Showing 48001 words to 51000 words out of 403653 words

Chapter 17 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

44

kyaleta tsaye baki buɗe galala.

Nima kai nasa na wuce izuwa kingdom of power na barta baki a sake galala.

=========================🔥

••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••••

Daga ita har Jawad ɗin kyakkyawar shiga irin na ƴaƴan manya manyan sarakuna aka yi masu.

Tsadaddun alkyabbars king da kansa ya ɓalle masu a ledarsu, dikka alkyabbar iri guda ne, babu wani bannanci.

Sai dai da amarya da angon dik basa a cikin nutsuwa da kwanciyar hankalinsu a lokacin da ake ƙoƙarin shirya su ɗin.

Ita Chuchu hankalinta gabaɗaya ya tashi tana neman ina Auta take? Dama a bisa ƙaida babbar aminiyarta ce zata tsaya a gefen hannun hagunta, while gefen damanta kuma angonta ne a wajen, shi ma ango a gefen hagunsa babban amininsa ne zai tsaya a wajen.

Sai dai daga shi har ita basu san ina aminan nasu suke ba, shi Jawad ya rasa Jaish a rayuwarsa wanda shi kaɗai ne amininsa kowa yasan da haka.

Ita ma Chuchu sai neman Auta take yi shiru bata ganta ba har lokaci ya kusa. Sai gwada numberta suke yi, wayar tana shiga amma ba'a ɗauka.

Hankalinta in ya kai miliyan to a tashe yake, ta shiga damuwa matuƙa, ga shi ba halin ta ce Auntynsu Jawad su dakata da yi mata kwalliya bari ta nemo Auta, ba zasu dakata ba, ga momma bata wajen bare ta nemi alfarmar momma ta dubo mata Autar, ita momma tana can tana fama da nata bakin.

Dik wannan kiran wayar Auta da Chuchu take yi Hoorain yana kwance saman bed ɗinsa yana kallon kiran, tin bayan barinsa wajensu Ansar ya dawo room ɗinsa ya kwanta.

Wayar tana hannunsa ya kasa matsar da ita daga kan face ɗinsa, ya kai ƙololuwa wajen shiga tashin hankali a yanzu, idanunsa sun fara rena fata, dik in ka gansa sai ka ji gabanka ya faɗi saboda yadda yake a hargitse.

Haka Auntynsu Jawad ta tsarawa Chuchu kwalliya, amma sai dai kash dik wannan kwalliyar da ake ta faman tsara mata idanunta ƙoƙarin cikowa da kwallah ma suke yi.

Auntynsu Jawad ta lura da hakan, dan haka sai ta shiga bata hakuri, a tunaninta Chuchu tana san yin irin kukan da amare suke yi nan ne, bata san ita wanna ba shi ne a ranta ba, Auta take nema yasa zata fara yi masu kuka babu gaira babu dalili.

A ɓangaren shi ma Jawad, su uncle Taheer suna yi mashi kwalliya hankalinsa yana a kan tunanin Jaish and Yah Rizwan, yau zai yi aure Jaish baya nan, bashi da babban aboki yanzu, shi ko ƙaramin abokin ma bashi da shi bare babba, Jaish jinin jikinsa ne kawai, komai nasa, ga shi babu shi babu labarinsa.

Hakan yasa ya ji tamkar a fasa wanna taran dinner ɗin, yanzu in sun je ma za'a nemi wanda zai karɓi mic ya yi bayani a kan halin ango babu, dan dik wanda zai san halin Jawad to fa ya biyo bayan Jaish kamar yadda dik wanda zai san halin Chuchu to ya biyo bayan Auta, haka suke!.

Karfe 11 dai'dai wajen taro ya cika makil da ƴan'mata da samari, kowacce tana ji da kanta, abu ne na jinin sarauta da jinin sarauta suka haɗe a wajen, kowa ji da kansa yake yi, babu mai ɗaga idanun ya kalli ɗan uwa, kowa yana jin ya wuce class ɗin ɗaga ido ya kalli mutum a wannan waje.

Da yake su momma ba halartar wajen zasu yi ba sai basu san cewa babu Auta ba, Fanan ita ta mayewa Chuchu gurbin Auta wanda kowa daga cikin family ya gansu sai ya yi magana ya tamabayi ina Auta da Fanan ta maye gurbinta?.

