Showing 243001 words to 246000 words out of 403653 words
daka mata tsawar ta faɗa mashi ina mutumin da ta kawo ɗin yake?.
A hanzarce ta miƙe tsaye tare da dirowa kasan gadan, jikinta na kerma amma taki faɗa mashi gaskiyar cewa wasa take yi mashi, dan Ammo ta ce kada ta yi saurin faɗa mashi su bari kishin tasa ta ɗan zafafa. Kin yin magana ta yi tana kumbura kumatu. Kara hasala sosai ya yi, ya zo har wuya, gadan gadan ya nufota da nufin kai mata duka tun da taki faɗa mashi ina mutumin, ɓacin rai yasa bai tsaya tambayar mai gadi akwai wanda ya zo gidan ne ko babu ba? Hankalinsa dik a kanta shiyasa ita ya fara tinkarowa kai tsaye.
"Where's ur phone?". Ya faɗa cikin tsawa, ya yi maganar kuma yana kara tinkarota gadan gadan tana ja da baya har suka kurewa jikin bango. Rumfa ya yi mata da kirjinsa, yana huci ya sake tambayarta ina wayarta? Dan a tinaninsa yanzu kenan tana hira da maza ta wayar, dan haka a yanzu zai yi rugu rugu da wayar ba kuma zai sake saya mata wani ba, sai yanzu ya gane ashe kuskure babba ya tapka da bai sanar da ita cewa ita matar aure ce dan haka ta nisanci mazan waje ba, yazama dole yau ta san matsayinta.
Shiru ta ki yi mashi magana, hakan ya kara zafafa kunan da ransa yake yi, cikin fushi ya cire hannu zai ɗauketa da gigitaccen mari. A hanzarce tasa hannu ta kare fuskarta haɗe da fashe mashi da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Dakatawa da yunkurinsa ya yi yana huci sosai, ya ɗauki zafin da har zata kaisa ga aikata aikin danasani, shi da bai taɓa dukan mace ba yau ya kwantanta, kuma a kan wadda yake kauna fiye da komai, sai ya ji rashin daɗin hakan a ransa.
Cikin zafa ya juya zai je wajen Ammo ya ji dalilinta na barin baby ta kula wani namijin bayan ita tasan komai. Yana juyawa baby ta yi saurin riƙo hannunsa tana kuka. Ƙasa ta zube gwiwowinta a gabansa ba tare da ta saki hannun nasa ba, cikin kuka ta ce. "Tin da nike da kai ban taɓa ɓata maka rai ba a rayuwata sai yau, tabbas ba zan manta da wannan rana ba a rayuwata, ka yi hakuri baby ba zan kara ba, na tuba ka ji? Bana fatan wara rana ta zo wadda zan ɓata ran wanda na fi so sama da komai a duniya, wanda ya so ni ya kuma sanyani da farincikin da ban taɓa zata zan shiga ba a rayuwata, tabbas na yi kuskure".
So mugun abu ne wani lokaci, lokaci guda ya ji zuciyarsa ta sanyaya, jin kukanta yasa ya ji zuciyarsa ta karaya, yana santa baya san kukanta. Dan haka a hankali ya juyo gareta yana sauke ajiyar zuciya. Ɗan duƙawa ya yi yasa hannunsa ya ɗagota, sai hawaye take ta shararawa. Rungumeta a jikinsa ya yi yana jin zuciyarsa ta sanyaya. Sai shessheka take yi, kukan gaske ta yi, dan bata taɓa tinanin ransa zai ɓaci har haka ba, sai dik ta yi nadamar abin da ta aikata.
"Baby ka yi hakuri ka yafe mun ka ji?". Ta faɗa tana kara shigewa jikinsa. Kasa ƙasa da kyar ya iya cewa. "Babu komai bab ɗin babynta, komai ya wuce, yanzu ki faɗa mun ina mutumin yake sannan meyasa zaki fara soyayya da wani ba tare da kin sanar da ni ba?". Wato dai har yanzu bai huce ba, buƙatarsa a faɗa mashi ina mutum yake kawai.
