Showing 99001 words to 102000 words out of 403653 words

Chapter 34 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

123

yaya ya zama bakin mugu, zaki iya taimaka mun mu jawo shi cikin addinin musulunci, na tabbata in ya musulunta zai ji irin daɗi da sanyin zuciya da nike ji, tabbas dik wani black heart dake cikin kirjinsa zata washe izuwa fara tas, tabbas musulunci alkhairi ce, nima daga yarda zan shiga dik zafin zuciyata na ji ta sanyaya".

Allah mai iko da hikima, tabbas hakane, Allah ya nunawa Ronnie aya ta hanyar sanyaya mashi zuciya daga yarda zai shiga musulunci, Allah yana sansa da rahma shiyasa ya kara sanya mashi ni'ima da kaunar addinin a ransa, tabbas musulunci duniya ce kuma gaskiya ce, hanya fara da babu ɗigon baki a kanta, hanyar riskar tsira da nasara.


Girgiza mashi kai ta fara yi a kan ita ba zata iya taimaka mashi wajen jawo Black Tiger addinin Musulunci ba, dan ita gaskiya bata shirya mutuwa ba tare da sake haɗuwa da Pretty and mom ɗinsu ba, tana san ƴar uwarta.

Kara yin ƙasa da murya sosai ya yi, sannan ya cigaba da cewa............ "Na san damuwarki da abin da kike jin wa tsoro, rasa ranki kike tsoro ko?". Ya jefa mata tambaya.

Kai ta gyaɗa mashi alamar hakan ne, ranta take tsoron rasawa, yar kaniya ta ji wahala shakar da ya yi mata a cikin ruwa, daga nan ta fara tsoronsa da shakkarsa.

"To ina san ki daina tsoro, ki sani da wata ce ko wani ko minti ɗaya ba zai karaba a duniya idan ya kalli fuskar yayana, amma ke kin kallesa ido cikin ido, kuma baki tsorata ba, daga nan yakamata ki sani cewa yaya ba zai iya kashe ki ba, sai dai ya azabtar dake, na san zaki sha wahala matuƙa, amma banda batun mutuwa".

Wani irin kallo ta wurga mashi wanda za'a iya fassara shi da me kake nufi da kace zan sha wahala amma ban da batun mutuwa?.

Ya fahimci abin da take san karin bayani a kai, dan haka sai ya ce......... "Tabbas sai dai yaya ya gana maki azaba, amma ba zai iya kashe ki ba, ke ɗin ƙaddararsa ce, dalilina a nan kuma shi ne Spender yana tare da ke, saboda Spender ne yaya ba zai kashe ki ba, da wannan dama zamu yi amfani wajen taimakawa mu juya black heart izuwa white, amma sai kin jure, zaki azabtu matuƙar, idan kuma kika jure har muka yi nasa tabbas sai mun fi kowa jin daɗi".

Ɗan dakatawa ya yi yana kallan face ɗinta, yaga alamar ta ɗan sauko jin maganganunsa na karshen nan, kwarin gwiwa ya samu wajen cigaba da ce mata.

"Tabbas yana haukar neman Spender, a da na yi niyar yi maki dabara in shiga jikinki dan ki bamu Spender, amma a yau ni nike tsaye a kan kafafuna ina mai umartarki da dik azabar da zai gana maki kada ki kuskura ki bashi Spender har sai mun yi nasara, zan yi ta razanaki dan ki bashi, kada ki yarda ki bashi".

A daidai lokacin da ya ce a da can baya ya yi niyar shiga jikinta ya mannu da ita dan ya kwatawa yayansa Spender daga hannunta ba karamun zaro idanu ta yi ba, dan bata taɓa expecting haka daga garesa ba, ya bata mamaki matuƙa.

Sarai ya lura da maganar ya girgizata, amma sai ya basar, ya cigaba da karfafa mata gwiwa a kan zata iya, dik da cewa ba lallai ne su yi nasara ba, amma zasu jarraba, kuma yana da yakinin ko basu yi nasara ba zasu samu cigaba sosai, zasu iya canza wasu abubuwa, kuma shi burinsa kenan.