Sai dai Chuchu ta ce masu ta shige cikin ƴan biki bata ganta ba. Sam basu kawo komai a ransu ba, dan babu wanda ya yi tunanin faruwar wani mummunar abin a wannan rana. So ga kuma baki dayawa, sai kowa ya ce kila tana wajen ƴan uwan mommarta da suka zo daga Dubai ne, kila zumuɗin ganinsu yasa ta je ta manne masu!.

A ɓangaren Jawad kuma Abdussalam wato yayan Sharifat ɗa ga Abu Abdussalam na farko shi ne ya maye gurbin Jaish wajen tsayawa a gefen Jawad suka shigo cikin hall ɗin.

Saman kujerar da aka tanadawa amarya da ango Jawad ya zauna, Abdussalam ya tsaya a gefensa, shi ma Abdussalam ɗin ba zai wuci mate na Jawad ɗin a shekaru ba, kyakkyawa ne sosai, da ka gansa zaka san jini ɗaya suke da su Jaish, ga shi very gentle so silent haka.

Amma wayayyene sosai, ga ilim both sides, bai da wani fara'a kamar dai Jawad ɗin, ya fi kama da Abu Abdussalam shiyasa akwai yanayin kama da su Jaish a tattare da shi, dan kun san babu abin da ya rabe Momma da Abu Abdussalam.

Saman kujerar da aka tanada masu Jawad ya zauna kansa a ƙasa, sai yau sabon kewar Jaish ya dawo cikin rayuwarsa, ji yake yi kamar ya yi ta kuka babu kakkaunatwa, ya kasa hakuri har sai da ya ce.

"Where are you my twins brother? I really missed you a lod, I feel like I'm not feeling well cause of u".

Dik da ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar Abdussalam ya ji shi, kuma yasan me yake yi wa wannan sambatu, dan haka sai bai kula shi ba, sai ma ya nemi kawar mashi da zancen ta hanyar cewa.

"Jawad where's my wife? Tin da nazo fa bamu haɗu da ita ba, taki zuwa in da nike, kuma nasan fushi take yi dani sabida wancan zuwanta Dubai na yi mata ba dai'dai ba, naki zuwa mu haɗu da ita har ta dawo, so nasan fushin ne har yanzu bata huce ba".

Magana yake yi a kan Auta wadda tun tana jaririya ya ce da Momma shi fa ga matarsa, tin suna ɗaukar abin wasa har suka fara mayar da wasa izuwa gaskiya, har yau har gobe da my wife yake kiranta, tin bata amsawa har ta fara amsawa, yana santa sosai.

"Tana nan zata shigo a tare da Jannat". Jawad ya bashi amsa da kyar, dan har voice ɗinsa bata fita sosai.

"Gaskiya yakamata na ganta, i really missed her fa, yanzu almost 8 to 9 month rabon da na sakata a idanuna, this time bata je Dubai ba".

Nisawa Jawad ya ɗan yi, cikin yanayi maras daɗi da damuwa ya buɗi baki zai yi magana kawai shararren mc da ake ji da shi a faɗin ƙasar ya yi sanarwa a kan amarya na shigowa.

Gabaɗaya kowa kallonsa ya kai a kan kofar shigowa, kowa dama yasan kalar amaryar, wato ƴar wanka ce, bare kuma yanzu da ya kasance ranarta ce, ai abin sai dai kawai ka daure ka kawar da kallonta daga kanta, amma ba wai dan zaka gaji da kallan kyanta da kwalliyarta ba.

Miƙewa tsaye Jawad ya yi a lokacin da ta sako kyawawan fararen kafafunta dake sanye cikin Queen cover shoes masu high sosai cikin wajen.

Ba komai ya sanya Jawad miƙewa ba face abubuwa guda biyu, na farko kyan da Allah ya zuba mata ya gaurayu da tsararren kwalliyar da ya tashi kan dik wanda zai ɗaura idanunsa a kanta, na biyu kuma ganin Fanan a side ɗinta ba Auta ba, ya girgiza matuƙa na ganin Fanan a gefenta, to ina Auta?. Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsarta.

A take ya ji gabansa ya yanke ya faɗi, har wani sara mashi ya ji kansa ta yi!.