"Am so sorry my baby, wasa nike yi maka, ni babu wani da nike so a duniya sai kai". Wani irin ajiyar zuciya mai sanyin gaske ya sauke, cikin sauri ya ce. "Are u sure?". Kai ta gyaɗa mashi alamar yeah.
Ai bai san lokacin da ya rungumeta kam a jikinsa ba, bai ma san time da ya hau zuba mata ruwan albarka ba, cikin sambatun nasa ne yake haɗawa da. "Kada ki yarda ki kula kowa, ke ɗin mallakina ni kaɗai". ....... "Baby mallakinka kuma?". Ta faɗa irin like bata san komai ba.
Kai ya jinjina mata tare da amsa mata da e. "Baby to kenan ba zan yi aure ba tun da ni mallakin ka ce". Cikin shagwaɓa ta yi maganar dan ma ya ɗauka har yanzu yarinta na damunta bata san komai ba........ Wato ita ma baby yar duniya ce fa, tasan kan tsiya kala kala, wai ya ɗauka har yanzu yarinta na ɗawainiya da ita bata san komai ba.
"Babu wanda zaki aura sai babynki, ke ɗin matata ce ni kaɗai, dan haka kada ki kula kowa kin ji?". Da alama yana out of control yake wannan sambatu, dik dan murnar bata kula kowa bane fa, kamar ba yanzu ya gama bambami kamar zai tashi gidan ba.
"Baby kai zaka aureni kuma?". Ta tambaya like bata gane me yake nufi ba........ "Yeah ko baki san hakan ne?". Ya jefa mata tambayar tare da ɗan raba jikinsa da nata yana kallan face ɗinta dan yaga reaction ɗinta. Tafukan hannayenta ta kai ta rufe face ɗinta tana murmushi.
Shammatarta ya yi ya ɗauketa cak sai saman bed yana faɗin. "Kin ɗaga mun hankali over, kin sa na ji wani irin, dan haka yanzu zo mu yi hira babu in da zan je, kwantar mun da hankali kamar yadda kika ɗaga mun, yau i think ma a nan zan kwana". Ya kai karshen maganar yana kwanciya da ita a saman bed ɗin.
A cikin kirjinsa ta tura kanta tana faɗin. "Zan ji daɗi idan ka kwana a nan, dama haka nike so, kwantar da hankali kuma yanzu kuwa zan kwantar maka".
Rungumeta sosai ya yi tare da ja masu bargo ya rufesu har kai. .............To baby sai dai mu ce asuba ta gari Allah yasa iya barci kawai baby zai yi....👀🥱
Bari mu leƙa wani part mu dawo muga ya za'a kwantarwa da baby hankali, sai mun bi kwakkwaf😅🥱
🔥🔥🔥BLACK WORLD.🔥🔥🔥
Yau ta kama Sartuday, bayan kwanaki biyar kenan da fara zuwan Sweetie school, daren yau za'ayi babban partyn su Ronnie. Tin safe ake ta shirye shirye, kayan da Black Tiger ya sayawa Ronnie da zai saka a wajen wannan party lallai ba'a taɓa wani ɗa da ya taɓa sanya kwantankwacin irinsu a faɗin birnin ba, dan kuɗin kayan kawai ya kusa kuɗin jirgi guda ɗaya cikin jiragen Black Tiger.
Tun kwana uku da suka wuce Ronnie da Sweetie suka haɗu suka zaɓi kayan da suke ga ya yi masu da irin design da suke so, kayan ya haɗu matuƙar haɗuwa, three-piece suit ce ajin karshe a tsada na Ronnien, cover shoes da zai haɗa da kayan ma almost hundred million take. Ita kuwa Sweetie dama wani irin daddatsetsen gown ya zaɓa mata wanda ya sha kwalliyar duwatsu na alfarma, kayan sun kai makurar haɗuwa, sai dai fa ita da Floris aka saya masu iri guda, kuma Ronnie ne ya ce hakan, dan shi har yau har gobe yana san Floris sosai, matsayinta bai canza a zuciyarsa ba, ita ce dai ta ja baya da shi.