Sosai ta ji kwarin gwiwa jin cewa ba zai kasheta ba, dama ita batun kisan ne a ranta, tin da kuwa babu kisa tabbas zata jure dik wata wahala, tabbas zata iya, dama ita burinta su yarda da ita su musulunta.

Katse mata tunaninta ya yi da cewa. "Yaya zai yi wuyar musulunta, amma ki sani idan muka yi sa'a ya musulunta to fa tabbas Birnin nan dikka zasu musulunta".

Wani irin sanyi ta ji a ranta, nan take ta fara hasko kanta a cikin al'ummar birnin nan tana koya masu karatun addini, nan take ta fara hasaso kalar ladar da zata samu idan suka musulunta, tuni ta mance da wahalar da za'a sha kafin ayi nasara, tin da dikka birnin zasu musulunta idan ya musulunta ai ita ko zai kasheta kafin ya musulunta in dai zai musulunta ɗin wlh a yanzu kam ta yarda, ko zata mutu ba gudu ba ja da baya. Tuni ta saki ranta, cike da kwarin gwiwa ta girgizawa Ronnie kai alamar ta yarda ta amince zata yi dik abin da ya ce.

Sosai ya ji sanyi a ransa, sannan ya yi mata raɗar yadda zasu fara tsara plan ɗin nasu, daga karshe ya buƙaci da ta shigar da shi addininta wato ta bashi kalmar shahada. Yana kai karshen maganar ya zame hannunsa daga ɗan bakinta domin ta bashi shahada.

Haka kuwa aka yi, a hanzarce ta juyo ta fara yi mashi raɗa ta kalmar shahada a kunne yana maimaitawa a hankali yadda kowa ba zai ji ba, har lokacin yana rankwafe a kanta, ko gaji bai yi ba bawan Allah.

Sai da ta kai har karshe, sannan ta matsa baya da shi like three step, sai ta fara binsa da kallo mai cike da kauna da farinciki, tana yi mashi kallon cikakken musulmi a yau.

Ya yi shiru yana kallanta yana jiran ya ji me next, sai kawai yaga ta daka tsalle ta faɗo jikinsa tana dariya kamar wadda ta zare.

Rungumeta kam ya yi a jikinsa yana jin wani irin farinciki na musamman, ya ɗagata sama ya manneta da kirjinsa suna ta sakin murmushi wa junansu.

A kunne ta raɗa mashi. "Is time, get ready to fight my Ronnie, da izinin Allah zamu yi nasara, zamu cetosu daga halaka zuwa tsira".

Juyowa ya ɗan yi shi ma ya fara yi mata nasa raɗan. "Kada ki bari yaya yasan da cewa na musulunta fa, zai kasheni dik san da yake yi mun, ko Floris kada ki bari ya sani".

Jinjina mashi kai ta yi kafin ta ce. "To taya za'ayi ka yi sallah?".

"Kada ki damu da wannan, a ɗakin yaya zamuna yi, dan yana kallan komai dake cikin birnin nan amma banda ɗakinsa, dan haka tin da ya fara shiga fada a nan zamu rinƙa yi".

Wani irin daɗi ta ji ya kara lulluɓeta, da karfi ta kara kankamesa kamar zata mayar da shi jikinta, shi ma wani irin daɗi yake ji na musamman.

Black Tiger dake ganin me suke aikatawa ya zaci soyayya Ronnien nasa ya fara yi, hakan yasa ma ya kawar da kallonsa a kansu, ya shiga kallan sauran wurare a cikin birnin.

Sake Ronnie ta yi, shi ma sauketa ya yi, cikin farinciki ta ce. "Muje ka rakani ɗakin yayanka yanzu!".

A ɗan rikice ya ce. "Me zaki je yi a can?".

"Kai dai muje zaka gani"........... Bai musa mata ba, ta wuce gaba ya rufa mata baya.

Me kuke tinanin zai kaita room na Black karfe a daren nan?.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️









"Kai dai muje zaka gani"........... Bai musa mata ba, ta wuce gaba ya rufa mata baya.

