Showing 171001 words to 174000 words out of 403653 words

Chapter 58 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

79

ta". ........... Cikin girmamawa mama Haulat ta amsa da okey a cikin zuciyarta tana kara jinjinawa kirkin momma da rashin girman kanta, ba kaman sauran matan King ba, idan su mama ne Mahreen ta isa ma ta zo in da suke ne?. Ai su basa zama kusa da talaka, ina momma ta dabance a cikinsu, bata ɗauki duniya a bakin komai ba.

Haka dan tana san farincikin Mahreen sai da ta amsa mata da Allah ɗin sannan Mahreen ta yarda, suka cigaba da hira Mahreen tana zuba mata shirme da hiran kauye da dai sauran shiririntarta.

Mahnoor kuwa mama Haulat ta ɗauki tray ɗaya na abinci ita kuma ta ɗauki ɗayan, tamkar wata tauraruwa haka ta bi bayan mama Haulat suka nufi part ɗinsa.

Sai kalle kalle Mahnoor take yi, dan idan baku manta ba bata yawace cikin gidan ba, part ɗin momma kawai suka sani sai ɗakin gyara. Bata kara zuba ƙauyancinta bama sai da suka isa part na mijin nata, wani irin daddaɗar kamshi ne ya daki hancinta har sai da ta lumshe idanu tana kara shaka.

A saman dining table dake cikin parlonsa suka zube abincin, sannan mama Haulat ta dubeta, cikin mutuntawa ta nuna mata kofar master room ɗinsa da hannun tana faɗin. "Ga ɗakinsa can shiga ki sanar da shi kin kawo mashi abinci".

Idanu ta zaro, ɗan bakinta ya sha lips balm sai kyalli yake yi yana ɗaukar hankali, kamar zata sa ihu ta ce. "Mama Haulat tsoron shiga nike ji". Tabbas mama Haulat ta fahimci akwai tsoronsa sosai a ranta, matsawa kusa da ita ta yi, da hannu bibbiyu ta dafa shoulders ɗinta, cike da kaunarta ta ce.

"Kina san Prince ko baki san shi?" Kasa ta yi sa kai ta gagara ba da amsa. Mama Haulat ta fahimci kunya ne da ita sosai kamar dai Jaish ɗin, dan haka sai ta ce. "Kada ki ji kunyata, ki ɗaukeni a matsayin mahaifiya, ina san ki faɗa mun kina san shi ko baki san shi".

Ƙasa sosai ta yi da murya. "Ina san shi". Ta bada amsa kunya kamar ta shige cikin ƙasa. "To lallai in dai kina san shi dole ki tsaya tsayin daka domin yaki a kan abin da kike so, ki sani Prince ta ko'ina tarin masoya yake da shi waɗan da suke haukar san shi, yana da kyau ki sani tin da momma ta tsaya maki In Sha Allah zaki mallakesa, kada ki ji tsoron komai, ba zai dakeki ba, dan su basa dukan mata, kin gansu hakan nan suna girmama mace musamman ke da kike marainiya, suna da zuciyar tausayin maraya, zaki yi nasara sosai".

Cigaba da kara mata kwarin gwiwa mama Haulat ta yi har sai da ta ɗan saki jiki ta aminta zata je, sannan ne ta saketa tana binta da kallo. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi bedroom ɗin nasa. Hannunta har rawa yake yi tasa hannu ta tura kofar tana haɗawa da ɗan siririn sallama ƙasa ƙasa.

Tana sanya kafafunta a cikin ɗakin ta waro idanu waje, ya subhanallah ɗakin ya haɗu ne sosai, sai tashin kamshi yake yi. Baya cikin ɗakin, yana balcony yana waya da Jawad, Jawad ya je office ɗinsa bai same shi bane yasa ya kira waya ya tambayi ina yake, shi ne ya ce mashi ya dawo gida baya jin daɗi.

