Showing 96001 words to 99000 words out of 403653 words

Chapter 33 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

131

san yara sosai. Miƙa mata babyn momma ta yi. Karɓa ta yi tare da buɗe fuskarsa cikin haske dan ta gansa da kyau.

Subhanallah, saura kaɗan ta saki yaron nan ya faɗi ƙasa, sai ta yi saurin rikesa da kyau tana zaro ido.

Cike da mamaki Momma ta ce. "Lafiyarki Raeesa?".

"Momma ina fa lafiya, naga yaron ne tamkar hoton uncle Jahiz yana jariri, hotonsa da take manne a jikin bangon bedroom ɗin Akka". Cike da mamaki sosai ta yi maganar.

"Jahiz kuma?". Momma ta jefa mata tambayar ba tare da nuna damuwa ba.

"E momma! Uncle Jahiz wlh, Allah sun yi kama ni dai na gani".

"Wannan yaron fa da Koreans yake kama, tayaya zaki haɗa shi da Jahiz?! Ko kuna da ƴan uwa koreans ne ban sani ba? Ko kuma Jahiz ya taɓa aure ne?". Cewar Momma, ta yi maganar tare da wucewa gaba dan ta je wajen love ɗinta wato King.

"Wlh momma ni dai dik da yake kama da Koreans ya yi mun kama da uncle Jahiz, bamu da ƴan uwa koreans, amma kuma shi ma uncle Jahiz ya so ya yi kama da Koreans time da yake ƙarami, baki ga hotonsa a ɗakin Akka bane?".

Momma da ko a jikinta ta juyo ta karɓi babyn haɗe da cewa. "Yanzu dai jeki wajen mijinki dare ya yi, da safe kyazo ki ga babyn da kyau sai ki tabbatar mana da waye yake kama? Nasan dare yasa kike ganin kamar Jahiz a tattare da shi". Tana magana tana cigaba da tafiya ta rungume baby da kyau da kyau.

My people's me kuke tinanin zai faru? Babyn Khadija kuma da uncle Jahiz? Muje dai zuwa, is time for surprised.🤍💘🔥

Aunty MieMie taso ta sake yin magana, dan ita wlh wannan babyn da uncle Jahiz ya yi mata kama, amma ganin momma taba saurin isa ga King yasa ta hakura suka yi sallama ta nufi part ɗinta, amma a ranta ta gudurta zata daka sammakon ganin wannan babyn, dan ba zata bari kanta ya kulle ba.

Sallama suka yi, Momma ta wuce izuwa wajen love ɗinta, Aunty MieMie ta wuce wajen nata flowern. My people's akwai cakwakiya fa, ni dai komai ta ɗauki zafi ina da Maltina mai sanyi, dan haka kowa ya samo Maltinars mai sanyi ta yadda idan kansa ta ɗauki zafi ƙwaƙwalwa ta ɗauki caji sai ya ɗan korata ko ya kuka ce?.

===========================🔥
••••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••🔥

9:30 pm.

Tsaye Sweetie take a gaban mirror na room ɗin Ronnie, ta fito daga wanka, wasu irin kyawawan kayan barci mai nitsar da tinani ne a jikinta, shi ya saya mata su ɗazun da ya je fada ya ga yayansa sai ya wuce super market ya yi mata sayayyan abubuwan da zata rinƙa tsantsara kwalliya.

My people's fitowar Black Tiger fada ya yi bala'in tada tarzoma, ya jijjiga zuƙatan mata da mazan Black world.

Ba matan ba ba mazan ba dik wanda ya gansa sai da ya haɗiyi yawu, jama'a dayawa sun mutu a kansa, sai a yanzu ƴan'matan Black world suka fahimci ashe haukar banza suke yi da suke mutuwa a kan kyan Ronnie, ashe ga uban Ronnie a kyau, sai dai kowacce ta gani a banza, infact tsoronsa ma ya hana dik mutanen birnin kallansa sau biyu.