Kayan nasu ita da Ronnie kalarsa ɗaya, yadda kuka san amarya da ango, dikka milk color ne, sai murna Ronnie yake yi ana ta hidima, jama'a na ta kai koma, dama jiya za'ayi partyn fa, sai Sweetie ta ce da Ronnie a ɗaga zuwa yau saboda girma da falalar ranar jumma'a bai kamata su yi party a ranar ba. Aminta ya yi da hakan shiyasa ya riko yayansa da a ɗaga wannan taro zuwa yau, da yake Black Tiger bai san dalilin ɗagawar ba sai ya yarda, da yasan saboda addinin Sweetie ne ba zai yarda a ɗaga ba, saboda bayan san musulunci, a jininsa tsanar addinin take. Kada ku manta autan ruhohi ne shi ɗin, kunga tsanar addinin a jininsa take.
Abin da baku sani bama, da Ronnie ya same shi da batun dakatar da halaccin luwaɗi a birnin sai ya ce kowa yana da ƴancin yin abin da yake so, dan haka shi ya halatta yin hakan, kada Ronnie ya kara zuwa mashi da wannan zance kuma kada ya kuskura ya hana kowa aikata luwaɗi ko zina, shi ya yarje masu su yi, su more rayuwarsu.
Da farko Ronnie ya damu sosai, har yake jin kamar ya gudu ya bar birnin saboda kyamar abin dake ransa, amma Sweetie ta tsaya tsayin daka wajen nusar da shi cewa ya yi hakuri watarana komai zai wuce, ba'a da'awa cikin sauki dama, kuma dama yadda suke ƙoƙarin nan dole shaiɗan ba zai so hakan ba, idan shaiɗan ɗin ya gwada ringayarsu ta ɓangarensu suka ki yarda Allah ya tsaresu daga sharrinsa, to sai ya koma masu ta wani ɓangaren, tana da tabbacin shaiɗan ne ya koma jikin Black Tiger yasa yaki yarda da wannan doka, dan haka ya kwantar da hankalinsa zasu yi nasara a kan big bro, da sun yi nasara kuma shikenan komai zai tafi yadda suke so, da kansa zai yarda da dokar, su zasu zama masu kafa doka kai tsaye ma ba sai sun ji ta bakinsa ba.
Da kyar dai Sweetie ta iya shawo kansa ya yarda, dik wani abin da Sweetie zata ce addininta ya yi hani da shi to shi kuma Black Tiger sai ya halasta wannan abin wa ƴan birnin, dik dan kiyayyarsa ga Musulunci, amma dik da haka Sweetie bata taɓa nuna ta damu ba, saboda tana koyi da annabawan Allah waɗan da suke da hakuri da juriya mai tarin yawa dan cinwa nasara...... ALLAH KA BAMU IKON YIN KOYI DA SU.
••••••••••••••••••••••••••••♥️
An ƙawata hall ɗin da za'a gudanar da wannan party matuƙa, yanayin tsarin hall ɗin hakika ya ƙayatar kuma kowa ya gani yasan anzubar da makuɗan kuɗaɗe ba kaɗan ba. Kayan Ado wato decorations masu zafi da tsantsar kyau. Yanayin theme na wajen launin white and gold ne, an zubawa gold ɗin kwayaye masu bata haske a in da suka kara haskaka wajen matuƙa, gold ɗin ya kara haske da ƙawata wajen.
A gabaɗaya wajen an ƙawata shi ne da wasu irin kyawawa kuma tsadaddun balloons, furanni masu kyau, da kujeru masu rufi (chair covers) da ribbons masu launin gold and white. A saman haɗaɗɗun tables dake wajen gabaɗaya akwai wasu centerpieces masu kyau irin su furanni, kyandiru da fitilu masu kyalli da suka kara ƙawata wajen.
Tables na wajen sun kasance a tsari mai kyau. Table da tsadadden kujerar da shugaban party zai zauna wato VIP table a gaban hall ɗin yake, yana fuskantar kowa kenan. Wajen da aka shirya abincin da aka shigo da su dan rabawa a wajen part ɗin yana ɗan nesa da wanen tables ɗin.