Ji ta yi tamkar ta juya a guje ta bar ɗakin, sai dai kuma tana san sanya shi a idanunta, ta yi kewarsa sosai. A hankali ta fara ɗaga kafafunta ta ƙariso cikin ɗakin, a kusa da bed ɗinsa ta tsaya tana kallan yadda king bed ɗin nan ya haɗu. Kamar ance ta ɗan ɗago kai sai ta hangosa saman wasu ƙayatattun kujeru masu laushi da kyau dake wajen yana zaune yana waya.

Subhanallah tsare shi da idanu ta yi tana kallansa ta cikin glass ɗin, shi baya kallanta saboda na waje baya kallan na ciki, na ciki ne zai iya kallan na waje. Tamkar yasan akwai mai kallansa ya kara juyowa da kyau yana fuskantar bedroom ɗin nasa. Lips ɗinsa kawai ta tsare da kallo tana tina lokacin da yake bata hot kiss a kauye, yanzu taga lips ɗin nasa su kara tura ja sosai sun ƙara kyau, da yake ya saba mata a baya sai ta ji tana kwaɗayin yi mashi kiss ɗin a yanzu, amma babu dama.

Ta shagala da tinanin soyayyarsu a kauye bata ga miƙewarsa ya nufo dakin ba sai ji ta yi ance. "Lafiya? Wacece ke?". Ya yi maganar kuma kallansa a kan zanen flowers ɗin hannunta.

A ɗan razane ta kyabta idanunta sau biyu tare da yin ƙasa da kai, a ɗan tsorace cikin sanyin murya ta ce. "Dama abinci ne na kawo maka". Tana matana tana satar kallan kayan jikinsa, ya yi makurar kyau sosai. Pj ne a jikin nasa masu silky launin milk color, kyawawan fararen kafafunsa suna cikin bedroom slippers ash colar mai laushin gaske.

Kawar da kallansa a kan hannunta ya yi izuwa kan face ɗinta, dai'dai lokacin ta ɗago kai dan ta kalli meyasa ya yi shiru. Unexpext suka haɗa ido. Wani irin faɗuwar gaba ta ji ya dira mata, shi kuwa wani irin shock ya ji a jikinsa, lokaci guda ya ji tamkar ya san face ɗinta, ƙwaƙwalensa ce ta amsa mashi, kamar walkiya ya ji tamkar an ambaci hamma a cikin kwakwalwarsa, kamar yana san tina rayuwarsa a gidan bappa ɗin.

Dik kunyar da take ji ta kasa iya zare idanunta a cikin nasa, shi ma ya kasa kawar da kallonsa daga kanta, yana jin ƙwaƙwalwarsa tana juyawa dama ga shi kansa na ciwo, bugu da kari yana bala'in san kwalliya, haba ai sai abin ya haɗe mashi, domin kuwa kwalliyarta ta fito sosai ta yi wani irin kyau na ban mamaki, ko iya kwalliyar kawai ya isa ya sanya ya kasa zare kallansa a kanta tun da yana son kyalliyar bare kuma ya haɗe da kyanta ga gyara da ta sha, sannan ga shi kamar ya san face ɗin.

Ita kuwa Allah sarki soyayyarsa yasa ta mace da kallansa, ta yi kewan kayanta sosai.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




No editing💔😥




Ita kuwa Allah sarki soyayyarsa yasa ta mace da kallansa, ta yi kewan kayanta sosai.

Abin ku da sun taɓa kasancewa masoya masu san junansu sosai a baya, kun san wannan abin ba zai taɓa barin zuƙatansu cikin sauki haka ba, shi kansa Jaish ɗin dik da ya dawo dai'dai ai soyayya ba karya bace, dole idan ya ga face ɗinta ko bai tinata ba zai ji a jikinsa kamar ya santa.

Nisawa ya ɗan yi, sannan ya ƙara ɗaure fuska tamau kamar bai san me murmushi ba, a takaice ya nuna mata hanyar fita da hannunsa tare da furta out. Tabbas bata san ma'anar kalmar out ba, amma ta fahimci fita ya ce ta yi ta hanyar hannunsa da ya nuna kofa da shi. Tamkar zata sa kuka haka ta juya ta nufi hanyar fita.