Dik wadda ta kalli face ɗinsa na farko bata sake ɗagawa ta kalli na biyu, dan ba zasu iya ba, tamkar mutuwarsu haka suke jinsa, yana razana zuƙata, tun basu gansa ba ya kasance tashin hankalinsu, yanzu kuwa ganinsa ya fi jinsa ashe. Ga shegen kyau amma ba halin ganin kyan a ji daɗi......😥💔

Jama'an birnin nan babu wanda bai ziyarci cikin empeir ɗinsa ba a yau, dik dan ganinsa, sai dai fa akwai dayawan mutane da suka suma a kallonsa na farko, dama in baku manta ba babansa ya faɗa mashi babu wanda zai iya kallan face ɗinsa kawai ya sake ɗaga idanu ya kalla, iya face ɗinsa kawai ba kwayar idanunsa ba.

Wanda zasu kallesa a kallon farko basu suma bama sai masu karfin zuciya, masu raunin zuciya nan take zasu sume, kuma haka ne, jama'a dayawa sun suma saboda raunin zuciya, masu juriya kaɗan ne. Gaskiya a gabaɗaya faɗin birnin Black world ko rabin mai karfin halin Sweetie ba za'a iya samu ba, domin kuwa ita kaɗai ce ta iya kallan kwayar idanunsa kuma ta zauna lafiya. Ni kam anya baban Black Tiger bai tsafe face ɗin ɗan nan nasa ba kuwa? Kowa baya iya kallansa saboda bala'in tsoronsa da suke ji!.

Master Devil dik wannan tauri da bakar zuciyar nan tasa ya ƙasa iya kallan face ɗin Black Tiger sai biyu, tin da ya kallah sau ɗaya ya yi ƙasa da kai bai sake ɗagowa ba, haka ma fa wai dan namijin gaske shi ɗin.

Abin haushin kuma dik wanda ya ɗaura idanunsa a kan face ɗinsa to fa da wannan kallo ɗayan face ɗin take zama mashi a ransa babu mantuwa, dik birnin fuskarsa ya kama zuƙatansu, tinanin kyansa ne kawai a cikin ransu. Ga shi da bala'in kwarjini da farinjini, idanunsa kamar na riƙaƙƙen ɗan love, ga su kaifafan gaske, akwai sirrika masu tarin yawa a kwayar idanunsa wanda ba zai iya bari a haɗa ido da shi ba.

In short shigarsa fada ya wuci tinanin mai tinani, abin ya yi matukar tashin kan jama'ar birnin Black world, sai da hasken fatar Ronnie ta ɗan dishashe lokacin da ya zo kusa da yayan nasa, hasken wata mai dishashe hasken taurari..

Kuɗi ta ci ubanta a wajen bayyanarsa a fadarsa, anyi tsare tsare da zuba sabbin abubuwa, motocin da aka zubo kawai sun kai kuɗin budget na wata ƙasar, dukiya dai ta zube ƙasa ta yi mubaya'a matuƙa.

Kunsan yanzu arzikin Black Tiger ya ci uban na da, yanzu suna da arzikin red gold a karkashin kasarsu, kunga kuwa ai abin sai wanda ya gani.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Floris tana zaune saman bed ɗin Ronnie, Allah sarki, Ronnie ya je ya rarraso kayarsa, sun shirya yanzu. Sweetie tana ƙoƙarin gyara gashin kanta, Floris tana daga zaune a bakin bed tana yi mata bayanin yadda zata gyara da kanta, ita ta ce a koya mata ta yi da kanta ba sai ta rinƙa jira ana yi mata ba.

Sai santin kyanta da kyan gashinta Floris take yi, ba shakka kayan barcin sun zauna a jikinta, bakara mun kyau ta yi masu ba, yanayin idanun Sweetie idan ta kalleka sai ka ji tsikar jikinka ya mimmike, shiyasa fa Kamran baya yarda ya kalli cikin idanunsu ita da Pretty.

Ta cikin mirror gabanta fararen idanun nata suka walwalo mata jarumin nasu tsaye a bakin kofa, sam basu ji shigowarsa ba, a yanayin tsarin kofarsa irin na yayansa ne, zaka iya saitawa kofar sillent, idan ka shigar mata da sillent ko ka buɗe ba za'a san ka buɗe ba, saboda ba zata yi kara komai ƙanƙantarta ba.