Me kuke tinanin zai kaita room na Black Tiger a daren nan?.

Sun zo zasu fita daga room ɗin kofar taki buɗewa, yanzu ta san password na kofar, dan haka ta yi ta yi yaki buɗewa, da ta gwada sau uku ma sai kofar ya fara karar jiniyar motar ƴan'sanda, alamar ansaka mashi wrong password kenan.

Da sauri ta juyo da kallonta a kansa, yana tsaye ya harɗe hannaye a saman kirjinsa, sai kallanta kawai yake yi.

"Ronnie meyasa kofar taki buɗewa? Kuma ka ji tana wata iriyar kasa!".

Ƙasa ƙasa ya furta. "Saboda yaya bai yarda mu fito yanzu ba, shi ya hana kofar buɗewa, mu koma kawai".

Ranta bai so haka ba, ta juya da nufin su koma kenan sai suka ji alamar ana taɓa kofar, da sauri ta juyo da kallonta a kan kofar. Kamar mai raɗa a ɗan tsorace ta ce. "WANENEN?". Ta tsorata jin ana taɓa kofar ne.

Gaba ya wuce ya koma cikin ɗakin, a bakin bed ya zauna, ta tsaya tana kallonsa tana jiran amsa. Murya a kasalance ya ce. "Robbot ɗin da suke aiki a cikin empeir ɗin nan ne, baki ji kofar ya yi karar an saka mashi wrong password bane? Shi ne suka zo dubawa, rabu da su ki zo ki bani tarihin yesu da Imam Madih, zasu tafi idan suka gama bincike suka tabbatar da babu wata matsala".

Tin da ya fara magana ta shiga mamaki jin kamalansa, lallai akwai tsaro mai karfi a empeir ɗin nan, tabɗijam.

Sai da ta ji ya ce ta zo ta bashi tarihin Imam Madih ne ta ɗan saki ranta, cike da fara'a ta ce. "Ba ranar na baka ba?".

Kai ya girgiza kafin ya ce. "Ranar tarihin yesu kika bani, kika ce zaki faɗa mun wanene Imam Madih, amma baki faɗa mun ba, kuma ni ina san Yesu sosai, bana gajiya da jin tarihinsa na gaskiya".

Shiru ta ɗan yi, ya zuba mata ido cike da kauna yana jiran ya ji me zata ce, kamar wadda aka sakawa battery ta ninka murmushin dake saman face ɗinta, cikin jin daɗin san samun iliminsa da yake yi ta fara faɗin.

"Ba iya Yesu yakamata ka mutu a kansa ba, ka mutu a kan fiyayyen halitta manzon rahma manzon tsira zaka ji matuƙar daɗi fiye da tinaninka a yanzu".

"Wanenen shi manzon tsira ɗin?". Ya jefa mata tambaya........... Cikin nitsuwa ta tako ta zo kusa da shi, a saman bedside drawer ɗinsa ta zauna, gyara zamansa ya yi ya zamana suna fuskantar juna, dik a matse yake da san jin yadda zata bayyana mashi manzon tsira, jikinsa har tsuma yake yi, shi yanzu yana bala'in san jin tarihin annabawa da Sahabbai da yadda suka rinƙa sadaukar da rayukansu dan mu a yanzu mu ji daɗi.

Cikin nitsuwa ta fara kora bayanai masu cike da ilimi da hujjoji masu karfi........ "Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) shi ne manzon Allah na karshe kuma mafificin halitta. Shi ne aka aiko domin ya shiryar da mutane gabaɗaya zuwa ga addinin gaskiya, wato Musulunci, musulunci shi ne yake bayyana mabiya Allah guda ɗaya tak ba Allah biyu ko uku kamar yadda yahudu da nasara suke faɗi ba, musulunci Allah ɗaya ne tak cikin Tauhidi hakan ta bayyana. An haife Manzon Allah a garin Makka a shekara ta 570 Miladiyya, a wani gida na kabilar Quraysh, kuma ya fito daga zuriyar Annabi Ibrahim (Alaihissalam) ta hanyar Annabi Isma'il (Alaihissalam)".

