Showing 192001 words to 195000 words out of 403653 words

Chapter 65 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

91

suka danna izuwa bakin gate. Gateman ya buɗe masu kofar suka nufi waje.

Ina kuma zai kaita?. Za dai mu dawo mu bisu mu gani, dan sai munga komai.....👀🥱


🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥

A hankali ya juya ta ɗayar side ɗin ya zura kafafunsa kasa, kamar zai miƙe sai kuma ya fasa, kome ya tina sai ya juyo da kallansa a kanta, ɗaure fuska tamau ya yi kafin ya ce. "Momma bata faɗa maki ɗakinki daban da nawa bane?".

Kun dai san yaran momma baya san raini, shiyasa kuka ga baya shiga harkar kowa, shiyasa yaki yin aure dan ma kada mace ta rai'na shi, a gaskiya Jaish ya rai'na mata dayawa, Allah zamu yi maganinka.

Kai ta girgiza mashi tare da cewa. "Momma bata faɗa mun ba".............. Da hannu ya nuna kofar fita kafin ya ce. "Fita mun daga ɗaki, akwai ɗakuna dayawa a cikin part ɗin nan, ki ɗauki wanda ya yi maki, kada ki bari mu sake haɗuwa dake, dan bana san sake ganin face ɗinki". Ya kai karshen maganar tare da yunkurawa zai miƙe ya bar ɗakin.

Cike da tsoro ta ce. "Ni momma ta ce mun a ɗakin da kake zan kwa............" Yanke maganarta ta yi saboda wani irin matsiyacin kallo da ya dallah mata, nan take ta ji tamkar an sanya kaca an ɗaure mata baki, da kyar ta haɗiyi yawu mai wuyar wucewa.

"Bana magana biyu, idan na yi na farko na yi kenan, na biyu zai iya zame maki abin da ba zaki taɓa iya mancewa da shi ba". Cikin natsuwa ya yi maganar yana ƙara kaifafa voice ɗinsa, yana kai karshen maganar ya wuce ya nufi balconynsa yana jin wani ɓacin rai, shi kansa bai san ainahin abin da ya ɓata mashi rai ba, ya dai danganta ɓacin ran da ce mashi da ta yi a nan ɗakin zata kwana, amma da ni da ku mun san ainahin ɓacin ran daga ina ta samo asali.

Wato abar tasu ta gado ce ta motsa, shi kuma baya san raini, shi ne silar ɓacin fa, amma sam bai gane hakan ba, sai wani haɗe rai yake yi............ Mahnoor da bata saba da irin halinsa na yanzu ba, idan ya yi abu ɗaya sai ta ji zuciyarta ta karaya, yanzu ma haka ne, dik sai ta ji anya ba zata hakura da shi ba kuwa? Ta jefawa kanta tambayar.

Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta lallaɓa ta miƙe, jikinta babu kwari ta nufi waje idanunta suna cikowa da kwallah. A parlour ta tsaya tana tinanin anya zata sake yarda su haɗu kuwa? Dan ya ce kada ta sake bari ya kalli face ɗinta, anya ba zata shiga ɓuya kamar yadda ya buƙata ba kuwa?.

Ta ɗan jima tsaye a parlourn tana tunane tunane har sai da ta kalli babu wata mafita sannan ne ta wuce ta nufi bedroom dake kusa da nasa. Ta yi mamakin ganin akwai komai a cikin ɗakin kusan kamar irin na bedroom ɗinsa. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi bakin bed ɗin ta zauna.

A ranta ta kuduri niyar ba zata sanar da momma abin da yake faruwa ba, zata yi shiru har ta ga me zai iya faruwa gaba, tana da hankali ta fahimci ba komai zata rinƙa faɗawa momma ba, yakamata tasan abin da yakamata ta rinƙa faɗa mata da wanda bai dace ba.