Sai da Ronnie ya ji wani irin faɗuwar baba, a take tsikar jikinsa ta mimmiƙe lokacin da ya ga walwalin fararen idanunta ta wurga mashi kallo da su, ga shi ta cikin mirror ne, abin sai da ya ɗan razana zuciyarsa.

"Ronnie yaushe ka shigo?". Ta jefa mashi tambayar ta zage tana ta ƙoƙari dole sai ta kama gashinta mai bala'in tsantsin da yaki kamuwar nan ta ɗaure, gashin yaki kamuwa ta samu ta ɗaure shi, har wani nishi take yi wajen ƙoƙarin kama shi, sai dariya Floris take yi mata tana tsokanarta da raguwa bata iya komai ba.

Jin ta ambaci Ronnie yasa Floris ta yi saurin kai kallonta a wajen kofar, yana tsaye cikin kayan barcinsa sak irin na jikinsu ita da Floris, sai dai na shi ash colar ne, na Sweetie milk color, na Floris black color, ya harɗe hannnu a kirji yana kallansu.

"Beb yaushe ka shigo bamu sani ba?". Floris ta jefa mashi tambaya. Yana ta kallan kayan jikin Sweetie bai amsa masu ba, sosai Floris ta ji wani abin ya soki ranta, kamar ta ji zafin kallon Sweetie da yake yi har ya kasa iya amsa mata maganarta.

Abin ya sosa mata zuciya, sai ta miƙe da nufin ta fita ta basu waje, tin da ta kalli yanzu shi idan yana tare da Sweetie baya kallan kowa bare har ya gansa da daraja!!.

"Floris ina zaki je?". SweetiE ta faɗa itama kallanta a kan Ronnie, ita tana kallan face ɗinsa shi kuma yana kallan zubin kyakkyawar halittarta mai tafiya da imanin namiji mai lafiya.

Rai a ɓace a ɗan kule ta ce. "In da ya dace da ni zan je Sweetie".

Gashin kanta ya ki ɗauruwa ne ta sakesa ya watse a gadan bayanta dan ta gaji, sai faman haki take yi ta ce. "To ki dawo da wuri"................... Sweetie duniya, sarai tasan ran Floris ya ɓaci ne, amma da yake ta san ta kan tsiya dik yadda suka zo mata a haka take binsu, wasa wasa ita ma ta iya tsiya sosai, sai ta nuna bata san ma Floris ta yi fushi ba, ta nuna abin bai dameta ba har da cewa ta dawo da wuri.

Kin amsa mata Floris ta yi, ranta ne ma ya kara ɓaci, wato ko hakuri ba zasu bata ba, sai ma suka nuna kamar basu san tana ɓacin rai ba, lallai dole ta san matakin da zata ɗauka a kansu, ba zata zuba masu idanu su rinƙa kunsa mata bakinciki ba.

Da ta zo wucewa a kofar ɗakin, matsa mata hanya Ronnie ya yi, kallansa a kan Sweetie ya ce. "Dama Angela tana nemanki".

Ya ilahi, wani irin bakin bargon bakinciki ne ya kara lulluɓe zuciyar Floris, wato har da Ronnie ma faɗi yake ta je bai wani damu da ranta a ɓace ba ko? Lallai ma sun walaƙantata, dole ta nemi hanyar ɗaukar mataki.

Bata bashi amsa ba shima tasa kai ta fice da sauri, tana fita ta rushe da kuka mai taɓa zuciya, da gudu ta biyo ta saman escletor, bata ma jira ya yi kasa da ita ba ta taka stairs ɗin da gudu ta sauko ƙasa.

A babban parlour ta wuce master Devil dake zaune saman sofa tana jiran Jack akwai aikin da Black Tiger ya basu, so yana zaune yana jiransa ta zo da gudu tana kuka ta wuce, da kallo ya bita yana mamakin meyasakata kuka kuma? Ya dai san ita ce sanyin idaniyar Ronnie, in ka taɓata to ka taɓo karar kwanarka, amma yau take kuka da hawayenta kuma Ronnie yana cikin gidan nan? Anya lafiya kuwa? Ya jefawa kansa tambaya.

