Showing 117001 words to 120000 words out of 403653 words

Chapter 40 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

83

sun wanke mata fuska ne yasa ya yi saurin sakinta, kansa ya dafe sa karfi, cike da danasanin biyewa zuciyarsa ya amayar da abin dake ransa ya fara faɗin.

"Dan Allah ranki ya daɗe ki yi hakuri! Ban yi tinanin kalamaina zasu yi maki zafi su sanyaki hawaye ba, kasa iya rike kaina yau na yi shiyasa, tuba nike yi". A tinaninsa dan ya ce yana sonta take kuka, yana ganin kamar zata ga ya ƙasƙantar mata da matsayi ne, bai kai ya sota ba shiyasa ya shiga bata hakuri!!.

Duka ta kai mashi a kirjinsa da ɗan karfi. Cigaba da bata hakuri ya yi yana danasani, Allah sarki zuciyarsa har ta raunata ganin yadda ta shiga damuwa a ganinsa.

Duka ta sake cigaba da kai mashi a kirjinsa tana kuka da hawaye bibbiyu, yana tsaye bai hanata ba, sai ma hakuri da yake bata yana faɗin ta dakesa sosai in dai har hakan zai sa ta huce.

Cigaba ta yi tana yi tana ƙara sautin kukanta mai taɓa zuciyar mai sauraro. Sai da ta gaji dan kanta da dukansa, sannan ta kama rigarsa wajen saitin kirjinsa, ta ƙanƙame sosai tare da kwantar da kanta a kirjinsa tana wani irin shessheka mai taɓa zuciya. Cikin kuka mai sauti ta ce. "Why Hoorain? Why, why sai da ka azabtar da zuciyata, ka wahalar da ni sannan zaka bayyana mun sirrin dake ranka? Meyasa? Meyasa baka faɗa mun da jimawa ba? Menayi maka ka bani wahala har haka?". Tana maganar tana bubbuga kirjinsa dake kamar dutse.

Shi dai shiru bai ce mata ko uppan ba, dan har yanzu bai fahimci a kan me take yin magana ba, ya ɗauka ya cuci zuciyarta ne da ya ce yana santa.

Tsabar farinciki ta rasa a ina zata sanya ranta ta ji sanyi, a cikin tsakiyar kirjinsa ta cusa kanta, dunkule hannunta ta yi tana dukan kirjinsa da ɗan karfi ta fara faɗin. "I really love you Hoorain, ban taɓa san wani abin kamar yadda na soka ba, please ka soni ko bai kai wanda nike yi maka ba".

Ina, ai ƙasa iya ɗaukar gangan jikinsa ƙafafunsa suka yi lokacin da ya ji kalmar i love you Hoorain daga bakinta, sai ya ji jikinsa ta yi mashi nauyi, hakan ya ja ya durkushe kasa a kan gwiwowinsa, kusan a tare suka durkushe kasar da ita. Kuka take yi sosai tana goggo kanta a cikin kirjinsa...........(DUKKA WANNAN DAƊI NE FA😅 GIMBIYA ZUNAIRA MANYA ƳAN LOVE, TA IYA BAWA FLOWER ƊINTA RUWA YADDA YAKAMATA🥱)

Jin abin yake yi tamkar mafarki ba gaske ba, soyayya wata aba ce mai matikar kwarjini haɗe da karfin gaske wanda a duniyar nan zata iya zama abu na farko mai tsananin karfin da babu biyunsa, komai sai da soyayya ake yi, son Allah da Manzonsa ya ja zamu iya bada rayukanmu a kansu, haka zalika san iyayenmu yasa muke binsu sau da kafa, muke kuma burin ganin farincikinsu ko da zamu rasa namu farincikin mu yi bakinci, su umarcemu ko da bamaso haka zamu aikata dan son da muke yi masu, soyayya ta fi karfin dik tinanin mai tinani.

Hannunsa ya kai da kyar ya iya riko nata hannayenta da take ta bubbuga kirjinsa ta rasa ina zata sanya ranta saboda daɗi. Yau ji yake yi kamar zai yi hawaye shi ma, idanunsa sun yi jajir kamar wuta.