Shiru ta kwanta a saman bed ɗin cike da tunane tunane a ranta. Shi kuwa sai da ya gama zaman da zai yi a balconynsa har zuwa karfe 8:40, sannan ya miƙe ya dawo cikin bedroom ɗin, shikaɗai ba wanda ya taɓa shi yake ta faman ɗaure fuska kamar wanda aka cewa wutar jahannama zai zama makomansa, yana ta faman jan tsaki, sai wani haɗe gera yake yi, a fili ya furta momma tana san lalata mashi komai ta ja mashi raini dama ga Jawad ya gama zubar mashi da mutunci ya auri Chuchu, wannan abin ta kona mashi rai sosai.

Mu fa mun san silar dik wannan ɗaure fuska da kake yi yaron Mommarsa, in zaka cire girman kai ka ajiye batun zata rai'naka ka daure ka rungumi ƴar matarka ka kawar da kai ma da ya fi maka, ko ya kuka ce my people's? Mu zaka ce baka san raini? Uhm na dai yi shiru.

Saman bed ɗinsa ya haye, har ya kwanta sai kuma ya tina da batun Auta, da sauri ya miƙe zaune, a hanzarce ya ɗauko wayarsa, call ya danna na wata number da aka yi saving da pure heart. Kara wayar a kunnuwarsa ya yi yana sauraron yadda suke zayyana mashi cewa number a rufe take. Yau kwanaki uku kenan yana kiran number a kashe, haka kawai a ransa ya ji tabbas akwai abin da ake ɓoye mashi dangane da Auta, dan kuwa ko Dubai ta tafi suna waya a kullum, ya za'ayi ya kira su Yah Ramish ma su ce mashi bata zo gidan Abu Abdussalam ba, ya kira kakansu King Badeen ya ce mashi bata nan, ya kira uncle Rahab kuma sai ya rinƙa ce mashi ko ta yi barci ko bata kusa, to gaskiya shi yanzu ya fara tantama a kan wannan lamari.

Yunkurawa ya yi zai miƙe ya nufi waje, dan ya je ya samu momma ta faɗa mashi gaskiya ina Auta take? Shi yanzu dik bai yarda da maganganunsu ba. Yan yunkurawa sallamarta ta daki dodan kunnnesa.

Ta wutsiyar idanu ya kallenta. Tin daga kan kyawawan fararen kafafunta da ya kalla ya gane wacece, dan lallenta. Kawar da kallansa daga kanta ya yi yana jan siriri tsaki, a ransa yake faɗin ba dan wannan yarinyar marainiya bace babu abin da zai hana shi sakinta a daren nan, amma yanzu ma bai sanya a ransa zai zauna da ita ba, yana dai ƙoƙarin tina mafita, saboda shi dai wlh ba zai zauna da wannan yarinya ba.

A gabansa ta zo ta tsugunna, tana sanye da hijabi black color zuwa gwiwowinta, ya dai rufe kayan barcin jikinta, hannunta ɗauke da cup of cappuccinon. Cikin sanyin murya ta ce. "Hamma ga cappuccinonka nan".

Tsawa ya daka mata mai firgitarwa a kan ba ya ce kada ta sake bari su haɗu ba? Tsawar da ya yi mata ne har yasa ta saki cup ɗin ya faɗi ƙasa ya tarwatse, hakan yasa ransa ta kara ɓaci har ya ɗaga hannu zai dallah mata mari, sai ta yi saurin sunkuyar da kanta ta ɓuye shi a tsakanin cinyoyinta.

Wani tsawa da ya sake daka mata a kan ta fita mashi daga ɗaki koku ma ya ɓaɓɓallata ne yasa ta yi saurin miƙewa da gudu zata fita. Mama Haulat kuma jin tsawan yasa ta shigo da gudu domin ta duba menene?.

Karo suka yi da Mahnoor a bakin kofa zata fita, da sauri ta yi ƙoƙarin riketa dan ta tambayi ba'asi, sai dai ina, Mahnoor bata bada damar a riketa ba, da gudu sosai ta danna waje tana sakin kuka mai tsuma zuciya.

Dawo da kallonta a kansa mama Haulat ta yi, cikin girmamawa ta ce. "Ranka ya daɗe lafiya?". Wani irin hararar da ya dallawa mama Haulat ɗin ma har sai da yasa ta ji ƴaƴan hanjinta sun kaɗa. Siririn tsaki ya ja tare da miƙewa ya zo ya wuceta ya nufi waje yana huci kamar ba lafiya ba.