Kawar da kallansa daga kanta ya yi yana tinanin wacece ita da har momma zata sanya ta kawo mashi abinci? Idan baku manta ba dama shi bai kalli matar da momma ta sanar da shi mallakinsa bace, an dai ce mashi yana da mata, amma bai ga face ɗinta ba, so yanzu bai san ita ce wannan ƴar kauyen ba, ya fi tinanin ma daga cikin ƴaƴan ƴan uwan momma wato su uncle Rahab daga can ne ta zo ziyara momma ta aikota kawo mashi abinci.

Siririn tsaki ya ja tare da hayewa bed ɗinsa ya kwanta, a ransa ya zayyana ba zai ci wannan abincin ba tin da momma ta aiko mashi wata. Hmmmm dama Jaish ai da wuyar sha'ani yake, kowa kuma yasan da haka, sai ka yi kamar zaka fahimci in da ya dosa sai ya sake watsawa mutum ƙasa a ido, ji abin da ya aikata yanzu fa, harda wani ba zai ci abincin ba.

Da sauri Mahnoor ta isa ga mama Haulat, wani irin kuka ne ta ji ya kubce mata, dan yadda taga ya ɗaure fuskar nan dik da bata jin turanci sai taga kamar zaginta ya yi, abin ya ƙona mata rai.

Tararta mama Haulat ta yi, sam bata yi mamakin ganinta ta fito cikin ɓacin rai har da guzurin kuka ba, dan ita tasan halin Jaish fiye da tinanin mai tinani, tasan dama ya yarda da Mahnoor cikin ƙankanin lokaci haka abu ne mai wuya gaskiya.

So bata tambayi Mahnoor ɗin menene ya faru ba, kawai ta riko hannunta suka koma wajen momma. A saman bed suka isko momma ta kwanta tana tinanin duniya, Mahreen ta tafi tare da Chuchu da suka dawo daga school ba jimawa, momma ta ce ta bi Chuchu ta kara koya mata abubuwa.

Momma na ganinsu ta miƙe zaune tana kallan Mahnoor dake sharar kwallah, dama tasan za'ayi hakan, kawai shahada ta yi ta gwada dama, to ba'ayi nasara ba.

Mahnoor na ƙoƙarin durkusawa ƙasa momma ta yi saurin ce mata ta hauro saman bed. Ba musu ta zauna bakin bed tana cigaba da sharar kwallah. Rungumota momma ta yi tare da bin mama Haulat da kallo alamar tana jiran karin bayani. Girgiza kai mama Haulat ta yi alamar bata da masaniya a kan komai.

Da hannu momma ta yi mata alama da ta tafi kawai. Cike da girmamawa ta amsa da to, sannan ta juya da sauri ta fita. Dawo da hankalinta kacokam a kan Mahnoor momma ta yi, cike da kauna haɗe da sigar rartashi ta fara tambayarta me ya faru?.

Kamar ba zata faɗa ba, sai kuma ta daure ta ce ya koreta daga ɗakinsa. Ajiyar zuciya momma ta sauke, dama ta yi expecting hakan, so sai ta rarrashi Mahnoor har ta yi shiru, sannan ta ce.

"Amma ba nace maki in dai ba a cikin ɓacin rai yake ba ko ya hantareki kada ki matsa kada ki damu ba?". Momma ta jefa mata tambayar.