"Ranki ya daɗe da gaske kina sona? Da gaske kike yi?". Da kyar ya iya faɗar hakan.

Kai ta gyaɗa mashi cikin wani irin tsantsar farinciki, ta kasa yin magana. Sake hannayenta ya yi tare da tallabo kanta da take ta gogawa a jikinsa, ya ɗagota suna fuskantar juna. Idanunta a rufe ruf sai hawaye dake ketowa kamar hanyar ruwa.

Hannayensa ya kai saman face ɗinta. "Ranki ya daɗe ina neman alfarma a mun inzini in goge waɗan nan hawaye".

Idanu a rufe cikin kuka ta ce. "Ka barsu su zuba my hero, ka kyalesu kawa, na farinciki ne". "To ai ni ganinsu a face ɗinki babban tashin hankali ne a gareni, ba zan iya jura ba".

Wani irin sanyi ta ji ya kara ratsa zuciyarta. Hannayenta ta ɗaura a saman shoulders ɗinsa.
"Dik yadda kake so ka yi my hero, ni dai nasan hawayen ba zasu dai'na fita ba, dan yau zuciyata ta karɓi sakon farincikin da bata taɓa karɓar irinsa ba, saƙon da ta jima tana jira, har mafarkinsa nike yi".

Goge mata hawayen ya fara yi cike da tausayi da soyayya. Ina ai kin dakatawa suke yi kamar yadda ta faɗa, yana gogewa wasu suna zubowa, ya rasa ya zai yi, ji yake yi kamar an mallaka mashi ita.

Zame hannunsa daga kumatun nata ya yi, da kyar ya miƙe tsaye, cak ya ɗauketa suka nufi wajen koramar nan, dan yaga da gaske hawayenta ba zasu dai'na zuba ba. A saman dutsen kusa da ruwan ya zaunar da ita, a kusa da ita ya zauna tare da sanya kyawawan fararen hannunsa ya taro ruwan dake zuba.

Face ɗinta ya fara wanke mata yana cigaba da rarrashinta. Da kyar ya samu ta yi shiru, kasa cikin ruwan dake gangara izuwa wajen da yake taruwa ya tsaya, a gabanta yana kallan face ɗinta, har lokacin idanunta a rufe, da alama akwai ɗan kunyarsa a tattare da ita.

"Ranki ya daɗe zaki iya buɗe idanu yanzu na gama wanke maki face ɗinki". A sanyayye sosai ya yi maganar.

A cikin ranta ta furta sai kace an ce mashi saboda ya wanke mun face yasa na rufe idanu. Shiru a fili ta yi bata amsa shi ba, kuma bata yi kamar zata buɗe idanun nata ba.

Yana tsaye yana kallanta unexpext wani tsuntsu mai bala'in kyau launin blue da ratsin yellow a wuyarsa ya sauƙa mashi a saman shoulder ɗinsa, hannu ya kai cikin dabara ya capko ɗan tsuntsun mai shegen kyau.

Zuba mashi idanu ya yi yana kallonsa. Ya ɗan shagala da kallan tsuntsun ya tsinkayo voice ɗinta a ɗan sarkafe ta ce. "Ruwa nike san sha my hero". Ta yi maganar tare da waro idanunta wajen.... Ni kam na ce ai dole ki nemi ruwa gimbiya ƴar daddynta......🥱

Tana buɗe idanu ta yi arba ta kyakkyawar tsuntsuwar dake hannunsa, kara ɗan zaro idanunta waje ta yi, cike da yarinta ta saki murmushi ga hawaye basu gama bushewa ba.
A hanzarce ta kai hannu zata taɓa tsuntsuwar. Ɗan ja baya kaɗan da ita ya yi alamar baya san ta taɓa kenan, cike da mamaki ta ɗago da kallanta a kansa.

Tin bata nemi jin ba'asin hanata taɓawa da ya yi ba ya yi saurin cewa. "Amin afuwa, ina tsoron ya cizan mun kene yasa na ja baya".

