Showing 339001 words to 342000 words out of 403653 words
ya amsata ba, ta yi gaggawar wucewa kawai ta fita. Jikinta sai tsuma take yi tana san kallan jaruminta.
Tana fita dai'dai lokacin kuma Abdussalam ya shigo part na family daga ɓangaren uncle Abbas, ya zo ganinta ne, dama ya yi kewarta sosai, so ya samu labarin ta dawo shi ne da marmarinsa ya zo ganinta. Ita kuwa a lokacin ta fita ta kofar baya, sai nemanta guyson ma yake yi, Chuchu and Aneesa dik suna ta nemanta, cikin sanɗa da dabara ta nufi ɓangaren mayaƙa, tana tafiya tana ɓuya. Har ta isa ɓangaren warriors ɗin. Kai tsaye ta nufi bedroom ɗinsa, sai murna take yi, a lokacin yana kwance saman bed ɗinsa, ya idar da sallar isha'i ba jimawa, ya yi wanka yana sanye da white arabs jallabiya mai shegen kyau, ya ɗauko wayarsa da nufin zai kirata kenan ya ji knocking, a tinaninsa Abbonsa ne ko su Ansar, sai bai yi magana ba ya ajiye wayar tare da saukowa kasan bed ɗin ya nufi door.
Ba tare da tambayar wanene bane yasa hannu ya ɓalle key na door ɗin ya ja ya buɗe. Ai bai san lokacin da ya zaro ido tare da blinking sau biyu a lokacin guda ba ganinta da ya yi. Cikin gaggawa ta raɓa gefensa ta shige cikin bedroom ɗin tana dariya, ƙasa juyawa ya yi ya koma, sai yake ganin abin kamar a mafarki, ko kaɗan bai yi zato ba, kuma ko kusa bai ji labarin ba, shi dai ya ga baki suna ta zuwa, idan baku manta ba Abbonsa ya ɓoye mashi lamarin, so bai da labari. Saman drawer dake kusa da bed ta zauna tare da ware tafukan hannunta ta rufe face ɗinta tana sakin cool smile. Ya jima tsaye a wajen yana al'ajabi kafin ya juyo ya dawo ciki, rufe kofar da key ya yi, gabaɗaya sai ya ji ya ƙasa iya ɗaga idanu ya kalleta, wani irin zazzafar sonta ne yake kara fisgarsa. Da kyar ya karisa in da take, a bakin bed ya zauna suna fuskantar juna, sai ya yi ƙasa da kai ya kasa magana ita ma ta rufe fuska tana murmushi ta ƙasa magana.
Abin like wow gwanin birgewa, yadda suka zauna abin ya ƙayatar, kamar wasu mata da miji da suka mallaki juna!. Almost five minutes suna a haka kafin ya ɗan nisa, kansa a ƙasa yaki ɗagowa ya ce. "What a wonderful surprised! Gaskiya ba zan taɓa manta wannan rana ba my Hoonaira". Taki cire tafukanta daga face ɗinta ta ce. "My Hero ka ƙara kyau sosai, ka ɗan yi kiba abinka"........ "Na sha drips ba adadi ai dole na yi kiba, kema ai kin kara kyau sosai, kinsa na ji tamkar yau na fara ganinki". Cike da mamaki ta ce. "Dama ka ganni ne?". Ta yi maganar ne saboda taga ko sau ɗaya bai ɗago ido ya ganta ba, kansa a ƙasa, kuma ya ce ta kara kyau, ko a ina ya ganta?..... Bata san ɗan ikka ne yana satar kallanta ba, mai kunya irin na Jaish😅
Kai ya jinjina mata alamar ya ganta mana. "My Hero kai ne fa kullum kake damuna a kan yaushe zan dawo, na dawo cike da muradin zuwa in ganka, na zo kuma ka yi ƙasa da kai, kaki ɗagowa mu kalli juna, to me yasa?". Cikin shagwaɓa sosai ta kai karshen maganar. Ɗan ɗago idanunsa ya yi ya saukesu a kan kyawawan kafafunta dake cikin wasu kyawawan flip flops masu laushin takawa. "Ni ai na ganki". Ya faɗa idanunsa na ɗan rawa, kamar yana tsoron ɗagowa ya kalli kayan jikinta ne!..... "No my hero, ni gaskiya ban yarda da irin wannan kallon ba, ni fa yanzu nasan gaskiyar abin da yake cikin zuciyarka kamar yadda kasan nawa, meyasa zaka cigaba da azabtar mun da kanka wajen hana idanunka kallan abin da kasan zai zama mallakinka koma in ce ni taka ce?". Kamar zata saka mashi kuka ta yi maganar.