Cikin kuka ta ce. "Momma tsoronsa nike ji"........... Tabbas ta fahimci tsoronsa sosai take ji, dan haka sai ta shiga bata wasu dabaru ta yadda zata bi har Allah ya bata ikon shawo kansa. Ƙasa kunne ta yi tana saurara sosai saboda kaunar da take yi wa mijin nata, dik wasu shawarin momma ta naɗesu a cikin kwakwalwarta, momma bata jin kunyar nuna mata hanyar da ake bi dan maganin mazan gidan King ba, kun san ita ai ta kware, wannan hanya da take bi dan yin maganin King har ya amsa abin da bai niyya ba, shi ta zauna ta warwarewa Mahnoor komai tsab, daga karshe ta rufe mata da cewa in dai har tana san shi da gaske to ta jure ta bi dik shawarin da ta bata.

In ta dage ta yi komai cikin nitsuwa tabbas yau Jaish ba zai zulle mata ba, dan rauninsu kenan.
Kunya tamkar Mahnoor zata shige cikin ƙasa, ta yi ƙasa da kai kamar ba zata sake ɗagowa ba, sai dai da yake tana san Jaish, zuciyarta ruwan madarar albarka take kwaranyawa momma da ta jajirce a kansu.

Momma kuwa, da bata ji kunyar komai ba har da cewa. "Zan yi magana da shi, kuma a daren yau, zan kira shi in sanar mashi da matsayinki a wajensa da kai'na, zan tayaki da yi mashi nasiha, daga karshe zan ce ya kama hannunki ku tafi part ɗinsa, ba zai yi mun musu ba, dan bai taɓa yi ba, tabbas zai karɓe ki idan na buƙaci hakan, amma ni da ke mun san ba dan ransa ya so zai yi hakan ba, dan haka ya rage naki sauran aiki, in kina san ransa ya so kuna shiga part ɗinku ki yi wanka a toilet ɗinsa, kada ki matsa ko nan da can, ki sanya ɗaya daga cikin kayan da zansa mama Haulat ta baki anjuma, ki shirya ki haye bed ɗinsa ki kwanta,kada ki damu da sai ya kulaki ya yi maki magana a daren, kada fa ki rusa mana shiri, kuma kada ki damu da dik abin da zai ce maki dan kin kwanta a bed ɗinsa, in kin kwanta ki yi gaggauwar rufe idanu dan ma ya zaci barci kike yi, tabbas ina da yakinin zai dawo gareki".

"Sannan kada ki ji tsoron kwanciya a jikinsa idan har ya hau gadan, dik zafin kansa da kike ganin nan bai kai mahaifinsa a lokacin da yake matashi ba, so ni na faɗa maki dik zafin nan nasa ba zai iya taɓuƙa maki komai dangane da faɗa ko kyara ba a lokacin da zaki zo garesa, in dai kin bi dik tsarin da na tsara maki, lastly dik abin da zaki yi ki sanya nitsuwa a ciki, dik da naga kina da nitsuwa, amma ki kara, dan dik wani namiji yana san mace mai nitsuwa, nitsuwar tana jan hankalinsu sosai".

Tsabar daɗin kalaman momma har ji ta yi tamkar ta jawo dare ya yi, a yanzu dai gani take yi tamkar zata iya aikata dik abin da momma ta ce, sai ta ji ta matsu lokacin ya yi, har ga Allah tana kewarsa, kuma ya saba mata da hot kiss kafin su yi barci a Jimeta, to yanzu babu, da kyar take iya yin barci, ga ɗamin jikinsa dik bata samu, kuma tana buƙata, sai ta ji tana buƙatar dare ya yi da wuri yau ta kwana a saman kirjinsa....... Wayyo my belly, Mahnoor is to much, love ya rufewa yarinyar nan idanu fa, Jaish ɗan duniya ne wlh, ya koyawa yarinya abu dan iskanci yanzu kuma ya ce bai san wannan ba, zaka yi bayani ne bari Queen Zarina ta aure samartakanka nan ne zaka gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah Sallallahu........😅🥱

Momma ta karanceta tsab, dan akwaita da iya harbo jirgi mutun da wuri, tuni ta gano Mahnoor fa ita ma a hannu take tana san kasancewa da mijinta, ta ji daɗin hakan, ba ƙaramar dama hakan ya bata wajen kara karfafawa Mahnoor ɗin gwiwa ba.

