.
A yau ranar da zata koma gabaɗaya fam sai da suka taru a main parlour na King dan a yi sallama da juna. A nan ne Mammie take samun labaran Jannat Jawad ya aura ba Rizwan ne ya aureta ba. Idan hankalinta ya kai dubu to sai da ya tashi, sai ta ji tamkar ta mutu saboda bakinciki, burinta bai cika ba, har kasa iya zama a cikn parlourn ta yi, hankalinta a tashe ta zame jiki ta yi waje babu wanda ya lura da ita.
Shi kam uncle Abbas godiya sosai ya rinƙa yi wa Auntynsu Jawad, sam momma bata kawo masu batun auren Jaish ba, ta ɓoye tamkar yadda suka yi da su Aunty MieMie.
Sai dai kuma wani abin guda, dole ta tilastawa su commander Zafar yakar Daular Qahtaniyawa dik da a lokacin da suka dinfari wajen King Al-Mustapah ya sanar da su shi bai ɗauki gimbiya Zunaira ba, kin yarda da shi suka yi dik da commander Zafar yasan gaskiya King Al-Mustapah ya faɗa.
Commander ya jima a fagen yaki, idan gaskiya ake faɗe ya sani, haka zalika idan karya ne ma ya sani, amma haka ya take wannan sanin dan basu da wata mafita da ya wuce su yakesu, a kan umarnin King Zuhair suke yanzu, dik wata hanya da Aunty MieMie ta buƙaci da su bi dan nemo Zunaira sun bi amma babu nasara, hakan ya tilasta masu dawowa kan umarnin King suka aiwatar da yakin.
Sai dai kuma kash, ko da suka yaƙi Daular Qahtaniyawa babu Zunaira babu alamarta a ciki, sun dai yi masu ɓarna na King karawa, King Al-Mustapah ya yi mubaya'a har ya gaji amma sam babu alamar King Zuhair zai karɓi nadamarsa ya kuma yafe mashi, kafiyar bala'i King Zuhair yake da shi wlh, idan ya tambara magana babu mai iya sanya shi ya canza ya yi ta kenan.
A ranar da Auntynsu Jawad da tawagarta suka bar Kingdom of power a ranar su commander Zafar suka kaddamar da wannan yaƙin tare da dawo da labari maras daɗi wanda sam King bai so ji ba shi ne babu gimbiya Zunaira a Daular Qahtaniyawa.
Sosai ran King ya sake sosuwa, hankalinsa ya tashi, yau shi da yake kwantarwa da Momma hankali a kan wannan case ɗin, sai yazamana ita ta juyo take kwantar mashi da hankali saboda bala'in ya kai mashi bala'i, ga ɓatar Hoorain assistant commander su, abin sai ya haɗe mashi biyu.
A can ɓangare kuma, wannan dai sadauki mai ɗauke da fuska kamar ta Hoorain namu ko ma muce Hoorain namu shi ya jagoranci tawagar mayakan Queen Zarina izuwa kingdom of power.
Tabbas ɗayan biyu ne, wannan sadauki ko dai tsafi suka yi amfani da shi wajen sanya mashi irin face ɗin Hoorain dan su firgitar da Kingdom of power, dan kunsan sun san komai ta hanyar mammie, so sun san bayyanar Hoorain a cikin mayaƙansu zai iya sanyawa su yi nasara a kan Kingdom of power, dan mamakin da dangerous warriors zasu shiga ganin Hoorain a cikin mayakan Queen Zarina shi zai iya tallafa masu su yi nasara sosai.
Abu na biyu kuma shi ne ko kuma robbot suka sanya mai irin zubin halittar Hoorain, ɗaya cikin biyun nan dole suka yi, dan sak Hoorain ɗinmu yake babu banbanci komai ƙanƙantarsa.
To shi dai ya jagoranci tawagar Queen suka nufo su King wanda a lokacin King Al-Mustapah yana ta neman ta yadda za'ayi su shirya da King Zuhair, hakan yasa dik da King ya yakesu bai sa ya janye kudurinsa ba, sai ya haɗa sauran mayakansa da suka rage ya fita ya tari rundunar mayakan Queen Zarina wanda already King Zuhair ya samu labarin zuwansu, sai kuma ya samu labarin King Al-Mustapah ya tare mashi yakin.
Abinku da jinin sarauta mai karfi, dik da ya ji hakan bai wani nuna mamaki ko kaɗan ba, sai ma ya nuna kamar bai san suna yi ba, ya umarci commander Zafar da ya haɗa kan wasu zataran warriors su fita su taya su King Al-Mustapah yaki dan su kaɗai ba zasu iya da bala'in Zarina ba.