Dik da cikin alkyabba take kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, hakan ba zai hana kaga tsantsar damuwa da take a ciki ba, idanunta har sun yi ja baiwar Allah.

Tin da ta shigo wajen har ta karisa kusa da ango hannunta na'a kan screen ɗin wayarta tana ta faman gwada number Auta, taki hakura sam.

Tana ƙarisowa kusa da angon nata ya sa hannun biyu ya riko nata hannayenta da suka sha kunshi dan ya taimaka mata wajen hawa saman stage ɗin dake wajen.

Jama'ar wajen ne gabaɗaya suka ɗauki tapi rap, rap, rap, kowa ya miƙe tsaye yana jiran amarya da ango su zauna sannan shi ma ya zauna.

Abin ya ƙayatar da mutane yadda Jawad ya taimaka mata wajen haurowa sama. Tsakuwa ta yi a kusa da shi kanta a ƙasa.

Kasa dannewa ya yi har sai da ya ce. "Jannat ina Auta?".

Kamar jira take yi wani ya yi mata magana ta fashe da kuka, haba ai sai ruwan hawaye wani na bin wani.

Kowa ya ɗauka kawai kukan amarci ne.

Rikicewa Jawad ya yi, a tsorace ya ce. "Jannat Auta na tamnayeki ba fa kuka nace ki yi ba, ina take?!".

Wayarta ta miƙa mashi tana ƙoƙarin juyawa da nufin ta bar wajen, a cewarta zata je ta nemo Auta, dan haka kawai take jin kamar akwai wani tazara mai tsawo a tsakaninta da Autar.

Riƙo hannunta da kyau ya yi tare da zama a saman kujerar ya zaunar da ita, sannan ya saketa ya mayar da hankalinsa a kan wayarta, number Autar shi ma ya shiga kira babu kakkautawa.

Mc sai cika mutane da surutu yake yi yana yabon amarya da angon da bai san yanzu haka wutar tashin hankali ce yake ruruwa a cikin zuƙatansu ba!.

•••••••••••••••••••••••••••••••••GUYSON💘

Kwance yake saman gadan Mommarsa, daga shi sai short, babu ko singlet a jikinsa, ya kudundune a cikin bargo kamar mai jin sanyi, a hankali hankali yake ɗan jujjuyawa a saman bed ɗin kamar wanda bashi da lafiya.

Tun da yamma gabansa yake faɗuwa, fargaba kamar zai kashe shi, ya kasa halartar wajen dinner ɗin, zuciyarsa haka kawai take tsinkewa, ya shiga damuwar da bai san dalilinta ba. Bawan Allah jini ai ba wasa ba, shaƙuwa kuma ba karya ba.

Haƙiƙa ko mu mun shaida gimbiya Zunaira wata ɓangarece ta rayuwarka Guyson, mun shaida hakan, Allah sarki, rashinta yasa mashi ciwo ba tare da ya sani ba.

Ya shiga mawuyacin halin da bai san dalili ba, ya faɗa damuwa ba gaira babu dalili, jikinsa dik tamkar wanda aka tsinkewa jijiyoyin jininsa.

Gajiya ya yi da juyin da yake ta faman yi babu wani sauki da ya samu dangane da abin da yake ji a ransa, hakan yasa ya miƙe zaune.

Kafafunsa ya zuro kasa, kamar wani ɗan yaro, sai turo baki yake yi, a haka ya miƙe. Sai dai yana da kunya dai'dai gwargwado, dan haka sai da ya ɗauki arabs jallabiya ya sanya a jikinsa, gashin kansa dik a watse kamar wanda ya taso daga ciwo.

Waje ya nufa yana jan kafafunsa kamar baya san motsa jikinsa. Part ɗin King ya nufa dan yana da tabbacin zai samu Mommarsa a can.

Babu wanda suka haɗu da shi a hanya har ya ƙarisa cikin part ɗin. King baya cikin room ɗin, yana cikin toilet yana wanka. Momma tana kwance a saman bed ɗin King kamar wadda bata da lafiya, ta yi shiru tana fuskantar sama, ita kanta tin ɗazun gabanta yake ta faman faɗuwa, zuciyarta yana ta tsinkewa, ta rasa menene sila.