Ɗayar bakar zuciyarsa ce ta amsa mashi da kila Ronnie ɗin ne ya bakanta mata rai, kila da shi suka samu saɓani, in kuwa haka ne kana da damar shiga jikinta ko dan fansar da kake san ɗauka a kan Ronnie. Jinjina kai ya yi tamkar yana magana da mutum mai rai, sai ya ji ya yi na'am da wannan shawara da zuciyar tasa ta bashi, a hankali cikin zuciyarsa ya furta................ "Now is my time Ronnie, wait for me am coming".

Shi kuwa Ronnie tana fita ya tako izuwa in da Sweetie take, hannu yasa a nitse ya fara tayata tattara gashin nata ta ɗaure, yana jin wani love period a tattare da shi mai matuƙar nishaɗantarwa.

"Ronnie meyasa ka kori Floris?". Sweetie ta jefa mashi tambaya.

"Very very sharp brain, kai Sweetie ke karshe ce, yanzu waye ya faɗa maki na koreta ne da gangan?". Ya kai karshen maganar tare da tsai da idanunsa a kan ɗan bakinta ta cikin mirror dake gabansu.

Kunga yadda suke tsaye a gaban mirror nan suke kallan kansu, haka Black Tiger yake tsaye a gaban nasa mirrorn yake kallan dik abin da yake faruwa a gabaɗaya faɗin birnin Black world.

"Ai daga ganin yadda ka yi mata na fahimci da gangan ka yi hakan dan ta fita, akwai wani abin special da zaka faɗa mun baka san ta ji ne?". Cewar Sweetie.

Jinjina mata kai ya yi, tamkar wanda yake a cikin maye, rage tsawonsa kaɗan ya yi, a dai'dai kunnenta ya saita ɗan bakinsa.................. "So special sosai ma zan faɗa maki, haƙiƙa ke yar baiwar ce Sweetie, Allah ya yi maki baiwar kaifin ƙwaƙwalwa ga iya magana mai daɗi, ga fahimtar halin da mutum yake a cikin cikin ƙanƙanin lokaci, kin cancanci a yaba maki, ba zan taɓa bari wannan kaifin ƙwaƙwalwa taki ta salwanta a banza ba, tabbas idan kika yi karatu jama'a da dama zasu ci riba a tare da ke, al'umma guda zasu karu da iliminki".

Tin da ya fara magana idanunta a kanta tana jin tamkar gizo ko mafarki take yi, hakan yasa ta ɗan zaro mashi ido ta cikin mirror, ba zai iya ganin cikin kwanciyar idanunta ba sai ya lumshe nasa yana cigaba da jawabi.

Sai da ya kai aya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin matsuwa da jin me yake nufi ta ce.
"Ronnie to me kake nufi da kalamanka?".

"Zan faɗa maki wani lokaci, yanzu dai ba shi ne a gaba ba".

"Menene a gaba to?". A matse da san jin komai dallah dallah ta jefa mashi tambayar.

Kara yin kasa da kansa ya yi, ya manna ɗan bakinsa da kunnenta, ya yi ƙasa da murya matuƙa yadda sai shi da yake furta maganar da kuma ita da ake yi a kunnenta ne kawai zasu iya jin me suke ciki, with his full confidence ya fara magana kamar haka.

"Ina yi maki albishir da ina san shiga addininki dan kuwa shi ne na gaskiya na yarda d.........."

Katse shi ta yi ta hanyar juyowa da karfi garesa, she was so surprised over, she didn't expect that wonderful word from him, she can't forget this days in her life koma da wasa ya yi mata!.

Zata yi ihun ban mamaki ya yi sauri rufe mata baki, ƙasa sosai ya kara yi da murya. "Kada ki kuskura ki yi hakan, ina san ki sani dik abin da muke yi yaya yana kallanmu, kuma yana jinmu, raɗa a kunne ne kawai ba zai ji me na faɗa ba, dan haka ki kiyaye, ki yi shiru ki saurareni".

Wani irin tsuma ta ji jikinta yana yi, tamkar ana mincininta, burinta kawai ta daka tsalle ta yi murnar ta yi nasara, amma ya zata yi? Dole ta yi shiru ta danne kada murna ya koma ciki idan Black Tiger ya jiyosu, har wani ciza laɓɓanta ta yi saboda irin tsananin farincikin da yake ratsa mata zuciya, tamkar mai jin sanyi haka take jin jikinta yana yi mata.