Sun jima a wajen suna hira har 1:30 na rana, sannan momma ta buƙaci da ta tashi suje lokacin sallah ya yi. Miƙewa ta yi ta fita ta nufi part ɗin mama Haulat.

Momma na ƙoƙarin miƙewa ta shiga toilet sai ga mama Haulat ta shigo baki a ɗauke da sallama. Dakatawa momma ta yi haɗe da amsa mata sallamar. Zuba mata idanu ta yi tana jiran ta ji dame ta zo. Cikin girmamawa mama Haulat ta sanar da ita Jaish fa yaki cin abincin da aka kai mashi, da mama Haulat ɗin ta je ta sake kiransa a kan ya zo ya ci sai cewa ya yi ba zai ci ba, kada mama Haulat ta sake dawo mashi cikin ɗaki a kan wannan abincin.

Jinjina kai momma ta yi tare da yi mata almar ta je kawai babu damuwa. Juyawa ta yi ta fice tana jinjina zuciya irin na yaran King.

Toilet momma ta shige ta ɗauro alwala ta fito. Sai da ta yi sallah ta yi addo'inta sannan ta tashi ya nufi dry kitchen nasu, a nan ta sake shirya mashi simple things da zasu ɗan rike mashi ciki, ta ɗauka izuwa part ɗinsa.

Tana shiga yana dawowa daga musque sanye da arab jallabiya milk color. Yana ganinta ya ɗan turɓune fuska tare da zama a saman sofa. Kasa saman sinfiɗar gashin jimmina dake parlourn ta ɗaura tray ɗin abincin, sannan ta koma saman sofa ta zauna suna fuskantar juna.
Sai kallanta yake yi yana jiran ya ji me zata ce mashi. Sallamar Jawad ya katse maganar da take san yi mashi, so sai ta fasa faɗin abin da zata faɗa ta miƙe ta nufi waje tana faɗin su ci abinci to.

Allah sarki Jawad ya kasa zama a office ɗinsa ne jin cewa Jaish bashi da lafiya, dik ya rasa sukuninsa har sai da ya dawo ya gansa.

Kallon time a wayarsa Jaish ya yi 2:00 dai'dai yanzu, dawo da kallansa a kan Jawad ya yi. "Bro me ya dawo da kai by this time around?".

Zama ya yi kusa da shi tare da kai hannu ya taɓa forehead na Jaish ɗin yana faɗin. "How's your body?".............. "Feeling better Alhdulillah" jinjina kai Jawad ya yi kafin ya ɗaura da cewa. "Ka tayar mun da hankali, all my tougth ciwon ya fi haka". Yana magana ya shafa goshin Jaish.

"No ba wani ciwo bane bafa, is just only headache, and momma ta ce rashin cin abinci ya kawo shi". ............ Allah mai iko, gasu dai kamar twins, amma shi Jawad a kan lokaci yake cin abinci, shi kuma Jaish sam bai damu da ci ba, wani lokaci sai yunwa ta yi mashi over ya ji zai iya faɗuwa sai ku gansa ya ɗan ɗauko maltina ko wani drinks ɗin ya sha, dik gudun cin abincin ne fa.

Jin haka yasa Jawad ya sauko ƙasa wajen da momma ta ajiye abincin. Buɗewa ya yi ya fara zubawa ɗan uwan nasa abin da ya dace da shi yana faɗin. "Since nike faɗa maka cewa sometimes yunwa zai janyo maka wani big problem ɗin, amma baka yarda, anyway come down and eat yanzu kam".

Jaish bai yi wani gardama ba ya sauko kasan suka fara ci a tare cikin plate ɗaya, suna ci suna hira sama sama.

3:00 dai'dai har lokacin suna tare momma ta kira Jawad a waya a kan ya zo. Tashi ya yi cikin sauri ya nufi bedroom ɗinta yana sanar da Jaish ya kwanta ya huta even for one

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login