Kai tsaye part na King ya nufa, dan ya fahimci momma a kan Mahnoor bazata wani goya mashi baya sosai ba, King ne kawai zai rarrashesa. Sai dai kuma maganganu suka yi a kan Auta sosai kafin ya sanar da King shi fa baya san Mahnoor, ya tsaneta a kusa da shi, dan haka shi ko a rabata da in da yake, ko kuma shi ya bar gidan ya koma Dubai.

Rarrashinsa sosai King ya yi kafin ya faɗa mashi cewa ya bashi nan da kwana goma zasu tsai da matsaya a kan hakan, amma yanzu dai ya yi hakuri suna tsaka da wani muhimmin aiki ne. (Aikin neman Auta kenan, kun san Jaish bai san ta ɓata ba, kuma an ɓoye mashi, so shiyasa ya ce mashi suna aiki kawai.)

Aminta da zancen King ya yi, dan haka sai ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa ransa a ɓace sosai. Kafin ya koma mama Haulat ta goge wajen da cappuccino da Mahnoor ta kai mashi ya zuba, so ta gyara ko'ina tsab.

Yana zuwa ya haye bed ɗinsa ya kwata, yau ba za'a sha cappuccino ba kenan. Amma fa ko da ya kwanta barci ta gagara zuwa, gabaɗaya ya rasa me yake yi mashi daɗi, shi kaɗai sai kunci yake yi har zuwa karfe 2 na dare. Ganin bashi da wata manufa yasa ya miƙe jiki ba kwari ya shiga toilet, alwala ya ɗauro ya zo ya fara gabatar da nafilfili, surorinma dik a daddafe yake karantasu, sai dai kafin ya idar da raka'a biyun farko tuni jikinsa ta wastsake ya koma normal. Qur'ani kenan my people's, dik damuwar da kake ciki kana fara karanta shi cikin ƙanƙanin lokaci zaka ji ka wastsake watsau, Allah dai ya ƙara ɗaukaka musulunci da musulmai bakiɗaya.

Sai da ya yi sallar rakatainil fajir sannan ya bar saman daddumar ya wuce toilet, wanka ya yi ya shirya cikin arabs jallabiya brown color, ya nufi masallaci. Bai tawo ba sai karfe 8 na safe, jiya kwata kwata bai yi barci ba kenan.

Yana dawowa karfe 8 ɗin ma dan kada su haɗu da momma sai ya wuce part ɗin King kai tsaye, dan a tinaninsa Mahnoor ta sanar da momma walaƙancin da ya yi mata daren jiya, shiyasa ya gudu.

Sai dai abin mamakin shi ne ko da ya je part na King baya nan, ya tafi fada, ya sha madarar mamakin jin hakan, me ya fitar da King fada da safe haka? Ya jefawa kansa tambaya. Ganin babu mai bashi amsa yasa ya wuce kai tsaye ya nufi fadan.

Sosai ya kara shan madarar mamakin ganin dik wasu masu muƙami a fada sun hallara, dik wasu manyan fada suna ciki, Aunty MieMie, uncle Abbas, uncle Jahiz, uncle Taheer, harda Guyson dik suna ciki, abin ya yi matuƙar ba shi mamaki.

Dai'dai lokacin da ya sako kansa a cikin fadar sai ji ya yi uncle Abbas ya ce. "Wannan babbar gazawa ce a garemu ace katafaren kingdom kamar wannan wanda babu biyunsa a kasar nan, ga tarin tsaro wanda ba'a taɓa yin biyunsa a duniya ba, dik wasu abubuwa muna da su, amma har a shigo a ɗauki Zunaira a cikin masarautar nan a fita da ita yau tsawon satika shidda, kai gaskiya wannan babbar gazawa ce a garemu, kuma a gaskiya Zafar na rai'na tsaronka, ka bani kunya".

Haba wani irin dum dum Jaish ya ji kirjinsa ta buga, har wani sara mashi ya ji kansa ya yi.