Sarai ya lura da tsananin farincikin da ta shiga, hakan ba karamun kara mashi kwarin gwiwa ya yi ba, ya yi farinciki matuƙa shi ma, kuma tin da ya yardanwa kansa zai shiga addinin Musulunci ya fara jin kansa a wani irin ni'ima, nishaɗi da farinciki na ban mamaki, yana jinsa tamkar ba shi ba, wani irin sakayau yake jin jikinsa yadda kuka san wanda ya kwashi shekaru yana ɗauke da wani kungurmin dutse mai nauyin gaske sai yau aka sauke mashi shi, ya ji komai tana yi mashi daɗi, shi kaɗai idan ya zauna sai ya tsinci kansa da sakin murmushi, wannan ne ya kara bashi kwarin gwiwa ya yarda da babu abin bauta da gaskiya sai Allah, lallai suratul iklas gaskiya ce, lallai ne Allah shi ne kaɗai abin bauta na gaskiya. My best part again!! Lallai ne Allah shi ne abin bauta na gaskiya, ka bisa ka more, akasin haka ka ɗanɗani madarar azaba!!.

Cigaba ya yi da cewa. "Zan karɓi addininki saboda na yarda shi ne na gaskiya, na yarda Allah shi ne abin bauta ba Yesu ba! Sannan na yarda da dik abin da kika faɗa mun hakan ne, sai dai ina neman wata alfarma guda ɗaya a gareki".

A hanzarce ta yi yunkurin yi mashi magana, hannunsa na saman bakinta tin da ya rufe mata ɗazun, tana san amsa mashi da wace alfarma ce wannan, sai ya yi saurin kara rufe mata baki da kyau.

"Kada ki damu, ba sai kin amsa mun ba, nasan so kike ki ji wace alfarma ce, ko baki amsa ba zan sanar dake, ni dai ki yi shiru ki saurareni kada ki yi wata magana".

Jinjina mashi kai ta yi alamar to, sai kara tsuma jikinta yake yi, tana jin tamkar ta rumgume shi da karfi saboda daɗi, tabbas idan Ronnie ya musulunta zasu iya cin karfin wannan yakin, shi kaɗai kusan kaso 40 ne cikin ɗari na wannan fafutukar.

"Wannan alfarma ba komai bace face ki taimaka mun mu canza yayana, mu yi ƙoƙari ya shiga addinin Musulunci, tabbas yayana yana da zuciya mai kyau, kema idan kika ji tarihin tasowarsa zaki yarda da hakan, yana da san taimakawa mutane, sai dai yana da wata ɗabi'a ɗaya wadda ita ta haifar mashi da bakar zuciya a cikin kirjinsa!!".

Dakatawa ya yi da yin maganar yana kallan yadda ta zaro ido tamkar wadda ta yi mutuwar tsaye, babbar magana, wai ta taimaka mashi su musulunta da Black Tiger? Wannan bakin mugu mai bakar zuciyar da babu imani bare tausayi a cikinta ɗin ne zasu musuluntar? Ita ko da take san kowa ba cikin birnin ya musulunta bata taɓa sanya shi a lissafia ba, dan tasan sai dai ta mutu kamar kare ba dai wannan ya musulunta ba, sai dai jikinta ya ɗanɗani azaba da ukubarsa har ya kai ga hallakata, lallai ne yau Ronnie ya zo mata da sabon zance mai haɗarin gaske wanda babban barazana ce ga rayuwarta. TASHIN HANKALI!!!!.

Sai dai kuma ta matsu da ta ji wace iriyar dabi'a ce wannan wadda ta canza zuciyarsa izuwa Black HEART?.

Dik da ganin tashin hankali ta damuwa haɗe da ruɗani a saman face ɗinta na jin bukatarsa hakan bai hana shi cigaba da cewa.

"Zallar san mulkar duniya ce a ran yayana shiyasa yake da bakar zuciya, zai iya yin komai a kan burinsa, kuma wasiya ce daga gabanmu kafin ya mutu, ya umarcesa da lallai ya mulki duniya, ya cika mashi burinsa ya riga Duniyar shaiɗanu yin hakan, mulki ita ce nan tasa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login