Tun daga farkon bata tarihinsa Ronnie ya ji wani irin kaunarsa tana ratsa shi, sai ya ji kamar ta cigaba da bashi tarihinsa har illah Masha Allah.

"A cikin Alqur'ani mai girma, cikin Suratul Ahzab sura ta 30 aya ta 40 Allah ya bayyana Manzon Allah a matsayin annabin karshe wanda babu wani annabi da zai sake zuwa bayansa".

"Cikin Suratul Anbiya, sura ta 21 aya ta 107, Allah ya ce ba mu aiko ka ba sai domin ka zama rahama ga talikai. Suratul Najm, sura ta 53, aya ta 3 da na 4, Allah ya ce Manzon Allah bai faɗi Al-Qur'ani daga son zuciyarsa ba. Ba komai ba ne sai wahayi da na yi masa, cikin Suratul Ahzab, sura ta 33 aya ta 21, Allah ya ce lallai a gare ku akwai kyakkyawan misali a wajen Manzon Allah, ga wanda ya ke fatan Allah ya cecesa a ranar lahira, to ya ambaci Allah da Manzonsa da yawa".

A cikin sunanun tirmidhi, hadisi mai lamba 3148, manzon Allah ya ce lallai ni ne shugaban ƴaƴan Annabi Adam, kuma ba na yin alfahari ko fariya a kan hakan".

"Ni ne rahamar da aka bayar." Cikin Sunan Ad-Darimi. Wasu daga cikin ayyukan Annabi Muhammad (SAW) Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi kuma ya yaƙi bautar gumaka. Ya kafa gwamnatin Musulunci a Madina bisa gaskiya da adalci. Ya yaɗa ilimi da hikima.Ya kyautata zamantakewa da zamantakewar aure da rayuwar jama’a gabaɗaya".

"Allah ya umarci musulmi da su koyi dabi'un Manzon Allah (SAW), domin duk abin da ya koyar da al'umma ya kasance bisa umarnin Allah ne. Wannan yana cikin abin da ke tabbatar da cewa ya kasance tsarkakakke kuma cikakken misali ga dukkan al’umma".

Ronnie ya gama tsumuwa da san Manzon Allah, dan ma Sweetie bata bashi kaso ɗaya cikin dubu na kyawawan halayen manzon rahma ba.

Ganin ya tsareta da ido ne yasa ta dakata da yin maganar. "Ronnie lafiya?". Ta jefa mashi tambayar cike da matsuwa da son jin amsa.

Girgiza mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, fuskarsa ɗauke da ƙayatattcen murmushi mai kwantar da hankali.

"Ni dai ka faɗa mun menene in ba haka ba in fasa baka tarihin Imam Madih".

Ƙasa ƙasa kamar mai raɗa ya ce. "Kaunar manzon Allah ce take ratsa zuciyata sosai shiyasa na kasa yin magana, ji nike kamar zan yi kuka".

Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta cigaba da cewa. "Ronnie kasan me?".

Kai ya girgiza mata alamar a'a,........... "Zan yi maganin yayanka wlh, tin da dai..........."

Yatsansa ɗaya ya ɗaura mata a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru, yana wani lumshe idanu alamar barci yake ji. Hakan yasa ta haɗiye maganar bata amayar ba.

Shiru ta yi cikin ranta tana tinanin irin tsiyar da zata rinƙa yi wa Black Tiger, har faɗi take yi ba zata taɓa barinsa ya zauna lafiya ba, ta rinƙa takura mashi kenan, sannan ba zata taɓa bari ya damketa ba bare har ya gana mata azaba, cikin wannan tinani da take yi ne tinanin magic dake hannunta ya faɗo mata a rai, cike da matsuwa ta ji menene wannan ta ce.

"Ronnie please ka faɗa mun menene a hannu da yake iya sarrafa wasu abubuwa?".

Dan zaro idanu kaɗan ya yi like mamakin menene?. Ta gane me yake zarowa idanu, so yake ya tambayi menene amma tongue ɗinsa ta yi mashi nauyi, dan haka sai ta buɗe tafin hannunta tare da saita kofar ɗakinsa da shi.