Sosai ta yi daɗi ya ratsa zuciyarta, irin wannan kulawa haka, ai sai yasa mutum ya mance a duniya yake, ya mance kowa da komai.
"My Hero shi fa tsuntsu baya cizo, ya mun kyau ne sosai fa shiyasa zan taɓa". A ɗan shagwaɓe ta yi maganar, ga murya a ɗan dashe.

Kai ya ɗan girgiza mata. "Ni dai gaskiya a'a, banyarda ba, kada in saki jiki baya ciwo ya zo kuma ya cijeki".

"Shikenan to, dik yadda kace hakan za'ayi, amma na so riƙesa a kusa da ni in gani, dan yana da kyau". ....... Takowa step biyu ya yi ya kariso dab da ita, a hankali ya ɗan rage tsawonsa, sannan ya matsar mata da ɗan tsuntsun kusa da ita.

"Ki gansa a kusa da ke, amma a hannuna".

Iyayi ne fa kawai irin nata, dan kuwa tana tsoron tsuntsun, da ya matsar mata da shi kusa da ita sai ga shi tsoronta ya bayyana, wai da ita zata nuna ita jinin bamodare ne, wato jinin King, shi ne har da wani nuna bata tsoro a farko.

Yanzu kuma sai ga shi ta koma har da ɗan ja baya, abin dariya ma shi ne ta ɗan kai yartsarta manuniya tana san taɓa jikin gashin tsuntsun, kun san yadda mutun yake dankwalar abu mai zafi ko? To haka take sanya yarsarta a miliyan tana ɗan taɓa gashin ta sake janyewa da gudu.

Shi dai Hoorain hakan ba ƙaramin birgesa ya yi ba, a duniya dik abin da ta yi birgesa take yi, sai ma idan ta haɗa da murmushi, ya ilahi ya lilliahi, sai ya ji tamkar ta yi ta cigaba har abada su kasance a haka. SOYAYYA MUGUN WASA.

Sai kallan face ɗinta yake yi, tana murmushi da guntun hawaye. Cigaba da wasa da tsuntsun ta yi tana taɓa shi kaɗan kaɗan. Zuciyarta ce ya raya mata yana kallan face ɗinta, dan haka sai ta ɗago kai da sauri.

Aikuwa karaf suka haɗa idanu da shi, da sauri ya yi yunƙurin kawar da kallonsa. Yatsunta ta fyasta mashi a saitin face ɗinsa, hakan yasa bai kawar da kallonsa ba, ya cigaba da kallonta ko da akwai wani sakon da zata faɗa mashi.

"Meyasa baka san haɗa idanu da ni my Hero?"........... Sake tsuntsuwar dake hannunsa ya yi ta tashi sama, sannan ya ce. "Zo mu je in baki ruwan da kika ce zaki sha".

Make mashi kafaɗa ta yi. "Ni dai a'a, sai ka faɗa mun abin da yasa baka san mu haɗa ido".
Ajiyar zuciya ya sauke, Auta ita ma ashe ta iya rigima da yake ganinta kamar ba haka ba, ashe dai ta iya ita ma.
"A da ne bana san mu haɗa ido saboda ban san ya zaki fassara kallona a gareki ba, kuma ke ma kin san dokace da take a kanmu na haramta mana ɗaura kallonmu a kanku, kin san ba wani mayakin da ya isa yake da ƴancin ya kalleku, kin san hukuncin da yake kansa idan ya yi hakan, ni kuma bana iya ƙasa kallanki a dik time da muka haɗu, shiyasa idan kika ɗago kika kalleni nike kauchar da kallona". Ya kai karshen maganar yana mayar da kallonsa kasa kan kafafunsa dake cikin ruwan gudun.

"To ai a da kace, yanzu kuma meyasa kake kin yarda mu haɗa ido?". A ƙagare da san jin amsa ta jefa mashi tambayar.

"Babu wani dalili yanzu kam, na dai saba kaucewa a da ne yasa har yanzu ma nike yin hakan".

Murmushi ta ɗan sakar mashi kafin ta riko hannunsa da ya harɗe a saman kirjinsa, a hankali ta sauko da ƴan kafafunta cikin ruwan da nufin ta miƙe tsaye.