Uncle Jahiz zai yi magana suka farga da Jaish dake tsaye a bakin kofa yana binsu da kallo yama rasa abin faɗe, sai yake jin kamar karya kunnuwansa suke yi mashi, kamar kuma mafarki yake yi, kenan dama Auta ba Dubai ta tafi ba? Kenan abokan gaba ne suka ɗauketa? Babbar magana lallai yau babu zaman lafiya.

Ganinsa tsaye a bakin kofar shigowa ne yasa gabaɗaya suka yi shiru, King ne ya bishi da kallon mamaki, dan bai yi zatan zai zo fada a yanzu ba.

Uncle Abbas ne ya yi karfin halin cewa. "Jaish ka shigo ciki mana, me ya tsayar da kai a bakin kofa kuma?".

Ba musu ya ƙariso ciki, sai dai yana addu'ar Allah yasa karya kunnuwarsa suka jiyo mashi, har zuciyarsa ta fara yi mashi tsananin zafi, dan ba zai iya ɗaukar maganganunsu ba in dai gaskiya ce. A sofar kusa da uncle Abbas ya zauna, kansa a ƙasa cike da fargabar amsa da zai iya samu daga bakin uncles ɗin nasa ya ce. "Uncles ku faɗa mun da gaske abin da na ji kuna faɗa haka ne? Kada ku ɓoye mun kamar yadda daddy ya yi, dan Allah ku faɗa mun, daddy ya ce tana Dubai, and kowa na kira a Dubai kame kame kawai yake yi mun, ga wayarta a kashe baya shiga, please second dad ka faɗa ina Zunaira take? Kasan ni mai iya karɓar kaddara ce a dik yadda ta zo mun, to ka faɗa mun zan yi imani da koma menene ya sameta in kuma hakura".

Dik wanda ya ji zantukan Jaish yasan cikin tsananin damuwa da ɓacin rai yake kalamansa, kuma sun san wlh karya ne ba zai iya ɗaukar wannan kaddara ba, kawai yana san su faɗa mashi ne ya ji wani hali Auta take ciki, idan suka faɗa mashi kuma sun san idan akwai abin da ya fi hauka ma zai yi masu, dan ba karamar yaki za'ayi ba, ba zai saurari kowa ba!.

Shiru fada ya yi suna sauraron kalamansa masu kama da sambatu, dan kamar bai san me yake faɗa sosai ba, dik cikin fadan nan babu wanda bai tausaya mashi ba, saboda kowa yasan yadda yake da Auta, shi fa ya yi renonta, dik wanda ya ga Auta a lokacin yarintarta to tabbas zai ga Jaish a bayanta, a tare suke koda yaushe, shiyasa suka yi sabo sosai, har su commander sun tausaya mashi matuƙa.

Allah sarki commander har ya yi wani irin mummunar rama sosai, saboda tashin hankalin da yake ciki a kan Hoorain, babbar abin da ya ɗaga mashi hankali ma shi ne King ya bada umarnin gani da kisa a kan Hoorain, saboda a tinaninsu amanarsu ya ci, kun san ya gudu ne ai, so sai aka saka dokan gani da kisa kai tsaye kawai a kansa.

Tsit fada ya yi, kowa jiran abin da King zai ce suke yi, gabaɗaya hankulansu a tashi. King kuwa, sai da ya ɗauki a kallah 5 mins yana nazarin abin da zai faɗawa Jaish ɗin, dan yana fargabar kalar balai'n da Jaish zai tayar masu, shi kansa yasan bafa za'a wanye lafiya ba.
Gyara zamansa ya yi tare da ɗan yin gyaran murya, cikin natsuwa ya ce.
"Zan faɗa maka komai, amma ba yanzu ba sai mun haɗu da daddare a ɗaki, yanzu kaga muna wani tattaunawa ne mai matuƙar muhimmanci dan haka ka bari sai mun kammala".

Kirjinsa ne ta amsa da karfi, ɗan dafeta ya yi kafin ya ce. "No Please dad, ba zan iya kara koda one minute bane idan har ban ji gaskiyar in da Auta take ba, you know my condition dad, please kada.............."