Nan take wannan hasken ya fita da karfi, kafin Ronnie ya yi wani motsi wannan haske ya daki kofar dakinsa da Black Tiger ya datse da magic ɗinsa, nan take kofar ta wangale kanta da kanta. Sai dai kuma magic ɗin ya juyo ta kansu da karfi.

Cikin zafa Ronnie ya hanyeta daga in da take zaune magic ɗin ya wuce ya dagi jikin bango sai ji kake kara mai sauti ta fito, bangon ya tsage. Ba komai ya haifar da magic ɗin ya juyo kansu ba face magic ɗin black Tiger dake jikin kofar, na faɗa maku nasa ya fi nata karfi, dama yana binta a hankali ne kawai, so a jijin kofar magic mai karfi ya saka, karfinsa ya daki nata yasa natan ya juyo kanta, Allah ya taimaketa Ronnie ya janyeta da ina ga sai dai gawarta za'a ɗauka, ku duba yadda magic ɗin ya tsaga bangon nan, da haka zai tsagata biyu.

Sosai ta tsorata, shi kam Ronnie ko kaɗan bai tsorata ba, sai dai ya yi matuƙar mamakin ganin magic a tattare da ita, bai taɓa expect ɗin hakan ba.

"Ronnie dan Allah ka faɗa mun menene wannan? Daga ina wannan haske yake fitowa a jikina?". A tsorace ta yi maganar, muryarta har ɗan sarkewa yake yi.

Jikinsa dik a mace ya amsa mata da. "Magic ne a hannunki, yakamata ki koyi sarrafa shi".

Kara zaro idanu ta yi. "A ina na samu magic to ni?". "Ban sani ba, nace ki bani tarihinki kin ki bani, watakila a cikin tarihinki zan iya sanin daga ina kika samu magic".

Shiru ta ɗan yi, wani zuciya yana ce mata ta sanar da shi dik abin da ta sani dangane da su, wani zuciya kuma yana ce mata a'a kada ta sanar da shi, a wani ɓangare kuma tana tinanin tin da ya musulunta kuma bata da biyunsa yanzu a cikin empeir ɗin nan me zai hana ta faɗa mashi komai? Amma kuma mom ɗinsu ta gargaɗesu a kan kada su yarda da mutane, anya ya cancaci ta yarda da Ronnie kuwa? Ta jefawa kanta tambayar.

Ganin ta shiga tinani yasa ya ce. "Ba sai kin wahalar da kanki ba, ni ban matsu da na ji wacece ke ba, haka ma is normal for me, dan haka kada ki damu".

Jikinta ne ya yi sanyi jin kalamansa, lallai ya cancanci Ronnie yasan wacece ita, kullum idan tana damuwa akan ta sanar da shi ko akasin hakan yana yawan faɗa mata kada ta wahalar da kanta ta bari, hakan na nuna shi bai wani damu da san jin wacece ita ba, so bai kullaceta da komai ba kenan!.

Dan haka sai ta gyara zamanta, cike da tsoron abin da zata faɗa me zai haifar ta fara magana kamar haka!.

"Ni dai sunana na gaskiya Omaish ina da sister mai suna Omnish, mu biyu kawai mahaifiyarmu ta haifa, mahaifiyarmu ta sanar da ni cewa mahaifinmu sarki ne mai ji da karfin iko da karfin mulki, baya ɗaukar wasa, jarumin gaske ne da ya kafa tarihi a masarautarsa, mutum ne mai jijjige dauloli a lokacin mulkinsa, ban san wanene shi ba, kuma ban san a wani ƙasa yake ba, mom bata faɗa mana in da yake ba, ta dai ce mana tabbas da kansa zai kawo kansa garemu ko dan abin da yake hannunmu da ta bamu amsarsa (Spender) saboda shi zai kawo kansa garemu, wannan dalilin yasa ta ce kada mu bawa kowa (Spender), mahaifiyarmu gimbiya ce mai ji da kanta, sannan tana da tausayin talakawa saɓanin wasu daga cikin kingdom ɗinmu, na fi tinanin a wajen babana magic

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login