Warware hannunsa ya yi da sauri ya riko nata, a hankali ya taimaka mata ta sauƙo kasa. Unexpect ta sauke ƴan kafafunta a saman nasa dake cikin ruwan. Sosai ya ji wani irin har cikin ransa, ita kuwa sai ta yi baya kamar zata faɗi. A hanzarce ya sanya hannunsa ɗaya ta baya ya riko waist ɗinta.

A wani irin slow ya dawo da kallansa saman face ɗinta, sai yaga ashe shi take kallo, yanayin yadda suka tsaya abin ya ƙayatar matuƙa, dama ga yanayin wajen fili ne na masoya, abin ba'a magana.

Hannunta ɗaya da ya saki ya riko waist ɗinta da nasa ta kai saman shoulder ɗinsa, da yake ya ɗan rage sawonsa hakan yasa ta iya dafa shoulder ɗin nasa. A kusa da kusa suka kalli zuna, wani azababben kaunar juna ne ya kara ratsa zuƙatansu, sanyi mai ni'ima ya ratsa fatar jikinsu, dikkansu basu ki su dawwama a haka ba.

"Hoorain". Ta ambaci sunansa a kurkusa kurkusa ba tare da ta zare kallanta daga kansa ba. Ya ƙasa iya amsa mata, saboda yadda ta yi magana a kusa tasa ya rasa control ɗinsa. He's in out of his control yanzu.

"Idan nace zan faɗi kyanka tabbas sai dai na rageta, dan baki ba zai iya zayyana shi ba, meyasa ka ɗauki tsawon lokaci kana mun rowar ganinka?". Ta jefa mashi tambayar tana ɗaga mashi gera guda.

Still dai da ido kawai ya bita, ya kasa iya amsawa.
"To shikenan mu je ka bani ruwan sha tin da ba zaka yi magana ba". Ta faɗa tana sauƙo da hannunta daga saman shoulder ɗinsa izuwa damatsan hannunsa.

Rike waist ɗinta da kyau ya yi, ya kara rage tsawonsa ya ɗauketa cak, bai yi magana ba, kuma ya gagara zare kallansa daga kanta. Ba komai yasa ya ɗauke wuta yaki yin magana ba face zai iya ketare iyakar musulunci idan ya ce zai cigaba da biye mata, dan haka shirunsa shi ne mafi a'ala a garesa!.

Bai zame ko'ina da ita ba sai dab in da koramar nan take ta aman ruwa, saman wani dutse ya tsayar da ita a kan kafafunta, da yake dutsen yana da faɗi sai ya hau sama shi ma.

Da kyar ya iya faɗin. "Wanke hannunki sai ki tara ruwan ki sha". Ya yi maganar voice ɗinsa tana sarkewa.

Cikin wani irin shagwaɓa mai ɗaukar hankali ta furta. "Ni dai a'a ba zan iya ba, kawai ka cire ɗayan hands gloves ɗin nan naka ka tara mun ruwan da hannunka sai na sha".

Wani irin bargon sanyin kauna ce ta ƙara lulluɓe zuciyarsa, ya ji matuƙar daɗin maganarta, ga shagwaɓarta dake ƙara kashe shi a koda yaushe ta yi, sai ya ji kamar shi kam an gana sallamarsa a duniya.

A hankali ya zare hands gloves ɗayan, ya sanya hannunsa cikin ruwan dake zubowa, tas ya wanke hannayen nasa kafin ya fara tara mata ruwan. Ɗan ƙara matsawa gaba kaɗan ta yi dan ta samu damar sha yadda yakamata.

A hankali ta fara sha, ji ta yi tamkar ruwan zuma ne saboda daɗi, ya ilahi ya lillahi, wato ruwan hannun masoyi daban yake in ji gimbiya Zunaira Auta.

Zuba mata idanu ya yi sosai yana ganin yadda take shan ruwan gwanin ban sha'awa. Har ta ƙoshi ta cire ɗan bakinta bai farga ba, sai ji ya yi tana faɗin. "Ga shi nima na tara maka da hannuna ka sha".

Mamakinta ne ya ɗan kama shi, wai ba ta ce ba zata iya tara ta sha ba? Ya aka yi ta iya tara mashi?...............Ni kuma na ce kanta ne ba zata iya tarawa ba, amma heronta tsab zata iya tara mashi ya sha cikin nitsuwa.