And manya manyan fitilu dake wajen masu duhu ne amma na alfarma, ga wani katan chandeliers mai wuta launika daban daban da ya kara ƙawata wajen a sama tsakiyar hall ɗin. Wajen kujerar zaman Ronnie namu and Black Tiger namu ya kasance da ƙarin haske na musamman don jama'a su samu damar ganinsa da kyau. My people's wajen nan ya haɗu, kuɗi sun yi kuka, tun daga kan tsarin wajen zaku gane ɗan gata kuma shalele ne zai yi party, abin ya haɗu fiye da tinaninku.
Shi kansa Black Tiger sai shirye shiryen zuwa wajen yake yi, dan tun karfe 4 na yamma za'a fara, kwana za'ayi ana yi. Ronnie kuwa tini ya gama shirinsa, dan yau rana ce ta musamman a garesa, yau zai shiga office ɗinsa a matsayinsa na babban Dr, apart from this hospital ɗin gabaɗaya mallakinsa ne. Ku kunsan abin ba'a magana sai shiru!!.
Tin karfe uku Ronnie ya tafi wajen part da nufin Sweetie zata biyosa daga baya, dan ita ta ce sai 4:30 zata zo, zata ɗan yi barcin rana ne, ya so su jera a tare, amma taki yarda. Sam bai nemi Floris ba, saboda yana tinanin zata zo a tare da Sweetie. So sai ya yi gaba, ya sha kwalliyarsa, sai dai har yau yana saka waɗan nan chairs and ring ɗin, ga earing, a yau ma dik ya zubasu a jikinsa, ya yi kyau kam matuƙa sai dai haramun ne, amma ya yi wa Sweetie alkawarin a hankali hankali zai dai'na sakawa In Sha Allah, ta taya shi da addu'a. Kun san sabo da yin abu barinsa lokaci guda abu ne mai wahala
Sai dai kuma tana can part na master Devil ba tare da sanin kowa ba, akasi aka samu tsakaninta da master ya yi mata fyaɗe, ya yi mata fyaɗen kuma ta ji ciwon sosai da yasa ta rasa jini sosai, kun san ba za'a haɗata da master ba dama, shararren mai bawa ƴan Wrestling horo, zakwakuri kuma zakaran da ya buge kowa except Black Tiger and Ronnie a faɗin birnin, namiji mai ji da karfi da lafiya ita kuma ƴar yarinyar da bata wuce Sweetie ba, da kaɗan ta fi Sweetie fa, kun ga kuwa dole karonsu ba zai yi kyau ba, ya kuwa yi mata fata fata saboda bashi da imani da tausayi, ko da yake shigarsu na banza ya ja masu ai, yana kan network ta samesa, shi kuwa ya cika aiki ya rage zafi da ita, ɗan ikka, ko da yake ba laifinsa bane, dik maza masu yin gym shegen jarabar tsiya suke da shi, saboda gym da suke yin nan yana kara buɗa jijiyoyin jikinsu ya faɗaɗa halittarsu hakan yasa sha'awarsu yake yawaita matuƙa ta yadda ba zasu iya zama babu mace a kusa ba.
So master yana tsoron fitar da ita zuwa hospital dan a iya saninsa yasan cewa budurwar Ronnie ce ita, so fitar da ita zai iya haifar mashi da babban matsala mai girman gaske, hakan hasa ya turata cikin toilet ɗinsa, a cikin jacuzzi ya sanyata ya rufe kofa da key, jininta na ta zuba har ta rasa ranta ba tare da ya sani ba, shi a cewarsa sai dare zai ɗauketa zuwa hospital a lokacin babu wanda zai sani, bai san cewa rai ya yi halinsa ba.
Sai dai fa dik abin da ya faru Black Tiger ya sani, amma ko a jikinsa saboda bashi da wata alaƙa da hakan, dama Floris Ronnie ya kawota empeir ɗin, dan haka shi ko cin namarta ɗanye ake yi ba abin da ya sha mashi kai, shi idan kunga yana magana a kan abu to fa ta shafe shi ne, idan bata shafesa ba ko kallo baya ɗaga idanu ya yi. So dik abin da suke aikatawa yana sane da kowa.