Nisawa ya ɗan kara yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗimi, lallai ba shakka yau ta yi mashi abin da tasa saura kaɗan farinciki ya kashesa, dan a lokacin da ya buɗe kofar nan ya sauke kallansa a kanta saura kaɗan numfashinsa ta dakata da breathing!. Slowly ya ɗago da kallonsa izuwa saman face ɗinta, cikin natsuwa ya ce. "Ba wai ina hana kaina kallanki bane, bana san kallan ya wuce na Musulunci ne, nasan in dai na ɗaga idanu direct na kalli face naki to fa zan zarce kallan musulunci, dan ba zan iya hakurin zare kallona daga kanki ba". Ya kai karshen maganar yana tsayar da idanunsa a cikin nata, kallansa take yi kawai tamkar ta mayar da shi cikin kirjinta haka take ji. Take idanunsu ya sarkafe cikin na juna, suka mace da zubawa juna kallon kauna, wani irin salon kallo da suke aikawa junansu mai cike da saƙonni da suke nuna tsantsar kewa da kauna juna tin da nike a wajensu kawai na taɓa kallan irin wanna salon kallon. Ko waye ya koya mashi? Gara ita Auta mun san daga ina ta koyo, shi fa? Mu dai mun san banda yaki babu abin da ya iya!.
"My Hero na yi kewarka fiye da yadda zato zai iya zata". Ta yi maganar ba tare da cire kallonta daga kansa ba. Ajiyar zuciya ya sauke. "Gaskiya na fiki shiga cikin kewa, kullum tinaninki ya zame mun tamkar iskar da nike shaƙa, kome nike yi ke nike tinawa, kina rai'na fiye da yadda tinani zai iya tinani". Cigaba da sakar mashi narkakken smile mai narka dakakkiyar zuciyarsa na warriors ta yi. "Please ina neman alfarman da a cire mun hannun nan in ga fuskar Hoonairata yadda yakamata". Ya yi maganar yana ɗan satar kallan dogon kyakkyawan wuyarta zuwa ƙasa kaɗan, ya ɗan yi mamakin ganin sauyawarta, kwata kwata fa bata cika wata biyu da barinta kingdom ɗin ba, amma ta sauya sosai, ya yi mamakin ganin yadda kirjinta ya ciko sosai, sai da ya ji tsikar jikinsa ta tashi, sai da ya ji kamar an jona mashi lantarki, ya yi danasanin kai kallansa wajen!.
"Ni dai a'a, kunyarka nike ji, ba zan iya buɗe fuskata ba". Ta faɗa tana zuba mashi wani irin salon kallo na musamman, ɗaya ne daga cikin irin salon da ta tanada zata rinƙa yi mashi a gidan aurensu.
"Yau kuma ni ake kunya?". Cikin sanyin murya sosai ya yi maganar. Kai ta jinjina mashi alamar e kunyarsa take ji!. Shiru ya ɗan yi, can kuma sai ya ce. "Kenan yanzu idan muka yi auren ma haka zaki mun? Ki ta rufe mun fuska da sunan kunyata?"...... Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. "E haka zan yi, idan ka takura sai ka rabani da kunyar in daina ji, kaga sai ka samu sauki". Wani irin daɗi ya ji ta lulluɓe zuciyarsa, ƙasa ya yi da murya, cikin tsigar dabara ya ce mata. "To shikenan, amma yanzu dai please a barni in kalla ko sau ɗaya ne?".
Kai ta ɗan girgiza tare da faɗin. "Ni kunya nike ji! Ba zan iya ba". Cikin wannan shagwaɓa tata mai tafiya da imanin ta yi maganar, sai ya ji tamkar an tsira mashi allura a tsakar ka.