Sai addu'a take yi a kan Allah Ubangijin ya sanya dik wani abin da zai tinkarota na masifa da yake sanyata faɗuwar gaba ya rikiɗa ya zamana alkhari.

Dik wani bawa da yake jin kamar wata musifa tana tinkaro shi, yana yawan jin faɗuwar gaba to ga addu'ar da zai yi wanda zai sa Ubangijinmu ya juya wannan abin zuwa alkhari, in ma kaddararsa ce ta zo a haka to Allah zai saukaka mashi abin ya zo mashi da sauki, zan rubutu maku addu'ar da hausa dan ina samun korafi a kan rubuta shi da larabci da nike yi, wasu basu iya karatun larabci ba, so addu'a addu'a ce koma da wace yare ka yi ta Allah zai jika, gata kamar haka haɗe da fasararta dik na haɗa na rubuta maku da Hausa dan ku fi fahimta da kyau, Allah yasa mu dace.

"Hasbiyallahu laa ilaaha illa Huwa, alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-‘Arshil-‘Azeem."
Fassara. Allah Ya ishe ni, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, a gare Shi na dogara, kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma, shi kaɗai zai iya kareni daga dik wata sharri.

Sai cikin Alqur'ani mai girma, Suratul Baqarah Surah ta 2 bayan Fatiha kenan, aya ta 286. Wannan ita ce aya ta ƙarshe a cikin Suratul Baqarah, kuma tana ɗaya daga cikin mafi girman addu'o'in Al-Qur'ani don neman gafara, rahama, da taimako daga Allah, wannan addu'a idan kika yi ta bata da shamaki da isa ga Ubangiji, kika yi ta da tawali'u ki kaddara addu'aki ta karɓu kawai, dan bata da shamaki kai tsaye take wuce zuwa ga rabbil izzati, ita ce addu'a kamar haka.

"Rabbanaa laa tu’aakhidhnaa in nasinaa aw akhṭa’naa. Rabbanaa wa laa taḥmil ‘alainaa iṣran kamaa ḥamaltahu ‘ala-l-ladheena min qablinaa. Rabbanaa wa laa tuḥammilnaa maa laa ṭaaqata lanaa bihi wa’fu ‘annaa waghfir lanaa warḥamnaa anta Mawlaanaa fanṣurnaa ‘ala-l-qawmi-l-kaafireen."
Fassara. Ya Ubangijinmu! Kada Ka kama mu idan mun manta ko mun yi kuskure. Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora mana nauyi kamar yadda Ka dora wa waɗanda suka gabace mu. Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora mana abin da ba za mu iya ɗauka ba. Ka yafe mana, Ka gafarta mana, Ka jiƙanmu. Kai ne Majiɓincinmu, Ka taimake mu kan mutanen da suka kafirta suke binmu da sharri.

Addu'a ta uku a kan Allah ya kareki daga dik wata masifa da kike jin kamar tana tinkaro ki shi ne.
"A‘oozu bikalimaatillahi-ttammaati min sharri ma khalaq."
Fassara. Ina neman tsari da kalmomin Allah masu cike da kamala daga sharrin duk abin da Ya halitta.

Manzon Allah (SAW) ya koyar da wannan addu'ar don neman kariya daga kowanne irin sharri, so addu'a ce mai karfin gaske, idan kika riketa wlh wane mutum sai dai ubangijin mutum!!!.

Addu'a ta huɗu kuma mafi tsada, wannan addu'a idan kika yi ta da safe kafa uku, Manzon Allah ya yi rantsuwa a kan babu wata sharri da zata sameki, safe da yamma ake yi, in kika yi ta uku da safe wlh a wannan wunin ranarkam babu wani sharri da ya isa ya kusantoki, dik balai'n mutum nan zai ganki kuma yarbi, Allah zai saukar da Mala'iku daga sama domin baki kariya wunin wannan rana har zuwa yamma, in kika sake yin kafa uku da yamma to fa har zuwa washegari da asuba kina cikin kariyar Ubangiji. Sai dai ki sani addu'a babu cikakkiyar Tauhidi fa Allah baya karɓarta, sirrin addu'a ita ce idan zaki roƙa ki sanya a ranki cewa Allah ya gama biya maki buƙatar ma kawai, ki sa a ranki dama babu wanda zai biya maki sai shi!!.