Fyaɗen da master ya yi wa Floris ne yasa bata zo janyo mashi Sweetie ba, kunga babu ta hanyar da zai samu Sweetie, da ya tabbatar wannan dama ta kubce mashi, cike da ciza yatsa na zafin rasa wannan dama ya fara ƙoƙarin shirya ta yadda zai yaudari Ronnie ya fitar da shi daga birnin, su je wajen birnin ya biya buƙatansa da shi kafin ya halaka shi, amma fa dik a tafin hannun Black Tiger yake dik wani shirinsa........... Hmm da shi ya raina capacityn Black Tiger ne, a tinaninsa ai baya kallan cikin ɗakinsa shiyasa idan ya shiga cikin yake sheke ayarsa son ransa. Bai san gar Black Tiger ya san komai ba, dik sheke ayar da suke yi shi da su Oxil yana sane da su, harta aman da Ronnie ya rinƙa yi ranar dik yasan da hakan.
(Wato guy ɗin nan Black Tiger ɗan duniya ne, wato dik wani iskancin da suke yi yana gani?🤔 Anya Black Tiger yana da feeling kuwa?🤔 Ina ƴan team ɗinsa? Maza ku fito ku faɗa mana ya aka yi yake iya kallan dik wani iskanci kuma baya jin komai?🤔)
••••••••••••••••••••••••••••••••••••♥️
Da misalin karfe huɗu dai'dai bayan Sweetie ta yi sallar la'asar, wanka ta tsantsara, ta shirya cikin wannan gown ɗin, da kanta ta gyara gashin kanta, Ronnie ya ce zai kawo mata mai gyata ta ce bata so, zata yi da kanta, dan haka da kanta ta gyara kayanta.
My people's Sweetie ta yi masifar kyau a cikin waɗan nan kaya, omg, her wellcome and goodbye so masha Allah, ta ko'ina tana cike ɓulɓul, yar 13 years kamar wata ƴar 15, sai kara cika take yi dan hankalinta a kwance yake tana samun farinciki sosai daga bro ɗinta Ronnie, wani ɗan siririn chain na zinari da Ronnie ya bata ta sanya a wuyanta, ɗaya daga cikin chains da yake sakawa ne, ta ce ya yi mata kyau sai ya bata, tsadar bala'i ne da ya shi.
Kara haskakawa gurun wuyarta ya yi, ga fararen hakwaranta na kara haskawa, wlh kyan da ta yi a yau baki ba zai iya faɗarsa ba, ku hasko yadda wannan golden hair ɗin nata yake kyalli, ba'a gyara shi bama tin ainahinsa mai kyalli ne bare kuma ya sha gyara? Ku kanku kun san dole ta tafi da imanin dik wanda zai kalleta.
Wasu shegun high heel ta sanya a kafafunta, irin covers ɗin nan ne, rigar tata na ja mata har ƙasa, a gaban mirror ta tsaya, ta juya ta sake juyawa, ita da kanta tasan ta yi kyau. Black Tiger yana ƙoƙarin nasa shirin shi ma, so hankalinsa sam sam baya a kanta.
Haba cikin wani irin taku mai kama da tafiyar hawainiya ta nufi waje, sai tashin kamshi take yi, kai tsaye bedroom na big bro ta nufa, tana tafiya tana wani yauki, dik Ronnie ya koyawa yarinyar nan sanka sanka na iyashege wlh, kowani rana sabon babi take buɗewa.
Dai'dai lokacin da ta buɗe kofar ta danno kanta ciki, shi kuma yana tsaye a kusa da bed ɗinsa yana ƙoƙarin ɗaura necktie na wuyarsa. Ya subhanallah, my people's Black Tiger ya haɗu, idanunsa kalar nata sak dama idan baku manta ba na faɗi wannan, yadda kuka san ya karawa idanun kala, sai suka yi olive sosai, da alama hankalinsa a kwance yake.
Sanye yake da three-piece suit shi ma irin na jikin Ronnie, da kalar da komai iri ɗaya ne, ya yi masifar kyau sosai, mutum zai iya ɓata tsawon