"Please my Hoonaira, wannan kunyar zai cutar da ni fa, Please mana, shin baki son in ji daɗi ne?". Murya a raunace ya yi maganar..... "To rufe idanunka sai in buɗe maka"..... Ba musu cikin sauri ya datse idanunsa, dan a tsananin ƙage yake da san ganin face ɗinta. Zame hannayenta daga face ɗin nata ta yi, sannan ta riko hannunsa da hannunta ɗaya, ɗayan hannunta kuma ta bayyanar da kyakkyawar diamond ring da ta ɓoye a ciki ta yi, ware kyawawan yatsun hannunsa ta yi a in da ta zura mashi ring ɗin a yatsarsa dake kusa da babba na tsakiyar nan, sai wani irin balai'n kyalli zoben yake yi. Tamkar dan hannunsa aka yi ta!.
Shi kuwa har cikin tsakiyar ransa ya ji ya amsa a lokacin da ta riko hannunsa, gabaɗaya sai ya ji tamkar ba'a duniya yake ba, amma ya daure yana jinta ta sanya mashi zoben, bai ta shi jin tamkar yana duniyar mercury ba sai da ta kai ɗan bakinta ta sumbaci ring ɗin, ai bai san lokacin da ya waro idanunsa waje ba, kai tsaye sai saman face ɗinta ya sauke kallonsa, nan fa ya kara kiɗimewa sosai, dan wani irin sihirtatcen kyau da ta kara yi, kumatunta ɓulɓul. A take yanayinsa ya fara canzawa, dannewa ya yi tare da ƙoƙarin kawar da dik wani tinani. Muryarsa na ɗan sarkewa ya furta. "Ring ɗin nan ya yi tsananin kyan da shi kansa kyau ya jinjina mashi, zan iya sumbatarsa?". Ya yi tambayar idanunsa a kanta babu ko kyaftawa. Yatsa ta kai saman ramin da ya lotsa a kumatunsa, wato kyakkyawan dimples ɗinsa. "Zaka iya sumbata, ai naka ne, my hero dimples ɗinka sun fi nawa kyau sosai".
Tamkar wadda ta jonawa lantarki haka ya ji da ta taɓasa, wani irin azabbabben shock ya ji, da kyar ya iya dannewa, ya kai hannunsa saitin ɗan bakinsa ya sumbata, sai ya ji tamkar lips ɗinta ya sumbata, dama saboda ta sumbaci ring ɗin ne ya ce zai sumbata shi ma, dan ya ɗaura lips ɗinsa a in da ta ɗaura tata!. Ƙasa jure jin hannunta a kumatunsa ya yi, tana jefasa cikin wani yanayi, hakan yasa ya kai hannunsa ya riko hannun nata, a hankali ya zameta daga face ɗinsa, sai dai kuma ya kasa iya sakinta, dan wani irin tsantsar kaunarta dake fusgarsa, ga skin ɗinta very soft shiyasa ya kasa iya sake mata hannu.
Ganin abin yana neman zame mashi wata matsala ne yasa ya ce. "My Hoonaira kada fa a nemeki a cikin gida"....... Ɗan zaro mashi eyesball ɗinta ta yi kafin ta ce. "Uhm nemakam ai nasan sai anyi, ban ma san ina zan ce na je ba".
"To mu je in mayar da ke kada a samu matsala". Yadda ya yi magana da mutum yana waje ko yaki ko ya so sai ya so bawan Allahn nan ya cigaba da yin magana kada ya dakata, cikin wani irin sigar soyayya mai sanyi da tafiya da imani ya yi ta.
"Amma ai ban gaji da kallonka ba". Tamkar zata yi kuka ta faɗa........ "Nifa naki ne, mu je ki koma ciki sai gobe mu sake kallan juna". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa rike da hannunta. "To amma zamu yi video call idan na koma bedroom ɗina?". Kai ya jinjina mata, sannan ta miƙe tsaye, jan hannunta ya yi suka nufi kofar fita, da kyar yake iya ɗaga ƙafafunsa, dan dik ta saukar mashi da wani irin kasala na musamman. A bakin door ɗin ya saki hannunta ya buɗe kofar, sai da ya leƙo waje ya tabbatar da babu kowa, sannan ya ce ta zo su tafi. Cikin natsuwa ta fito, janyo kofar ya yi tare da jan hannunta suka nufi hanyar komawa.