Sam baya jin ƙishin ruwa, amma da yake da hannunta mai tarin albarka ta tara mashi nan take ya ji wani irin ƙishin ruwa ta kamashi.

Matsawa ya yi ta bayanta, ya haɗe hannayensa da nata, ya tallabo nata cikin nasa kenan, ya kwanto da kansa ta gefen shoulder ɗinta, cikin nitsuwa ya kai bakinsa ya fara shan ruwan. A hankali ta juyo da kallanta a kan wuyarsa, da yake yana da tsawo sosai sai wuyarsa ma ta zamana tana da tsawo da kauri.

Bayan wuyarsa wani irin bakin gashi mai curlyn ne a kwance a wajen, gwanin ban sha'awa da burgewa. Ji ta yi tamkar ta kai hannunta ta taɓa wannan gashi, ya tafi da imaninta.

Shagala ta yi da kallansa bata ankara ba sai ji ta yi ya hura mata iskar bakinsa a fuska yana ɗan limshe idanu. Ajiyar zuciya ta sauke, bata san time da wani haɗaɗɗen murmushi ya subce mata ba. Shi dai bai yi murmushi ba, kuma babu alamarta ma a face ɗinsa, amma ya ji sanyi a ransa na sakin murmushin da ta yi.
Ya shagala da kallan murmushinta unexpext ya ji saukar ruwa a face ɗinsa.

Wani irin jan numfashi ya yi tare da limshe idanu, a hankali ya saki numfashin. Ita kuwa kara faɗaɗa murmushin nata ta yi tana ƙara watsa mashi ruwan.

"Sai ka yi ta kallanwa daddyna ƴan'matansa ba tare da ka nemi izni ko ka biya ba ko? To ni ba zan bar hakan ta cigaba da faruwa ba". Cewarta kenan, tana magana tana ɗan watsa mashi ruwa....... Oh my people's kun ji Auta da tsara zance, wai ayi ta kallewa King ƴarsa ba'a biya ba.

Hannu ya kai saman face ɗinsa, a hankali ya sharce ruwan da ta watsa mashi ɗin, sai ya yi kamar ya datse idanunsa da karfi ya rungumeta a jikinsa kawai kada ya saki idan ya so daga baya ya yi istigifari, dan tana tafiya da imanisa, sai ma idan yana kallan lips ɗinta a yayin da take magana, ohohohoho, ji yake tamkar ya sa hannu ya matse ɗan bakin nan nata ya yi ta sha ba hutawa.

Zuba mashi ido ta yi tana jiran taga me zai yi next da ya datse idanu kam haka. A miliyan ya zaro mata idanunsa.

Ai tsabar tsorata sai da ta yi baya baya wai zata gudu sai ta tafi luuuu zata afka kasa cikin ruwan dake wajen. A miliyan ta kai hannunta ta capki rigarsa ta saitin kirjinsa, unexpext ta damkosa ɗin, dan haka bai rike jikinsa ba, sai suka tafi a tare suka afka cikin ruwan da karfi. Da karfi ta riƙosa ta kuma datse idanunta gam tana jiran ta jisu a cikin ruwan kawai.

Kafin su kai cikin ruwan ya yi zafin namar janyota jikinsa shi ya faɗi ƙasa cikin ruwan, ita kuma ta faɗa saman kirjinsa. Kusan a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Shiru suka ɗan yi na ɗan lokaci, da yake ruwan wajen ba zurfi sosai. Ita ta tara motsawa bayan ɗan lokaci, da kyar ta iya tashi daga jikinsa. Shi ma da kyar ya iya miƙewa, hannunta ya riko tare da cewa. "Zo mu je mu leƙa Pretty".

Ya faɗa mata hakan ne ba dan komai ba face dan su bar wajen, yana tsoron ta jefa shi cikin wani halin da zata sa ya kauce koyarwar addininsa.

Wucewa suka yi izuwa in da ya tsaya ɗazun yana wanke takobinsa. Hular yakinsa ya ɗauka tare da hands gloves ɗinsa ɗaya. Yana ƙoƙarin maida

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login