Ga addu'ar kamar haka.

"Bismillahil-ladhi la yadurru ma’asmihi shai’un fil-ardi wa la fis-sama’i wa Huwa-s-Sami‘ul-‘Alim."
Fassara. Da sunan Allah wanda ba zai yiwu wani abu ya cutar da mai ambatonsa ba a sama ko a ƙasa, kuma Shi ne Mai ji, mai sani a kan komai.

A karanta sau uku safe da yamma, domin samun tsari daga sharrin duniya gabaɗaya!. Allah ya cigaba da karemu daga dik wata sharri!.

Waɗan nan addu'oi Momma take ta karantawa dan ta samu saukin abin da take ji, hakan ne ma yasa mutuwar Zunaira bai yi mata wani tsananin tasiri ba, Allah ya dafa mata zuciyarta ya ɗan sanyaya dalilin wannan adduoi.

Guyson na shigowa ya haye saman gadon, kusa da ita ya matso, tana kwance idanunta a sama, jin motsinsa yasa ta ɗan yi kasa da kallonta izuwa kansa.

"Lafiya Omar?". Ta yi maganar da kyar.

"Momma jikina ne dik yake mani some how na kasa ganewa, and kaina yana ɗan sara mun, kamar bani da lafiya".
Tin da ya fara magana idanunsa suka cicciko da kwallah, dama kun san halinsa mai kukan ciwo ne, da zarar ya fara ciwo zai fara kuka. Allah sarki babu juriya!.

Yana kai karshen maganar kuma ya kwantar da kansa a saman laps ɗinta yana shirin fara yin kuka mai gabaɗaya.

Miƙewa ta yi zaune a tsakiyar bed ɗin, hakan ya bashi damar kara gyara kwanciyarsa a saman laps ɗin nata.

Daidai lokacin King ya fito sanye da jallabiya ruwan hoda a jikinsa, sai tashin kamshi yake yi.

Ganin Guyson nasa a saman bed ɗin ga kuma hawaye a face ɗinsa yasa ya kariso da sauri yana tambayar ba'asin meyake faruwa?.

Yana ganin King ya kara rushewa da kuka mai ɗan sauti, kukan shagwaɓa har da shessheƙa.

Hankalin King ne ya kara tashi, dama shi bai wani san halinsa sosai ba, dan in baku manta ba girman Dubai ne shi, Momma ce tasan kayanta tsab, dan haka bata wani rikice sosai ba, dan tasan a kan ɗan buge hannu a jikin bangoma guyson kuka yake yi bare azo ga ciwon kai ko ciki, ai sai ya wuni yana kuka!. Sakalene.........😅

A hanzarce King ya haye saman bed ɗin yana kara tambayarsa me yake faruwa?. Ya yi maganar tare da kai hannu yana ɗan ɗagosa daga jikin momma.

Ai tin bai gama kai hannu jikinsa ba ya miƙe ya faɗo jikin daddyn nasa yana kara tsara kukan shagwaɓar tasa da kyau, har da hawayen iyashege!.

Kallon momma da bata wani damu sosai ba King ya yi. "Rahilarh lafiya? Me kika yi mashi?". A rikice ya yi tambayar.

"Wai jikinsa ne yake yi mashi ciwo shi ne yake kuka".............. Ta bada amsa tana kai hannu zata taɓa gaban goshinsa.

Zaro idanu King ya yi, ya kara shiga damuwa. Muryarsa har tana ɗan sarkewa saboda saurin wajen furta magana ya ce. "Miko mun wayata bari in kira Dr ya zo".

Ganin yadda ya rikice ya tashi hankalinsa haka abin ya ɗan bawa momma mamaki, dan ita tasan halin kayanta, a ganinta yanzu haka idan aka bincika ba wani ƙwaƙƙwaran ciwon da yake damunsa.

"A'a dare ya yi, ka bari sai zuwa da safe se mu kai shi hos........"
Wani irin cin burki ta yi a maganar tata bata karisar ba, ba komai ya ja hakan ba kuma face zaro mata idanu da King ɗin ya yi.

Cike da mamaki ya ce. "Rahilarh kin san

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login