Suna tafiya suna hira gwanin birgewa, tana faɗa mashi cewa lallai yau har waye wan gari suna video call, shi ma da giyar soyayya na ɗebansa ya ce mata sallar asuba ne kawai zai sa su yi sallama. Allah sarki soyayya. Sai daɗi take ji har suka isa kusa da door ɗin da zai sadata da cikin gida, sun kuwa yi sa'a basu ci karo da kowa ba. A bayan wasu dogayen flowers dake wajen ya tsaya tare da juyowa suna fuskantar juna, daga in da suke suna iya kallan kofar shiga cikin gida, sannan akwai hasken bulb dake wajen Flowers ɗin da suke haskota, sai dai a in da suke ɗin ba haske sosai bane, hasken kaɗan ne yake riskarsu. Zubawa kyakkyawan face ɗinta idanu ya yi. "I will going to miss you my Hoonaira". Ya faɗa can ƙasa ƙasa.
Jingina da jikin bangon dake ɗan gefe kaɗan ta yi, sannan ta ɗan ɗago kanta kaɗan dan ta samu damar ganin face ɗinsa, kunga ya fita tsawo nesa ba kusa ba, cike da salo mai jan hankalin da yakamata ace ta bari sai bayan auren nasu ya rinƙa yi mashi irin wannan salo ta ce. "My Hero zan fi kewarka sosai fa". Wani irin kafiya ya ji ta soki zuciyarsa, ta kara birkita mashi lissafi.
"Rabuwa da kai tamkar za'a rabani da numfashi nane, ina jin zan bar iska da haskena a nan in shiga cikin gida, na tabbata babu wata light da zata iya haska mun bedroom ɗina, dan na baro light nawa a nan, bana san komawa ciki my Hero, zan ji tamkar a ƙarƙashin ƙasa nike".
Tin da ta fara magana idanunsa a kan ɗan bakinta har ta dire aya, sam kunnuwansa basu saurari kalamanta ba, hankalinsa ya yi nisa sosai. Ai tana dire aya ta rufe baki ya tsinci kansa da matsawa dab da ita, a hankali ya matso da face ɗinsa dab da tata, tana tsaye tana kallansa bata ce mashi ko uppan ba, soyayyarsa ya rufe mata ido, hankalinta ya yi nisa a kallan face ɗinsa..... "My Hoonaira, can I have a one kiss?". Ya faɗa murya can ciki ciki a dishashe kuma, yana jin faɗuwar gaba sosai, tamkar zai rasata ne haka yake ji.
Ita kuwa da yake sonsa ya rufe mata ido sai bata san lokacin da ta ce mashi. "Whyn't". Ba. Haba aikuwa wani irin sanyi ya ji ta ratsa zuciyarsa, slowly ya haɗe face ɗinsa da tata, kirjinsa na harbawa da karfi karfi sosai ya sanya hannunsa ɗaya a saman waist ɗinta, ɗayan hannun nasa kuma ya ɗaura a saman bayan wuyanta, cike da tsantsar kaunarta ya haɗe bakinsu waje guda.
Ko kaɗan bata yi ƙoƙarin taka mashi birki ba, sai ma hannunta ɗaya da ta ɗaura a saman faffaɗar kirjinsa, ta ɗaura ɗayan kuma a saman bayansa. Hot kiss ya shiga bata cikin salon da bai san ta ya aka yi ya iya bama, ita ma mayar mashi da martani ta shiga yi cikin salon soyaya mai kara narka zuciya, ai bai san lokacin da ya janyo waist ɗinta ta tafi gabaɗaya ta faɗa saman kirjin nasa ba, macewa suka yi da kissing na juna babu kakkautawa. Woooooo yau Hoonaira ta bawa heronta abin da ba zai taɓa mantawa ba, gabaɗaya ya fita a hayyacinsa, ya ƙanƙameta sosai sai juya tongue ɗinsa a cikin bakinta yake yi, abin mamaki, ko waye ya koya mashi kiss cikin salo har haka kuma? Shi da yake so silent bai san komai ba!.