Hakan kuwa aka yi, suka fita domin tallafa masu.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥
Jawad bai zame ko'ina ba sai part na King da gudu, Jaish bai rabu da shi ba sai da ya bisa har can, dan yau ya ci alwashin sai ya kuntatawa Jawad ya ji idan da daɗi shi ma yadda ya ja mashi kima da mutuncinsa a kan titi.
Dai'dai lokacin King ya kammala shirinsa na nufar fada zai fito ya yi breakfast kenan. A bayansa Jawad ya laɓe yana haki yana hararar Jaish da ya tsaya ta gabansa yana bin daddyn nasu da kallo.
Abin ya yi matuƙar bawa Jaish mamaki ganin rama a tatare da King, tun da ya dawo dama basu wani zauna sosai ba, so bai wani san halin da suke ciki ba.
"Daddy ka ce wannan tuzurun ya rabu da ni, dan kawai na yi aurena na barshi shi ne yake jin haushina zai fasa mun baki yajawa amaryata asara". Cewar Jawad kenan, yana magana yana kara laɓewa a bayan King.
Bakinciki ne ya ƙara lulluɓe zuciyar Jaish, lallaima Jawad ya raina mashi wayo yake faɗe a cikin ransa. King da ya rasa abin faɗe ai binsu da ido kawai yake yi, a ransa yake faɗin tun suna yara suke wannan tsiya, har yanzu basu dai'na ba!.
" Ko ka zo ko kuma yau sai dai mu kwana a nan". Jaish ya faɗa ransa a ɓace, shi serious ya ɗauki abin, Jawad kuma wasa yake yi, shi fa da ace Jawad wata ya aura ba kanwarsa ba to da da sauki abin, amma tsabar cin mutuncin ya kama ya auri Chuchu da ya gama yi masu jan ido, yanzu haka kawai ya janyo mashi wani abin da ba haka nan ba, wlh ba zata saɓu ba.
Amma kuma a matsayinsa na yayan Chuchu ya ji mata daɗin ta samu mutumin kirki wanda yasan ba zata taɓa yin kuka ba a duniya, wani ɓangare na zuciyarsa ya so da ace Auta ma Jawad ya aura, kunga masoyiyar kanwarsa ba ita ba kuka, kuma har abada in dai tana matsayin matar Jawad shi zai cigaba da kula da ita.
Sai dai kash, tsakanin Jawad da Auta babu aure, shiyasa ma ya so Chuchu shi ma, da akwai aure kun san dole ita zai so shi ma, ko dan ya ramawa Momma alkhairinta a garesa, sannan kuma Auta ta fi Chuchu komai dik da ita ma Chuchun ba baya ba.
Amma babu halin ya aure Auta saboda ya sha nonon Momma a tare da Jaish, kunga babu aure a tsakaninsu, matsayin yaya yake a wajenta, kuma fa ba wani sosai ya sha nonon momma ba, kawai dai rabon auren ƴaƴan momman ne ya fita a ƙaddararsa.
"Malam bafa zan fito ka fasawa amaryata bakina ba, wai kai dan kana gwauro sai ka zalinceni ne? Daddy hasada yake yi mun dan shi bashi da wadda take son shi, ka canza wannan bakin halin naka sai ka samu koda kuyanga ce ta ce tana sonka a lallaɓata ku shiga daga c............."
Kasa kai aya ya yi sakamakon hannu da Jaish ya kai zai yi mashi wata capka ya zille yana harararsa. Ran Jaish ya ƙara ɓaci, lallai ma Jawad ya kai in da ya kai, shi yake faɗawa magana dan ya yi aure? Danasanin tafiyar da ya yi ya shiga yi, dan da yana nan wlh ba zai bari ayi wannan aure ba.
Sai yanzu na gane rabon auren Jawad da Chuchu ne ya kawar da Jaish daga kingdom of power, kun san rabo fa har kisa tana yi, babu abin da bata sakawa, so da alama rabo ta kawo sanadin wannan tafiya, dan kuwa tabbas da yana nan ba zai yarda ayi wannan aure ba, sai ya hana ya zuga a bawa Rizwan ita tun da shi Dubai zai wuce da ita.
Kaucewa capka da Jaish ɗin ya kawo mashi ya yi, yana faɗin. "Daddy ka mun tsakani da wannan gwauron, ni yanzu ba class ɗinsa bane, haka kawai zai cutar dani ya zalunceni".
King da ya fahimci Jawad wasa yake yi Jaish kuma da gaske ya ɗauki abin sai ya yi ƙoƙarin yi masu tsakani kada faɗar gaske ta tashi, yasan halin kowannensu, waɗan nan kalamai na wasa da Jawad yake jifan Jaish da shi zai iya haifar masu da gagarumin faɗa, shi kuma Jawad ɗin sam bai lura da gaske Jaish ya ɗauki abin ba. Kuma kunsan akwai wani bakinciki a gefe na batun Mahnoor a zuciyar Jaish, sai abin ta haɗe mashi yazama haushin kowa da komai yake