Hannu kin ya ɗaga mashi alamar ya yi ba sai ya ƙarisa ba. Dakatawa da yin maganar ya yi yana sunkuyar da kansa ƙasa, saboda wani irin bugawa da karfi da kirjinsa take yi.

"Zan faɗa maka menene yake faru". King ya faɗa.............. Da sauri Jaish ya ɗago kansa zuciyarsa na harbawa da ɗan karfi karfi, cike yake da fargabar abin da zai ji, baya san jin zancen da gaske bata nan.

"Lallai ne tabbas Zunaira ta ɓata". Cewan King agin........... Dum dum ya ji kirjinsa ta sake bugawa, take ya ji hankalinsa na neman gushewa, a wani irin zabure ya miƙe tsaye kamar wanda ya rasa control ɗinsa.

Hankalinsa a matuƙar tashe ya miƙe tsaye, uncle Abbas ne ya yi saurin riko hannunsa yana ƙoƙarin mayar da shi ya zauna, ya ƙasa yin magana, yau tsawon sati shidda babu Auta babu labarinta, gaskiya wanna abin ya girgizata shi. Dole ya koma ya zauna yana tunanin yadda zai yi?.

King ne ya cigaba da bashi labarin yadda komai yawakana. Daga karshe ya rufe mashi da cewa.
"A yanzu dai bayan assistant commander Hoorain babu wanda ya rage muke zargi da sace Zunaira! Dik wanda muke tunanin tana hannunsu ko suna da sa hannu a saceta mun bincika bata nan a hannunsu, Hoorain ne kawai bamu san in da yake ba, kuma muna kyautata zaton shi ya ɗauketa!!".

Tashin hankali, wani irin zaro idanu commander Zafar ya yi, kenan dama King yana zargin Hoorain har haka ne? Sam bai taɓa yin wannan tinani ba.

Shi kuwa Jaish zaro idanu ya yi, a miliyan ya sake miƙewa tsaye, zuciyarsa ce take tafasa tamkar an ɗaura dalma a wuta, jikinsa har tsuma yake yi yana tuna idan da zai ga Hoorain a yanzu sai Allah kaɗai yasan me zai faru.

Dik su uncle Abbas kallansu a kansa, sun tausaya mashi matuƙa, sun kuma shiga damuwa dan abin da suke gudu shi ne yake shirin faruwa. Su commander Zafar dik kallansu a kansa, suma sun tausaya mashi matuƙa.

Yana tsaye yana fuskantar King, a take ya fara zuba huci kamar mayinwacin zaki, ya buɗe baki cike da ɗacin rai zai yi magana unexpect aka turo babbar kofar fadar aka buɗeta.

Gabaɗayansu kai kallansu a kan kofar suka yi. Ai a miliyan commander Zafar ya miƙe tsaye daga zaune a saman sofar da yake yana kallan kofar shigowar. A tare uncle Jahiz da Aunty MieMie ma suka miƙe tsaye. Shi kansa King abu kaɗan ya hana bai miƙe tsaye ba. Guyson and uncle Abbas suma a tare suka miƙe tsaye.

Dikkansu sun zaro idanu tamkar idanunsu zai faɗi ƙasa, a matuƙar razane suke binsa da kallo. Tsaye yake cikin jarumta sosai, yana ɗauke da Auta a saman shoulder ɗinsa, gabaɗaya jikinsa jini ya lalata, ga fuskarsa babu hularsu na mayaƙa, so face ɗinsa ma dik ya yi dama dama da jini, da alama yaki ya gwabza kafin ya iso kingdom of power.

Pretty na tsaye a gefensa ta riƙe hannunsa ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya tallabo Auta da shi dan kada ta faɗi, ita ma sai jini ne yake zuba a jikinta........... To me ya faru da su kenan?.

Ciwon dake cikinta ne ya fama yasa jininta yake zuba, kallo ɗaya zaka yi wa Hoorain sai ka razana matuƙa, saboda yadda face ɗinsa take ɗaure kamar hadari, ga wani irin fusata dake kan face ɗinsa, jikinsa har lokacin tsuma yake yi.

Guyson ne ya katse masu wannan shirun da cewa. "Tabbas Auta ce, tabbas ita ce

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login