Sai da ya sha lips ɗinta son ransa, ya gama yin musayan yawun bakinsu, sannan ya saketa yana wani irin numfashin da kana ji kasan yana a cikin tsananin buƙata, ƙasa iya yi mata magana ya yi, idanunsa a ƙasa ya yi mata nuni da kofar shiga cikin gida, alamar ta tafi da sauri tin kan shaiɗan ya cigalaba mai gabaɗaya a kansu wajen sanya shi ya aikata fiye da abin da ya yi. Ita kanta gabaɗaya jikinta tamkar an zare mata laka, bata da karfi ko kaɗan, da kyar ya iya jan kafafunta ta nufi cikin gida, ko sau ɗaya bata waiwayosa ba, shi kuwa, tana tafiya ya ɗago idanunsa ya tsareta da kallo har ta shiga ciki, lokacin da ta turo kofar nan sai ya ji tamkar kofar zuciyarsa ta datse, gabaɗaya sai ya ji tamkar an jefasa cikin kunci da matsi, da kyar ya juya ya nufi bedroom ɗinsa. Yana zuwa ya faɗa saman bed ɗinsa ya fara juyi dan samawa kansa sassaucin abin da yake ji.
Ita kuwa kai tsaye bedroom na Momma ta nufa, sai dai ko da ta je babu kowa, hakan yasa ta fito ya nufi wajen King, har zata shiga sai kuma ta fasa ta koma bedroom ɗinta. A lokacin Pretty ta jima da yin barci abinta. Saman bed ta haye tare da ɗauko wayarta, lokaci guda ta ɗauke wuta na ƴan mintuna, gabaɗaya abin da ya faru a tsakaninta da shi ne ya dawo mata cikin kwakwalwarta, lumshe idanunta ta yi tana tariyo yadda ta ji tausasan lips ɗinsa wanda ta san babu wata mace da ta taɓa ɗanɗanawa sai ita, dama kuma mallakinta ne, shi da ko face ɗinsa ba a gani yaushe wata zata samu damar ɗanɗanar lips ɗinsa? Ai ba wannan magana, ita ce first and last in ji zuciyarta. Lokaci guda ta saki cool murmushi, bargon sanyin ne ya lulluɓe zuciyarta. Wayarta ta janyo tare da danna mashi kira. A daidai lokacin da kiran ya shigo yana juyi a saman bed ɗinsa, dik yagama birkicewa ya fita a hayyacinsa.
Wayar ta yi kara har ta katse bai ɗaga ba, sake kira ta yi, a karo na biyu ma bai iya yin picking ba, sai a karo na uku ne ya miƙa hannunsa da kyar ya ɗauki wayar, ba tare da duba mai kiran ba kawai ya yi picking, manna wayar a kunnesan ya yi ya ƙasa iya yin magana. Daga can ɓangare ta saka mashi shagwaɓa tana faɗin. "My Hero shi ne kaki picking da wuri?". Wani irin zoki bananarsa ta kara yi mashi ma jin sautin muryarta, da kyar ya iya amsa mata da. "Am sorry my Hoonaira".
Zare eyeballs ɗinta ta yi kafin ta ce. "Ya naji voice ɗinka a haka? Ko dai ka fara barci ne?". Ɗan datse idanunsa ya yi tare da girgiza kai irin wanda yake cikin tsananin azabar nan, ya ɗan datse lips ɗinsa na kasa da hakwaransa, bai iya ce da ita komai ba. Jin shiru yasa ta sake maimaita tambayar tata, a zatanta barci yake yi.
Da kyar ya iya sake lips ɗinsa ya amsa mata da e barci ya fara yi. "To mu bar wayar sai da safe ko?". Ta jefa mashi tambayar, ko kaɗan bai iya sanin amsar da bakinsa ya bata ba, daga haka ya saki wayar ta cigaba da juyinsa dan nemawa kansa sassauci. Ita ma cire wayar ta yi daga kunnenta tare da katse